ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

babban likita yace "lafiyarki ae tamuce mommyna, samun lafiyarki ae shine kwanciyar hankalin mu," 

Omar yace "maganarka gsky ne bro, goggonmu ataimaka adaina zuba magani a dustbin pls yakamata kina sha," 

Murmushi tasaki jin yadda suka damu da ita tace “shikenan, naji zan rinƙa sha daga ynx,”
Bayan sun ɗan tsagaita na wani lokaci Omar yace “goggo ina fata sun sanar dake cewa atare yau zan wuce dasu kaduna gidan yaya ishaq,”
Zumbur goggo tayi ta miƙe hankali atashe tace “bangane me kke nufi ba Omar? dama ba abusufyan bane yace akawo munsu nan ba su zauna wurina ? Bansan shegentaka fa ? Rabani zakuyi dasu ?
shiru Omar yayi just speechless ya ma rasa amsar da zai bata,
Babban likita ne yace “goggo go back to ur seat, lemme explain to u”
tsoki taja tare da cewa “Nifa bana gane ko wane yare a yanzu, in zakayimun magana da hausa kamun,” tayi maganar tare komawa ta zauna don sarai taji mai yace, tsohuwar ƴar boko ce ,”
ƴar dariya dr haris yayi kafin yace “mommyna kin gane, yaran nan school suke yi acan, kuma exam suke zana wa, shiyasan ya muke so mu maida su makaranta kar asamu matsala,”
juya masa ƙeya goggo tayi tare da cewa “In ansan exam sukeyi a makaranta maiyasa to aka kawo munsu ? Don aja mun rai ! I hate nonsense wlh,’
Yadda tayi maganar ba ƙaramin dariya ta basu ba gaba ɗayansu, hatta saude dake tsaye a ƙopan kitchen tana sauraran firar tasu sai da ta dara, jikinta duk yayi sanyi Allah Allah take aranta Allah yasa kada goggo ta amince akai yaran nan kaduna gidan Aunty Babba,”
Atare da Omar suka shiga lallashinta don ta amince, sam taƙi yarda har sai da dr Haris babban likita yace “mommyna i promise u da sun samu hutun school zansa akawo mana su nan, su zauna wurinki ko ba haka ba Omar? Yayi maganar yana kallon omar,
Marshal Omar yace “Yeah hakane, dakaina zansa akawo su goggona,”
jiki asanyaye gaggo tace “shikenan na amince amma karku sa6a Alƙwari da zarar ansamu hutu akawominsu in ba haka ba zan sanarwa Abusufyan ɗina,”
Murmushi suka saki atare kafin Omar yace “insha Allah, ‘ sannan ya kalli su hosana ganin sun kammala cin abincin harsun wanke hannayansu yasa shi cewa “Kuje ku shirya,”
Atare suka miƙe sam basu so zasu rabu da gaggon su da aunty saude, har sun fara tafiya jahad ta dawo zata ɗauki kayan abincin da suka ci Marshal Omar yace “just leave it, bari saude tazo ta kwashe,”
Juyawa tayi suka wuce bedroom ɗin saude suna shesshekar kuka, har cikin ransu basu son rabuwa da gaggonsu da aunty saude jiya izuwa yau sunji tsananin ƙaunar kasancewa dasu,”
Shaf shaf jahad ta fara yin wanka sannan hosana tayi, dukansu suna ɗaure da towel suna shafa mai ajikinsu,”
Hannu tasa da sauri jin hawaye a idonta, goge su tayi da sauri, sannan ta gyara natsuwarta, ta shirya musu breakfast ɗinsu ta shigo da shi palor,
Bin ta kallo dr haris yayi tare da cewa “Omar ga fa future wife ɗina danake baka labari,” .
ɗan kallonta Omar yayi tare da cewa “Oh dama ita ce kenan, ni bansan ta ba,”
Dr haris yace “taya xa’ae kasanta, daga rugar fulani nazo da ita, amatsayin wadda zan aura don na nunawa goggonku amma goggo ta maida mun mata ƴar aiki, “
murmushi omar yayi batare da cewa komai ba, goggon kam tuni ta wuce ɗakinta saboda rashin jin daɗi za’a tafi da ƴa’ƴan abusufyan ɗinta
Saude jiki amace ta gaishe su, suka amsa sannan ta ajiye musu tray ɗin, sannan ta juya ta kwashe kayan abincin da su hosana suka kammala dashi ta zuba a tray ɗin ta wuce kitchen, bayan ta ajiye kayan ta koma ɗakinta wurin su hosana, ko ido batasan ta haɗa dasu saboda kukan da take ji, saboda turken wawa,
Wardrobe ta buɗe ta ɗauko musu kayan da zasu sanya, jahad tabata riga da skirt na atampa da mayafi, sannan ita kuma hosana doguwar riga ce ta larabawa, baka sai ƴar guntuwar hijab fara, ba ƙaramin kyau su kayi ba,
Bayan sun shirya tsaf, ta haɗasu duka ta rungume ajikinta, gaba ɗayansu sukaji kuka yazo.musu nan suka shiga yinsa, sun jima kafin su fito,
daker aka samu goggon katsina tafito tayi musu sallama tasanya musu albarka idonta cike tab da hawaye, bayan sun kammala yi musu bankwana suka fito waje,
a jere motocin marshal Omar suke a harabar gidan, dakanshi ya buɗe musu motar da zasu zauna ciki suka shiga atare, sannan shima ya shiga motar dake bayan tasu ya zauna,
a natse ake driving ɗinsu har motocin suka fice daga gidan, suka miƙi hanya har suka fi ce daga welcome To katsina,
(* New destiny has started), ????????????????ABBAN SOJOJI????????????

page 88-89

wuce azmee tayi dakinta agajiye saboda ta samu ta huta, yayin da tabar sehrish tana faman kwashe dishes ɗin izuwa kitchen, bayan ta kammala wanke komai ta mayar dasu inda suke ta jera,
Sannan ta kama hanyar futowa daga kitchen ɗin, sam bata lura dashi ba sai dae taganshi agabanta kamar Aljani,
Tsorone ya kamata jikinta ya shiga kerma, dariya haroon yayi tare da cewa “Ina son ganinki baby da yaushe zamu haɗu ne,”? Ya tambaya yana kashe mata ido,
Murya na rawa sehrish tace ” Zuwa anjima yanzu agajiye nake, inaso na huta,”
Jinjina kai yayi tare da cewa “Okey, ki tabbatar kin kawomin kanki ɗakina, zan jira ki anjiman,”
“Insha Allah,” ta faɗi tare da bi ta gefenshi ta wuce hankali atashe, tuni hawaye sun soma zarya a kuncin ta ,

tana shiga bedroom ɗinta ta shiga yarfa hannu tana safa da marwa, damuwa iri iri daga nan sai wancan, babban tashin hankalinta a yanzu batasan da wata manufa haroon ke nemanta ba, runtse ido tayi tare da faɗin “Ya Allah ka tsare ni daga sharrin wannan bawan naka, Ya ilahi ni ynx bansan ya zanyi ba, gashi yace nakai mashi kaina ɗakinsa,” ta ƙare maganar tana mai jin bugun zuciya da fargabansa,
Daker ta tsagaita da zagaye zagayen da take yi a ɗakin nata,
gefen bed ɗinta ta hau ta ɗan kwanta eyes ɗinta na facing ceilling thinking abt many things, a haka har bacci 6arawo yayi awon gaba da ita, tasha bacci Ssae, dama ga weather ɗin is so comport,
Ba ita tafarka ba sai around ƙarfe 2 da mintuna har time ɗin sallah ya haura, tashi tayi tana dafe ƙirji domin kuwa har mafarkin haroon sai da tayi wai yace zai tona mata asiri wurin babban yayansu, da ta tabbatar da cewa mafarkine sai ta sauke ajiye zuciya tare da furta “Thank God it was a dream,”

Da hanzari ta shiga toilet tayi wanka ta ɗauro alwala, sannan ta fito ta nufi wardrobe tayi dressing kanta cikin riga da wando, sannan ta ɗauki hijab ta sanya, ta janyo sallaya ɗinta dake a saman murfin wardrobe ɗin dama nan take hanging ɗinta sometimes hada hijabin sallanta,
Shimfiɗawa tayi sannan ta kabbara sallah, a natse take yin ibadarta ta, bayan ta kammala sallar ta zauna saman carpet ɗin ta lankwashe ƙafarta, ta ɗaga hannayenta ta shiga jero addu’a, ta jima hada hawayenta domin tabbas tana ji aranta akwai wasu ƙalubalen da zata fuskanta acikin watan nan, tana roƙon Allah ya bata ikon cinye koma wata irin jarabawace sannan yabata damar tsallake duk wani ƙalubalen da zata fuskanta,” ????

Bayan ta kammala ta miƙe tare da naɗe sallayar ta ninke ta sannan ta cire hijabin ta ninke ta itama ta tura su cikin wardrobe dukansu,

Hayaniya taji daga harabar gidan alamar ana buga ball daga wajen murmushi tasaki tabbas tasan su junaid ne ke wannan, wasan,
Ji tayi tana marmarin itama ta kalli wasan ball ɗin nasu wataƙil ta rage ƙuncin da take ji a zuciyarta,

Da azama ta ƙarasa jikin window ɗinta ta naɗe curtains ɗin sannan ta zuge glass ɗin ta tsaya tana leƙensu,
Su 6 ne acikin ragar filin ball ɗin dake acikin gidan , shi da wasu daga cikin soldiers ɗin dake tsaren gidan,
time ɗin da ta aza idonta akan junaid sai da taji zuciyar ta ta buga, sanye yake cikin kayan kallonsa riga da gajeran wando dai dai guiwarsa kana ganin waɗannan fararen ƙafafun nasa na rainon madara abun ba’ace wa komai,

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74Next page

Leave a Reply

Back to top button