ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Time ɗin da junaid yaje ƙopan kitchen ɗin domin ya shirya musu abunda zasu sha, Sehrish yasamu aciki ta kammala jera Fancy cups masu ɗauke da Coffee aciki sai plate mai ɗauke da snacks acikin tray, sam bata lura da junaid ba, shima tun da yazo ya tsaya yana ta faman kallonta fuskarnan ɗauke da murmushi har kullum ƙara burge shi tayi,
Gyaran murya yayi, hakan yasanya Reesh ɗagowa a ɗan firgice a tunaninta Haroon ne ashe junaid ne, tana ganin sa ta sauke ajiyar zuciya tare da faɗin “junaid sannunka,”
“Yawwa sehrish na jima a tsaye ina kallon ki, wa kika shiryama wannan ne,’ yayi maganar tare da idasa shiga ciki yana nuna tray ɗin dake saman table,
Sehrish tace “babban yaya nagama hada abokinsa suka zo”
Junaid yace “yawwa Good girl kin hutasshe ni, dama nima zuwa nayi na shirya musu sai naganki,”
Murmushi tasaki tana faman sunnar dakai,
“Bari naje ciki inaso na yi wanka, sannan pls in kina da free time mu haɗu a garden mana”? ya tambaya yana kallonta,
Cike da zumuɗi sehrish tace “Shikenan wurin ƙarfe nawa”?
“After magrib prayer yyi maki”?
“Eh” ta amsa mashi kafin yasa kai ya fice daga kitchen ɗin Izuwa br ɗinsa, dama a ƙagare yake daya cire kayan ball ɗinsa,
bakomai yasa ta ɗoki ba fa ce tana tsananin son garden ɗin gidan ya haɗu sosai dama ita ma’abociyar son kayataccen wuri ce mai shufke shufken flowers da ruwa mai gudana,
A hannu ta ɗauki tray ɗin ta fuce dashi izuwa upstairs part ɗin babban yaya, sai da ta ɗan jinkirta da ta iso ƙopan shiga, tasama ma kanta Calmness, Sannan tayi sallama a natse “Assalamu Alaikum,”
Ta jira aka amsa mata sannan ta shiga A hankali take tafiya kamar wadda ta ɗauko Kwai a hannunta,
Kowannansu wayace a hands ɗinshi, sai da taje gabansu tace “ina wunin ku,” sannan adams ya ɗago yana kallonta yace “yawwa fine boy, drinks ne aka kawo mana,” yayi maganar tare da sa hannu ya ɗauki one cup, matsawa tayi ta miƙawa sgr tana kallon shi sam bai ɗago ba har sai da tace “ga shi,” sannan yasa hannu ya ɗauka, ta ajiye musu tray ɗin a saman table,
kamar karta fuce haka take ji, wani irin sanyi take ji in tana kallonsa, yayi wani fresh abunsa cikin singlet da shorts,
“Ji mana,” adams ne yayi mata magana cikin sauri ta juya ta kallesa tare da cewa “Na’am”
“Amma kai sabon mai aiki ne ko? Ina aunty azmee ne?
ya tambaya yana neman jin ƙarin bayani
Sehrish tace “Eh sabone, aunty azmee tana nan,”
Jinjina kansa yayi kafin ya kuma cewa “Suna fa”?
Rishi tace”Tukur,”
Abun mamaki sai taga yana mata dariya gashi kuma yana bin ƙafafunta da kallo abun ya ɗan bata tsoro,
Tsagaitawa da dariyar yayi tare da cewa “Wow good wasan kwaikwayon fa yayi kyau sosai,” sam Bata gane me yake nufi ba duk ta dabarbace, duk wannan maganganun nasu a kunnan sgr,
“u can go mr Tukur,” adams ya umarce ta yana mai ci gaba da ɗan murmusawa,
Jiki asanyaye sehrish ta fuce tana mai mamakin wannan abokin na Sgr, komai yake nufi da dariyarsa Oho, ta faɗi tana yarfa hannayenta,
Kurbar coffee ɗin yayi yana cewa "Sgr ina kuka samu ɗan aiki ne?
"Don't know," ya bashi amsa,
Adams yace “Wannan fa maca ce tayi shigar maza wlh, amma fa ta iya shiririta,”
ɗan kallonsa sgr yayi tare da cewa “Wa kenan?
“House boy ɗin nan mana, daya kawo mana drinks yanzun nan,”
Sgr yace “Are u serious ?
Adams yace “Of course baka ta6a lura bane?
Sgr yace “taya zan lura, bayan ko face ɗin mai aikin bansani ba,’
Adams yace “No wonder that’s y baka lura da hakan ba, amma fa maca ce wannan hada sa gashin baki, ‘ ya ƙare maganar yana dariya don kam ba ƙaramin nishaɗi abun ya bashi ba, shigar yarinyar amatsayin namiji kamar ɗan chali chali,
“Amma ko meyasa tayi hakan”? Adams ya tambaya yana kallonshi,”
Ajiye cup ɗin dake hannunsa yayi tare da cewa “Zan bincika, koma wa ya turo ta, zan sani ne, zasuyi bayani,” Acewar sgr,
“Gsky kam, u ave to investigate about it, kasan mugun mutun bakasan da wata siga zai shigo rayuwarka ba, especially yadda kke da suna haka ba’a rasa enemies masu son kawo muku hari ta bayan fage, ya kamata ka miƙe tsaye akan lamarin wannan mai aikin tukur, kasan da wata manufa yazo domin kuwa wlh maca ce ba namiji ba,”
Adams ne yake kora masa bayani yana ƙara jaddada masa akan mai aikin Don ayi saurin dakatar da shi daga abunda yake ƙoƙarin aikatawa, ????
Sehrish fa batasan wainar da ake toyawa ba, Ashe watan cin uban wata yayi acikin gidan nan ????
bedroom ɗinta ta koma tana safa da marwa, cike da tunanin dariyar da taga abokin sgr nayi mata aranta tace wata’ƙil shigar mazan da nayice ta bashi dariya Allah saki,
A hankali motocin marshal Omar suke shiga cikin katafaren gidan General Ishaq wanda ke a Unguwar rimi,
Hamshaƙin gidan wanda sojoji ke tsare dashi ta ko’ina, jahad sai faman bin gidan take da kallo ganin haɗuwarsa ta cikin glass ɗin motar, jinjina kanta tayi aranta tace “Aljannar duniya,”
Juyawa tayi ta kalli hosana wadda ta kwantar da kanta a kafaɗar Jahad ɗin sai faman bacci take shararawa murmushi jahad tasaki tare da cewa “Nasan hosana in taga wannan haɗaɗɗen gidan dole ta susuce,’
Mayar da idonta tayi kan glass ɗin tana ƙarewa gidan kallo aranta tace “Allah yasa kamar yadda gidan nan yake da kyau mutanen gidan ma zuciyarsu ta kasance mai kyau ce kamar haka, Ya Allah kasa kasancewar mu acikin gidan nan yasa ƙarshen wahalar mu kenan, Allah yasa mutanen gidan suyi marhaban da zuwan mu kuma su tarbemu hannu bibbiyu kamar yadda goggon katsina tayi mana,” ta ƙare maganar tana mai jin wani sabon yanayi atattare da ita,
A jere motocin suka tsaya, sajan ɗin dake driving ɗinsu ya fito ya buɗe musu mota,
fitow jahad tayi tana faɗin “Hosana ki tashi mun iso fa,”
daker hosana ta buɗe idonta da sukayi luhu luhu tana bin jahad dake mata magana da ido, daker ta iya sa ƙafa ta futo daga motar tana murje idanunta don taƙara tabbatarwa kanta cewa dagaske ne hamshaƙin gidan da take ganinsu aciki ba mafarki ba, aiko ta shaida hakan,
Fitowa Marshal Omar yayi daga tashi motar, yana sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya kalli su hosana yace ” ku biyo ni,”
Bin bayansa su kayi atare suka shiga hadaɗɗen jigunannan babban falon Aunty babba, wani irin daddaɗan ƙamshi ne ke fitowa ta cikinsa abunka ga ƴan maiduguri dama an shaidasu akan hakan,
Wasu irin haɗaɗɗun Sofas ne masu Numfashi sets guda, launinsu Maroon colour, ga sofa tables ɗinsu launinsu,
Falon yasha ado da decorative object ga vase ajiye (tukunyar flower) ga wata irin faskekiyar plasma manne a wall ɗin kai komai fa yaji ya haɗu,
Babu kowa a falon sai sanyin A.c dake ratsa sassan jikin mutun,
“Have a seat,” umar ya umarce su sai faman bin ko’ina suke da kallo , a tare suka zauna saman 2 seater suka takure junansu tsoransu dawa zasu fara cin karo,
Shima yasamu wuri saman 3 seater ya zauna yana facing ɗinsu idon shi nakan hosana wadda ke ta faman lumshe ido saboda baccin da takeji ga yunwa,
Phone ɗinsa ya zaro daga trouser pocket ɗinshi ya danna numbar aunty Babba ya buga mata Calling,
Da ƙarfi wayarta ƙirar Iphone 13 pro max ta soma ringing tana ajiye saman bedside drawer gefen lamp,
Hajiyar na hakimce tana sharar bacci Saman haɗadɗen gadon nata, jikinta na sanye da riga da wando masu kyan gaske ga laushi kamar sleeping dress haka suke,
takurar da ringing ɗin yayi mata ne yasa ta buga uban tsoki a ƙule cikin bacci take cewa "Mtsww Wai wanene ne yake son takuramin ina tsaka da jin daɗin baccina," ta ƙarasa maganar tana buga Uban tsoki rai a bace ta tashi zaune fuskarnan kamar Alkubus a kumbure take don ma Allah yasa akwai kyau da haske ssae da ba ƙaramin muni zatayi ba,
Hannu tasa ta fisgi wayar ta duba ta ga wanene, sunan (Marshal Omar ) ne ya bayyana akan screen ɗin wayar, ae tuni ta wartsake daga baccin da take yi, jiki na rawa ta ɗaga tare da karawa a kunnanta tace "salamun Alaikum," bai amsa mata ba sai cewa yayi "Muna a palor muna jira,"
Cikin sauri tace “oh to gani nan zuwa,”
Ta ajiye wayar tare da miƙewa tasa hannu ta ɗauki mayafin kayan jikinta dake ajiye saman gadon, ɗaure shi tayi akanta maimakon tayafa shi a jikinta, sumar kannan nata tasha ƙananun kitson kalaba,