ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE
Hafsat Bature ????????????????ABBAN SOJOJI????????????
Mallakin
????Hafsat Bature Moh’d????
❤????BossLady❤????
Junaid was the heart beats of my story not because i loved him so much, zaku shaida hakan
~page 76-~
Murmushi hosana tayi daga kwancen da take tana kallonta, miƙa mata hannunta tayi tare da cewa “pls taimakamin na tashi kasala nake ji ajiki,”
Ruƙo hannunta jahad tayi daker ta miƙar da ita tsaye, tana faɗin “wash Allah ba dole ki ji kasala ba, kinci uban abinci kin kuma zo kin kwanta,” acewar Jahada,
Wuce wa hosana tayi tare da shigewa toilet ɗin, tana jiyo muryar jahad tana cewa “Hosana akwai shampoo ciki pls ki wanke wannan mahaukacin gashin kan naki, mara tsari nasan ki da taurin kai, bakisan wanke sumar kan ki, ko nazo na taya ki wanke wa..”? ta tambaya tana jiran amsa,
“Banso,’ ta cikin toilet ɗin tabata amsa, dafe kai jahad tayi tare da cewa “Oh God!!” saboda tasan hosana bazata ta6a yarda ta wanke sumar kanta ba, kuma bata so wani ya wanke mata, shiyasa kullum gashin kanta a cukurkuɗe yake, gashi duk tafisu yawan gashi da cukowa, duk da kowa da yawan nasa,
jahad na zaune saman stool gaban mirror tana shafa cream ajikinta, sai ga saude tashigo da sallama, da fara’a a face ɗinta tace “wow masha Allah, tubarkallah wannan dogon gashin fa kamar na larabawa,” tayi maganar tana kallon sumar kan jahad wadda ta zubo mata har wurin waist ɗinta,
Cikin jin kunya jahad ta sunnar dakai, saude taci gaba da cewa “duk da nake bafullatana, nima ina da gashi amma bai kai ko rabin naki ba, ke wata ƙabila ce ? Jahad tace “BUXUWA,”
Saude tace “No wonder, shiyasan ya, hakan na nufin cewa ku ƴan niger ne ko?
“Mahaifiyar mu buzuwa ce ƴar niger, amma mahaifin mu bafullatani ne ɗan nan,”
saude tace “Wow wow!, haba ! ae dole kyau ya haɗu a wurin nan, dole kuyi kyau yara,” murmushi kawai jahad ke saki, ganin yadda saude ke zuzuta su duk da itama ɗin kyakkyawa ce,
Wuce wa ciki saude tayi ta buɗe wardrobe ɗinta, riguna ta ɗauko musu dogaye sun sha guga ninkakku, ta ajiye musu asaman gadon sannan tace “Gashi nan kusanya rigunana ne, duk da nasan sunyi muku tsayi sosai,”
“Mungode sosai aunty, Allah yasaka da alkairi,” saude tace “mention not pls,” sannan tafice don tabasu damar wataya wa,
“Jahad kinji yadda iska ke shiga jikina, ga wani ƙamshi dake fitowa sako da lungu na hammata ta,” hosana ce tayi maganar wadda fitowarta kenan daga toilet ɗin,
A lokacin jahad ta kammala sanya doguwar rigar da saude ta fiddo masu, na materials ne pink colour masu kyalkyali, ba karamin kyau su kayi mata ba, cikin 6acin rai take kallon hosana
“Meyasa wai baki da hankali ne, ke shashashar ina ce? Ba sai da nace miki ki wanke sumar kanki ba,”? ta tambaya a ƙule tana kallon hosanar,
Da buɗar bakinta sai cewa tayi “Gashina ne ko Gashin ki”? Shiru jahad tayi don tasan ynx zata tada rigima har ajisu,
“Gashin ki ne hosana, zo kisanya kaya gashi nan aunty ta fiddo mana mu sanya,” wuto wa tayi daure itama da towel ajikinta, ta zura rigar materials ɗin, tayi kyau amma gashin kanta sai uban wari ya ke yi, babu yadda jahad ta iya da ita, bayan sun kammala shiryawa, atare suka haye saman gadon suna facing ceilling, “what are u thinking about jahad”? Hosana ce ta tambaye ta, cikin sanyin murya jahad tace “SEHRISH, ke fa me kike tunani? Murmushi hosana tayi kafin tace “Wannan kyakkyawan mutumin, mai ƙarfi wanda ya ceto rayuwarmu daga shiga haɗari, daga na rufe eyes ɗina shi nake gani, lokacin da na faɗa jikinsa, bakiji ƙamshi ba wlh ya haɗu” ????
Jahad tace “shegiya ashe kina cikin hayyacin,” ???? dariya su kayi gaba ɗayansu
………………….SEHRISH…………………
Ta gyara komai tsaf na bedroom ɗinsa, tsayawa tayi tana kallon hoton dake jingine saman side drawer ɗinsa bayan bedside lamp, hannu takai ta ɗauki hoton tana kallo, wata mata ce acikin hoton fara tas baturiya, mai kyan gaske kai kace itace tayi kanta don kyau, jikinta sanye da uniform ɗin na sojoji, kakin ba ƙaramin kyau su kayi mata ba, tsaye take tayi saluting a cikin hoton, bin sumar kanta sehrish tayi da kallo, launin gashin matar yayi yellow mai tsayin gaske, kwayar idonta kuma blue colour ce, wannan ba kowa bace faceAlexandra Ummu Rafayet, ummun Ayan da jahan kuma ummun micheal(makel) da ROMEO ????
Murmushi sehrish tasaki matar ta burgeta, duk da batasan kowacece ba amma kamannin fuskarta sak irin na Babban yayansu, akwai kyau, daga ganinta wayayyiya ce ajin farko,”
Hannu sehrish tasanya tare da shafa hoton a fili tace “kowacece wannan matar amma ta haɗu kuma ta burge ni, gashi tana kama da Babban yaya sosae,” ta karasa maganar tare da mayar da hoton inda yake ta ajiyesa,
Sannan ta tura kopar toilet ɗinsa ta shige ???? uhmmm hmmmmmm, tsayawa sehrish tayi tana tunanin anya ba kuskure tayi ba, wannan ae ba toilet bane, jimmmm tayi tana ƙarewa toilet ɗin kallo, lokaci guda ta dabarbace saboda haɗuwarsa, an raba shi biyu 6angaren toilet da kuma na bathroom wurin wanka kenan, ba ƙaramin girmane dashi ba, kamar a mafarki take bin komai da kallo, shiga ciki tayi ƙamshin wurin na dakar hancinta,
ba komai yaja hankalinta ba face wurin wankansa, wato irin standing jacuzzi ɗin nan ne (kwamin wanka), wande ke zagaye cikin glass, sakin baki sehrish tayi galala tana kallon ikon Allah, mayar da eyes ɗinta tayi kan bathroom cabinet ɗinsa, jerun wasu matsiyatan Shampoo ne, mayuka iri iri masu kyau da tsadar gaske, duk na gyaran jiki ko mace albarka wannan,
Jinjina kai kawai sehrish ke yi, haɗaɗɗen mirror ɗin dake cikin toilet ɗin mai girman gaske, ga wash basin agabansa, mai ɗauke da taps biyu na ruwa, daga gefe kuwa soap dispenser ce, gashi an ƙawata shi da vase a ajiye ƙasa, (Tukunyar flowers)
Zuƙunnawa sehrish tayi ƙasan hadaɗɗen tiles ɗim mai walkiya, ta zabga tagumi, aranta tana mamakin cewa wai nan toilet ne ? Idan har nan toilet ne to mukuma irin namu toilet ɗin ya sunan shi ? (Nace ba kewaye ko ki ce banɗaki) ????
ta jima tana shirita, domin ba abun da ke buƙatar gyara a toilet ɗinsa, komai tsaf, kallo kawai ta tsaya yi daga bisani ta ɗanyi goge goge kawae ,
Fitowa sehrish tayi ta sauko down tana ko zata ganshi, basa nan ba kowa duk sun fita,
Wuce wa nata room ɗin tayi, tayo wanka, ta fito ta zura riga ta maza dai dai guiwa, ta zauna gefen gadon tana tunanin duniya, kallon sama tayi tana cewa “Oh ni yanzu wata rana nima zanyi saurayi, har nayi aure na haifi ƴa’ƴa,? When ? Ina so nima nayi shiga irin ta mata, na wataya nayi rayuwar ƴanci yaushen hakan zata faru ? ????
Ajiyar xuciya tasaki tana tunane tunane,
Kwankwasa kopan akayi, cikin sauri tace” wanene? Azmee tace “wa kika sani yake zuwa ɗakin ki in ba ni ba,”?
Murmushi Sehrish ta saki tare da miƙewa ta buɗe mata kopan, sanye take da hijabi milk colour hannunta riƙe da Cazbaha, da murmushi a fuskarta tace “ƙanwata ina fata dae ba zaune kike hakanan ba kina tunane tunanen duniya? karfa ace bakiyin zikri? Ba istigfari da sauransu?
Sunnar da kai sehrish tayi, don kuwa batayi, ae tun ran da tasanya SGR a idonta, ta rage duk wani abu da take yi,
“Hmmm dama raina ya bani, gsky zamuyi faɗa dake muddin baxaki, daina zama hakannan ba kina sa damuwa aranki ba,
“Insha Allah aunty azmee zan rinƙa ƴi,” jinjina kai azmee tayi kafin tace “Albishirin ki,”?
Cikin mamaki sehrish tace “Goro,”
Azmee tace ” an bani sabuwar waya nabaki,”
Ɗan zaro ido sehrish tayi cikin mamaki tace “Who”? Murmushi azmee tayi tare da cewa, ” i will let u know but not now, yanzu dae da anjima bayan magrib kina da baƙo,”
Waro ido sehrish tayi tare da cewa “baƙo kuma aunty azmee ? wurin wa zai zo? Tayi maganar cikin ruɗu,
Azmee ta dafa kafadarta tare da cewa “bakowa bane , fa ce wanda nace miki, yasan cewa ke maca ce !! yau zaku haɗu, na shirya muku haɗuwa a Garden, ki same shi immediately after magrib prayer,”
Murmushi sehrish tasaki tana jujjuya ido, ta ɗan jinjina kai kafin tace “shikenan aunty azmee Allah yasa naga alkairi,” yanayin yarda tayi maganar taba azmee dariya,
“Ni zan wuce, maganar wayarki kuma, sai zuwa gobe zan baki ita, salon kuma in ga yarinya ta buɗe tiktok ko insta don na lura kan ƙanwar tawa rawa yake yi,” ta ƙarasa maganar cikin zolaya da dariya a face ɗinta,
Itama sehrish dariyar take yi, duk da batasan menene tiktok da insta ɗinba, sunan kawai ta ta6a ji ana faɗa,” .
Bayan azmee ta fita, sehrish ta daka wani uban tsalle sai saman gadonta, tsananin murna ne ya bayyana a fuskarta, rawa ta dinga yi tana tsalle tsalle asaman gadon jin an mallaka mata waya, gashi kuma zata haɗu da wanda yasan cewa ita maca ce acikin gidan, addu’a take yi Allah yasa koma wanene acikinsu yakasance mai sauƙin kai kamar hafsat bature,