ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Husannsa & Jahad
A 6angaren husanna dake kwance rai hannun Allah magashiyan, ba’a son inda kanta ya ke ba,
Likito ci sun gaza gane, menene matslarta, iya abunda suka sani tana da mental ilness sai asthma, bayan nan binciken su bai nuna masu komai ba,
Rashin kwanciyar hankali ne ya hana, jahad ta yi masu bayanin cewa tana da Iska, sam ta manta da wannan sbd ba natsuwa kullum cikin kuka take asibitin,
Atare suka shigo inda aka kwantar da ita, suna tattauna wa akan ciwonta, su biyu ne professional doctor ne wanda su ke kira da Babban likita (big doctor) tare da wani jami’in ɗan sanda, dr ɗin na koƙarin yi masa bayani akan yarinyar,
Sam basu lura da husanna wadda ke kwance, magashiyan sai faman fisge fisge take tana nishi, hannu tasa ta cire roban oxygen ɗin da suka sa mata, tari wurgi da shi, tana wani irin huci kamar zakanya, idanunta sun juye sun canza launi,
A haukace ta ƴunkura da ƙwarin gaske takai hannu ta zare bingidar dake soke ƙugun police man ɗin da suke magana da big doctor ba tare da saninsa ba,
sai da ta zare sannan likitan ya lura cikin tashin hankali yace “Innalallahi wa’inna ilahirrraji’un !!”
A firgice ɗan sandan ya shafa waist ɗinsa yaji ba gun ɗinsa, gaba ɗaya hankalinsu ya tashi ganin tayi sai ta su da ita, kuma ta rike maɗalllin, nan fa ido ya raina fata, lallashin ta suka shiga yi don ta ajiye bindigar amma ina, sai ma ta fisgi hanya da gudun gaske tana harba bindigar a duk inda ta samu ji ka ke daram!! Daram !! , zo ka ga yanda mutane ke gudu ba likitocin ba, ba nurses ɗin ba hatta marasa lafiyan dake kwance magashiyan neman hanyar gudu wa su ke yi, a tunanin su, ƴan bindiga daɗi ne suka kawo masu ziyara ta musamman ????????????
Jama’a gawa na tsoran rami, ????????
Husanna fa ta haukace, misbehaving take yi kamar ƴar mahaukaciya,
Gashi dama ba hijabi ajikinta sun cire mata, da za’a kwantar da ita,
Wannan mahaukacin gashin, nata mai yawan gaske da tsayi ya bazo mata ta ko’ina har gaban fuskanta, tana gudu yana kara rufe mata ido ko gabanta ma bata kallo,
“Jama’a kowa ya watse, kowa ya gudu yayi takansa an samu matsala, mahaukaci ta gudo daga psychiatric hannunta riƙe da bindiga kowa yayi takansa,” ????
Wani copral ne ke bada wannan annoucement ɗin, don asamu kowa ya kare kansa,
Bin ta police men ɗin suke da gudu suna rokon tabasu bindigar nan, amma ina Husanna tayi nisan da bata jin kira,
Jahad ta gama rikicewa ganin bala’in da husanna ke ƙoƙarin ja, musu a guje itama take binta tana faɗin “Husanna dan Allah ki daina, kada ki kashe wani kija mana bala’i, dan Allah ki basu bindigarsu, innalallahi wa’inna ilaihirraji’un
Asibiti fa ya harmutse, kowa gudu yake yi , gashi ita husannar sai yawo take musu da hankali sai zagaye cikin asibitin suke, duk inda tabi mutane sai su watse, sai ihu ake ana zabga salati kai ka ce zombies ne suka bayyana,
Ƴan sandar sun fusata sosai ransu yayi mugun 6aci, kiris ya rage su harbe ta gudun kada tasa ayi asarar rayu ka, sbd ko’ina tasamu harbi take yi,
Abunda basu sani ba wannan ihun da ake yi shi ke ƙara haukatar da ita, bata cika son ƙara ba,
Sannan ita kanta husannar a tsorace take sbd police ɗin dake bin ta,
Tana cikin gudun nan hankalin ta atashe , gudu take amma tana waiwayon su cike da tsoronsu, cikin rashin sani kwatsam taji ta faɗa ajikin mutun,
Gam ta faɗa a faffaɗan ƙirjinsa, ta ƙankamesa, ta rungumosa sosai, a tsananin tsorace,
Nan take komai ya dakata, ji ka ke tsit kamar mutuwa ta gifta, babu mai kwakkwaran motsi acikinsu,
Gaba ɗaya duk suna tsaitsaye likitocin da nurses ɗin da wasu daga cikin marasa lpy masu ƙwarin jiki da ƴan dubiya, ga ƴan sanda , kowa dai
Saukar ajiyar zuciya kowa yake saki, ita kam jahad ta tsorata, da ganin mutumin da Husanna ta faɗama wa, duk da yasa face mask a fuskanshi, amma ƙirar karfin nan tasa, dole tasa hankali tashi,
Tsoranta karya ce zai hukunta Husanna da ta faɗa masa bagatatan,
A tare zuciyoyinsu ke bugawa, bugu bana wasa ba, ta kwanta luf ajikinsa, wato wata irin ni’ima ce atattare dashi wadda tasanya husanna dawo wa cikin hayyacinta lokaci guda, sam tagaza tashi daga jikinsa, ƙamshin turarensa ya gama kashe mata dukkan wani ƙwari na jikinta, ????
Sai faman ajiyar zuciya take saki, hannunta ta ƙarasawa ta zagaye waist ɗinsa so tightly,
Ganin hakan yasa Soja dake bayansa mai riƙe da mukamin major, yasa hannu ya zare gun ɗin dake hannunta , saboda ta zagayo da hannun nata a ƙugunsa ga bindigar a fili,
NOT EDITED
Keep sharing everywhere???? ❤️ Alhamdulillah ynx sai monday
BossLady ????????????????ABBAN SOJOJI????????????
????????????Romantic Love story????????????
Writer HAFSAT BATURE ????
~Boss Lady~????????????
frm today, na dakata da rubutu har sai naji sauƙi insha Allah zan ci gaba, seriously bani lpy so i won’t kill my self ????????
~page 71 to 72~ ✨
✨✨✨✨✨✨✨✨
Not edited, ????
At same time heart ɗinsu ke beating da karfi, ya jima yana mamakin wata zararriya ce wannan ta faɗo masa a ƙirjinsa haka, this is d first time da mace ta faɗa masa a jikinsa, wadda ba muharramarsa ba, babban abunda ya ɗaure masa kai yadda yarinyar ta ƙanƙamesa bama Alamar zata sake shi, yana jin duk wani moving ɗinta ajikinsa, hatta numfashi ta dake fita cikin sauri sauri, kamar jinjira haka ta kwanta masa luf tana sauke ajiyar zuciya,
Mutanen dake wurin kowa yayi zuru yana kallon ikon Allah, wasu kam sai godiya suke wa Allah daya kawo masu sauƙi, har aka amshe gun ɗin dake hands ɗinta,
Jahad kam wadda ke cikin matsanancin tashin hankali, ganin bala’en da hosana ke ƙoƙarin ja musu, cikin yanayi na firgici ta ƙarasa inda hosana ke jikin bawan Allahn nan ta ruƙo hannunta da ƙarfi ta fisge ta daga jikinsa tana cewa “Dan Allah kayi Haƙuri bawan Allah, ba da sanin ta tayi hakan ba, she did it unintentionally, tana da ta6in hankali ne…..’ muryar na rawa Jahad ke kora masa bayani,
Har time ɗim bai cire face mask ɗinsa ba, kuma bai janye idonsa daga na Yarinyar ba,
“Ki rabu dani !!!!” honasa ta faɗi tare da cire hannunta daga na Jahad ta matsa wurin mutumin nan, da ta faɗa mawa ta sa hannunta cikin nasa ta riƙe kam tana kallonsa cikin muryar kuka tace “dan Allah ka rabamu da waɗannan masu baƙaƙen kayan wlh sun takurawa rayuwarmu, duk inda mu ke bin mu suke yi, wlh ba mu bane muka kashe ta ba, mun faɗa musu sunki yarda, ni dai kace su rabu ni in ba haka wlh zuciya ta bugawa zatayi na mutu kowa ya huta…..’
“Hosana !!! Ba ki da hankali ne !! Kinsan wanene shi ki !! meyasa ki ke tona mana asiri ne agaban mutane,” jahad ce tayi maganar ranta a 6ace ta janyo hosanar da karfin gaske ta dawo gefenta,
Su dae mutanen dake tsaye tare da police ɗin sun zuba ido suna sauraron su,
Rai a 6ace hosana ta sake fisge hannunta daga na Jahad cikin ƙunar rai tace “ki rabu dani, ki ƙyale ni nace !!! meyasa kowa bai son mune !! Laifin me muka aikata, babu mai ƙaunar mu wlh Jahad ba zan koma cell ba sai dae a shigar da gawa ta, amma bani ba,’ tana gama fadar hakan ta koma wurin mutumin nan dae dake a tsaye, ta zura hannunta cikin lallausan tafin hannunsa ta rike gam, ta marairaice masa da kyawawan idanuwanta tace “Dan Allah ka tafi dani,ka da kabarni anan, bana son ganin waɗannan masu fararen kayan (wato likitocin dake tsaye da nurses ɗin dake wurin) kuma bana son waɗannan masu bakaken kayan,” ta faɗi tana nuna ƴan sandan dake tsaye baki asake suna kallonta,
kwantar da kanta tayi a damtsen hannunsa, sannan tasanya dukkan hannayenta ta rungumo nashi, (mutu ka raba kenan)
Lumshe idonsa yayi a hankali, sai lokacin kallon police men ɗin dake tsaye a wurin yace “wane irin shashanci ne yasa ku kabar yarinya harta kwaci bindiga daga wurinki!!”? Ya tambaya yana kallonsa,
Rai a6ace wani inspector yace “kaga malam ka iya bakinka, mu jami’an ƴan sanda ne munsan me muke…” tunkan ya ƙarasa major ɗin dake bayansa wanda ya fusata rai a6ace yace “Ka iya bakin ka !! Kasan wanene shi!!!”?
“maganar wanene shi bata shafe mu ba, mu dae a bakin aikin mu mu ke,” wani inspector ne ya bashi amsa a yayn da ya fiddo da ankwa alamar zai sanya masu hosana,
Itakam ƙara kanƙameshi take yi, gaba ɗaya ta gama kashe mishi jikinsa, daurewa kawai yakeyi,
“Laifin me suka aikata”? Ya tambaya yana kallon ƴan sandar,
Wannan copral ɗin ne yayi saurin cewa “ana suspecting ɗinsu da kisan wata tsohuwa wadda take riƙonsu,”
Shiru ya ɗanyi tare da jinjina kai, kafin yace “Cancel the case (akashe case ɗin)”
ɗagowa su kayi jami’an ƴan sandan suna kallonsa cikin mamakin jin abunda yace, a fusace wannan inspector ɗin yace “malam wai wanene kai !! dame kake taƙama ne !! kaga ka kama gabanka kawai cikin salama, in ba haka ba, zamu haɗa dakai mu tafi police station…..’
Jikin major ɗin dake bayansa har tsuma ya ke yi wurin cewa,” Shut Up Stupid !!! ka iya bakin ka ƙaramin ƙwaro ko kuma nayi ƙasa ƙasa daku a wurin nan….’ cikin hanzari ya dakatar dashi tare da cewa “i did not allow u to talk again, last warn,’
Shuru major ɗin yayi sai faman huci yake yi tamkar zaki, rai a6ace ya wurgawa ƴan sandar bindigarsu ƙasa,
Matsawa Inspector ɗin yayi da nufin yasanya wa hosana ankwar dake hannunsa, amma sai mutumin ya dakatar dashi da cewa “karka kuskura !!! domin ban bada izini atafi da yarinyar nan cell ba, kamar yadda ta roƙe ni cewa bataso ta koma, daga nan ba inda zata je,”
Mamaki ne ya rufe ƴan sandan, inspector ɗin yace “idan ka cika shisshigi zamu sa bindiga mu kashe ka !! A wurin nna,”
Jinjina kai mutumin yayi tare da cewa “idan kuka kashe ni, ba hukumarku kaɗai bace zata shiga haɗari ba, gaba ɗaya sai an tada nigeria saboda raina kawai,”
Kansu fa ya gama ɗaukar zafi kowa mamakin wannan mutumin ya keyi, ganin ya toge yaki bari su ta6a yarinyar dake kwance ajikinsa yasa inspector ɗin cewa “wai dan Allah wanene kai!!”?
“Yanzu naji bayani” acewar mutumin bayan ya faɗi hakan ya zura hannunsa cikin aljihunsa ya zaro ƴar waya nokia, ya yi dialing wasu numbers da basu fi 5 digits ba ya miƙa wa, inspector ɗin wayar yace “Ka kira numbers ɗin dana sanya ka tambaye suWANENE MARSHAL OMAR za ka samu amsar da kake so,”
Jikin kowa yayi sanyi jin ance marshal, shi kansa inspector ɗin yana ɗan sauko, hannu yasanya ya kar6i wayar, ya danna call tare da karawa a kunnansa, one bugu on ɗauka, cike da kwarin guiwa ɗan sandar yace “WANENE MARSHAL OMAR, cikin harshen turanci yayi tambayar yana jiran amsa daga cikin wayar,
tunkan ya cire wayar a kunnansa, wasu irin jibga jibgan motoci ne suka soma antayo wa cikin asibitin aguje masu ɗauke da fusatattun sojoji zafafan gaske, runduna guda kamar a filin yaƙi, zaro ido su kayi gaba ɗayansu cikin tsananin mamaki, kowa dake kallon wannan al’amar tsantsar mamaki ne a fuskarsa,
Da gudun gaske sojojin nan suka shiga dirowa daga saman motocinsu kowanne riƙe da manyan bindigogii, da gudun gaske suka tunkaro inda Marshal omar yake sukayi masa ƙawanya, tare da buga ƙafa suka sara mashi sannan suka haɗa baki wurin cewa “We’re waiting for your command Sir !” (Umarninka mu ke jira yalla6ai) ????
Gaba ɗaya hankalin kowa yayi mugun tashi, sun tsorata ainin ganin sojojin ma ba na nan qasar bane, Black americans ne masu wata irin ƙira ta zakuna, kai kana ganinsu ba ɗigon Imani a fuskarsu, umarninsa kawai suke jira, koda hospital ɗinne su tada gaba ɗayansa ????
Cikin rawar murya ɗan sandar nan wanda yaci ka zaƙe wa yace “Yalla6ai, dan Allah wanene kai”?
“dan Allah ka miƙa masa wayarsa, salin alin mu tafi,” acewar wannan copral ɗin daya gama tsorata,
Hosana ta firgita sosai, amma maimakon ta cire hannunta daga nasa, sai ma ta ƙara ƙanƙamesa sosai, duk yana jin motsin hannun yarinyar acikin nasa, ita kuwa jahad ƙiris yarage tasaki fitsari don tsabagen tsoro, gashi tayi tayi da hosana ta janye hannunta daga nashi amma taƙiyi,
Hankali fa ya tashi, kowa da ke wurin so yake yaga fuskar marshal Omar, sun jinjinawa ƙarfin ikonsa, .
“Yalla6ai! dan Allah ka karbi wayarka, wlh zamuyi biyayya akan abunda kace,” acewar wannan copral ɗin,’
sai lokacin Marshal Omar yasanya hannu cikin natsuwa, a hankali tare da zame face mask ɗinsa, Wow zo ka ga ido
Cikin wannan Cool voice ɗin tasa yace “Sunana Marshal Omar, U.s Army ni ɗane ga Chief of Army staff wato Abban sojoji,’
tunkan ya idasa maganar tasa gaba ɗaya police ɗin dake wurin suka sara masa, hatta sauran mutanen dake tsaitsaye a wurin duk suka sara mashi jin sunan daya ambata,
“Nayi muku uziri ne, saboda na lura bakusan koni wanene ba, duk da nayi mamakin hakan,”
Sauke hannayensu su kayi, Tabbas sai yanzu suka shaida shi, abunda yasa suka rikice sun san cewa Marshal Omar ɗin da su ka sani suke yawan gani tare da SGR ba anan suke zaune ba, kuma basu ta6a tunanin zasu ganshi ido da ido ba, sun saba ganinsa a kafafen sada zumunta, shiyasa su kayi tsammanin ko raina musu hankali zaiyi, gashi kuma yayi hiden face ɗinsa da mask sannan, babu uniform ajikinsa shiyasa komai ya shige musu,
“Ynz yalla6ai ya zamuyi kenan? Domim Case ɗin yaran ya kai har wurin commissioner of police, cikin week ɗin nan ma muke shirin miƙa su court don gudanar da shari’a, rashin lpyr yarinyar ne ma ya dakatar da komai,” inspector ɗinne ya kora masa bayani,
“Ku bar komai a hannu na, zan yi magana da commissioner ɗin, zaku iya tafiya,” ya basu umarni
Yayi magana tare da amsar wayarsa daga hannunsa, ba musu ƴan sandar suka kama hanya tare da barin asibitin suna masu tsananin mamakin ƙarfin ikon Marshal Omar lallai shi ba ƙaramin jan wuya bane ????????????
(Yanzu shikenan an kashe case ɗin su Hosana da jahad kurmus ya mutu) ????????
Mutanen wurin gaba ɗaya murmushi kawai suke saki, kamar a shirin film haka suke kallon lamarin, haƙiƙa marshal Omar ya gama tafiya dasu,
Ajiyar zuciya kawai Jahad ke saki tarasa me zatayi don farin ciki, sam bakinta taƙi rufuwa (shin bana faɗa muku ba? Cewa dukkan tsanani yana tare da sauƙi? Sannan bawani yanayi na arayuwa da yake kasance wa na dundundun ba? this is an example) ????????
Murmushi kawai hosana ke saki, sam taƙi barin jikinsa har sai da yace “My hand” sannan ta janye jikinta, daga nasa tana zazzare masa waɗannan kyawawan idanuwan nata, sai faman murmushi take zabga mashi, shi kam binta kawai yake yi da kallo,
“Kowa ya koma bakin aikinsa!!” Marshal Omar ya faɗi yana kallon jama’ar dake wurin, cikin sauri doctors ɗin dake wurin da nurses ɗin da other peoples ɗin suka watse,
Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da eyes ɗinsa akan major ɗin dake bayansa yace “A tafi da twins ɗin nan, akai munsu gidan goggona, asanar da ita cewa zandawo later,”
Ya ƙare maganar da cewa “asan irin driving ɗin da za’ayi dasu,” murmushi kawai major ɗin ke saki, aransa yace “Oga fa yayi kamu da alama, Allah yasa ayi da ran mu” ????
A fili kuma yace “Consider it done Sir!!”
Haka suka tasa ƙeyarsu hosana, waɗannan hot soldiers ɗin suka sasu agaba, har aka fice dasu marshal Omar bai dauke idonsa daga kan yarinyar ba, sai da yaji tashin motocinsu sannan,
Haka motocin nan suka fice dasu, daga asibitin, ????
Police ɗin nan yajima yana mamaki, daga cewa wanene marshal omar sai kawai yaga rundunar sojoji, sojojin ma bana nan ba tab, lallai ba ƙaramin Jan wuya bane, ????
Murmushi kawai babban likita ke saki wanda ya rage a wurin tsaye, sai lokacin marshal omar ya lura dashi, cikin sauri ya ƙarasa tare da hugging ɗinsa yana cewa “Am sorry ban lura dakai ba wlh,”
Babban likita yajanye jikinsa tare da cewa “Shege Omar ! Mutanen U.S wlh yau ka bani mamaki, kayi matuƙar burgeni sai naga abun kamar ashirin film, shin wai ma ni dirar yaushe ? dama ka shigo garin kenan ?
Ɗan ƙayataccen murmushi marshal omar yasaki tare da cewa “3 weeks kenan da zuwan mu, tare da Captain mu ka taho daga kd shi ya wuce zariya wurinsu ammi ni kuma na wuto nan kai tsaye, tomorrow insha Allah zan juya nima,”
Ruƙo hannunsa babban likita yayi suka tunkari office ɗinsa, domin samun damar tattaunawa dakyau, sai faman murmushi yake saki, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi, yama rasa ina zai sa Marshal Omar saboda tsabar farin ciki,
Yana lura da nurses ɗin dake ta faman leƙensa, wato sun ƙyasa koda yake dole ne abunda ya faru ya burge kowa,
A office ɗinsa suka zauna, ga sanyin A.c komai tsaf tsaf, suka zauna suna facing juna,
“Bari nasa akawo maka abunsha,” acewar Babban likita, cikin sauri umar yace “A’a no need”
“Wai ni kam ina SGR? wato shi bazai ajiye makaman yaƙin nan ba , yazo ya kawo mana ziyara ba ko”?
ɗan murmushi omar yayi tare da cewa “rikicinsa da Ammi ne, kasan tace ita ƴa’ƴan fatima, ba jinin ta bane don haka bata buƙatar, waninsu ya sada zumunci da family ɗinta,” .
tsoki doctor yaja rai a6ace yace “wannan guyababban jarababbiyar tsohuwar bansan meke damunta ba, ƙiri~ƙiri ki tsani yara grand child ɗinki kuma? inace faɗanta da Aunty fatima ne ba da su ba, haba !!” ya ƙare mgnr cikin ƙunci
Omar yace “Abun yana damuna nima, especially yadda take nunawa su junaid tsana batasan su ƙiri-ƙiri, yanzu ni ba wannan ba game da Twins ɗin can,’ ya ɗan dakata da maganar,
Murmushi big doctor yayi tare da cewa “me kake son sani game dasu”?.
“Me ke faruwa dasu ne, kuma wacece bata lafiya acikinsu, sannan ina iyayensu ne “? Omar ya tambaya cike da son jin taƙaitaccen bayani,
Gyara zama dr ɗin yayi tare da cewa” ita wadda ta faɗa maka ajikin ka, itace bata da lpy, she has a mental illness har aiki ma an ta6ayi mata, ina ji anan asibitin ne, sannan tana da asthma, bansan dae taƙamaiman labarinsu ba, amma ita ɗayar mai hankalin munyi magana da ita, ta gayamun cewa, basu da kowa a hannun wata tsohuwa suke, so tsohuwarce ta rasu kuma bincike ya nuna cewa poison aka bata, tace mun basu ne suka kashe ta ba, iya abunda nasani kenan,”
Shiru Omar yayi na ɗan wani lokaci kafin yace “zanyi binci ke akansu amma ba ynx ba, suna buƙatar kulawa ssae, ynx ita mara lafiyar, me take bukata,” .
“drugs ne kawai dama ake bata, ynx ma already na rubutamusu waɗanda zata yi amfani dashi, sannan suna buƙatar abinci mai gina jiki sosai tabbas, akwai yunwa atattare dasu,’ babban likita ya kare jawabin yana kallonsa,
Shiru yayi baice komai ba, yana wani tunani,
” ynx ya zakayi da twins ɗin naji kace akaisu wurin goggonku,” babban likita ya tambaye sa, .
Ajiyar zuciya Omar yasaki tare da cewa “as frm now dukkan wani responsibilities ɗinsu ya dawo underneath ɗina ! ban damu da sanin su wanene parent ɗinsu ba ko family ɗinsu, saboda banga kowa atare dasu ba, that means anyi watsi dasu, don haka na mallakawa kaina su !!!!!
Wani irin Murnushi babban likita yake saki yana kallonsa, wannan ƙarfin halin da ƙwarin guiwar Omar ba ƙaramin burgeshi su ke yi ba, .
Sam bakinsa ya gaza rufuwa don murna cikin tsananin farin ciki yace”haƙiƙa Omar kai na dabanne ko acikin mutane, halin ka na musamman ne, ka cancanci fiye da komai ma, Allah yasa ka maka da mafificin alkhairi, ya ci gaba da ɗaukaka ka, sakamakon wannan ceton da kayi Allah yasa ka maka da gidan Aljanna first step,”
Murmushi kawai Omar ke saki, shikam babban likita ya gaza rufe baki addu’o’i kawai yake masa, a ƙarshe yashe “Allah yasa su zama Alkhairi agare ka,”
“Ameen” ya amsa mar,