ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

????????

Yini tayi tana zullumi acikin ranta,wanene wannan dayasan cewa ita maca ce ba namiji ba, wayyo Allah yasa junaid ne don yafi su sauƙin kai, ko ba komai wannan wani mataki ne nasara arayuwata, ga kyautar waya kuma an bani, wayyo daɗi bisa daɗi yanzu ya’azayi na rinƙa waya da ƴan uwana? ta faɗi jiki a mace,.
Zama tayi saman gadon ta janyo pillow tare da rungumesa jiki amace, taso ace lokacin da zata riƙe waya, ta rinƙa samun su Hosana da jahad, amma kash tun time ɗin da junaid ke ara mata wayarsa, ta daina jin ɗuriyarsu kullum switch off, sehrish ta jima tana tunanin menene yasa ba’a samun wayar tsohuwa ne ? What’s happening wit them?

????????????????????????????????????????????
…………..AMANI……………………
tunda taji dirar motoci acikin gidanta, kuma dama Cg abbas ya sanar da ita cewa, Rafayet yace masa zai zo gidansa ya kawo masa ziyara, hakan yasa sai faman rawar kai take yi, shiri na musamman tayi, ta ɗauki wankar less maroon colour wanda akayiwa ado da stones doguwar riga ce tabi shape ɗin jikinta, ko mayafi bata sanya ba, ta zubo da gashin kanta har gadon bayanta, dama fa akwai kyau abun saiya bada Citta, kai kace ba matar aure ba, ƙanin miji zai zo an dage ana ta zabga uwar kwalliya,”
fitow tayi daga bedroom ɗinta, tana saukowa daga saman stair, cikin tafiyar rangwaɗa da yanga, dama legs ɗinta nasanye cikin highheels launin kayanta, ta fito fess abunta Balarabiya
Ƙamshin turarenta ya gama gauraye falon, tunkan ta idasa isowa ta zuba mishi ido yana a zaune saman 3 seater, ya aza ƙafa ɗaya bisa ɗaya yana daddana wayar hannunsa cikin natsuwa,
gaba ɗaya ya tafi da imanin Amani, saboda tagaza janye eyes ɗinta daga nashi, daker ta iya samun natsuwa har tace mashi “sannu da zuwa Babban yaya, ashe kaine nayi mamaki wlh, ban ta6a tunanin zan ganka ba agidan namu,” tayi maganar tare da samun wuri itama tazauna suna facing ɗin juna,
Ya jima bai bata amsa ba, kusan 5 minutes sannan yace “Yawwa ya nasame ku,”?
Cikin kashe murya tace “lfy lou Alhamdulillah,’ .
shiru su kayi ba magana aranta tace “tabɗijan can ! Wai dama haka yake da miskilanci? Ko kallo babu balle magana,’? ta tambayi kanta acikin zuciyarta,

Just managed ba editing,

~HafsatBatureBossLady~

In kina so ki gode mun kiyimun share na novel ɗina, shine first novel ɗina don haka ayimun share ɗinsa ko’ina ????????

Page 77-76

????????????ABBAN SOJOJI????????????

????Hafsat Bature Moh’d Boss Lady????

~page 77-78~

❤‍????Extraodinary Love❤‍????

(Don’t forget to share it everywhere) ????

Miƙewa tayi tare da cewa”Bari na kawo maka snacks da abunsha,”
dakatar da ita yayi da hannunsa yace”No need thanks”
Murmushi ta ɗan yi tare da komawa ta zauna, tana ci gaba da kallon fuskarshi, kafin ta mayar da idonta kan surar jikinsa tana haɗiyar yawu,
“Banason Kallo,” ya faɗi yana ci gaba da dannar wayarsa, cikin jin kunya Amani ta janye idonta, tana mai mamakin taya akai haryasan tana kallonsa,
Cikin kashe murya tace ” Babban yaya ae dole na kalle ka, kai fa abun kallo ne, kuma ni ban ta6a ganinka ba ido da ido, shiyasan ya,’ ta ƙare maganar tana cizon pink lips ɗinta alamar ya cije ta,
shi kuwa ba ta ita yake ba, burinsa yayansa Abbas ya ƙaraso, su ga juna, yayi kewarsu sosai,
Muryarta ce ta ƙara ratsa shi “Babban yaya, ko dae baka farin ciki dani ne amatsayina na matar yayanku ishaq,’? ta yi maganar tana kallonsa,
“Why’? ya tambaya har time ɗin bai ɗago ya kalleta ba, gyara zama tayi tare da cewa “to naga u don’t even want to look at me, atlease u should put ur eyes inside mine,”
Amani ba ƙaramin takura masa tayi ba, ji yake tamkar ya tashi yabar gidan, don baisan nacin magana,
“Plsss babban yaya,”
dogon tsoki yaja tare da cewa “becareful with me,” gabanta ne taji ya faɗi jin gargaɗin da yayi mata, tabbas mace bata gabansa,
Jiki a mace Amani tabar falon, cikin bedroom ɗinta ta koma, jiki na rawa ta ɗauki phone ɗinta dake ajiye asaman pillow ta dannawa AUNTY BABBA kira,
Ringing 3 ta ɗaga kiran bayan sun gama gaisawa cikin zumuɗi Amani tace “Aunty ko kinsa cewa SGR na cikin gidan nan yanzu haka? tayi maganar da murmushi a face ɗinta,
A can 6angaren kuwa cike da mamaki aunty babba tace “Are you serious? shi da kansa kuma”?
dariya Amani tayi tare da cewa “wlh kam,baki ji yadda naji ba dana gansa duk da rashin maganarsa, yaci ka ji dakai wlh,”
Aunty babba ta fashe da dariya ta cikin wayar tare da cewa “ki barshi zai zo hannu ne yanzu dai ya maganar Ziyartar wurin bokan nan baba ibliss? kin sama mana kuɗin?
Ajiyar zuciya amani tasaki tare da cewa “tukunna dae auntyna, ina nan ina tarairayarsa, ina so nabi komai a sannu, insha Allah nan ba da jimawa ba, zaki ji daga gare ni, da kaina ma zanzo kd na kawo miki ziyara,”
Aunty babba tace “To shikenan, Allah ya kaimu lpy, shiri na musamman zamuyi, domin ganin munci nasara akan waɗannan zafafan guda biyu,”
sun jima suna waya a tsakaninsu, agame da yarda zasu ziyarcin wurin hatsabibin bokan nan Baba iblisssss ????
A can ciki kuwa, dirar Abbas kenan fuskar nan dauke da fara’a kamar gonar auduga jin cewa Sgr ya kawo masa ziyara da kansa, sanye yake cikin kakinsa na sojoji daga headquater yake,
yana shiga falon Rafayet ya miƙe fuska a sake suka rungume juna sosae, kamar karya sake shi haka Abbas ya ji,
“Am really glad to see u bros, nayi kewarku sosae kamar kamar me,” abbas ya faɗi hakan cikin tsananin farin ciki, ruƙo hannunsa yayi suka zauna a mazauni ɗaya, suna kallon juna cike da kewa,
Cikin sanyin murya babban yaya yace”Nayi kewarku sosae, har ma bazan iya faɗa ba,”
ƴar dariya abbas yayi tare da cewa “Wake koya maka hausa ne? nayi mamakin jinta raɗau abakin ka duk da har yanzu da sauranka, last time da kazo daker kake fahimta in anyi magana,”
Jinjina kai Babban yayan yayi tare da cewa ” bana so nazo ƙasar nan ne arinƙa gulmata bana ji, that’s why na dage na koya saboda su Ammi,”
Dariya abbas yayi sosae jin abunda Rafayet yace, a wasa wasa shima ya iya zolaya in yaso , bayan abbas ya tsagaita da dariyar ne yace “Am wai baku gaisa da Amani ba? naga ko abunsha ma bata kawo maka ba,”
“No tazo mun gaisa, ni nace bana son komai shiyasa,”
Jinjina kai Abbas yayi tare da cewa “meyasa baka son shan abu ko cin abu in kazo gidan mutanene nifa ɗan uwanka ne jinin ka, shikenan nima duk ranar da kayi aure nazo gidan ka, matarka tayi mun tayin abinci bazan ci ba,”
wani kallo babban yayan yayi masa tare da ɗan ta6e baki kafin yace “NEVER,” wato bashi ba aure har abada,
Murmushi abbas yayi yana kallonsa yace “hmmm haka dayawa irinka suke cewa but at the end sai ga lamarin ya sauya, irin ku ma mace tafi juya ku, sannan maza irinku da basa ra’ayin mata ko aure wlh basu iya faɗawa tarkon so ba, haukace wa suke yi idonsu ya makance lokaci guda,” .
Abbas ya ƙare maganar da zolaya yana kallon fuskar Sgr, wanda ya tamke fuska yana sauraran bayanin yayan nasa,” .
Miƙe wa yayi tare da cewa “Ni zan wuce,”
“Haba Babban yayansu, nasan magana tace tayi hurting ɗinka am sorry 4 that, it was a joke,”
Abbas ya faɗi tare da miƙewa shima ya ruko hannunsa cikin lallami,’
“Ba abunda kake tunani bane yaya abbas, time ɗin tafiyana ne yayi, saboda ko wane lokaci na rayuwata yana da amfani, kuma a ƙirge yake”
Murmushi abbas ya saki yana jinjina kai yace “kuma fa hakane, na tuna da wannan, ae nama gode ssae da ziyarar da ka kawomin, Allah yabar zumunci,” ya faɗi hakan a yayin da ya matsa suka sake hugging junansu, sannan su kayi sallama,
……………………SEHRISH……………………….
Bayan sallar La’asar wuraren ƙarfe 5 na yamma, suna kitchen ana ta faman girke girken abincin dinner, ƙamshi ya gauraye ko’ina,
tana tsaye tana yayyanka kayan lambu a saman chopping board, fuskar nan a washe abubuwa biyu na mata yawo aranta, na farko shine wanene wannan wanda xata haɗu dashi yau a garden wanda yasan cewa ita maca ce, na biyu kuma shine new phone ɗin da aunty azmee tace an bata kyauta, bakomai take ɗauki da wayarnan ba fa ce shegen son kallon fina finai dake gare ta, ga son sauraron music gata mayyar selfy kamar hafsat bature ????
“Ji mana, ki dubamin girkin nan , ynx zanje na dawo,” azmee ce tayi maganar a yayin da take fi ce daga kitchen, ..
Cikin sauri sehrish tace “To aunty azmee,”
Ajiyar zuciya tasaki tare da cewa “ko ƙarfe nawa yanzu i ave to check the time, ina da baƙo fa,” ta faɗi cikin zumuɗi tana kallon agogon dake manna a bagon kitchen ɗin, shida saura murmushi tasaki tana faɗin “lokacin haɗuwa ya kusa Ya Allah ka bani ƙwarin guiwar tunkarar koma wanene wanna,”
ta faɗi tana nuni da knife ɗin da ke hannunta,
Azmee kuma da ta fice bedroom ɗin junaid ta wuce, domin ta ƙara tunasar dani haɗuwar da ta shirya musu da sehrish,”
Sai faman knocking take yi, amma sam baiji ta ba, yana tsaye riƙe da ƙugu gaban closet ɗinsa ya buɗe yana kallon jerin kayansa, yama rasa wanne zai sanya domin haɗuwa da sehrish ɗinsa for the first time, sai zabga murmushi yake yi ba magana, tun da azmee ta sanar mishi da haɗuwarsa da sehrish yarasa tsaye ya rasa zaune, sai rawar kai da zumuɗi yake, kamar sabon ango ????
daga shi sai short ajikinsa, sai da azmee ta ɗaga murya da cewa “Junaid ka buɗe aunty azmee ce inason magana da kai,”
Ae yana shaida muryarta a kunnansa jiki na rawa, yayi hanzari zuwa ya buɗe mata kopan, yana sakar mata murmushi,
“Ango kasha ƙamshi,” azmee ta faɗi cikin zolaya,
“Ka ce ka shirya haɗuwa da amaryar taka kenan,”?
Cikin ɗan jin kunya yace “Kai aunty azmee, nifa kunya nake ji,”
yadda yayi maganar da shagwa6a yasa ta yin ƴar dariya tace “uhm junaid kenan Romeo shugaban ƴan soyayya yau zai haɗu da juliet ɗinsa akaro na farko, yakama ka rubuta wannan a diary ɗinka saboda tarihi,” .
ɗagowa yayi da dariya a fuskarsa yana kallon azmee jin abunda yace,
“Insha Allah aunty azmee, dole na rubuta wannan, saboda rana ce ta farin ciki da bazan ta6a mantawa da ita ba arayuwata,” cikin sanyin murya junaid yayi maganar, alamar yana jin abun aransa sosae,
Azmee tace “hakan yayi kyau, ynx dae ni zuwa nayi na ƙara karfafa maka guiwa kasan kai mutumina ne, inaso ka saki jiki sosae, sbd rishi yarinya ce mai shegen tsoro, tana da wani hali dana lura dashi yanayin yadda mutun ya tarbe ta itama haka xata kar6esa, i mean yadda kasakar mata fuska haka itama zata sakar maka tata, kuma zata saki jiki da kai sosai kamar ɗan uwanta, Junaid nasan baka da ƙanwa mace, gaba ɗayanku maza ne, to inaso ka ɗauki sehrish amatsayin ƙanwarka, kai kuma ka zama tamkar yayanta mai share mata hawayenta, kuma abokin shawararta,” natsuwa junaid yayi yana sauraran maganar azmee har cikin ransa bayaninta ya kwanta masa aransa,
Bayan ta kammala maganarta ta tace “Junaid ni zan koma kitchen, nasan gobe akwai labari mai daɗi daga wurinka, zanji ya haɗuwarka da juliat ta kasance,”
Dariya kawai junaid yake yi, yana faɗin “insha Allah aunty azmee, ngde ssae ke ce silar farin ciki na,”
Murmushi azmee tasaki tare da juyawa ta fice tana cewa “Karka manta kaifa ɗane a wurina junaid, cikina ne kawai baka zauna ba, amma ni na shayar dakai ina alfahari da hakan,”
Rufe door ɗin yayi, tare da daka uban tsalle na murna, runtse idonsa yayi tare da dunkule hannunsa yana faɗin “Can’t wait to seeeeeee you Sehrish My dreamy Girl………….
koma wa kitchen ɗin azmee rayi suka ci gaba da aiki, tana lura da sehrish cikin sauri take yin aikinta fuska ƙumshe da murmushi, ba don komai ba sai don tayi saurin taje tayi wanka ta kimtsa bayan sallar magriba ta wuce garden wurin wanda aka ce zata haɗu dashi ????
????????????????????????????????????????????????????
…………..Twins………………………………
kwance su ke rungume da juna a katafaren ɗakin da suka ɗauka na hotel ya haɗu iya haɗu, da alama sun gama biyan buƙatar junansu ne bacci ya kwashe su, sam babu sutura ajikinsu zir suke manne da juna kamar tip da tyre,
Wayar Jahan ce dake saman bedside table ta soma ringing taken waƙar Shape of you ta Ed shareed,”
Almost 3 times tana ringing an rasa wanda zai ɗauka cikinsu saboda daɗin bacci, har calling ɗin yayi rejecting, wani ya sake shigo wa da ƙarar gaske,
Ayaan ne yafarka cikin kasalalliyar murya ta wanda ke cikin shauƙi da jin bacci yace,”babe ur phone is ringing pls get up and pick the call, its disturbing my ears,” ya ƙare maganar yana bubbuga ƙafadar Jahan da hannunsa,
daker jahan ya buɗe idonsa da su kayi jawur ya kallesa da su kallon so da ƙauna yace “Honey bazaka gane bane, ko yatsana bana ji zan iya motsawa, wata irin kasala nake ji kasan fa mun jima muna yi,”
lumshe ido Ayaan yayi tare da ƴunƙurawa ya tashi shi, yakai hannu ya ɗauki wayar, jahan na cewa “Yawwa honey duba ka ga wane ɗan takurar ne, ke kira na,
natsuwa yayi yana dubawa, cikin tsananin tashin hankali yace “Jahan!!!! wlh Babban yaya ne ke kira !!!” yayi maganar da ƙarfin,
Ae tuni Jahan ya miƙe garas jin an ambaci sunan Babban yaya, jiki na rawa yasanya hannu ya karbe wayar dake hannun Ayaan yana kallon sunan da ya bayyana akan screen ɗin wayar,”
Wani irin kallo jahan ke bin Ayaan dashi cikin kashe murya ta masoya yace “Ayaan ka daina mun irin wannan abun Allah! kamin kowane irin wasa amma banda wannan,’
Tuntsirewa da dariya Ayaan yayi yana masa gwalo tare da cewa “Ni zaka cema wae kasala kake ji ko yatsa ba ka iya motsawa, shiyasa namaka wannan wasan,”
Pillow Jahan ya wawura dake gefensa ya kifa masa a fuska, nan suka shiga wasa da junansu,
A ƙarshe suka koma suka kwanta, ba tare da sun bibiyi kiran da ake masu ba, Jahan ne ya kwanta yayin da Ayaan ya kwantar da kansa a ƙirjinsa, shi kuma jahan ɗin yana shafa masa sumar kansa, cikin sanyin murya Ayaan yace “Jahan! anya kana tunanin ranar da asirin mu zai to nu? wane hukunci za’a mana,”
“Kisa,” kaitsaye Jahan ya bashi amsa, cikin tsananin tsoro Ayaan ya janye jikinsa daga na jahan ya tashi zaune saman gadon yana kallonsa a tsorace yace “Jahan dagaske kisa ne? Kashe mu za’ayi,”?
Tashi zaune shima Jahan yayi tare da cewa “Am serious Ayaan kai fa mai ilimi ne ! Sarai kasan hukuncin waɗanda ke aikata homo a addinin musulunci,! munsan da hakan kuma muke aikatawa tabbas duk ranar da Babban yaya yasani wlh kashe mu zaiyi bazae ƙyale mu ba, duk son da yake mana hakan bazae hana yaƙiyi mana hukuncin daya dace damuba domin nema mana sauƙi wurin Allah,”
Wasu irin hawaye ne ke zuba a fuskar Ayaan cikin tsananin tsoro yace “Jahan ni banso na mutu yanzu, banso na mutu ina aikata wannan mummunan zunubin wlh banso, Jahan kullum babban yayanmu yana ja mana kunne akan mu riƙe mutuncin mu, mu ji tsoran Allah mu guji sa6a mashi domin muyi kyakkyawan ƙarshe kuma mu tsira ranar gobe ƙiyama amma meyasa zamu zama na farko da zamu karya masa zuciya duk irin soyayyar da yake nuna mana”? cikin ƙunar rai Ayaan ke maganar yayin da idonsa ke zubar da hawaye masu raɗaɗi,
Jikin Jahan ya gama mutuwa shima idon nasa cike tab da hawaye yace “Ayaan yaya zamuyi? bamu da za6i, kaima kasan bada san ranmu muke aikatawa ba, Ayaan….kafi kowa sanin azaba da raɗaɗin da muke sha in har mu ka wuce 24 hours bamu sadu da junanmu ba,’
Cikin shesshekar kuka Jahan ke kora masa bayani, cikin sanyin murya ayaan yace “Babban yayan mu yazame mana komai arayuwa, ya sama mana rayuwar farin ciki, kullum yana ja mana kunne akan kar muja masa abun magana a family roƙonsa kenan amma mun gaza cika masa hakan, ko da yaushe dangin abbanmu suna cewa ƴa,ƴan momyn mu basu da kunya fitsararru ne, tabbas sunyi gaskiya tunda gashi nan, bamu tsoron Allah muna aikata zunubi irin wannan,…….” .
“Ya isa haka !!! Nace ya isa Ayaan , kadaina cewa bamu tsoran Allah, mu bayin Allah ne kuma masu tsananin tsoransa, Allah yana sane damu kuma asannu zai kawo mana ƙarshen matsalarmu, zai warware mana duk wata masifa dake damun mu,”
Jahan ne yayi wannan bayanin a yayin da ya komar da jikinsa ya kwanta tare da jan bedsheets a lullube jikinsa yana sharar kuka, .
Shima ayaan ya kifa kansa jikin pillow yana matsar kwalla, suna masu danasanin rayuwarsu da tazo musu a haka,” ????
‘Shin meke damun su TWINS ne ? da son ransu suke aikata hakan ko kuwa akwai wani abu a ƙasa ne? Nifa na rikice ina buƙatar ƙarin haske game da waɗannan bayin Allah,’ . ????

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button