ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

A tsiyace ya shigo da motar layin gidan a dai dai gate ɗin gidan ya dakatar da ita, ya shiga buga uban horn kamar zai tada motar gaba ɗaya saboda karar da take yi,
“Kai!! uban waye ke mana horn haka,”? ɗaya daga cikin sojojin dake gadin gidan ne ya tambaya da ɗaga murya, akwai yasamu amsa dai dai dashi sai ji yayi ance “Ubanka ne kazo ka duba,”
Abun ya basu mamaki aiko afusace sojojin nan suka tunkaro motar kamar wasu zakuna har haɗa hannu suke wurin buga glass ɗin motar tare da cewa “Come out !! ,”
“Ae basai kunbar umarnin na fito ba, ɗan tasha ne ni dai dai daku,”
Zuge glass ɗin motar yayi tare da sa hannu ya cire ƙumeman glass ɗin dake manne a face ɗinsa yace “Akwai magana,”?
Shiru su kayi dama ransu ya basu cewa shegen ne, ae duk duniya ba mai musu haka sai shi tantirin ɗan duniya,
Bama cikin hayyacinsa yake ba ae mafi yawancin lokaci a buge yake yasha yasha har takai masa karo,”
dogon tsoki ya buga tare da cewa “abani hanya na wuce kona bi takan mutun ba ruwana, kuma in na kashe mutun na kashe banza abanzance,”
Ransu yayi mugun 6aci a dole suka matsa mishi ya shige babban gate ɗin gidan da motarsa yana raira waƙa,”
Parking ɗin motarsa yayi sannan ya fito hannunsa riƙe da kwalbar giya, jikinsa na sanye da t-shirt baƙa sai wando crazy jeans ɗinnan ne, wani irin ɗan iskan aski ne akansa na shaiɗanu jigunannun ƴan duniya gefe da gefe an aske sumar kan, tsakiya kuma an mikar da wata tsaye ba ladabi, wuyansa na sanye da sarƙa yayin da kunnansa ke manna da earrings kai kace ba musulmi ba, saboda kwata kwata bai kama da musulmai ma, don kyau fa akwai kyau kana ganinsa ka ga bafullatani sak, duk da ba fari bane sosai amma yana da hasken fata mai kyau, yana da tsaga ta fulani agefen fuskarsa,
daker yaja ƙafarsa izuwa cikin babban falon gidan babu kowa aciki wayam, ɗaga murya yayi yadda kowa zaiji sa yace “NADAWO !!!! Hhhhhhhhh Woooo !! Yaro ya dawo gidan Ubansa !!! Abba !! Gani fa nadawo !! ɗanka HAROON ya iso dira ta kenan na ƙaro sabon wulaƙanci buhu buhu hhhh,
Gaba ɗaya hayaniyarsa ta cika musu kunne kamar zararre haka yadinga sambatu,
Ba arziƙi suka soma fitowa kowa jikinsa sanye da kayan bacci kanal yousouf ne yafara fito wa yana buga tsoki sai Khaleed da jabeer da irfan kowa ido cike da jin bacci ya katse musu baccinsu, atare twins suka sauko daga upstairs hannunsu cikin na juna sai hamma suke yi,,
Abba ma tare da junaid suka fito sanye cikin phyjamas hannunsu cikin na juna, kowa sai faman buga tsoki yake yi a ƙuntace, tun da suka ga Commender haroon gabansu ya faɗi hankalinsu ya tashi ainin, sam babu mai farin ciki da zuwanshi duk da kasancewarshi ɗan uwansu na jininsu amma munanan ɗabi’unsa da halayyarsa tasa sun tsane shi sbd mugune na bugawa ajarida,
Cike da takaici suke kallonsa kwashewa ya sake yi da dariya tare da cewa” ƙananin ƴan iska sun bayyana ga kuma fararen balbelu,” yayi maganar yana nuna su Twins da fawan da hannu ɗaure fuska su kayi har time ɗin ba wanda ya tanka masa binsa kawai suke da ido,
“Kutmelisiiii! Ni kuka maida shashasha ina magana kowa ya zubamin ido wato ga zautacce ko?baku farin ciki da zuwana ne, ae nayi tunanin ina zuwa zaku watso aguje kamar karnuka ku rungumeni ku sunbace ni muuuaaah a baki na,’ cike da futsara Haroon ke musu magana baya jin kunyar Abbansu,
Gaba ɗaya duk wannan suratan da Haroon yake yi a kunnansa kaf ya gama fusata yagama hasala, aiko a harzuƙe ya ƴunkura tamkar zaki yabi ta gefen Sehrish ya wuce ita kanta ta tsorata sosai ganin yadda Sgr ya fusata,
A wani irin slow sauri sauri yake tattakowa izuwa downstairs ɗin, yana idasa sauko wa kai tsaye inda haroon yake tsaye riqe da beer a hannunsa ya tunkara,
Kanal yousouf ne kawai ya lura dashi wani shu’umin murmushi yasoma saki saboda yasan mai zai faru,
Haroon na cikin wannan sambatun baiyi wani aune ba yaji saukar wasu zafafan maruka ajere saman kuncinsa,
Sai gashi ƙasa baje saman tiles idonsa na facing sama, wato wasu irin black stars yagani a ƙwayar idonsa masu wutsiya, kowa dake wurin bakinsa kumshe da dariya,
Sgr kuwa kara naɗe hannun rigarsa yake yi,
daker haroon ke kallonsa muryarsa na rawa yace “Ya Allah ka yafemun in zunubi nayi ka haɗani da wannan Ifritun minal jinnin, wlh danasan cewa kana acikin gidan da ba abunda zai kawo ni, Abba mai yasa baka sanar dani cewa Babban yaya na cikin gidan nan ba…? Yayi tambaye agalabaice har lokacin bai samu ya miƙe ba yana daka kwancen yake sambatun nasa idonsa na kallon ceilling,
mayar da hannu Sgr yayi ya damƙi wuyan rigar haroon da hannu guda ya ɗago shi tare da Buga shi ƙasa ya ƙife a susuce, shin wai ina kwalbar giyar dake hannun haroon ae tuni tayi gefe guda ta tarwatse,
Ganin Sgr na ƙoƙarin sake kai hannu yakaiwa haroon wani naushin yasanya abban su cikin sauri ya riƙo hannusa yana cewa “Ya isa haka pls rabu dashi ae yaji jiki,”
Jinjina kai Babban yayan yayi yana cije lips ɗinsa da ace abba yabarsa wannan naushin da yaso yakaiwa haroon da to tabbas sai yayi jinya a gadon asibiti,
ɗagowa haroon yayi ido luhu luhu yana kallon babban yayan nasu murya na rawa yace “Yanzu babban yayan mu don rashin imani ka daddage ka dunkule wannan hannun naka ƙirar samudawa da adawa bakaji komai ba ka jibge ni agaban ƙanne na,”? yayi maganar akasalance yana kallonsa,
Wato bai daddara ba rae abace sgr yace “kai wai waye ya kawo wannan ɗan iskan acikin gidan nan !?
“Da ƙafafuna nazo,” haroon ya bashi amsa a raunane, mayar da idonsa yayi akan haroon yana huci in ya biyewa haroon to tabbas zai iya halaka shi a wurin nan, don shi bakinsa bai mutuwa ana bugunsa yana magana sai dae akashe shi,
In kina so ki gode mun kiyimun share na novel ɗina ???? Kar a Manta da Comment ????????????????????????ABBAN SOJOJI????????????
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭ ﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ❤️????
Episode 83-84
Hafsat Bature Moh’d
Meaning of Name Rafayet, arabic name ne, kuma sunane na Mace da Namiji both suna amfani dashi, Ma’anarshi Ur highness????,sublimityhigh rank*,
*power*????
Dariya kawai junaid ke saki bama shi kadae ba hadasu irfan da sauransu in ka cire Kanal yusif da fuskarsa ke adaure shida babban yayansu,
duk wanda abun dake faruwa a kunnan sehrish tun da babban yayan nasu ya fito itama tabiyo bayansa, tana 6oye abayansa shi kansa baisan da mutun ba, sai dae ta leƙo ta saci kallon haroon dake baje yana sambatu ta takoma ta boye kanta, hakanan taji bai burgeta ba tunda taga fuskarsa taji bai kwanta mata arai ba,
junaid ne kawai ya lura da ita, amma ita bata ganshi ba, sai yi mata alama yake yi da hannunsa alamar ta matsa daga bayan babban yayan nasu, saboda gudun idan zai juyo kar yayi wurgi da ita, amma ita sam bata lura ba,
“Dad pls kabarni na koyawa bastard ɗinnan hankali,” ya faɗi yana kallonsa a ƙule
Haroon yace “hankali kuma na yaushe babban yayan mu ? ae tun ranar da ka fara aza tafin hannunka a kunci ne na zama cikakken mai hankali,”
ƙokari fa Rafayet yake na ya janye hannunsa daga na abbansu yakai wa haroon bugu, amma abban ya hana hakan saboda tsoran karya naƙasa shi,
Sam bazai iya jure kallon haroon ba a fusace ya zame hannunsa daga na abbansu tunkan ya juya junaid yayi hanzarin riƙo hannun sehrish ya janye ta, ita kanta ta tsorata da ganin yadda sgr ya juyo tabbas da baƙaramin buguwa zatayi ba, cikin hanzari ya haye upstairs azazafe yake tattaka steps ɗin benen ya wuce part ɗinsa,
“Kowa ya koma bedroom ɗinsa ya kwanta,” kanal yusif ne ya basu umarni duk suka juya shima ya wuce nasa ɗakin,
Ya rage daga Abbansu sai junaid sai sehrish dake gefe boye bayan junaid tunda ya janyota gabanta ke faɗuwa,
Kallonsu yake fuskarsa kamar zai fashe da kuka yace “Abba akan idonka yaran nan duk sun raina ni, ba wanda yayimun tarbar arziki shikenan ba komai ni daga nan zan koma inda na fito,”
yayi maganar yana ƙoƙarin tashi cikin sauri junaid ya ƙarasa inda haroon ɗin yake gaba ɗaya yasa hannu ya rungumosa cikin sanyayyiyar muryarsa yace “Yaya haroon ni ina farinciki da zuwanka sosai, i missed u so much ka tambayi Abba kaji kullum saina ce mashi yaushe yaya haroon ɗina zai dawo, (Allah sarki junaid wato shi na musamman ne, kowa nasa ne baya gudun kowa, baya son ganin kowa cikin damuwa burinsa koda zai rasa nasa farin cikin indae hakan zai farantawa wani to tabbas zai rasa nashi,)
hannu haroon yasa ya ƙara ƙanƙame Junaid tare da cewa “Dama nasani junaid kai kana sona sosai, kai kaɗae ne ka damu dani, Allah sarki ɗan uwa mai daɗi,”
“Nima ina farin ciki da zuwanka haroon, ka ta6a ganin inda uba ya guji ɗansa ? najima ina jiran ranar da zaka dawo saboda nayi kewarka sosae,” acewar abbansu,
Farin ciki ne ya lullu6e haroon cikin hanzari ya miƙe bayan sun rabu da junaid ya rungume abbansu yana cewa “nasani Abba kaima kana farin ciki da zuwana,”
Juya junaid yayi ya kalle sehrish wadda take tsaye kamar gunki alama yayi mata na cewa itama ta gaishe da yayan nasu haroon,
Murya na rawa tace ” Sannu da zuwa yaya haroon, nima ina farin ciki da zuwanka,”
tun da muryar rishi ta ratsa kunnansa a wani irin yanayi ya ɗago da idonsa ya kalle ta, sai taji gabanta yayi wani irin mugun bugu har ta ɗan firgita a bayyane,
A wayance haroon ya saki murmushi tare da cewa “Wow junaid wanene wannan ko friend ɗinka ne,”? Ya tambaya yana kallonta,
Junaid yace “a’a mai aikin mu ne tukur bai jima da fara aiki a gidan nan ba,”
Lumshe ido Haroon yayi yana kallonta duk tsigar jikinta ya tashi saboda kallon da haroon yake yi mata ba irin kallon da namiji keyi wa ɗan uwansa namiji bane, wani irin kallo ne dake nuna cewa akwai wani abu a ƙasa,
daker ya janye idonsa daga face ɗin sehrish yana ci gaba da sakin wani shu’umin murmushi,
“My son ya kamata kaje ka huta a brdroom ɗinka dare yayi ssae, gobe zamu tattauna mu ƙara gaisawa ko,’?
abba ya tambaya yana kallonsa, haroon yace “hakane dad, but ina buƙatar abunda zan sawa ciki na, a sanya wannan mai aikin tukur yake da suna ko wama ya kawo mun abinci naci,” ya kare maganar yana yatsina fuska,
Cikin sauri sehrish tace “shikenan bari naje na kawo maka,” a tunaninta a nan zai ci saman dining,
Amma sai muryarsa ta katse ta da cewa “a bedroom ɗina nake so akawomin junaid ka nuna masa ɗakina pls,” ya faɗi hakan tare da wuce wa yana cewa Abban nasu “Good nyt abbana,”
Abban ya amsa masa da cewa “Sleep well my son,”
ji tayi zuciyarta na bugawa, tunda ta haɗa ido da haroon taji tashin zuciya, wuce wa abbansu yayi shima bedroom ɗinsa yana barwa Junaid sakon ya same shi acan ɗaki su kwanta,”
Tsayawa su kayi suna kallon juna murmushi junaid ya sakar mata tare da cewa “Muje kitchen ko? ki haɗa wa yaya haroon abincinsa,’
itama murmushin tasakar mata tare da cewa “toh, amma babban yaya fa? inaso naje na idasa saving ɗinshi abinci,
“Shikenan kije wurin babban yayan namu, ni bari naje kitchen na shirya masa abincin nakai masa,”
Wani daɗi ne ya rufe rishi dama batason zuwa wurin wancan baƙuwar fuskar da ta gani yau a gidan,
“nagode junaid,” ta faɗi cikin sanyin murya,
Junaid yace “Never mind ina yinki sosai,” wuce wa su kayi ita takama hanyar upstairs shi kuma ya miƙi hanyar zuwa kitchen suna tafiya suna waiwayon juna,
Time ɗin da ta shiga part ɗin babban yayanmu samun shi, samu tayi babu shi a falon nasa alamar ya kammala cin abincin nasa kenan,
tunanin kwashe kayan abincin tayi amma sam tagaza samun natsuwa burinta atlease tasan wane hali yake ciki don ta lura da yadda ya fusata akan wancen baƙuwar fuskar da taji sun kira da haroon, hakan yasa ma taji bai kwanta mata a ranta ba,
tana cikin wannan tunanin tajiyo muryarsa yana faɗin “who’s there,”
Cikin sauri tace “Tukur ne mai aiki,”
“Ok brings my phone, i left it there on seater,” yana acikin bedroom ɗinsa yake magana,
Murmushi sehrish tasaki cike da rawar kai tasanya hannu a saman 3 seater ɗin, ta dauki wayar tashi bin ta kawai take da kallo waya sai kacw wadda aka ƙera da zallar diamond saboda tsantsar kyau, juya bayan wayar tayi tana kallon sunan dake a jiki karantawa tayi a fili (SGR)
Jinjina kai tayi tare da cewa full meaning ɗinsa na nufin SURGEON GENERAL RAFAYET, kamar yadda aunty azmee na faɗa,
da sallama sehrish ta shiga room ɗin nasa ae tana ɗagowa wa’iya zubillah cikin sauri ta sunnar da kanta jiki na kerma, tsaye yake daga shi sai shorts ajikinsa babu riga wannan surar tashi mai rikitarwa ta bayyana muraran, sehrish taga abunda yafi ƙarfinta dole ta kawar da ido,
Da alama daga toilet ya fito don ga danshin ruwa nan ajikinsa, sai faman lumshe blue eyes ɗinsa yake alamar bacci yake ji sosae,
Ƙarasawa tayi zuciyarta na bubbugawa kamar zata fito waje saboda tsoransa,
Miƙa masa tayi hannunta nata faman kerma tamkar wayar zata faɗi, har time ɗin fa sgr baisan ya idonsa akan na sehrish ba, itama kuma saboda shegen tsoransa har yau bata bari idonta ya shiga cikin nashi ba, duk da bata da burin daya wuce ta haɗa ido da shi~~~
A ƙoƙarin ya sanya hannunsa ya kar6i wayar hannunsa ya gogi nata, wayyo zo gaka yadda sehrish ƙanƙame idonta ruff ta cije lips ɗinta saboda shock ɗin da taji,
Tamkar tayi hugging ɗin sgr harka take ji saboda wani irin ƙamshi dake fesowa daga jikinsa,
muryarsa ce ta shige ta da cewa “thanks,” bayan ya karbi wayar ya furta hakan batare da ya sa idonsa ba akanta,
Tsaye tayi tana kallonsa har ya wuce izuwa saman shimfiɗeɗen round bed ɗinsa mai ɗauke da wata irin haɗaɗɗiyar mattress irin wadda kai tsaye mutun na hawa zata lomatse dashi ga wasu irin lumtsa lumbutsan matasssan kai a jere dayawa, idan muka zo kan Blanket ɗinsa kuwa wayyo just speechless wani irin lallausan bargone nama rasa yadda zan kwatantashi, jibgege ne mai gashi gashi ajikinsa irin wanda mutun na shiga cikinsa ko baiyi niyar yin bacci ba nan take zaiji sa,
Sehrish fa bata bar room ɗin nasa ba kai kace tare zasu kwana ne,
Shikansa mamaki yake na ganin alamar cewa har yanzu fa house boy ɗinnan bai bar masa part ɗinsa ba, kawai zubawa sarautar Allah ido yayi yaga iya ƙarshen abun,
A natse a hankali ya kwanta tare da miƙer da dogayen kafafunsa harya so ya wuce gadon ma don Allah yayi sa da tsayi ga kuma ƙira abunsa duk shi kaɗai,
Zira ziran yatsun hannunsa yasanya tare da janyo blanket ɗinsa ya rufe har iya ƙirjinsa, sannan ya ɗan lumshe idonsa yana sauke ajiyar zuciya,
sam tagaza janye idonta akanshi komai nasa burgeta yakeyi yana yin komai a natse ba hayaniya,
Har bacci ya ɗauke sa sehrish bata fita ba leƙen beautiful face ɗinsa take,
matsawa tayi a hankali dab da bed ɗin nasa sannan ta ɗan jinkirta ta shiga yi masa addu’a daga tsayen da take, addu’o’i sosae sehrish tayi wa Sgr batare da sanin shi ba don yayi nisa a cikin baccin nasa,
Bayan ta kammala ta juya ta fice tana mai jin sanyi aranta har cikin ranta Sgr ya kwanta mata sosai,
Cike da wannan shauƙin sehrish ta wuce nata room ɗin ta haye saman gadonta fuskar nan da murmushi, abu biyu take tunawa haɗuwarsu ta yau da junaid sai kuma Babban yayanmu, duk in ta rufe idonta shi kawai take gani sai juyi take cikin bargo cikin nishaɗi,
(Allah sarki na tausayawa sehrish sosae domin ta faɗa tarkon so, son ma wanda ba son maso wani ba wannan son ya zarce hakan domin ta faɗa tarkon son wanda sam bai ra’ayin mace arayuwarshi bai da burin yin aure har abada)
________________________________________________hafsat Bature
A hankali motocinsa suka shiga cikin gidan yana zaune a back seat a hakimce ana driving ɗinsa,
Bayan sunyi parking ɗin motocin cikin sauri major ɗin nan ya fito ya buɗe masa mota,
Fitowa marshal Omar yayi yana sauke ajiyar zuciya bakomai idonsa ke marmarin gani ba face wannan Zararriyar yarinyar da ta faɗa masa a chest ɗinsa da ita ya yini a zuciyar shi,
Ba shi kaɗae bane tare da Babban likita suka dawo gidan, saboda dama nan ne makwancinsa,
Bayan sun shiga cikin main palor ɗin agajiye babban likita ya wuce side ɗinsa, yayin da Marshal Omar ya samu wuri saman 2 seater,
Shigowa major ɗin nan yayi hannunsa ɗauke da laptop ɗinsa ya miƙa masa,
Kar6a Omar yayi tare da furta “thanks,” sannan major ɗin ya sara masa kafin ya fice,
Tsit bakowa sai shikadae a falon, aza laptop ɗin yyi saman table ɗin dake a gabansa sannan ya zaro wayarsa daga trouser pocket ɗinsa,
Zubawa wayar ido yayi yana tunanin wa zai kira ma domin a kira msa yaran yana son ganinsu kafin ya kwanta, bai son kiran goggon katsina don yasan halinta da rigima, gashi bai da numbar saude
Zama.yayi shiru yana tunanin mafita, kamar daga sama sai ga jahad ta fito cikin sanɗa ashe batayi bacci ba komai ya fito da ita Oho,
“Ke zo nan,”
Daram !! Taji gabanta ya faɗi rass jin muryar mutumin nan tsaya wa tayi a hankali tana kallonsa,
Kafin ta tunkaresa zuciyarta na ɗar ɗar ta samu wuri ƙasa tazauna tare da lankwashe ƙafa ta gashe shi “Ina wuni,”
Bai amsa mata wannan ba sai ce mata yayi “where’s your sister”?
Jahad tace “Bacci take yi,”
“Je ki tasarmun ita, ina son ganinta,”
Mamaki ne ya kama jahad alamu sun nuna cewa marshal Omar fa yana iya banbance su tunda gashi ya nemi ta kira masa yar uwarta wato wadda ta faɗa masa ajikinsa,
Kallo guda yayiwa jahad ya gane cewa ba ita bace wadda ta faɗa masa a ƙirjinsa ba, kaji masu aiki da kwakwalwa,
farat ɗaya ya karanci wani abu a tsakaninsu daga ɗazu a asibiti zuwa yanzu,
tashi jahad tayi cikin sauri ta shiga ɗakin kamar yadda tabar hosana haka ta same ta kwance a tsakiyar gadon ta lumbutse abunta, baki wangame sai sharar bacci take.tana hura hanci kamar SA,
ɗan bubbugata Jahad tayi tare da cewa “Hosana !! Hosana ki tashi,”
Tsoki taja tare da juya mata baya “Leave me alone,”
a ƙule jahad tace “wai baxaki tashi ba,”
“Eh baxan tashi ba, in kinji haushi ki ɗauke ni mana,”
murmushi jahad tayi tare da cewa ” to shikenan bari naje na ce masa kince baki zuwa,”
jin abunda jahad tace yasa ta yin wani irin juyi ta ƴunƙura cike da zumuɗi tace “Wa,?
ƴar dariya Jahad tayi tare da cewa”mutuminki mai ƙarfi,” ????
Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar hosana, tasowa tayi daga saman gadon tana gaggyara rigar jikinta, hannu tasa ta ɗauki mayafinta dake anan saman gadon ta yafa,
Sannan suka fito atare ita da jahad ɗin, ƙarasawa su kayi gabansa riƙe da hannun junansu,
ɗagowa Omar yayi ya kallesu atare ya sauke idonsa kan Hosana wadda ke ta faman zabga mishi murmushi kamar gonar auduga,
“Have a seat,” ya umarce su
Zama su kayi saman 2 seater ɗin dake facing ɗinshi,
“What’s Ur names,’? Ya tambaya yana ci gaba da danna laptop ɗinsa,
Cike da zumuɗi hosana tace “Ni sunana Hosana ita kuma sunan ta Jahad,”
Jinjina kai Omar yayi kafin ya kuma cewa “Wacece mai ta6in hankali acikin ku,”? Ya tambaya tamkar bai gane ta ba,
Cikin sauri hosana tace “Ni ce,’
Murmushi kawai jahad ke yi shiriritar hosana nabata headache,
“Au kece kenan,? Ya tambaya yana ɗan kallonta,
Hosana tace “Eh nice bani da hankali but not always ynx ina cikin hankali na,
ɗan ta6e lips ɗinsa yayi kafin ya kuma cewa “Ina iyayen ku suke,”?
Shiru sukayi saboda sun rasa amsar da zasu bashi sai can hosana tace “Bamu da kowa, bamu son kowa ba, mu kawai muke rayuwarmu….’
tunkan taƙarasa ya dakatar da ita tayi shiru , ci gaba da danna laptop ɗin dake gabansa yayi kusan 15 mins bai sake cewa komai ba sai dai ya ɗan ɗago da idonsa ya kalle su ya mayar,
“A matsayin me zaku ɗauke “?
ya tambaya yana kallonsu har haɗa baki sukeyi wurin cewa “Yayanmu,’
Jinjina kansa yayi tare da cewa “Good, as frm now na zama yayanku, a shirye nake dana ɗauki dukkan wata ɗawainiya taku daga yanzu kun dawo ƙarƙashin kulawa ta, komai kke so just feel free ku sanar mun ko wani abu na damunku haka, sa’annan ku shirya tafiya gobe domin ba’a nan zaku zauna ba, zan mayar daku kaduna state gidan ƴaƴana, zaku samu kulawa sosae acan,
Har haɗa baki suke yi wurin yi masa godiya,
“No bana son wannan, bana son ana min gdy, zaku iya tafiya gobe ku tashi da shirin tafiya,
Miƙewa su kayi atare har sun ɗanyi nisa sai kuma suka juyo suna kallon shi atare suka haɗa baki wurin cewa “Sai Allah ya kaimu yaya Omar,”
Ba ƙaramin daɗin sunan yaji ba, jinjina musu kai kawai yayi sannan suka shige, shima tashi yayi ya wuce can cikin part ɗin big doctor domin dama acan suke kwana in sun zo,”
“Hosana ya kika ji muryar mutumin nan na ɗazu wanda goggon nan ta bamu mu gaisa dashi a matsayin mahaifin mu?
Jahad ce tayi wa hosana wannan tambayar ayayin da suke kwance su biyu saman gadon suna fuskantar junansu,
“A time ɗin naji shine tamkar mahaifina Jahad banso ya kashe mun waya ba kuma yace zai kira da anjima amma bai kira ba,”
Ajiyar zuciya jahad tasaki kafin tace “Nima haka Hosana, tun da naji voice ɗinshi naji zuciyata ta karye, shiyasanya na miƙa miki wayar sbd kukan da yazo mun,”
Hosana tace “dama ace shine mahaifinmu ko?
jahad tace “how that can be possible, we already ave our own father hosana, so stop expecting that pls,”
Shiru hosana tayi suka zuba ma juna ido na wani lokaci kafin Jahad tace “Allah Sarki Sehrish nayi kewarta sosae kullum tunani ya rayuwarta take, yaushe zamu sake sanyata a idonmu duk in na tuna hakan sai naji tsananin ƙunci da baƙin ciki araina, sehrish tasha wahala akan mu, tayi mana irin sadaukarwar da uwa ke yiwa ƴa’ƴanta, duk da kasancewar ko a wurin haihuwarmu Oumma ta faɗamin cewa sai da muka fara zuwa duniya da minti 30 sannan sehrish ta fito Allah sarki mai kyakkyawar zuciya insha Allah rayuwarki zatayi kyau Sehrish no matter what the situation is I wll neva stop praying 4 u,
ta daka da maganar a yayin da hawaye ke zubo mata daga eyes ɗinta izuwa saman pillow ɗin da take kwance,
Jikin hosana ne yayi mugun sanyi itama murya akarye tace “duk nice Sila jahad da ace ban jefa wayar nan ba, da yanzu muna nan muna waya da ita har ma yaya Omar yakaimu wurinta……..’
Kuka ne yaci ƙarfinta har ta kasa ƙarasa maganar da take yi,
“Oumma ta faɗa min cewa mu ba ƴan uku bane ta haifa, amma Abba ya kwashe sauran ya siyar dasu saboda shegen son kuɗinsa, narasa wani irin uba ne shi ya azabtar da rayuwar mahaifiyarmu da kuma rayuwarmu Allah ya isa bazamu ta6a yafe mishi ba har abada……….
cikin kuka take magana itama hosanar kukan take yi domin komai ya faru arayuwarsu in suka tuna sai zuciyarsu ta karaya, mummunan Labari mara daɗin Ji
Matsawa su kayi jikin juna suka rungume junansu suna ta faman shesshekar kuka Allah sarki kowa da irin tasa kaddarar, ????
___________________________________________Hafsat Bature Moh’d