ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

❤‍????Extraordianary Love❤‍????

       *Writer*

©️Hafsat Bature Boss Lady✍️✍️✍️

End of chapter one

~page 75~

daga inda ku ka ga na sanya part 2, to daganan Labarin ya soma da zafi zafinsa ????????????

………..Sehrish……………….
Idonta na facing ceilling a yayin da take kwance tsakiyar bed ɗinta, cike da tsananin shauƙin babban yaya, tabbas ta tsorata da fusatar shi, amma hakan ba ƙaramin burgeta yayi ba, musamman yadda ya hauro da doguwar ƙafarsa yayi wurgi da tray ɗin hannunta, lumshe idonta tayi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa, ita dai sgr yayi mata ya kwanta mata aranta (nace ba Allah ya bar ƙauna)
ta jima tana juyi a saman bed ɗin nata, har sai da ta tabbatar cewa sgr ya isa ya fita ynx sannan ta tashi domin zuwa gyara masa bedroom ɗinsa,
A time ɗin junaid ya fita daga part ɗinsa ya koma nasa room ɗin, sai faman zullumi yake, tun da azmee ta sanar dashi cewa zata faɗawa sehrish cewa yasan cewa ita maca ce, zama yayi saman bedmattress ɗinsa ya lankwashe kafarsa, sae faman smilling yake yi, burinsa sehrish ta amince dashi a matsayin ɗan uwanta na jininta suyi shiri sosai, murmushi yasaki tare da yunƙura yakai hannu daga gefe Jikin gadon akwai side drawers ajikinsa, janyo wa yayi wato bakomai yake ajiyewa ciki ba face Chocolates,biscuits, sweet da sauransu, junaid baya rabuwa da shan zaƙi, ajinin sa yake, ledar dairy milk ya ɗauko guda biyu da snickers, ya zauna yana gatsa yana turawa a mouth ɗinsa sai faman lasar baki ya ke yana tunanin Sehrish ɗinsa ????
Gabanta har faɗuwa yake yi addu’arta Allah yasa sgr ya fita daga part ɗinsa, tafiya take yi cikin sanɗa, ta wuce parlor ɗinsa, adai dai kopan shiga bedroom ɗinsa suka ci karo dashi ƙiris ya rage su gabji juna,
Waro ido tayi tana kallonsa cikin tsananin tsoro, ya shirya tsaf da alama fita zaiyi, ya ɗau wankan jeans da t shirt irin na jikin junaid, ga wannan haɗaɗɗiyar sumar tasa, gyara na musamman tasha, ya daure ta abayansa, yayin da ya saki wata daga ƙasa ta ɗan zubo masa, hakan ba ƙaramin kyau yayi masa ba,
Ƙamshin turarensa sai wankar mata hanci yake yi, kai kace da ruwan turare yake wanka,
gyaran murya yayi alamar abashi hanya ya wuce, da sauri ta ɗan ja gefe, ya bi ta side ɗinta ya wuce da wannan tafiyar tashi mai jan hankali, sam tagaza ɗauke idonta akansa, wani tunanine ya faɗo mata aranta, cikin sauri tace “adawo lpy”
“yawwa” ya amsa mata a time ɗin da yake idasa fita daga falonsa, .
Saboda murna yasa sehrish ta ɗan yi tsallen farin ciki, tare da sakin murmushi koba komai, wannan wani mataki ne, na narasa tunda yana amsa magana in akai masa, ????
Shiga bedroom ɗinsa tayi har time ɗin tana ayyana muryarsa da yadda ya bata amsa, taci alwashin daga ynx zata dinga yi masa magana, tunda yana amsawa,
Ajiyar zuciya tasaki tare da mayar da hankalinta ga abunda ya kawo ta, bin ɗakin nasa tayi da kallo, Aljannar duniya komai tsaf a gyare, sae ƙamshi ke tashi kamar, koda yaushe tana jinjinawa haɗuwarsa da kuma dollars ɗin da aka kashe masa, nan gaba sehrish zata zayyana mana ya haɗuwarsa yake ????
A hankali take shafa lallausan blanket ɗinsa, ta janye sa daga saman gadon ta ninke sa, tare da hugging ɗinsa a chest ɗinta tana shaƙar kamshinsa, ta jima tana lalaci a ɗakin nasa kafin ta shiga gyarasa,
………….Hosana ………….Jahad ……………
a hankali motocin nan suka shiga dasu a katafaren gidan goggonsu, yadda motocin nan na sojojin nan suka zagaye motar da suke ciki ko shugaban ƙasa albarka,
Sunyi shiru acikin motar,ni’imtaccen sanyin a.c ne kawae ke ratsa, sassan jikinsu, tsantsar farin ciki ne a fuskarsa, ita dai jahad sai godiya take ma Allah daya kawo musu ƙarshen wahalarsu acikin zuciyarta, yayin da hosana ke ta faman zabga murmushi kamar zautacciya,
A tsakiyar gidan suka tsaida motocin, da sauri major ɗin nan dake driving ɗinsu, ya fito tare da buɗe musu kopa, riƙe da hannun juna suka fito, suna bin gidan da kallo ya haɗu masha Allah,
Major ɗinne ya shiga dasu cikin babban falon, saude ce ke ta faman goge goge, tana kakka6e kujeru, ɗagowa tayi jin anyi sallama,
Zuba ma yaran ido tayi tana kallonsu, cikin mamaki ganin tagwaye kyawawan gaske, sam ta gaza magana,
Sai da taji muryar major ɗin yana cewa “Marshal Omar ne yace akawo su nan, shima kuma yana nan shigo wa da anjima,”
yana gama faɗan hakan ya fice, zuru su kayi suna tsoron wata irin tarba za’ayi musu, don sun lura kamar baƙin jini ne dasu kowa baisan su,
ganin matashiyar ta soma sakin murmushi a fuskarta yasa su suma suka ɗan saki fuska,
Cike da zumuɗi takara inda suke kamar tasan su, ta ruƙo hannayen su tana cewa “masha Allah ku shigo ciki ku zauna, ku saki jikin ki ku,”
Haka saude ta ruƙo hannunsu, ta zaunar dasu tare da cewa “bari na kawo muku abunsha ko”?
Cikin sauri hosana tace “ƴunwa muke ji…..,” tunkan taƙarasa jahad tasa tafin hannunta ta rufe mata baki, tare da cewa “Hosana banasan wannan abun, daga zuwa gidan mutane kinsan su ne,”
murmushi saude tayi tare da cewa “ba yaya Omar bane yace akawo ku nan ba? Don haka ku saki jikin ku kamar kuna cikin jirgi mai ya ƙare” ????
“Sannan naji kince batasan mu, ae musulmi ɗan uwan musulmi ne, akwai sanayya da ƴan uwantaka ta addinin musulunci, sannan kuma baƙon ka annabin ki, ku baƙi ne dan haka zan karramaku sosae,
Saude ta karasa maganar tare da sa hannu ta shafa kan hosana tace “kada ki damu ƙanwata, yanzu nan zan kawo miki abinci lafiyayye ki ci,”
“nima zanci,” jahad ta faɗi tare da sunnar da kai, murmushi saudat tayi tare da cewa “shikenan bari nazo ga tv nan kuyi kallo,” tayi maganar tana nuna musu plasman dakw manna a bango, sannan ta wuce kitchen,
Ajiyar zuciya suka saki atare suna ƙare wa haɗaɗɗen falon kallo,
“Hosana dan Allah ki daina zuba, kina bani kunya sometimes, kin ci ka ɗumi daga zuwa gidan mutane sai ki fara tambayar abinci kamar mayya”?.
Harara hosana ta watsa mata tare da cewa “bani ce mayya ba kaɗai kema mayyar ce, saboda ke ma ae kince zaki ci, ” tayi maganar tana murguɗa mata baki, jinjina kai kawai jahad tayi, ba yadda zatayi da ita,
Shigowa saude tayi hannunta ɗauke da tray ta aza katuwar kula aciki, sai plate wit 2 spoon, gefe kuma jug ne mai ɗauke da juice,
Tunkan ta ƙaraso hosana, ta sauko ƙasan carpet ɗin ta zauna tana washe baki,
Ajiye musu tayi tare da cewa “yakamata ku wanke hannayen ku, bari na kawo muku wurin da zaku wanke,” ta faɗi kafin ta juya izuwa cikin kitchen ɗin,” .
Buɗe kular hosana tayi, zaro ido tayi tare da cewa “Lahh ha ilah Jahad !! Shinkafa kaza ce wlh, hada wasilla masu yawa wayyo daɗi,” shiru jahad tayi batace mata komai ba, saboda yunwar da take ji,
Ji su kayi bazasu iya jiran saude ba, takawo musu ruwan da zasu wanke hannu ba, ai kafin saude ta fito daga kitchen ɗin tuni hosana ta ɗauke jug da plate ɗin dake saman tray ɗin ta ajiyesu on carpet ɗin , ta ɗauki kular ta zazzage musu farar shinkafar da miyar duka acikin tray ɗin, gaba ɗaya suka sa hannu suka motse ta suka shiga zubawa cikinsu, hannu baka hannu ƙurya kamar wani yace zai kwace musu abincin,
Tsaye saude tayi akansu tana kallon ikon Allah, gashi har ta ɗauko musu bottle water da bowl ɗin da zasu washing hands ɗinsu aciki, tausayinsu ne yakamata, alamu sun nuna cewa yaran na cikin mawuyacin hali na ƴunwa,
Kamar wasu kuraye haka suka dinga, zuba uwar loma suna ci, Allah sarki anjima ba’a haɗu ba, kitchen saude ta koma cups da dauko musu,
Ta dawo ta zukunna inda suke, tana tsiyaya musu ruwan bottle ɗin hannunta mai sanyi, tunkan ta gama hosana ke miƙa mata hannu tana cewa “ruwa !ruwa!!,’ wato taci taci harya shaƙe mata makoshinta,
Miƙa mata saude tayi cikin sauri ta kar6e, ta kai baki tana sha, har wani sauti throat ɗin ta ke badawa “ƙut ƙut kut,
“Hosana nima zan sha in kin gama,” jahad ce tayi maganar tana yarfa hannayenta, cikin sauri saude ta zuba mata itama a ɗayan cup ɗin ta miƙa mata, karba tayi tana faɗin “mungode,”
Zama saude tayi kamar ta samu tv tana kallonsu, yadda hosana ta dauki cinyar kaza, ta tura acikin baki kamar kura ta bata tsoro, amma abun mamaki hada ƙashin ta haɗa duka ta taune, zaro ido saude tayi cikin tsoro tana cewa “ki ci a hankali dan Allah,”
“Bazaki gane ba aunty, wlh yunwa muke ji, dan Allah in akwai sauran abincin ma akwaso mana shi duka hada ƙanzoma,” ????
Hosana ce tayi maganar, tana ta fama lashe la66a, mouth ɗinta yayi dama dama da jar miya, kamar mayyar dae,” ????.
Jahad dai ba baka sai kunne, sam bata gane da wane yare suke magana, bata ankare ba hosana ta ɗauke tray ɗin duka tasanya harshenta tana lasa ????
Ita kanta saude batasan time ɗin da ta, fashe da dariya ba hada dafe ciki, sam tagaza stopping kanta, sae da tayi mai isarta, sannan ta tashi daker tana ci gaba da dariyar ta amshi tray ɗin dake hannun hosana tana cewa “bari na zubo muku alkubus da miya kuna so,”? tayi maganar tana kallonsu, ae har haɗa baki suke yi wurin cewa “eh komai ma in akwai hada ƙanzo ma azubo mana muna ci pls , mu ko ciyawa ce in dai za’a sama ta miya muna so,” ????????????
Dariya kamar zata kashe saude, haka ta ɗauki tray ɗin ta wuce dashi kitchen, duk wannan budirin da akeyi goggon katsina bata sani ba, tana can haye saman gadonta,daga sauraron radio bacci ya kwashe ta,
Sai da jahad da hosana su kayi kulu wash rabu hani’an , sannan suka dawo hayyacinsu, sun ƙarar da abincin gidan duka, dole saude ta ɗaura wani girkin,
Bedroom ɗinta ta shigar dasu,bin ɗakin su kayi da kallo komae tsaf ba tarkacen hauka, sai ƙamshi ke tashi, daga bed sae wardrobe, ƴar bedside loka da sauransu,
Toilet ta nuna musu tare da cewa “nasan zaku buƙaci yin wanka, ga toilet nan, ku cire kayan jikin ku naga sun tsufa kuma sunyi datti, kusanya munsu acikin laudry basket ɗincan,” tayi maganar tana nuna inda basket ɗin yake gefen wardrobe ɗinta,
Sannan tace ” duk abinda baku gane ba kuyi mun magana, just feel free,”
“Mun gode sosae aunty,” acewar jahad, murmushi saude tasaki tace “kada ku samu damuwa, ni zan shiga ciki,” tayi maganar tare da fice wa daga ɗakin,
“Wai !! Allah hosana kin ga yadda Allah ke ikonsa ko? mun fita daga wancen kurkukun kaddarar (Next novel) ynx gashi zamu fara sabuwar rayuwa mai kyau,”
Murmushi kawai hosana ke saki, gaba ɗaya hankalinta nakan Marshal Omar duk in ta tuna yadda lamarin ɗazu ya wakana sai taga abun kamar a mafarki,” ????
Sun jima suna shiririta, kafin jahad tafara shiga wanka, komai na toilet ɗin a tsaftace, ya ji tiles har jikin bango, shower ce ta tsaye, sai kwandon wanka, mai ɗauke da sabulu mai ƙamshi da lallausan soso,
Bakomai ya burgeta ba acikin toilet ɗinba sai shampoo da tagani jere, saman mirror, saboda gashinsu yayi dauɗa, duku-duku sai uban wari, ga ƙura, murmushi tasaki cikin sauri ta tu6e rigar jikinta kamar tsumma, ta yi hanging ɗinta jikin towel holder,
Baƙaramin dauɗa jahad ta fidda ajikinta ba, sai da ta wanke ko’ina tayi shaving gashin under ɗinta dana armpit ɗinta da Shaving cream, dogon gashin kanta ma yasha wanki da shampoo,
Zanso ku ga yadda jahad ta fito daga toilet ɗinnan, Fesss fesss kamar wadda tayi wanka da ruwan zam zam, da daurin gaba ta fito, towel tasanya ajikinta, hannunta kuma na riƙe da rigarta, cikin laundry basket tasanya rigar kamar yadda saude ta basu umarnin,
Sakin baki jahad tayi ganin hosana nata faman sharar bacci a tsakiyar shimfidaɗen gadon saude, girgiza kai tayi tare da faɗin “basa ban ba, gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas” ????
( this reminds me our class mates Allah sarki, wannan sararsu ce, wato daga anyi abu sai suce gida babu makwabta babu gidan miji ba tabbas)
Allah sarki hosana dole kiyi bacci baiwar Allah, munyi rayuwar ƙunci sosai, yanzu lokaci ne da Allah ya amshi addu’armu, zamuyi rayuwa ta jin daɗi da walwala,” jahad ce tayi wannan maganar sannan ta ƙarasa, inda hosanar take, ta ɗan russina tare da sa hannu da bubbuga ta, ” Get up hosana, bacci bazai yi maki daɗi ba, da datti ajikin ki, ki tashi pls,” a hankali hosana ke buɗe dara daran idanuwanta, tana lullumshe su, cikin kasalalliyar murya tace ” meyasa kika tashe ni dan Allah ! bakiji yadda nake ji ba, ‘
“Sorry hosana, nasan ba daɗi amma ki tashi kije ki cire dattin dake jikin ki, wlh zakiji wata irin ni’ima mai daɗin gaske na shigarki, ba ki ga yadda nayi fess ba”? tayi maganar tana jujjuya mata jikinta don tagani dakyau,’
Murmushi hosana tayi daga kwancen da take tana kallonta, miƙa mata hannunta tayi tare da cewa “pls taimakamin na tashi kasala nake Ji ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button