ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

“Naji kamar ana maganata a wurin nan,” junaid ne yayi maganar wanda ke saukowa daga saman stair ɗin, jikinsa sanye da jeans da farar t shirt,
Bin su yayi da kallo musamman sehrish wadda ke tsaye, ido luhu luhu tasha kuka, yau taga tashin hankali,
Ajiyar zuciya Azmee tasaki ganinsa cikin sauƙi,
“Junaid matsala aka samu,” azmee ta faɗi tana kallonsa,.
“Meya faru”? Ya tamvaya yana kallonsu,”
Nan azmee ta kwashe dukkan abunda ya faru ta sanar mishi, kamar yadda sehrish ta faɗa mata,”
Murmushi yasaki tare da kallon sehrish wadda ta sunnar da kanta kasa, yace “Calm down ur mind, in dai Babban yaya ne, ni ne controller ɗinsa, just wipe ur tears,” ya faɗi yana nuna tears ɗin dake zubowa daga eyes ɗinta,.
Hannu tasa tana goge su kamar yadda junaid ya bata umarnin ta share su,”
Sannan yace da aunty azmee “a shirya masa wani breakfast ɗin, ynz zan zo na karba,” yana gama faɗan hakan ya juya tare da wuce wa izuwa upstairs part ɗin Sgr,”
“Yanzu sai kiyi murmushi, junaid da ki ke gani shine masarrafin babban yayansu, shi ke juya shi kuma ya juyu,” azmee ce tayi maganar tana kallon sehrish,
Ita dae har yanzu bata dawo cikin hayyacinta ba, ta jima tana mamakin abunda sgr yayi, yadda ya hauro da ƙafarsa ya harba tray ɗinta ya kife kasa ba ƙaramin mamakin hakan tayi ba, maimakon taji haushinsa, sai ma taƙara jin ƙaunarsa na ninkuwa azuciyarta ????
Da sallama junaid ya shiga falonsa yana faɗin ” babban yayan mu, gani na iso, nazo na takura maka na hana ka sukuni,”
Jin Voice ɗin junaid yasa, Rafayet tashi zaune daga kishingiɗen dayake, ya mayar da laptop ɗinsa, saman desk ɗinta, a hankali ya ware idonsa akan junaid tare da cewa “sai ynx zaka so wurina? Ina ta fama da yunwa arasa wanda zai tashe ni ko”? yayi maganar yana lumshe sexy blue eyes ɗinsa,.
da murmushi junaid ya karasa yana faɗin “am so sorry babban yayanmu, kaima kasani, na damu da cikin ka sosai, shiyasa ko breakfast banyi ba tun safe, kai kawai nake jira ka farka muci atare” ya karasa maganar tare da russinawa ya rungumosa sannan ya manna masa kiss a gefen face ɗinsa,
Lumshe idonsa yayi, har cikin zuciyarsa, tsananin kaunar yaron ya keyi ba don komai ba, sai don kasancewarsaa mai tsananin biyayya ga iya magana, minti 5 yayi yawa ga junaid ya sace zuciyar mutun especially da wannan murmushin nasa, shiya sanya Hafsat bature ta kamu da tsantsar ƙaunarsa ????
Juya wa junaid yayi ya kalli, tray ɗin da babban yayan nasu yayi watsi dashi a ƙasa, cike da daɗin baki yace “subhanallahi ya akai kayan abincin nan suka zube ƙasa, ni nasan aikin tukur ne bari na kwashe na canza wani,”
Ya karasa ya zuƙunna yana tattare kayan, duk rafayet nabinsa da ido, sai da ya kammala kwashe komai ya mayar acikin tray ɗin sannan ya ɗauka yana cewa “am coming now yayanmu,”
Sannan ya fice, ajiyar zuciya yasaki lokacin da ya fito daga part ɗin nasa, kitchen ya wuce, azmee kaɗai yasamu aciki ta kammala hada masa wani bf ɗin acikin tray,
Miƙa mata na hannunsa yayi ta karba sannan ya ɗauki wanda ta haɗa masa asaman table, ya dago yana kallonta yace “Ina Sehrish take,”? Murmushi azmee tayi kafin tace “ta tsorata ne sosai, ta koma ɗaki ynz,” .
Yace “ok amma aunty azmee yaushe zaki faɗa mata cewa nasan cewa ita maca ce ? Inaso tasani pls !” yayi maganar da shagwa6a,
Ƴar dariya azmee tayi kafin tace “insha Allah yau zuwa anjima, zan faɗa mata,”
Murmushi yasaki ya fice yana faɗin “Can’t wait to see,” dariya azmee tayi tare da cewa “Romeo kenan,”
Itama fice wa tayi daga kitchen ɗin don tajima yau tana aiki acikinsa since morning kamar enjine,
Yana zaune yana jiran junaid, sai gashi ya shigo, hannu rike da tray, a saman table ɗin dake gabansa daga gefe ya ajiye masa shi, sannan shima yazauna gefensa tare da cewa “Babban yaya zan iya baka a baki,” ɗagowa sgr yayi yana kallonsa face ɗinsa tamkar zaiyi murmushi yana kallonsa, wannan fadancin na junaid ba karamin tafiya yake dashi ba,
Plate junaid ya ɗauka, ya shaƙe masa shi da chips har yayi sauro don yasan Babban yayan nasu baya wasa da cikinsa, akwai bama ciki haƙƙinsa ????
Tura masa plate ɗin yayi agabansa, naɗe hannun jallabiyar jikinsa yayi, junaid ya zuba masa ruwa ya wanke hannunsa acikin bowl, sannan ya soma ya zura hannusa yana ɗibar chips ɗin yana turawa a bakinsa, in kaga yadda yake wawuro wa yana turawa a small mouth ɗinsa sai kayi mamakin tayadda akai abincin ke shiga, saboda ƙankantar bakin nasa,
Robar cool milk ya dauka ya zuba masa acikin glass cup ya tura masa a side plate nasa, ga fresh fruits ya acikin hadadden plate ya ajiye masa ga sauran delicious,”
Junaid ne yazauna yana saving nashi, bayan ya tsagaita ya zuba msihi ido yana murmushi, ɗagowa sgr yyi suka haɗa ido yace “what”
“Kyau nake kallo fuskar babban yayana,” junaid ya basa amsa,
“Duk kyau na, nakai ka junaid,”? Ya tambaya yana kallonsa, ɗan sunnar da kai junaid yayi tare da cewa “kai na musamman ne yayana, komai naka na musamman ne, haka kyan ka ma,”
dan ta6e baki sgr yayi yana kallonsa ayayin da yake mika hannu ya dauki cool milk ɗin dake acikin cup ya kurba sosai tare da mayar wa ya jiye,
Sannan cikin natsuwa yace “Ni kam tunda nake aduniyar nan, tun da Allah ya halicce ni a duniyar nan , ban ta6a ganin yaro mai shiga rai mai sace zuciya ba irin ka! junaid u are so special to me i don’t know how to explain it but I really really love u so much, just tell me whatever u want am ready to do it for u,”
daɗi kamar zai kashe junaid jin yadda babban yayan nasu ke yabonsa, sam ya gaza rufe bakinsa har sai da sgr ya maimaita cewa “ka faɗamin komai kake so nayi maka insha Allah,”
Cikin sanyin murya junaid yace “babban yaya murmushinka kawai nake so, dan Allah kayimun koda yaushe face ɗinka a daure…” ya ƙare maganar cikin shagwa6a hada ɗan bubbuga ƙafa,
Shiru sgr yayi yana tunanin wai ma ya ake murmushi aduniya, ae shi yama manta when last yayi murmushi aduniyar nan, muryar junaid ce ta ƙara katse shi”smile 4 me plsssssss..”
shiru su kayi gaba ɗayansu, zuba mishi ido junaid yayi yana jiran yaga murmushin babban yayan nasu,
ɗagowa rafayet ya ɗanyi ya kalli junaid wanda ya ƙura masa iso yana jiransa, mayar da idonsa yayi kan plate ɗin dake gabansa mai dauke da farfesun da junaid ya zuba masa,
wa’iyazubillah , A natse a hankali wani irin ƙayataccen murmushi na side face yafara bayyana a kyakkyawar fuskar sgr, Subhanallahi tabarakallahu ahsanul qalikin, wato wasu irin lotsattsun dimples ne suka bayyana a fuskarsa masu shegen kyau, dole babban yaya ya dinga rowar murmushin sa wato wani irin ruwan kyau, madarar kyau yake badawa, irin murmushin kashe zuciyar nan, irin wanda kai tsaye namiji yayiwa Mace shi duk min ji da izzarta sai ta susuce,
A susuce junaid yadinga yarfa hannu yana fadin “wow!!wow !! Oh my God yaya rafayet am just speechless wannan heart killing smile ɗin naka ya tafi dani,”
Lokaci guda kuma ya mayar da face ɗinsa yadda take, kai kace murmushi bai ta6a wanzuwa a fuskarsa ba, sannan yace “Junaid sa hannu muci abinci atare,” cikin sauri junaid ya zura hannu suka shiga ci atare abun gawanin burgewa, ????•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·
????????????ABBAN SOJOJI????????????