ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE
Jikin sehrish ya gama yin sanyi , bin jikinta tayi da kallo tasha kayan maza , ga uban burgujejan wandon da tasa kamar zata tashi sama, kara kankame jakar dake hannunta tayi wacce ke kumshe da y’an kayan da hajjaju ta bata kyauta ,
Hatta purse din hajjaju sai da suka bincika , zuciyar sehrish sai bugawa takeyi tunanin ta masu gadi sun kasance haka da ban tsoro ina ga y’ay’an gidan da taji ance they’re all soldiers ????
Muryar sojancce ta ratsa kunnanta “lemme see your bag “! cikin sauri ta mika mar jakan , zazzago kayan ciki yayi kasa yana duddubawa , trousers ne da riguna na maza , da hijabai da ta kudundunesu saboda sallah , bayan ya gama checking dinsu ya dago ya zuba mata ido yana kallonta , nan take taji fitsari ya cika mata mararta , sunnar da kanta tayi kasa , jikinta na rawa , Ji tayi yasa hannunsa ya dankwashi kanta yana cewa “mara kunya kana namiji baka iyasa Cap akan ka , kai ga d’an daudu ko ? sai dai kasa abu na mata ka nannade kai kamar wani limamin masallaci “,
Karasa maganar yyi tare da wurga mata jakar , sannan ya juya ya tafi , hannu tasa ta dafe wurin don taji zafin rankwashinta da yayi mata wannan gabjejan hannun nasa , dole ita ta zukunna ta kwashe kayanta daya zubar a kasa ,
A karshe dai Sun sami shiga ciki , a jiyar zuciya Sehrish tasaki , time dinda motar tasu ta wuce babban gate din ta shantalelen titin da zai kai ka can cikin gidan ,
A hankali take bin ko ina da kallo ta cikin glass din motan , tana kara jaddada haduwar ginin , taga wurare daban daban masu ban sha’awa , sai ta dinga tunanin cewa kodai tabar nigeria ne domin daga inda kasa kafarka cikin gidan kamar ka fita daga 9ja ne ????
ihu da sowar da taji ne yasa takai idonta wurin , y’an matasan samari ne kyawawan gaske suke wasan football , acikin playing field n gdn , gwanin burgewa tabisu da kallo har sai da suka wuce su ,
A wurin da aka ware na parking space , hajjaju ta tsaida motarsu , wurin cike yake da motocinsu Na gayu ga kuma jibjibgan motocin irin na sojojin man
Waigawa hajjau tayi ta kalle ta tace “sehrish ki natsu dan Allah in mun shiga kada ki jamun , kuma kada ki manta sunan ki tukur daga ynx ,” cike da gamsuwa ta masa mata da “Toh”
Fitowa sukayi daga motan suka miki hanyar data zata sada ka da babban falon gidan , tuni sehrish ta raina kanta , tamkar karta taka kasan tiles din take ji saboda wani irin design ne mai daukar ido , duk yadda ka taka saiya bada sauti kwas kwas ,
Komai na cikin living room din mai tsadar gske ne , kana gani kasan bana nan bane , an kawata shi da expensive furnitures , wasu hamshan royal sofa ne aciki , set shida ne a jere , ko da ido ka kallesu kasan zasuyi laushi da dadin zama , duk yawansu basu cike falon ba saboda girmansa ya isa a gina madai madaici gida acikinsa,
Komai da ake bukata acikin falo akwaisa sai da ba tarkacen nan na hauka komai a natse ,
Bin ceiling din tayi da kallo ba irin rufin da tasaba gani bane , wannan na glass , acikinsa akwai light bulbs masu haske wurin ,
Hankalin hajjaju ba karamin kwanciya yayi ba ganin falon tsit ba kowai sai sanyin a.c dake ratsa sassan jikin mutun, dama zullumin ta ace wadannan sojojin na nan ,
Ruko hannun sehrish tayi wadda hankalinta ke kan twin stairs din da tagani wato tagwayen bene guda biyu wadanda zasu kai ka upstairs, tsantsararrun gaske ,
Sehrish tace “hajiya naji tsit ko ba kowa ne ? hajjaju tace “ina ga duk suna wurin aiki , mu samu wuri mu zauna mu jira wata’kil mai aikinsu na nan ,”
Suna kokarin zama suka ji takon takalmi daga left dinsu , karfaffar maca ce irin giantess dinnan , tana da hasken fata , jikinta na sanye da doguwar riga ta atampa har kasa ta kashe daurin d’an kwalinta , tana ganin hajjaju ce ta saki fara’a tana fadin “me nake gani kamar hajjaju makkatin “? murmushi hajjaju tasaki tare da cewa “kwarai kuwa nice AZUMI ashe kina ciki , nayi tunanin ba kowa ciki ne ,”
Karaso wa tayi inda hajjaju take tayi hugging dinta tana cewa ” I really missed u alot hajjaju kin boye mana nayi expecting din bakya kasar ne ,” sakin juna sukayi hajjaju tana dariya tace “Ina nan mana ina zani an gaya miki ynx barin kasar nan sauki ne yadda komai ke kara farashi , yar dubai dinnan danake zuwa kamar hauka ynx nadaina saboda rashin kudi ,”
Murmushi azmi tasaki , tare da nuna masu wurin zama tace “bismillah ku zauna bari na shiga na kawo muku abin sha , firar zata fi dadi idan kuka jika makoshinku ,
tana gama fadan hakan tajuya ta nufi hanyar da zata kai ka kitchen dinsu , zama sukayi a tare saman 3 seater , har lokacin sehrish na makale da yar jakarta a kirjinta , sai karewa falon kallo takeyi tana jinjina kyansa , wai itace zata rayu a cikin katafaren gidannan , wayyo dadi boye farin cikinta kawai take yi , ta wani bangaren kuwa hankalinta a tashe yake , saboda batasan ya rayuwarta zata kasance ba a matsayinta na yar basaja , matsayin namiji a gidan sojoji ,
Dawowa azumi tayi hannunta dauke da tray , plate ne mai dauke da snacks , sai 2 cups da jug , a jiye su tayi a sman table sannan ta janyo shi izuwa gabansu ta ajiye ,
Koma tayi tazauna tana murmushi , Sehrish kuwa sai kallon matar take yi har taji ta burgeta saboda tana son mutum mai fara’a ,
Lemu ne a cikin jug din zuba musu hajjaju tayi ta mika ma sehrish , cikin sauri ta karba dama kishi take ji , kurbarsa tayi wani irin sanyi ya ratsa ta ga dadin gaske ,
Azumi ta bi ta da kallo cikin mamaki tace “in ce ko wannan ne d’an aikin da akace za’a kawo mana”? hajjaju ta danyi guntun murmushi tace “eh shine sunan shi tukur kwararre ne wurin iya sarrafa abinci ,” saboda jin karyar da hajjaju ta shirgo akanta yasa ta kusa fetsar da lemun da takurba a bakinta , abunda ya kusa sata ta shake shine da ta ce kwararrene wurin iya sarrafa abincin shin yaushe ta son da wannan ?
Sauraron hajjaju ta ci gaba dayi jin tana introducing dinta a wurin azumi ” yaro ne mai matukar basira ga wayau , zakiji dadin yin aiki dashi ,” takarsa maganar tare da ajiye cup din dake a hannunta saman table din gabanta , sannan ta kalli sehrish tace “tukur wannan itace azumi , itama y’ar aiki ce a gidannan amma taji ssae tana kula da yaran gidan hakan yasa ta zama tamkar uwa agaresu , ina fata zakuji dadin yin aiki da juna ,”
Dakyar sehrish ta kakaro murmushin dole tace “Insha Allah hajiya ,”
Ita kadai tasan halin da ta shiga , wannan zaman da tayi ji ta , kamar ta dosa na ass dinta a saman wuta , saboda tsabagen tsoro , A ranta sai maimaita kalmar ‘yaya goma sha takwas kuma duk sojoji take yi ,
Azumi ta janye idonta daga kan sehrish (tukur) ta mayar da idonta kan hajjaju tare da cewa “am inaso na tambaye ki tundazu maganar ke shigemin meyasa kika daina leko mu bayan ina da tabbacin cewa kina zuwa abuja zuwane kawae ke baki yi ,”
Murmushi hajjaju tayi tare da yin yar dariya tace “ai dole zuwa gidannan ko jaraba ! oh kin manta Abunda ya faru last time dana zo ko ? Ina wannan BABBAN YAYAN nan nasu wani mai shegen kyau tubarkalla kamar d’an sarkin aljanu mai kirar zakunan nan ,” dariya azumi tayi tare da cewa “wai wa kike nufi cikinsu , kinsan suna dayawa , akwai major , akwai Captain ga janar , akwai Marshall ga kuma Canal da sauransu , kowa da sunan da ake kiransa ” takarasa maganar tana kallonta