ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣0⃣

“Au Hajiya. har ‘yan makaramar islamiyyar taki sun tashi ne? (Da ya ke akwai makarantar islamiyya da ya gina daga bayan gidan. da daddare matan aure na yi, har ita ma Hajiyar tana yi ban sani ba, da ya ke- har yanzu su ke kai wa ka Kalli agogo, karfe goma ra wuuce fa”. Ya zauna yana dariya,allah dai ya; sanya ba ki ajiye mini komaiba?“ “Ban son sakarci yaronnan, Wai ina kake zuwa ne ba dai ka fara ’yawon banza ba?” “Na fara yawo, amma ba na banza ba, na yin abin da ki ke so, aure nake nema Hajiya”. Yadda ya ke .zolayarta wani lokaci kamar kakarsa ya ke maida ta, sai gata ta kasa motsawa, ya isa kusa da ita ya zauna yana murmushi. ‘ “Allah Hajiyata da gaske na ke yi, bayan tsawonn lokacin da na dauka a rayuwata naqinson aure yanzu Allah ya hada ni da wacceta rusa mini dukkan alkawarina da burina . “Kai amma na ji dadi, wacce’ yar albarka ce wannan‘? Amma mahaifanta sun iya haihuwa tabbas”. ‘ Ya yi dariya,yace”Sunanta Hasna, dalibata ce, dukkan ciwon da na yi kwanaki a kan sonta ne Ta fashe da dariya, tana tafa hannu. “Oh ni Falmata, daman akwai abin da zai lallasa wannan taurarrar zuciyar taka Abduljabbar? Kai Allah na gode maka…. Yana dariya ya kuma fadin. _ , “K0 dai asiri ta mini na fara sonta ya kamata ki bincika Hajiya”. “Kai tafi can ba asiri ba k0 tsafi tayi maka in dai’ a kan auré ne, wallahi ta kyauta, min, Zan taya ta biyan malamin k0 nawa ne Ta fadi tana dungure masa kai kamar, wani karamin yaro. ‘ Ya mike tsaye, “Balle ma ba asiri ta mini ba, watakila irin abin nan naki ne da Baba Abduljabbar”. Ya wuce yana dariya, ta bi shi da kallo tana jijjiga kai da dariya, duk farin ciki ya cika ranta, ta rasa me ya dace da yi ne don dadi. sai ta ji ta wartsake daga baccin gabadaya. lallai yau za ta raba dare tana yi wa Allah godiya. *** *** *** A can gidan su Hasna kuwa sabanin abin da ya faru a gidan su Abdul ne ya faru a gidansu, domin tunda Alhaji Sammani ya dawo gidan ya ke ruWan bala‘i kamar zai cinye Hajiya Aisha a dakinta, ta yi shiru ita dai tana jinsa. Ya dube ta afusace, “Aisha wai ba ke na ke yi wa magana ba kika, yi mini shiru ne, uban waya ke zuwa. gurin Hasna har ta ke wulaqanta dan uwanta Abba ‘?” “Haka ya kamata ka ce Alhaji, amma ka zo ka rufe ni da fada ban san dalilin yinsa ba, to ban san kowa yana zuwa gurinta ba bayan wani data ce malamin makarantarsu ne DR Abduljabbar. ..” “Karya ne, babu wani ‘malami. ‘ Saurayinta ne Abba ya sanar da ni komai, don haka daga yau kada ya qara zuwar mini gida na gaya miki”. Ya juya zai fita yana huci. ta yi karfin halin kiran sunansa, “Alhaji!” ya waigo da sauri ya kalle ta, “Na‘am, ya ya aka yi kuma‘?“ “Shin Alhaji ka taba tambayar yarinyar . nan k0 tana son Abba kuwa?” Mamaki ya bayyana a kan fuskarsa da takaici. “Au ki ce kece ke zugata a kan ta Ki shi ke nan ko?“ “A’a ba wannan ba ne, ya dai dace kafin ka matsa a kan komai ka tambayi ra’ayin yarinya, bai kamata kai ba a yi maka dole ba, ba a__taba yi ba ma a gidanku k0 danginku ba ka ceza ka yi wa diyarka ba. Ra‘ayinta ya kamata ka fara ji…” ‘ “Ko Aisha dakata haka!” Ya fadi cikin karaji da hargowa. “Idan ma wani abu ki ke nufi k0 kina ‘ son hana wannan auren ne, to wallahi ba ki isa ba kin ji na gaya miki, aure tsakanin Abba da Hasna babu fashi in dai ina raye“. Ya juya ya bar kofar dakin a fusace. Ta bi shi da kallo tana tabe baki. “Lallai kana shirin ganin bori mai girma a gidanka ke nan, don wallahi ba zan yarda a yi wa diyata dole ba Duk abin da a ke yi ,su Hasna ba su sani ‘ ba, sun kule a cikin dakinsu ana ta kwasar hira da dariya, suka jiyo muryar mahaifinsu daga falo yana kwala wa Hasna kira. Ta mike zaune da fargaba tana kallon ‘yar uwarta, “Sister kamar kiran daddy na ke ji k0?” . “Ba kama bane, kiransane, amma na ‘kasa gane wa yake kira ke k0 kuma ni‘?”_ Suka mike gabadaya da sauri jin ya Kara Kwala kiran suka nufi kafa kai tsaye. Yana ta kai wa da komawa a falon goye da hannayensa a baya suka fito a tare. “Daddy ga mu”. Yawaiga ya kalle su, yace. ‘ “Hasna kadai na‘ke son gani, koma ke ki kwanta”. Suka kalli juna cike da fargaba, don ba su taBa ganin mahaifinn nasu .cikin damuwa kamar haka ba Husna ta koma daki tana waigen’yar uwarta. ‘ Muryar mahaifin nasu ta kara dukan dodon kunnenta. “Zo nan Hasna!”. ‘ Ta isa ‘jikinta yana dan rawa ta durkusa a gabansa. ’ ‘ ‘ “Ga ‘ni Daddy”. . Ya zuba mata ido na tsawon daqiqa kafin ya iya fara magana. Waye Abduljabbar ne?” Ta dago kai da sauri ta danyi Shiru bugun kirjinta ya karu; “Uhm! Uhm? “Ba uhm! Umh nace ki min ba, amsa za ki ba ni, waye shi?” ‘ Ta yi kokarin tattaro dauriya da nutsuwa ta sanya a ranta, ta ce. ‘ ‘ “Malaminmu ne, kuma…” ” Ta kasa‘ karasa abin da take son fadi Cikin tsawa yace, “Kuma me, ki fada da bakinki na ji mana”. “Kuma saurayina ne…” . Maganar ta fito daga bakinta ba tare da ta Shirya fadin hakan ba. – “Saurayin uwaki! Na ce saurayin uwaki Hasna yanzu ashe har za ki iya kallon tsabar idona ki ce kinada wani ‘saurayi bayan dan ‘uwanki Abba?” ” Sai a sannan ta tuna taBargazar da tayi, Kuma ta gano dalilin da ya sanya baban nata keta hargagi kamar zai cinye ta. Ta dan matsa. da baya bisa gwiwoyinta ganin ya kuma kaurewa da fada kamar zai rufe ta da duka. “Daga yau na sassara katangar karfe tsakaninki da shi, ba ni bukatar kara ganinsa a ‘ cikin gidan nan, Abba shi ne mijinki na gaya ‘miki. dan kuma ba kiji ba xa ki ga mummunan Bacin raina Wanda baki taba ganin irinshi ba”. Ya juya ya kuma nufa dakinsa. Ta dafe kai da hannaye biyu kamar za ta. kurma ihu, Mamansu da ‘yar uwarta suna ,tsaye Suna jin dukkan abin da ke‘faruwa, hankalin kawo ya tashi kwarai da gaske. ta fashe da kuka; . Alhaji Sammani ya waigo ya kalle’ ta kamar zai yi magana sai kuma ya yi ido hudu da Hajiya Aisha dake tsaye kofar Bangarenta ‘tana kallonsu, sai ya fasa ya sanya kai ya? shige dakinsa, daidai lokacin Husna ta fito da – sauri ta rike ‘yar uwar tata da ke kuka -ta fara _ lallashinta. Ta lallaBata .suka shige cikin- dakinsu, Hajiyarsu tana kallonsu tana kada kai kawa’ta koma cikin sashinta. ranta na suya lallai ta’san mijinta yana Cike da son_ dan’uwansa, amma ba zaiyiwu yarufe‘. idonsa kamar haka ba. ’ Bayan sun iso cikin dakin, Husna ta zaunar da ita a gefen gado, taci gaba da‘ lallashinta. .- ’Don Allah ki yi shiru Hasna. ba fa ance an daura auranki yau da Abba bane, ba yanzu akwai sauran lokaci. Kaddara zata iya sauya komai. Ina ji a jikina Abba ba mijinki bane ba”. .. “Idan har Daddy baya raye k0?” Hasna ta fada da kausasshiyar murya. abin daya sanya Husna dan yin shiru kenan ta kasa cewa komai, ta kula ‘yar uwarta ta kan shiga cikin hauka wani lokaci, ko na wucin gadi da akan ce kowane mutum na shiga, ban da haka me ya kai ta furta wannan magana, sai ta ji ta Ci gaba da zuba. Kinf1 kowa sanin halin Daddy Husna, idan yace abu bai janyewa har abada, da kuka k0 damuwa na sanya shi fasa‘abu, da bai yi auren Anti Kubra ba, domin babu irin kuka da damuwar da Momy ba ta yi ba, amma sai da ya yi, don haka yanzu Ina k0 zan mutu na san ba zai fasa ba, za a aura mini Abba, ni kuma da na zauna da shi gwara na kashe kaina na huta….” “Subhanallahi, Hasna-ko kin yi hauka ne. kina diyar musulmi kike ambaton haka? Don Allah ki daina fadi kin san da kin kashe kanki kin mutu kafira babu ke babu gafarar Allah har abada, ki daina fadin haka don Allah. ki samo wata kalma da ta fi ta sassauci ki maye gurbinta da ita”. Husna‘ ke‘ mata wannan dogon wa’azin. Ta kada kai tanayarfe hannaye “Ba za ki gane abin da na ke nufi ba : sister. tunda ba ki shiga cikinshi ba. ba ki san dandanon ciwon so irin nawa ba, ba ki wahala a kan neman so ba, sai bayan da na wahala na samo soyayyarshi da kyar sannan za a ce za a raba ni da shi‘.’ Wallahi ba zan yarda ba, to idan ban kashe kaina ba kuwa zan shiga duniya, zan gudu…” Husna ta-mike a kidime, tace “Ohh my God, haba Hasna ya ya ki ke. yin abu kamar jahila ce, wacce bata taBa‘ karantar komai” na addinin Allah <ba‘?‘Wannan magana ce irin-ta jahilai, idan kin gudu ki je ina? K0 ba ki da labarin matan da suka gudu karuwanci suke cin birki rayuwarsu ta lalace ta tagayyare. sun Ki yarda da zabin, iyayensuji sun je suna bin garadan banza da ba su san darajarsu ba. da yawansu sun fi mutuwar wulakanci, gudun bai amfanar dasu komai; ba, idan .ki ka kwantar da hankalinki komaii zai zama daidai. Xa ki auri Abduljabbar’ insha’Allah”. ” Ta hadiyi zuciya kamar za ta hadiye ta” gabadaya. “Shi kenan. na daina fadin komai, sai dai k0 ban yi wani abu ba wallahi na san sai zuciyata ta buga ta fashe idan har zan dinga kallon Abba mazaunin mijin aurena”. “Kin ga yanzu dare ya yi, daure mu kwanta, gobe muna da lakca komai zai zama daidai insha’Alllahu”. Da kyar ta lallaBata ta samu ta kwanta, sai dai kwanciyar kawai ta yi, amma bacci ya gaza daukarta sam. sai Barawo da ya sace ta- cikin dare, hakan ya sanya su yin latti. *** *** *** Dr. Abduljabbar yana. shiga ajin suna isowa, su da wasu dalibai cikin gaggawa. babu wanda ya yi zaton zai bar su su ya wuce, amma ga mamakin sai suka ga ya tsaya cak yana kallonsu suna ta shigewa. Sauyawar halaycnsa yana bai wa dalibai da yawa mamaki, domin ya fara laushi babu hargowa da disga mutane. Bayan kowa ya zauna ya nufi kofar ya rufe, ya Kara dawowa gaban allon ya tsaya hankalinsa gabadaya yana kan Hasna wacce Tayi wata irin shiga, kamar mai zaman takaba idanuwanta sun kode sun yi jajir. Kallo daya’ zaka yi mata ka‘ san akwai damuwa a tattare da ita, amma sai ya basar ya gyara glass dinsa- domin kada dalibai su ramfo su yace “Good mornin class”. Gabadaya suka amsa, ya yi dan jim‘; kamar ba zai ce komai ba, amma ya dake ya fara zubo turancin nasa, lokaci zuwa 1okaci‘ kuma ya kan saci kallon ‘Hasna Wacce ke yawaita goge idonta da bayan hannu, k0 dav gefen hijab dinta, ‘yar uwarta ce kedan zungurarta idan ta yi zurfl a tunani, ta kasa yin komai; Sai ta dan dawo cikin nutsuwarta,‘ amma dan lokaci Kankani sai ta.” kuma‘ mantawa ta shiga damuwa. A haka ya kammala lakcar tasa ya fara tattara komatsansa, amma a dan wannan lokacin sai da ya tura mata saKo gajere. Tana satar kallonsa sai ta ji wayarta ta- dan yi Kara alamar shigowar sako. Ta dauki wayar da sauri ta duba, ga abin da ya ce. ‘ “Ki same ni a offis yanzu.” ‘ Ta kashe wayar tana goge idonta, Husna ta kalle ta da alamun tambaya a kan fuskarta, sai dai kafin ta furta wani abu Hasnar ta miKe daidai lokacin tuni Abdul din ya fice aji ya dauki hayaniya. ‘ “Ina za ki kuma?” Tambayar da Husna ta iya yi mata ke nan. “Ina zuwa Ta ba ta amsa ‘a takaice, sannan ta nufi kofar fita kai tsaye. Husna ta bi ta da kallo ba ta ce komai ba har ta fice, daidai lokacin Fatima ta shigo ta zauna kusa da Husna. _ “Ya ya dai qawagta, yau fa kun kusa makara”. Husna ta ‘Waiga da sauri tana kokarin kakaro murmushi a kan fuskarta. “Wallahi kam? Allah dai ya kiyaye bai – kore mu ba”. Fatima ta tabe baki. “Lallai kam, amma ba ki kula da ya sau‘ya gabadaya ba ma, duk wannan zafin kan babu shi?” Husna ta taBe baki ita ma. “K0? Ban kulaba ma ni sam”. Fatima ta Kara gyara zama, ta ce. “A’a dan Falmata ya sauya, da alama ya fadatarkon soyayya ne” “Soyayya kuma?” Husna ‘ta; fadi da mamaki da fargaba. * “’Haka dai na‘ji ana gulmar,-.ke baki kula da yadda ya ke yawaita kallon Hasna ba?” – Husna ta Bata ‘rai’ gabadaya, aranta kuwa cewa. ta; yi, na shiga uku lallai ; kiwon mutum akeyi ‘ba dabba ba yanzu har sun kula ,da wani abu tsakanin Husna da Abduljabbar? Amma a fili sai ta ce, “K0? Amma ni‘: ba ni da masaniya a kan haka keda ki ke magana‘ a akai.‘ Hasna na da’ wanda takeson aura kuma, ban san wani zance ba Yadda ta ke maganar babu sakin fuska ya sanya jikin Fatima yin sanyi, ta ce. “Kin ga tsokanarki fa na ke – yi, mu; sauya hirar, ya ya bayanin kayan nan da na ce kiba ni aro zan yi irin dinkin?” Sai a sannan Husna ta sakar mata fuska suka ci gaba da tattaunawa. Ga Abduljabbar ya kasa tsaye, ya kasa zaune sai zazzaga ofis din ya ke yi hannayensa goye a bayansa, Hasna ta turo kofar ofis. din a hankali tare da sallama Cikin siririyar muryarta mai dadin sauraro. ‘ Ya ,waiga da sauri, Sannan ya’ riko hannunta kamar wata qaramar yarinya,. yana fadin. .ZO,nan sanar dani kOmai, me ye ya faru?” Ta zauna a kujar’ar da ke gefe na laushi amma sai ta kasa cawa kumai, sai kuka da ta Barke da shi. Yace “Ya salam, karki sanya raina ya Baci Hasna don Allah sanar dani abin da ke faruwa”.. Cikin kuka ta ce “kasan Yayana Abba da kuka taBa gaisawa da shi?” Ya yi dan jim sannan ya ce “Ba zan “manta shi ba, .domin kallonsa‘, ya tsaya’a rainakwarai’da gaske, me ‘ya faru‘?” “Shi ne Wanda ke tsananin sona, shi ne wanda Daddynmu ke burin aura mini, ni kuma wallahi ba na sonsa, na tsane shi”. Ya yi ajiyar zuciya da Karfi yana fadin. “Wannan kadai da man ya sanya ki‘i kuka’.’ Gaskiya kin tayar mini da hankali… “Ai wannan ba abin tashin hankali bane yanzu Abdul? Ina shirin rasa ka ka’ce ba abin damuwa ba ne‘?” Sai ta kuma fashewa da kukan. Ya dafe kai a rude, “‘0h my God, ba nufina haka ba, na dai yi zaton matsalar ta wuce hakane. Ki bari anjima zan zo gida mu tattauna…” ‘ “Daddy ya ce bai son Kara ganinka a gidanmu har abada”. ‘ Ya zaro ido a firgice. . ” What? Haka ya ce? Lallai abin babba; ne yanzu me ye mafita ke nan?” _ Daga can awaje aka Kwankwasa kofar ofis din. Ya mike da sauri ya nufi gurin zamansa ya zauna. sannan yace. -” Yes. Come in”. Aka turi kofar aka shigo. wata hadaddiyar budurwa ce ta Ci kwalliya da wasu qananun kaya. sai yauqi ta ke yi kumar za ta tsinke. Hasna ta bi ta da kallon takaici. tsananin kishi ‘ya bayyana a kan fuskarta yarinyar ta dan kalli Hasna a sheke sannan ta wuce ta nufi gurin Dr. Abduljabbar kai tsaye wanda ya hade rai gaba daya. “Sannu malam”. Ta’ fada tana wani kwarkwasa. “Yauwa, ya aka yi ne?” Ya tumbaye ta rai Bace. “Babu komai Malam, na shigo ne kawai na gaishe ka”. ‘ Hasna ta dinga hararta kamar ta miqe ta shake ta ran DR ya qara baci yace “Haka kawai saiki zo gaishe ni, please kada ki Kara haka, na gode ba na buqata”. Jikinta ya‘yi sanyi ta dan kalli Hasna wacce ta kauda kanta gefe sai tace “Haha Malam, ai. gaisuwa naxoyi ba fadaba Ya mike .a fusace kamar zai kifa mata mari. ‘Malama ki fitar min daga ofis na ce Ya fada cikin hargagi yana dukan tebur. Ta dan tsorata ta ja da baya. “Yi haKuri malam,ban san ranka zai baci ba…” “Na ce ki flta k0?” Ta juya da sauri ta nufi Kofar fita jikinta yana kyarma, ba ta san haka ya keba sam. Hasna ta ji dadin hakan da ya yi mata, amma ba ta nuna a kan fuskarta ba sai ma ta mike tsaye a fusace. Ya kalle ta da mamaki. ‘ “Ya ya aka yi kuma?’1na zaki “Nan ba gurin da ya dace muyi magana Bane. k0 ba ka kula da matan da ke shigowa koda yaushe ba ne‘?” Ya runtse ido yana yarfa hannaye, ‘Please, kada ki‘ yi haka, ban santa ’ba. ‘ ban san me ya kawo ta ba’ Sam bata kula shi ba ta. nufi kofar fita da sauri. ya isa da sauri ya sha gabanta yana nunata da yatsa. ‘ “Ban son haka Hasna. ki zauna mu yi abin da ya dace wannan ba ita ce hanyar warqare wannan matsalar ba Ta yi ajiyar zuciya. “Da gaske nan bai dace mu yi wannan maganar ba, kowa ma zai iya shigowa k0 ba matan ba”. ‘ Ya yi ajiyar zuciya shi ma. “Haka ne, yanzu me ye abin yi ke nan. ga shi kin ce Daddy ya ce kada na kara zuwa gidanshi?” Ta yi shiru damuwarta na kuma linkuwa. Ya zuba mata ido ganin hawaye kawai ke zubowa daga idonta, ya daure ya ce. “Tsaya Hasna, ban son kukan nan. Na yi tunanin inda ya kamata mu hadu. gidan abokina Murtala‘ nan ne gurin da ya dace, please za ki je mu hadu a can?” Ta daga kai cikin ‘karsashi, ta ce. “Zan je insha’Allah, a ina ya ke?” “Yauwa, babu nisa yana nan Sabuwar unguwar nan ta makarantar Gaddafl daga gefe, zan tura miki address din ta waya, amma nafi son ki daina kuka da dukkan damuwar”. Ta Kara gogc idon nata. “Na daina”. “Yauwa ki maida hankali a kan karatunki.don wannan ce damarki ta karshe. saura‘ kiiris ki kammala komai ban son ki sami matsala Hasna”. ‘ Ta ji dadin yadda ya damu da ita, -da’” yadda ya ke kula da ita ta ce. “Kar ka damu sai mun hadu acan ka matsa na wuce”. Ta fadi da shagwaBa gamida babbake kofar” Ya yi dariya ya dan matso gefe ta nufi kofar kai tsaye, ya bi ta da kallo yana ajiyar- zuciya, Allah kadai ya san yadda ya ke son yarinyar nan. ya kasa daina soma k0 Boye shi. Sanda suka hadu da Husna ‘ta yi; mamakin yadda. ta saki jikinta . babu wata, damuwa a kan fuskarta kamar ta yi mata tambayar garin ya ya hakan ta faru, sai kuma ” ta ga taqi ba da fuska dole ta kyale ta. Da yamma suna isa gida Hasna ta fada ? wanka ta sake shiri cikin wata doguwarriga mai hadin shadda da wani Swiss an yi mata kwalliya da duwatsu ruwan zuma na kayan da kuma ruwan kofi. don haka suka amshi jikinta ta nade kanta da karamin mayafi ta sanya dogon takalmin nata na sabo. ta dauki ‘yar Karamar jaka. ’ Husna ce kadai zaune a babban falo tana kallo ta fito Husna tabi ta da kallon mamaki. “Ya ya dai Hajiya, ina zuwa kuma da sakaliyar yamman nan?” Hasna ta murguda baki. “Ban son sa ido, ina ruwanki ne?” Husna ta yi murmushi ta koma ta kishingida. “Babu idan ta yi wari ta fashe zan ji k0?” “Ke ki ka Sani. idan Momy tazo ki gaya mata na fita Ta nufi kofa kai tsaye. tana gab da fita Abba yana shignwa, suka ci karo a bakin kafa ta dan ja da baya tana kallonshi, kallon harara. Ya yi murmushi yana dubanta komai nata mai kyau ne kamar ya rungumc ta ya kulata Ya ya dai ‘yammata. ina zuwa?” Ya Yana maganar Yana murmushin. Ta murguda baki. “Inda ka aike ni”. Ta yi tsaki ta wuce da sauri ya bi ta da kallo kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya fada falon da‘ sauri ya taddo Husna na kallo. ya karasa da sauri, “Yuuwa qanwata, don Allah ina yarinyar can ta nufa ne?” Husna ta daga kafada, “Wallahi ban sami ba. amma ina zaton shopping za ta”. “Bari na bita Ya kuma juyawa da sauri ya nufl waje, sai dai sanda ya fita k0 kurarta bai ganiba an ma rufe kofar. Ya dafe kai da: takaici, domin ya so yau su yi hira k0 mara dadi ce, tunda ya yi nasarar korar Abduljabbar, amma babu komai zai jira ta har ta dawo ** *** *** A can kofar gidan Murtala suna tsaye a kan motar Ahduljabbar suna tattaunawa akan matsalar Murtala ya dan doki kafadarsa ‘yace “Abokina na gaya maka aure dole ne k0 ba; ka yi don komai ba ka yi don samun zuri’a..,‘ idan kuma ka sami matar da ke sonka ma bata damu da halin da ka ke ciki ba”. Abduljabbar ya Bata rai, “Mu bar wannan maganar, ka gaya mini hanyar da zan bi gurin warware burina na qarshe a kan aure, rasa ‘ta na nufin rasa k0 kuma fasa aurena har abada wlh Murtala ya harare shi a wasa, yace “Kai kuma matsalata da kai ba ka iya, son kanka ba, dubi yadda ka koma don Allah, ka kwantar da hankalinka, za ka same ta ma”. Daidai lokacin motar Hasna ta iso gurin da suke tsaye”, Abduljabbar ya yi “ajiyar zuciya, “Ga ta nan ta iso ma”. , Ya nufe ta da sauri tana Kokarin yin fakin. “Kada ki tsaida motar,’ bari mu shiga ciki kai tsayé”. . . Ya nufi motarsa lokacin tuni Murtala, ya nuf’i gidan kai tsaye yana bugawa, maigadi ya bude suka Shige da motocin nasu ciki. Bayan’ta yi fakin din ta dan tsaya tana jirar fitiwarsa, ya bude tasa ya fito bayan ya gama tsaida motar ya nufe ta, har lokacin tana Zaune bata motsaba, ya kwankWasa glass din: motar “Yaya madam fitO mana”. Ta bude ta t Fito ta jingina da kofar motar. Ta harde hannaye a’kirji “Yaya dai‘ na ganki haka. ko da wata matsalane ?”Da mace a gidan ne; k0 shi daya ne‘?”“ Tambayar da ta wurga kenan tambayar kuma datadan girgizashi Ya yi murmushinnan nasa mai kada mata hanjin ciki a duk sanda yayita yana kada kai. “Kina zargin zan sai da kene ko zan miki ‘fin qarfi ne?”………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button