ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

BossLady❤️ Inaso naji ta bakin ku game da annoucement ɗina nasan kowa ya karanta, sannan comment akan page ɗin yau ????????????
????????????ABBAN SOJOJI????????????
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ????❤️
Mallakin
*????Hafsat Bature Moh'd*????
~BossLady~????
Page 81-82 part 2
Meaning of name sehrish is an arabic name, ma’anar sa kuma Glamorous Personality ????
Har haɗa baki suke yi wurin cewa “mahifinmu kuma ! A waya !?.
Da ƴar dariya a fuskarta tace”Eh mana, ae kullum sai ya kira ni mungaisa,’ tayi maganar ayayin da ta kama hanyar zuwa bedroom ɗinta don ta ɗauko wayarta,
Hannu suka aza akai alamar sun shiga uku, ita kanta saude tama rasa me zatayi abun ya ɗaure mata kai, lamarin goggo sai addu’a tsufanta da rigima yazo mata,
“Kada ku damu kunji kawai, ku kwantar da hankalin ku, in ta kawo muku wayar ku amsa ku gaisa dashi amatsayin mahaifinku, Uncle sufyan ya riga da yasan rigimar Goggonmu wayayye ne shi zai fahimce ku,”
Saude ce tayi musu wannan bayanin, jiki amace suka amsa mata da cewa “Toh,”
Sannan ta juya ta koma kitchen saboda tabar girki saman gas,
Zuru su kayi suna jiran zuwan gaggon katsina da waya, babban tashin hankalinsu yarda zasuyi waya da mutumin da goggo ta ƙaƙaba musu a matsayin mahaifinsu wanda basu ta6a gani ba kuma basu san kowanene shi ba,”
suna nan zaune zuciyarsu nata bugawa sai ga goggo ta fito daga ɗakinta, hannunta riƙe da waya sai faman zabga murmushi take yi,
Koda su ka ganta gabansu ne ya faɗi rass don su a tsorace suke,
Miƙa musu wayar tayi tare da cewa “Maza ga mahaifinku nan akan layi kuyi masa magana,”
Kamar bazasu kar6a ba haka su kayi daker Jahad tasa hannu ta karbi wayar goggon tare da karawa a kunnanta tace ,”Assalamu alaikum,”
daga can 6angaren taji wata natsattsiyar murya ta amsa mata da cewa “Wa’alaikum salam,”
sai da jahad tayi jimmmm kafin ta daure ta cije tace “Abba Jahad ce ɗiyarka, ina fata kana cikin koshin lpy,”
Abusufyan ya amsa mata da cewa “lpy lou Alhamdulillah My daughter, kin yi missing ɗin abbanki kuwa,”? Yanda yayi maganar ba ƙaramin kashe ma jahad jiki yayi ba, sai kawai taji hawaye na ƙokarin zubo mata,
Murya na rawa tace “Nayi missing ɗinka sosae abbana, ina kewarka,” tayi maganar ayayin da take dab da fashe wa da kuka, cikin sauri tace “Abbana ga hosana ku gaisa, itama tayi kewarka sosae,”
“Okey bata wayar,” ya umarce ta,
Miƙawa hosana wayar tayi jikinta na kerma, hannu hosana tasanya ta karbi wayar tare da karawa a kunnata, duk goggo na tsaye tana kallonsu sai faman murmushi take yi, (ta haɗa Bomb)
Tashi jahad tayi cikin sauri ta wuce bedroom ɗin saude tana shesshekar kuka tana idasa shiga ɗakin ta faɗa saman gado tare da fashe wa da matsanancin kuka, bakomai bane ya karya mata zuciya ba face tunda suke arayuwa basu ta6a sanin daɗin soyayyar mahaifi ba ga Uban amma bai da amfani,”
A can kuwa tun da hosana tasanya wayar a kunnanta tace “Abbana dagaske kaine mahaifin mu kamar yadda goggo ta faɗa,”
On the other hand abusufyan yace “My daughter are u doubting abt ur father? nasan kinyi kewata ne shiyasanya kike kokwanto akaina,”
aikuwa jin ya tabbatar mata da cewa shi mahaifinsu ne yasanya ta fashe masa da kuka tare da cewa “dama nasani kaine mahaifinmu, ba wancen mugun ba, sai da nace ma Oumma mu bamu kama dashi mummunane shi mai baƙar zuciya amma taƙi yarda, ni nasani ba abban mu bane, babu uban da zaiyi wa ƴa’ƴansa haka, kaine mahaifinmu,……”
Katseta yayi tare da cewa “Silent pls, sorry my daughter bana fahimtar zancen ki i was busy now, zan kira anjima,’
yana gama faɗan hakan ya kashe wayar saboda baisan inda zancen nata ya dosa ba, shi dai kawae ya amsa kira ne kamar yadda goggonsu ta sanar dashi cewa ƴa,ƴanshi sun zo, sarai yasan rigimarta shiyasa yabisu a hakan,
Ganin ya katse kiran yasa hosana fashewa da kuka, wurgi tayi da wayar goggon saman kujerar sannan itama ta miƙe tana ci gaba kuka ta wuce ɗakin saude,
Jikin goggo yayi sanyi, ita a tunaninta abusufyan bai kula da yaransa shiyasa suke kuka, don haka taci alwashin zata sashi dole saiya zo nigeria ya ɗauki ƴa’ƴansa ya koma dasu can qasar da yake zaune, a ranta tana cewa “in banda shiririta irin ta abusufyan ka kama hanya ka tafi ƙasar Turƙiya kabar yara cikin damuwa, gashi nan sai faman kuka suke yi, Allah ni da kai ne, saina sanar wa AMMI halin da ake ciki,
Ta idasa maganar tata tare da sa hannu ta ɗauki wayarta ta wuce dakinta tana ci gaba da surfa bala’e akan rashin adalcin abusufyan,
……………………………………..SEHRISH…………………….
tun da suka koma ciki take jin zuciyarta wasai, hankalinta kuma ya ƙara kwanciya yanzu,
Gaba ɗaya matasan gidan sun kammala dinner ɗinsu kowa ya koma bedroom ɗinsa,
Babu kowa ita kaɗae ya rage ta kai wa Babban yayansu dinner ɗinsa, shine kaiwa bai sauko yaci ba, dama azmee tace sometimes kai masa ake a part ɗinsa,
Tsoranta kar yayi mata abunda yayi mata da safe, wato da yayi watsi da tray ɗin hannunta,
A natse take tafiya zuciyarta na ɗar ɗar hai ta haye upstairs ta wuce part ɗinsa da sallama ta shiga babu kowa aciki, agyare yake tsaf haske ta ko’ina ga ni’ima acikin palor insa,
A hankali tasanya kafa tashiga ta ƙarasa gaban table ɗinsa ta ajiye tray ɗin ta tsaya riqe da ƙugu tana jiran fitowarsa bin ko’ina take da kallo tana ƙara jinjinawa haɗuwarsaa, .
bakomai ke fisgarta ba fa ce sanyayyan ƙamshin dake tashi tana burin wata rana ta samu damar da za ta ɗan miƙe ƙafa a saman 3 seater ɗinsa ta kwanta, ????????
Sauko ƙafarsa yayi fara tass babu takalmi a kafar jikinsa na sanye da sleeping dress red color masu laushin gaske, jikinsu akwai zanene flowers masu kyau, riga da wando ne abunka ga handsome stylish man ga kira sun bi shape ɗin jikinsa kai kace don shi akayi kayan, kyau kam ba’a magana ku kun sani ae,
tana cikin wannan kalle kallen idonta ya hango mata shi to fa nan take ta rasa duk wani karsashi na jikinta, bin shi kawai take da kallo, cike da wannan tafiyar tasa ta nigogin basawa ya karaso hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa, halittar kyawunsa ta kara fitowa sosai daga saman rigar ƙirjinsa a buɗe yake farar fatar sa ta bayyana muraran,
Sai kamshi jikinsa yake kamar wanda aka tsamo daga kogin turare,
Ga sumar nan tasha gyara sai salƙi take tana ɗaukar ido,
Zama yayi yana naɗe hannun rigarsa,
Sai da rishi ta dai dai natsuwarta sannan tace “Barka da fitowa Babban yaya,”
“Yawwa,” ya bata amsa a takaice,
Har cikin ranta jin daɗin muryarsa take saboda yanayin yadda hausarshi ke fita irin ta wanda bai ƙware ba,
Cikin girmamawa sehrish ta sake cewa “Me kake buƙata na zuba maka,’?
ta tamabaya saboda kartayi ba dai-dai ba,
“Abun da ya dace,” ya bata amsa,
Murmushi tasaki tana kallon face ɗinsi musamman gashin girarshi da eye lashes ɗinsa,
Hannu tasa ta buɗe plate ɗinda ke ɗauke da friend meat (tsiran nama) yasha kayan ƙamsi yaji mai yaji komai,
tura mishi tayi agabansa sannan ta ɗauki bottle milk ta zuba mishi a glass cup ta ajiye masa,
bayan ta gama ta ɗan ja da baya tana ƙare masa kallo, yanayin yadda yake ɗaukar tsiren yana turawa a bakinsa ba ƙaramin kyau yayi mata, ji take ina ma da hali ta bashi abaki saboda ta sauƙaƙe mishi wahalar ,????
Wayar sa ce dake ajiye cikin bedroom ɗinsa ta soma ringing da sautin gaske taken wakar nan ta Imran khan (Satisfya) wadda yake cewa “am rider,provider, bring the heat girl i will bring the fire,”
gyaran murya yayi tare da cewa “My phone,” cikin sauri sehrish ta wuce bedroom ɗinsa asaman pillow ta samu wayar ɗauka tayi jiki na rawa kamar ta riƙe bomb haka take ji, ta riƙe wayar manya ba,
Fitowa tayi da sauri taje ta miƙa masa, sai da ya fara cirar tissue ya goge hannunsa sannan ya sake tearing ɗin wani acikin hannunsa sannan ya miƙa hannu ya karbi wayar tare da picking call ɗin ya kara a kunnansa,
Zuru sehrish tayi tana jira taji mai zai tattauna acikin wayar, sai dai kash cikin harshen spanish yake magana kalma ɗaya ce sehrish ta tsinta, da taji yace “Mom,”
Jinjina kai tayi aranta tace “Ina ji da mamansa yake waya, ashe mahaifiyarsu na nan, ko tana ina ne ita?
ta, tambayi kanta ba amsa,
babban burinta yanzu shine su haɗa ido dashi atlease yasan da zamanta sam bata tunanin hakan zai iya janyo mata matsala acikin gidan,
A tunanin sehrish SGR bai ta6a kallota ba, tabbas hakane amma rana ta farko da tayi masa 6arin fruits a bedroom ɗinsa, ya hangeta ta cikin mirror ya ganta a matsayin namiji tsaye cikin fargaba a time ɗin, duk da bai shaida kamannin fuskarba amma yasan cewa namiji ne mai kula dashi wato ɗan aikinsu,’
Kammala wayar yayi tare da mayar da wayar ya ajiye gefensa, yaci gaba da cin dinner ɗinsa sehrish na saving ɗinshi in ya kammala da wannan ta zuba mishi wancan haka suke abun nasu,
Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana kallon sumar kanshi ba ƙaramin jan hankalinta Sgr yake yi ba, hakan yasa bata gajiya da tsayuwarda take yi na saving ɗinshi tamkar mirror haka ya koma mata, tana cikin masa wannan kallon muryarsa ta ratsa ta da cewa “Kallon ya isa haka, ko saina shaƙe ne,”
Cikin sauri da jin kunya sehrish ta mayar da idonta ƙasa tana mai mamakin yarda akai Sgr yasan cewa tana kallonsaa murmushi tasaki saboda jin daɗin mgnarsa tabbas tana ji aranta cewa yana da sauƙin kai he’s not arrogant kamar yaddda ta ɗauka,
…………………. ..,,……………………………….