ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

After some minutes duk sunyi shiru sai da arinƙa jefa wa juna murmushi ana satar kallon juna, rishi jin abun take tamkar a mafarki wai yau itace tare da ɗaya daga cikin ƴa'ƴan abban sojoji mai sauƙin kai haka, addu'arta shine Allah yasa sauran ma su kasance masu sauƙin kai a duk lokacin da Allah zai sa su gane cewa ita maca ce,"
Jin tayi masa shiru yasanya shi sake cewa "a matsayin me zaki ɗauke ni yanzu Aboki ko ɗan uwa"?
Sehrish tace "Da so samune duka biyun, I need both,'
Wani irin daɗi ne ya rufe junaid kamar kamar me, ji yake kamar ya rungume sehrish ajikinsa, farin cikinsa sam yagaza 6oyuwa,
Sun sha fira har wurin sallar magrib sannan suka tsagaita, sehrish ta maida gashin bakinta da hularta duka yadda suke sannan suka kama hanya atare suna ƙara tattaunawa kamar karsu rabu da juna, sai da rishi ta fara shiga ciki da jimawa, sannan junaid ya shiga saboda kar a gansu atare,
(Guys nima fa sun burgeni wlh, haɗuwarnan ta rishi da junaid ta tafi dani)????
Dama nace akwai annoucement to gashi, Littafin nan littafi ne mai yawan gaske Kuma idan nace zan datse shi to tabbas zan lalata littafin daɗinshi zai ragu sosae bama zai yi tsari ba don haka Part 3 of this Novel will be paid Book, abubuwa da dama waɗanda basai na faɗa ba Ina fata zaku goyi bayana, Nasan duk ranar dana ce na dakata da rubutun littafin nan babu wanda zaiji daɗi acikin readers ɗinshi don haka muyiwa juna Adalci, Sorry 4 the late annoucement ????????
Ci gaba
Zuba musu ido goggon katsina tayi tana kallonsu ko kyaftawa babu, kamar wadda tayi gamo da aljanu,
Zaune suke suna facing ɗinta sun matse juna cike da tsoran abunda tsohuwar zata ce musu,
Ta jima da farka wa daga bacci amma batasan dasu acikin gidan ba, saboda suna can cikin ɗakin saude suna bacci, ita kuma sauden bata sanar da ita cewa Omar ya sa an kawo wasu ƴara ba sai yanzu bayan sallar magrib ta ke sanar da ita, shine tasa ta kira mata yaran tagansu,”
“Jahad me yasa take kallon mu? bata son mu ko? Korar mu zatayi ko”? Hosana ce tayi ƙasa ƙasa da murya tana raɗawa Jahad a kunne,
Jahad tace “nima bansani ba, amma ina tsoran kartace bata son mu, in ta kore mu, ina zamu sa rayuwarmu? Cikin raɗa suke maganar tasu, duk sai da suka gama raɗe-raɗen sannan su kaji goggon katsina ta fashe da dariya tare da cewa
“kun ta6a jin inda uwa ta guji ƴa’ƴanta !? Ku fa jinina ne, ƴa’ƴan abusufyan ae ƴa’ƴana ne halak malak,”
Kallon juna su kayi jin abunda tsohuwartace, atare suka hada baki tare da cewa “ABUSUFYAN kuma wanene shi ? mu bamu son shi ba,’
ɗaure fuska goggon katsina tayi tare da cewa “Bansan shashanci in ma zolayata ku keyi to ku daina, ni ba amun irin wannan wasan yanzu na burkice, ku faɗamin gaskiya ku ba ƴa’ƴan abusufyan bane,?
Babu wasa a fuskarta tayi tambayar,
hankali atashe suka ce “wlh bamu son shi ba, bamu son wa kike magana akai ba, mu yau muka zo gidan nan,”
Sassauta murya goggon katsina tayi tare da cewa”kuna nufin ku ba ƴa’ƴan abusufyan bane ? Ni zaku raina wa hankali ko? Kubar ganin nafara tsufa da hankali na wlh Wannan furfurar da kuke gani akaina, bata tsufa bace ta arziƙi ce,” ????
ta yi maganar tana hararansu, cikin tsananin tashin hankali jahad tace “wlh goggo gaskiya muke faɗa miki, bamu son shi ba, mu ba ƴa’ƴansa bane,”
Jin yadda jahad ta karyatata yasa ta fashe wa da matsanancin kuka, zaro ido su kayi ganin tsohuwar na sharar kwalla, kuka fa sosai hada jan majina tana faɗin “saboda na fara tsufa kke gudu na ko? ban ta6a tunanin ƴa’ƴan abusufyan zasu guje ni ba, wlh sai na kirasa a waya nasanar masa tashin kunyar da kukayi wa goggonsa wlh baxai ƙyale ku ba…’
tayi maganar tana shesshekar kuka abun kamar a mafarki su hosana da jahad suke kallon lamarin,
Jin kukan goggo yasa saude fitowa daga kitchen hankali a tashe karaso wa tayi tana faɗin “Subhanallahi goggonmu me nake gani haka kamar kuka a idonki,’
Ƙara fashe wa da kuka gaggon katsina tayi tare da cewa ” saudatu dan Allah waɗannan ba ƴa’ƴan abusufyan bane? tayi maganar tana nuna su Hosana da hannunta,
Sakin baki Saude tayi galala cikin mamakin rigimar goggon katsina, girgixa kai tayi tare da cewa ” wlh narasa meke damunki goggo ! Sarai fa kinsan cewa Uncle abusufyan bai ta6a aure ba ko? wai yaushe ma yayi budurwar ballantana ma aure har akai ga ƴa’ƴa, anya goggo kina shan maganinki akai akai’?
Miƙewa tsaye goggon tayi idonta cike taf da kwalla fuskarta a damuje tasa idonta cikin na saude tace” saudatu hada ke za’a ƙaryatani ko? ke ma kallon zararriya kike mun ko? saudatu da hankali na wlh, waɗannan yaran ƴa’ƴan abunsufyan ne, Jini na ne ina ji ajiki na, dan Allah kudaina mun yawo da hankali wlh zuciyata zata iya bugawa in mutu a wurinnan,”
Goggo tayi maganar cikin ƙunar rai da jin ɗaci aranta saboda ita harga Allah ta tabbatarwa kanta cewa tagwayen nan ƴa’ƴan abusufyan ne, mutun da bai ta6a aure ba, hasalima ma ba a nigeria yake zaune ba gaba ɗaya,
Shiru saude tayi tana kallon goggo dake ta faman kuka kamar ƙaramar yarinya aranta tace “tabbas goggo fa hauka ya tashi gadan gadan, don haka a kunnan babban likita dole nasanar mishi a bincika kwakwalwarta in ba haka ba kawai daga ganin yara sai kice wai ƴa’ƴan Uncle sufyan ne, yau yau ɗinnan fa yaran nan suka fara zuwa gidan nan tab lallai akwai matsala awurin nan……..”, muryar goggonce ta katse ta da cewa
“Saudatu kinyi shuru baki ce komai ba? ƴa’ƴan abusufyan ne ko?
Yarfa hannu saude tayi saboda tama rasa amsar da zata bata,
Jinjina kai goggon katsina tayi tare da mayar da idonta kansu hosana da jahad waɗanda jikinsu keta faman kerma saboda tsoran tsohuwar don sun lura tana da ta6in hankali,
Rai a6ace tace “Wlh ku ƴa’ƴan abusufyan ne !! Ni zakuyiwa karya don kutmar ubanku !! Kunci buhun ubanku ƴan kan uba
!!! ,
Hankali atashe su hosana ke kallonta, saude kuwa aza hannu tayi akai tana faɗin”goggo dan Allah kidaina !! Kidaina zaginsu mana akan abunda basu sani baaa……
tunkan ta ida goggon tasa hannu ta buge mata baki, dafe baki sauden tayi don taji zafin bugun,
Ci gaba da magana goggon tayi a birkice tana kuka, ” Ae dama nasani ba wanda zai goyi bayana akan magana ta, amma ni nasani wlh ku ƴa’ƴan ZAINABU ne, dama haka uwarku take kamar ku ɗinnan, shegen taurin kai da kafiyar tsiya, kunnan ta kamar na zomo, fitinanniyar yarinya ƙiri-ƙiri ta guji jini na, dama sai da nace mata cikin jikinta na Abusufyan ne amma taƙi yarda ae dama nace mata jiki magayi amma taƙii ji, kunnan ƙashi ko ae ynx nasan taji jiki bawan Allah bai mata komai ba amma taƙisa, wlh cikinsa ne ku ƴa’ƴansa ne amma kunƙaryata ni, ga falo falon kunnuwanku nan irin na abusufyan shima dayake baijin maganata kangararre ne yaƙi jin magana ae gashi nan……
Zuba kawae goggon katsina takeyi ba ƙaƙƙautawa kai kace radiyon da bata da saiti, notikan kanta sun kwance sai faman zazzaga musu bala’e take yi, tana yi musu magana akan mutanen da basu san da zamansu ba,
tashi su kayi atare su ka tsaya suna kallonta haƙika sun tsorata da tsohuwar tuni idonsu ya cicciko da kwalla,
Goggon katsina bata dakata da surutun ba har sai da Saude tace “goggon kiyi hakuri dan Allah, nima na yarda cewa su ƴa’ƴan Uncle sufyan ne, sai yanzu na ƙara lura da kamannin nasu dagaske ne abunda kika faɗa,
saude na gama faɗan maganar ta kalli su hosana tayi musu alamar su amince suma da maganarta don asamu ta lafa,
Cikin sauri suka zube saman guiwowinsu agabanta tare da cewa “Dan Allah kiyi haƙuri goggonmu, munyi miki laifi, tabbas mu jininki ne mu ƴa’ƴan abusufyan ɗinki ne, ki yafe mana munsa kin zubda hawayenki,”
Sanyi goggo taji aranta dama ita burinta kawai su amince cewa su ya’yansa ne, hannu tasa tana share hawayenta, bayan ta kammala ta miƙa hannayenta tare da ruko nasu ta tsayar dasu tsaye fuskarta da murmushi sai kace ba wadda tagama sharbar kuka tace ” Alhamdulillah har hankali na ya kwanta ynx, amma fa kun wahalar da gaggonku sosae kun sani ina ta faman zubda hawaye na, da ace abusufyan na nan kuma yasan abunda ku kayi ma goggonsa tabbas sai ya muku dukan tsiya” ,
Sunnar da kai su kayi tare da cewa “ayi mana afuwa goggonmu, bazamu ƙara ba insha Allah,”
Murmushi tasaki tare da cewa ” ku koma kuzauna ƴa’ƴana, yanzun nan zan kira mahaifinku a waya ku gaisa,” ????♀️????♀️????♀️