ABBAN SOJOJI BOOK 1 COMPLETE

Sarai tasan wa take nufi amma tafiso taci gaba da zuzutashi don hajjaju ta iya bada labari ,
taci gaba da cewa “oho nidai nasan shi kadai suke ce ma babban yaya , ina gaya miki last dana zo , lokacin nazo dubiyar wannan younger bro dinnasu mai asthma wanda aka fidda kasar waje akayi masa aikin a kirjinsa , ” azmi tace “oh nagane junaid kike nufi ae suna waje suna buga ball ynx yaji sauki Alhmdllh ,”
Hajjajun ta ci gaba da cewa “ina fadamiki daga zuwa abun arziki , wlh ina shigowa falon nan ni bansan meya faru ba , nasame shi da y’an uwannan nasa sae faman rirrike shi sukeyi sai huci yake yi just like a hungry lion from the bush gaba daya yayi watsi dasu kasa , ya daga dining table yayi wurgi dashi , gabana ya fadi rass banyi aune ba naji yace “don ubanki kama hanya ki fice, ashe ya ganni “
Wallahi a tsorace a fujajen nabar gidan don tsabagen rudi , da kafa nakama hanyar fita babban gate din saida wani soja cikin security din gidan nan yace mun hajiya kin manta motarki , sannan fa natuna jiki na rawa nakoma nadauko,”
Tun kafin ta idasa labarin azumi da sehrish suke ta faman tikar dariya , kamar cikinsu zai kulle , ita kanta hajjajun dariyar take yi ,
dakyar azumi ta tsaida dariyarta tace
“Hmmm sai ynx nagane wa kike nufi , ai da kinsani ba ki daina kawo mana ziyara ba domin shi ba sojan nigeria bane , US ARMY ne ba a kasar nan yake ba yna dai zuwa sometimes in yasamu hutun aiki ,”
Hajjaju tace “bazaki gane ba ne , yadda na tsorata , ai ko ba don shi ba , wadannan tantiran na gidannan marasa jin magana…” Azumi ta katse mata maganarta ta da cewa “twins kike nufi , tom & jerry suna nan haryanzu basu canza ba sai ma abunda yayi gaba “,
Hajjaju tace “ehen su nake nufi”,
Ci gaba da fira sukayi , yayin da hankalin sehrish ke atashe , tunda taji sun ambaci babban yaya sai taji tsoransa har ya shiga ranta , sam ta nemi natsuwarta ta rasa ,
Sun jima suna fira har time din ba wanda yashigo daga cikin soldiers din , har hajjaju tayi shirin tafiya , bayan ta yiwa azumi bayanin akan nemawa tukur wato sehrish alfarmar in tayi one month da fara aiki ta taimaka a ansar mata kudin wata uku a dunkule ,
A tare suka fita har bakin motar ta , sannan suka tsaya suna idasa takarkare zancen
“meyasa bazaki jira abban ba yazo? koya yi miki sallamarki ne “? hajjaju tace “ae indai abba ne bani da matsala dashi nasan zanji alert kinsan hannunsa a bude yake , kuma Abunda yasa nake sauri zan shiga gwarinpa ne gidan wata goggo na “
Murmushi azumi tayi tana kallonta,
Ita ma murmushin tayi mata , harta bude mota zata shiga tasake juyo wa ta kalli azmi tace “pls game da tukur na baki amanarsa , ki kula da duk wani motsi nasa pls ,”
Azmi tace “in dai nice u don’t ave to worry about it I will look after him insha Allah ,” sallama sukayi hajjaju ta shige cikin motarta ta ja ta ,
Bayan fitarsu sehrish ta zabga uban tagumi tana jin kewar kasancewarta ita kadai a wannan hamshakin gidan da batasan kowa a cikinsa ba , gashi tazo a matsayin namiji , duk in ta tuna wannan hankalinta tashi yake , abu dayane ke kara mata karfin guiwa , y’an uwanta in ta tuna su sai taji ba irin kasadar da bazata iya shiga ba ,
Dawowa ciki azumi tayi fuskarta a sake tace da sehrish ” tashi mu shiga ciki na nuna mka bedroom din ka , in ka huta zuwa anjima before magrib zamu shiga kitchen”,
Sehrish ta amsa da toh tare da mike wa tabi bayan azmi , suka shiga ciki tayi mamakin bedroom din da azmi ta nuna mata a matsayin nata na yar aiki , wannan koda amayarce tasamu wannan falillahil hamdu , ba tarkace a ciki , single bed ne , ga beside drawer mai dauke da bedside lamp a samanta ga wardrobe madai-daiciya ta manne jikin bango , ga wadatattun curtains a kowane window , komai na cikin bedroom din brown color be banda labulayen da suka kasance milk colour , da zanen gadon ,
Ba abunda ya kara burgeta sai dressing mirriow din da tagani , duk da ba cosmetics a samansa , madubin yayi mata da yar chair din dake gabansa ,
Murmushi azumi tayi ganin yadda yaron yake ta farin ciki don haka tace “komai yayi ko “? da sauri ta amsa da “eh hajiya harma yayi yawa “
Dariya azumi tayi jin yace harma yayi yawa ,
“Ynx dai ni zan shiga ciki , ka zauna ka huta , sannan akwai bedsheets a cikin wardrobe din nan , in zaka canza saika dauka ,” tana gama fadan hakan ta fice ,
Kamar jira takeyi azumi ta fita tahau ihu tana tsalle , kafin ta tsagaita da haukan nata ta shiga bathroom din dake ciki ,
Nan fa ta soma wani sabon kallon , ko a mafarki bata taba tunanin zata mallaki irin wannan tsantsararren bathroom dinba mai kama da bedroom saboda haduwarsa ,
Dakyar ta samu natsuwa , ta dauro alwala tafito , a cikin wardrobe din ta samu prayer mat (sallaya) ta dauko ta shimfida , ta kabbara sallah , duka ta hada tayi zuhr da isha saboda batasamu damar yi ba a kan hanya , gashi ynx ankira isha’e shiyasa ta hadesu duka tayi ,
Bayan ta idasa sallar , ta daga hannayenta sama tana addu’ei at the end ta fashe da kuka , Sbd tuna wa da halin da y’an uwanta ke ciki , magana ta soma yi cikin kuka ” har ynx na gaza yarda cewa nice zan yi rayuwa a cikin wannan daular ba tare da y’an uwana ba , taya zanji ddin rayuwata batare dasu ba , ni ina nan sukuma suna asibiti cikin wani hali , Allah sarki rayuwa ! bazan taba yafe ma wanda yayi silar shigarmu cikin wannan tashin hankalin ba , Ya Allah ka hana sa jin dadin duniyar nan gaba daya , Ya Allah ka kaskantar da rayuwarsa kamar yarda yayima ta mu…..” kuka ne yaci karfinta har ta kifa kanta saman sallayar tana cewa “I will never forgive u in my life and I will neva forgt u ! i must take revenge koda ace nikadai ce na rageda zan yafe maka ka shiga aljanna to tabbas bazaka taba shigar ta ba.
Hafsat Bature
~(Boss Lady)~
Page 9-10
Bata tashi daga saman sallayar ba har aka kira Magriba tana tunanin abu daya, sai da ta kammala sallar sannan ta nad’e carpet din ta turasa cikin wardrobe , tare da hijab din duka.
tsayawa tayi gaban dressing mirror tana kallon kanta a cikinsa , sak namiji ba wanda zai gane mace ce sai yanayinta ya koma kamar d’an daudu , hannu tasa tare da shafa gashin bakin da ma’reeya ta sanya mata , murmushi ta d’an saki a ranta ta ce “Sehrish ke nan dramatic girl.”
Kara kimtsa kanta tayi saboda azmi tace mata akwai aiki a kitchen da zasuyi, sai da ta fara rufe kofar dakin gudun kada Azumi ta same ta tana canza kaya , ta gane cewa maca ce ita ,
Cire kayan jikinta ta yi , ta maida su cikin bag dinta , sannan ta dauko wasu riga da wandon , ta rige a hands sinta gaban mirror din ta koma ta tsaya tana kallon jikinta , ziririn pant ne a ajikinta , takai hannu tasha fa flat tommy dinta , wanda yake a dam’e kaman bata cin abinci saboda shafewarsa ,
Mayar da hannun tayi saman boobs dinta wadanda ta matse su gam , da abun matse belly , har cikin ranta ba taso hakan ba tana son abunta ssae , amma ba yadda zatayi duk cikin aiki ne ,
ga hairs dinta da aka maida mata shi guntu , amma hakan bai dame ta saboda a iya sanin ta in aka aske mata gashi irin hakan cikin one month zai koma yadda ya ke tsayinsa ma harya karu ,
Jin alamar tafiyar mutun kamar bedroom ta ake nufowa shine ysa ta yin saurin , zura dogon wandon tare da rigar sa , tayi gaggawa gyara daurin da m’reeya ta yi mata , mai kamar rawani ,