ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

PAGE
0⃣5⃣

Kanta sannan tayi doguwar ajiyar zuciya taci gaba da rubutun Har izuwa lokacin da yaima kowa umurni daya dakata da rubutun ananma dalibai uku ya kora waje wadanda sukaqi tsayawa sannan ya fara vi wuru wuri yana amsa har ya kammala ajin yai tsit duk dalibai suna waje sunata dan surutai qasa qasa da yawansu zaginsa sukeyi Fatima qawarsu ta matsa kusa da husna tana tambayarta ina hasna ne yau ban ganta ba Husna tai ajiyar zuciya cikin alhini tace wlh batada lfy ne ga masifaffen malaminnan yayi test don nasan duk wanda baiyi test dinnan ba da wuya idan bai samu carry over ba Hakane amman inaga kamar idan kika sanar dashi tun yanxu zai iya daga mata qafa don kowa ai yasan lalura fatima ta shawarceta tayi dan jim da damuwa kamin tace “Kin san ni ban san disgi shi’kuma dabi’arsa ce dan idan ya disga ni zan iya ramawa. shi ya sanya kikaga ina kamewa daga shiga duk wata mu’amalarsa”.Fatima ta kada kai. “Ba kamarmu ba. ni har so nake na sami dan dalilin da zan kula shi don kin ga‘ duk iskancinsa wallahi bala‘in burgeni yake hakanan kowa cikin dalibai mata burge su ya keyi,duk wacce ta auri gayennan nan ta huta. wallahi da zan same shi k0 ta asiri ne da na gwada”. Takaici ya kuma cika Husna. Tace “Banzaye. ai kune ke hura masa kai har ya dinga ganin kamar yafi Karfin ko wacce, mace. Daidai lokacin Dr_Abduljabbr ya iso inda suke a tsaye Allah ya sanya Husna ce ta fara ganinsa tayi saurin jan bakinta tai shiru tana kallonsa. Ita kam Fatima har dan tsorata.tayi amma ganin ya nuna kamar bai ji abin da suke tattaunawa’ ‘ba ya sanya su yin ajiyar zuciya dajin dadi Fatima ta kamo hannunta tana fadin “zomu je don Allah mu yi masa magana”. Kafin husna tace wani abu Fatima tace zomu tafi kafin tai wani magana ta figeta suka rufa masa baya cikin daga murya fatima ke kiransa malam malam ya waigo gamida tsayawa_ har suka karasa kusa da shi. Ya kallesu da dam mamaki. “Wai’ da ni kuku ne.” Cikin jin dadi da kulawarsa garesu Fatima ta ce. malam. da kai muke. Daman ‘yar alfarma zAmu roqa”. Ta zunguri Husna dake kokarin gayyato dakiya ta sanya a ranta. “Ki yi masa bayani mana”; Ya maida kallonsa ga Husna. “Ina jinki. me ya faru?” ’ Husna ta gyara tsayuwa.”Daman akan ’yur uwata ne Hasna. wallahi tama gida babu lafiya. bata san halin‘da take ciki bama shi ne nace bari na_ gaya maka don bata samu yin gwajin (test) dinka ba ya daga kafada irin na ‘Turawa. “”No problem. ‘idan ta samu sauKi kice ta sanar da ni a ofis zan mata tata ko ita daya ce Dadi ya kamasu. Husna tace “Mun gode Malam “Babu damuwa”. Ya basu amsa a taqaice ya wuce. Fatima ta maqaIqale Husna tana “Kai amma naji dadi. Wallahi tunda nake da shi bai taBa saurarata irin na yau ba. Lallai’ ‘yar baiwa ceke Husna. ko dai yana ciki ne?” Husna ta daka mata harara. “Cikin wasa mutumin da bai burgeni ko kadan taya zan soshi idan ma haka ne ina zan kai rabin raina. Suka yi dariya suka tafa Fatima na fadin, “Kina burge ni wallahi Husna. Baki daukar komai‘ da zafi amma sai naga kamar Hasna ta fada tarkon son malaminnan kamarmu don yadda take kallonsa kamarta lashe shi”. Gaban Husna: ya fadi; hankalinta ya tashi. Ashe har Wasu ma Sun fahimci halin da ‘yar uwarta ta shiga Amma sai ta duke ta Kara hade fuska tace “In ji wa‘.” Ai idan akwai:wanda‘hasna ta tsana .a duniya bai wuce Dr Abduljabbar ba. ko baki kula da ~sam basa shiri ba duk sanda ki kaga ta kalle shi idan kin kula xa’ kiga harara ce kawai take aika masA”.Fatima tace “Au Ai mu; munyi zaton sonshi take yi don duk wanda ya sanya kanshi a Sonsbi wallahi ya shiga, uku da shan wabalar duniya”. ‘ “Lallai kai da , alama haka ne. amma zano ganin matar da zai aura. don duk iyakacin isgilancinshi dole mace dai zai aura ba namiji ba”. Husna ta bai wa Fatima amsa. Fatima ta tabr baki‘ tana kallon kanta‘ “Sau da yawa na kan qare wa kaina .kallo a madubi nagano k0, ina da wata nakasa’da ta sanya ban burge Abduljabbar amma na kasa gani, duk namijinda ya kalle ni sai ya girgiza amma ban da shi. mutum sai kace shaidani‘.” Husna tayi dariya har ta isheta tace Wlh iska tana Wahalar da mai kayan’kara. kin ga zo raka ni capteria nadan ,sanya wani abu a cikina. ban yi karin kumallo ba na sbd sauri Bari na kira Mummy ma naji jikin sister Ta dauko waya cikin jakarta ta fara kokarin daddanawa. suna ci gaba da lafiya suna hira. ’ *** *** *** Tunda garin Allah ya waye Abba ke kiran wayar Hasna. amma sai ya ji ta a kashe. duk ya kasa sakewa don haka da’ ya ga ya kasa sukuni a of’is dinshi, ya saci jiki ya nuf’i gidan .su Hasna din. Tunda mommy ta sanar da shi halin da ta ke ciki. anyi mata allura tana bacci. . Hankalinsa ya yi mugun ‘tashi. ya tsare Mommy da tambaga kamar ita ce Hasnar “Mommy Wai meye damuwar Hasna ne data kamu da wannan ciwon sai nake ganin kamar talakawane da marasa galihu ke kamuwa da irin wannan ciwon ko? Mommy tace haba Abba ka da kayi sabo mana. ai . shi ciwo babu ruwanshi da mai kudi ko talaka To idan haka “ne mai ya sanya mutuwa ke daukar masu kudi har da masu-mulki’? Ka yi saurin yin istigfari domin wannan sabone dukkanmu’ daya muke gurin Allah. sai’ wanda yafi tsoronSa ne kawai Ya yi ajiyar zucia. “Haka ne amma sai nake ganin kamar ya yi gaggawar kamata. duka duka shekaruntA nawa har da zata kamuda hawanjini momy Ta kalle shi ya gama qular da ita don haka tace”Abba idan ba xaka iya fadin magana mai kyau ba-kayi shiru da bakinka. har sai hankalinku ya dawo jikinka. Ya kake. Son yin sabone?” Ya yi shiru da-damuwa’. “Allah na tuba, inajin kamar .na yi haukane.banson abinda zai taba Hasna Mumy: ban son-ta rasu na sami amman wadannan maganganun ba zasu hanata ciwo ko mutuwab ka kiyaye bakinka da sauri yace to momy bari naje na gano jikin nata ya miqe da sauri ya nufi sashin nasu momy ta bishi da kallo tana kada kai abba ko rigima ta fada cikin ranta a lokacin daya isa hasna ta fito daga wanka tana tafe daqar tana dafa bango ya turi qofa ya shigo yama manta da ganinta daga ita sai towel yaddah ta rame dare daya tana tafiya daqar kamar mai koyon dabo hakan yafi daga masa hankali ya nufeta da sauri da rawar jiki Hasna haka jikin naki yayi xafi zona kamaki ya miqa mata hannu Kunya duk ta rufeta ta tsaya cak gamida sunkuyar dakai don towel din iyakacinsa cinyarta cikin zafin rai da bacin rai tace na hanaka shigo mana daki kai tsaye babu sallama ko? Sai a sannan ya kula yaji kunya tadan kamashi ganinta a hakan saiya danja da baya yana fadin sorry sorry na rudene amman zaki iya qarisawa bakin gadon ?ta qara fusata da kaine ja kawoni da zakace haka dukda cikin sanyin murya take maganar amman ya lura da ranta a bace yake don haka ya juya da sauri ya fice yana fadin sorry sorry ta isa bakin qofar cikin hanxari tasa key ta jingina da qofar tana haki Sbd saurin da tayi da kuma haushin abba da takeji ta lallaba ta dauko doguwar riga mara nauyi ta saka ta dauko hula mara nauyi ta saka tadan shafa roll on ta koma gefen gado ta zauna gamida dafe kai Batasan tuna komai da kowa a ranta tanason warkewa daga wannan ciwon ta koma yaddah take babu damuwar kowa a ranta Abba dake zaune a qaramin falonsu ya kalli agogon dake hannunsa rollex minti talatinfa kenan ko wacce irin kwalliyace ya dace yanxu ace ta kammala haka don yana son jin yAddah jikin nata yake ya mike ya nufi bakin kofar ya kwankwasa Ta kalli kofar sai a sannan ta tuna da shi yana jiranta tayi tsaki gami da miqewa ta nufi qofar ta bude Abba yana tsaye yana kallonta da dumuwa a ‘fuskarshi ta kauce ya shige ciki..sannan tabi shi ta samu gefen gado ta zauna yana tsaye shi qikam ya harde hannaye a kirji yana kallonta. “Ya ya jikin naki Hasna‘.” Ya tambayeta “Da sauqi’ Ta bashi amsa a takaice. Ya kada kai da damuwa. “Ban san dulilin kamuwarki da wannan ciwon ba. kinyi yarinya da yawa Ta dubesa domin. ta san halin Abba tamkar dan fari .yake ‘koda yake baiyi zurfi a ilimin addiba ga kuma gata da ya ratsa shi matuka; cikin sanyin murya tace “Ka sani, shi ciwo bai shawara da kowa kafin ya shiga jikin mutum. Allah ne kadai ke Kaddara shigarsa”. “Haka ne. na manta da malama nake Zaune yanxu meke damunki kin rame kin fada komai ya dainamin ciwo sai kasala da rashin qarfin jiki ta bashi amsa amman ya kamata ku koma asibiti a dubaki idan zaki yardama na nema mana visa na jamani don kwararrun likitoci sunfi yawa a canma doctonama yake bari nai masa yawa tai saurin katseshi duk abinda za,ai acan anyi anan namace maka na warkefa ba inda kemin ciwo ta komar da qafafunta kan gado ta kishin gida ya qaraso ya zauna kusa da ita yana kallonta ji yake kamar ya rungumota jikinsa don komai na hasna birgeshi yaKe ya jima yana neman isa gareta koda da rungumane amman ya kasa samun hakan saima dai ya janyoma ransa bacin rai yana ganin dumbin gidadanci gurin yan biyunnan kamar ba yaran da suka taso cikin kudi da gata gamida wayewa ba haka suke tafiyar da rayuwarsu babu kodan holewarnan amman dole ya dangana ya yard hasna ba irin matan da yake samu a titi bane saidai da aure Zai sameta dole Yadda yake kallonta ke Bata mata rai. don haka ta lumshe idonta tana son bacci ya dauke ta k0 ta huta daga damunsa duk da wani lokacin yakan dan ba ta tausayi. don tasan yana matukar sonta tun tana da quruciyarta. bai damu da shirun da tayi ba, a gare shi ya yi ta kallonta ma Wata ni’ima ce don haka suka zauna a haka har baccin gasken ya dauke ta. Ba ta san lokacin da ya gaji ya fita daga dakin‘ba. amma dai a nan gidan ya wuni yana ta mata sintiri daga karshe ma sai da ya gayyato mahaifansa suka zo dubata. duk wanda ya kira’ shi a waya sai ya ce yana nan jinyar matarsane. siyayya kam tasha shi abin da ya tunzura zuciyar mahaifiyarshi wacce ta ke ganin kamar asiri aka yi masa anason raba ta da shi. da fari tana cikin wadanda suka yi ‘murna da Soyayyar yaran nasu. amma ganin yadda dan nata ya take da yawa ya sanya ta dan’ fara dawowa daga rakiyar abin. don dai babu yadda .za ta yi ne ya sanya ta zuba ,ido. domin sun‘shagwaBa Abba da yawa. har ba a isa a kwabeshi ba don shi kadai Allah ya basu. Rawar kan da ya kama yi yau sai ya Kara sanya abin lalacewa daga zuciyarta. Ta tabbatar da lallai idan aka yi auran ta rasa danta kenan sai shadan ya sami guri cikin ranta ya fara kitsa mata auran ma badon Allah ake son yi ba. don dai anga Abba yana da arziqi ne uwa da uba, don kawai a ci ,gadon dukiya ne.’ Gabadaya sai ta sauya fuskarta, yau daya har Momy ga gano hakan, amma dai ta basar kawai aka Ci gaba da hira. shi dai Abba kam bai ma kula ba wai k0 a jikinsa an tsikari kakkaura. A nan suka tafi suka barshi,‘ duk da Maman nashi ta so su wuce da shi. amma yace ba yanzu zai tafi ba. sai dare ya ga yadda jikin Hasna ya yi. . Mahaifinsa hakan dadi yayi masa ya dafa kafadarsa yana duka kadan. yace “Lallai offis ma zai san Hasna babu lafiya. Don ba zai sami aikin manaja yadda~ ya dace ba”. Abba ya yi murmushi. “Kada ka damu Daddy. daga nan ma zan yi komai. Don ina tare da Ipad da laptop dina zan tafiyar da komai online Mamanshi ta hade fuska. “Ni ban ga amfanin zaman ba. tunda ta sami lafiya‘ ai ‘kamata ya yi ka wuce kawai. kuma dukkan abun da ta ke bukata ka yi mata”. Ya yi dan yake, “Daddy, Mom ba za ta ganeba. Ka yi mata‘bayani Cikin mota ka ji k0?” ‘ . Alhaji Sammani da ke zaune ya yi murmushi yana fadin, “Abba har yanzu yana daukar kansa a yaro fa Yaya, ka ji abubuwan da ya ke fada. Hajiya Aisha “ta dan yi yake kawai ta kau da kanta, don ta kula da inda facakalar ta sanya gaba. shi kam Amaji Auwal .dariya ya yi yana fadin, “Don ya ga bai da qanne ne shi ya sanya ya ke ganin bai girma ba. amma idan aka yi masa aure ai zai girma”. Gabadaya aka yi dariya ban da Abba da ya sunkuyar da kanshi wai kunya.‘ sai ya nufi dakin Hasna yana cewa. “Bari na duba k0 ta tashi daga baccin. Daddy da mom sai mun hadu a gida”. Ya shige ba tare da ya surari abin da zasucebA Alhaji Auwul ya miqe yana to mu munwuce Alhaji Sammani ya miqe shi ma don taka wa dan uwansa, Hajiya Aimana ma ta miqe har lokacin fuskarta a dame ta ke. don haka da Hajiya Aisha tayi mata agaida gida ma a ciki- ciki ta amsa. ta bi bayansu. Hajiya ‘Aisha ta riqe haBa tana mamakin abin da ya faru, amma dai. Ta bar abin a Cikin zuciyarta kawai. Har Husna ta dawo Abba yana nan. Hasna na kokarin basar da abinda ke ranta ta amsbi Abba, fuskarta amman ta gaza bayyana hakan musamman ganin‘ Husna data san komai amma shi kam bai gano komi ba. dariyur dake kan fuskarta da dan murmushin da take masa ya gamsar dashi dari bisa dari Sai wajen takwas ya bar gidan shi ma ba don ya soba. sai don roqon da Hasna din ta yi masa akan ya barta haka donta samu tai hira da yar uwarta sannan ya tafi Hasna ta gano yar uwar tata sarai so yake ta bata lbrn makaranta ko wani abu daya shafi masoyinta ita kuma ta shareta taci gaba da hidimominta amman ga mamakinta sai taga hasna ta dangana ga dauko ipad dinta tana game a ciki abindaya dauke mata hankali kenan can ta shigo da faranti mai dake da yakkakkun tufa a ciki ta ajiye a kusa da hasna din tana fadin ga mutumin nakifa hasna tadan kalli tuffan tai murmushi ji nake kamar nai amansu donyau abba wuni yayi yana yankaminsu tunda yasan inasonsu husna tai murmushi tace allah sarki sarkin hidima shidai bai gajia indai akan hidimarkine hasna batace komai ba taci gaba da danne dannenta a ranta tanajin kamar ta tambayeta abinda ke damun zuciyarta amman kuma tana dakewa don tayi alqawarin watsar da DR Abduljabbar da dukkan hidimarsa hakanne kawai zaisa ta samu sauqi dukda ta kula da hakan abune mai matuqar whl wai gurguwa da auren nesa amman xata gwada ta gani husna dai ta kula da yar uwar tata bata da niyyar cewa komai akan abdul din don haka tara magana yau wani abu mai ban mamaki da daure kai ya faru a makaranta sister kamar an tsikara mata allura ta miqe zaune zumbur farin ciki ya cika fuskarta tace meya faru yar uwa fadamin don allah yau kunyi lakcar Dr Abduljabbar ne ?husna tai murmushi a fili a zuci kuma tace ai nasan dariyar taki ba zata wuce cikin cokali ba amman saita dake tace Mutuminki ya shigo department dinmu ya qarena hall din gaba daya kallo ya lura da da yawa ba,a zoba kawai saiya rubuta test a jikin allo hankalin kowa ya tashi amman mugun ko,a jikinsa wlh saida yayi nikam kosanin abinda na rubuta banyiba na miqa masa kobanciba zan tsira da maki goma na atendance dayace zan bawa duk wanda ya samu rubutawa Maimakon hankalin Hasna Ya tushi na rashin samun jarabawu da tayi Saima wani annuri da farin ciki daya cika A fuskarta. mamaki ya kama-‘yar uwarta ‘tace Kamar baki damu‘ da rasa gwajin da ki kayi ba”. “To idan ke kin yi ai kamar nima na yi ne. don na san dole ki jira ni na biya spill over‘dina kafin kiyi aure ko‘.’don haka damuwarmu da murnarmu dole ta zamo daya Husna ta kai mata dukan wasa tana fadin “Muguwa. dalilin da ya sanya baki damu ba kenan. amma’ kin san zan yi aure‘ko baki kammala karutu ba. don ke daya za kiyi spilling dinki”. “To kiyi mu gani. dole dai a jira ni mubar ’wuccan butun. ya ya ya qare baiyi wannan korar tasaba “Kema kin san dolene Ni ‘kaina Allah ne ya tsareni ni don na dalla masa harara ya ganni da yanxu banyiba Suka fashe da daria Kamar ba hasnar data wuni a kwance yau ba Cikin mutu kwakwai rai kwakwai ba “Dama ya koreki da mun yi daidai wallahi”. Hasna ta fadi da .zolayaya Husna ta bata ran wasu. “ke sister. muguwace ke . Ni kuwa na damu da rashin yinki. har Fatima ta gane ta mini rakiya gurinsa, don nemar miki arziqi Dadi ya kuma cika Hasna ta nutsu gaban ‘yar uwar tata ta riqe hannunta da gaske sister bani labari. me yace muku “Ban sani ba”. Ta. Fada da zummar jan rai. ‘ zan biya ko nawane meya fada “Fada mini don Allah”. ‘ “zan fada miki don Allah. Ba don halinki ba: cewa yai idan ki sami Sauki ki sameshi yai miki naki Hasna ta rungume husna dadi ya cikata don Allah da gaske kike Don allah sakeni karki shafamin ciwo na taba miki wasa da irin wannan ne Ta“ zame ‘ta ture ta tana dariya ta mike tsaye. ~ ‘ ‘ Dadi’ya ‘cika Hasna ta‘ma ‘rasa’mai ya dace ta yi, sai ’kawai‘ ta -bi- _’yar uwar ‘tata da kallo tana dariya, Sai ka Ce ta ‘ sami * taBin KwaKWalwa Ita ‘dai Husna‘mamaki da‘ tausayin yar uwarta kawai ta ke yi, tabbas ta hadu da. ciwo mai wahalar warkewa, wato san maso wani,‘ wanda HauSaWa ke kira‘ ‘qOShin wahala, amma ta danne wannan tunanin ‘cikin ranta, ,tace‘, “Ya kamata ki dakata’ da’ dariyar haka kada ki’ Zare”. ’ Tana fadin haka ta fice daga dakin, don ranta ba zai iya jurar abin da ’yar uWar tata keyiba “‘Hasna‘ ta kwanta; ta: kura: wa ~silin”ido sanyi da farin ciki yana Qara cika ranta; to ya gane bata da lafiyane ya sanya ya fadi haka < k0 kuma ya fada ne kawai, wannan ce tambayar data dace ta yiwa-Husna, amma: Husnar’ta fice; Dole’ta‘hakura‘ ta bar abin ciki‘ranta’ don: – zata gani da idonta‘ranar da-ta isa makarantar’ Kwanaki sunyita wucewa har tsawon kwana shida a gare ta tun ranar da ta samu albishir din Abduljabbar cewa za ta yi gwajinsa ta sami sauqi, tun washegari kuma ta so komawa makarantar sai dai iyayenta sun ce sai ta warware.~ sosai da kuma bayanin likitan, wannan ya tsaidata ga komawa, amma kullum ta kan damu ‘yar uwarta da tambayar abin da ya faru a makarantar har zuwa randa “ta sami‘ saukin tafiya kamar yadda iyayenta suka‘ce; Ranar ma tun asubar fari ‘Hasna ta yi wanka ta fara qOKarin gyara jikinta da kwalliya, kayanta kusan rabi suna zube a kan gado domin zaBar wanda .zata sanya , da kyar ta tsaya a kan wani lafiyayyan material mai taushi da aka dinko mata su daga Dubai, aikin duwatsu ne masu bambancin kala, riga da sike din da kan amshi jikinta. Gashinma ya sha gyara, gurin zaBar takalmi ma an jima da Kyar aka dace ranta ya tsaya a kan wani tsikarere mai kama da tsani, wanda kamar da Kashi aka Kera shi, akwai zaruruwa da suka zagaye shi ya ba da kyau mai gamsarwa. Ta jima tana kallon agaban madubi. Ji take kamar bata taBa irin Wannan kwalliyar ba tsawon rayuwarta Husna da ta fito daga wanka tajima tana kallonta. k0 ita ta burgeta, tare aka haife su da Hasna amman kowa halinsa da ra’ayinsa daban ne tun suna yara Hasna ma‘abociyar son kwalliya ce sai ka ce ‘yar tsana, ita kam husna abin da bai cika damunta ba kena shi ya sanya k0 babansu ya ba su kudi ‘rabin‘na Hasna tana kai wa gurin kayan shafa da kyale kyale ne, shi ya. sanya ma tafi ta tara samari da qawaye. Hasna ta juyo ganin ta zuba mata ido tace “Ya ya dai sister‘? K0 na sauya miki ne’?” Husna tace“Wannan kwalliyar wai duk ta zuwa makarantace kamar za ki filin fati “Babu ruwanki, shirya ke dai mu wuce kada mu makara dan jidali ya riga mu shiga ya kulle hall din Husna ta zunBuro baki gaba amma bata ce komai ba ta wuce ta fara shiryawa. sunyi ‘sa’ar shiga da wuri yau, don sai da sukayi; kusan mintuna goma sannan Dr. idan ya ga dama. Hasna tama jin kamar don ita kadai ya keyin lakcar yau, don a ganinta tafi kowa fahinta. Husna tana satar kallonta sai ta dan zungureta don ganin yadda ta ke tsare malamin da kallo. wanda bai kula da ita ba sam. Har zuwa sanda ya sanya ayar gamawa. ya juya ga daliban yana lambayarsu k0 da mai tambaya. Wata ‘yar kwalisa ta daga hannu cikin yauki. Ya gyara gilashin idonsa. gami da bata damar fara tambayarta. Gaba daya ajin aka juya” ana kallonta ganin yadda ta ke wani rangwada da karairaya, daman ta sanya wasu kaya da suka matse ta, babu gyale a jikinta sai wani dan gyale da ta zagaye kanta da shi, ga shi tana da wadatar dangin Fulani, samari da dama sun sha latsafa saboda kyanta da iya gayunta, amma tana yarfa su don tana ganin tafi karfinsu kasancewar kyakkyawa diyar mai kudi Haushi da ta’kaici ya cika hasna ganin yadda ya kura mata ido yana kallo, har ‘yana wani gyara gilashinsa. sai take ganin Nana ta tafi da zuciyarsa yau dai. Dr. Abdul jabbar ya yi dan taku kadan ya Kara isa inda Nanan ke tsaye ya cire medicated din class din idonsa yana kallonta, wannan abin ya sanya dalibai yin. shiru kamar mutuwa. ta ratsa. su maganar shi ta Kara daWO da kowa cikin hayyacinsa. “Kina nufin dukkan Iakcar da nayi ba ki fahinci k0mai ba?” Ya watsa mata tambayar cikin haushi don saukar da ita dogon turancin da take zabgawa kamar tayi‘ arba da ()bama shugaban qasar America. ‘ Ta daga kafada “E Malam. abin da nake nufi kenan. please ko zaka sami lokaci ka Kara koyar da ni ?” Gaba daya ajin akayi tsit ‘Sai , wasu ’ dake gunguni, kamar su kamota su rufeta da duka. Dr Abduljabbar medicated dinsa ya maida idonsa yana murmushi ya fara- tafiya kamar bazai bata amsa.ba,.sai da ya dangana da gaban alllon sannan ‘ya kalli sauran daliban Yace’ “K0 akwai wata k0 wani da bai gane abin da nake koyar da shi ba. ya ke kuma buqAtar na bashi lokaci don sake tishi’?” \Vata ‘yar Kwalisar ma muryata a make da sauri tace. “Yes Malam; nima haka” Gabadaya sai ‘kallon ya koma gurin kairat ita kuwa Nana ta, hade rai kamar ta fashe don so tayi ta Same’shi daga ita sai shi yadda zata Kara shigar da’kanta wata qila k0 tayi dace a‘can. don tana‘ganin yana yawan kallonta sosai Ya’ kada kai yana irin’ murmushinsa da kan Kara masa kyau da qarjini Bangaren ya juya bangaren maza yaCe, “Kufa ‘babu wanda bai ganebA Mazan suka“ amsa da‘mungane sir yace “To”. Sannan ya Kara-juyawa ga Nana da kairat yace. “‘A Cikinku akwa wacce ubanta ya” taBa biyana alawus k0 albayshi’ na wata guda‘?” ‘ Gaba daya ajin ya rude da hayaniya; har. da dan ihu daga Bangaren maza. Ya daka tsawa cikin hade fuska ya sanya _kowa komawa cikin hayyacinsa. akai tsit sannan Ya juya ga daliban da ke tsaye ya kallesu a fusace. Yace “Da ku nake magana. idan akwai waccu wani nata ya taba bani wani Cin.‘hanci k0 wani alawus na daban tai bayani”. , Cikin sanyin gwiwa da tsananin kunya suka ce. “Babu Ya dan Kara taku gaba kadan yana huci. “Amma ku ke fatan shiga lokacina, wannan shi ne kadai lokacin da gwamnati ‘ta biya ni domin na koyar da ku. dukkan sauran lokacin nawa ne na kaina. Bahu wanda ya isa ya siyeshi. don haka k0 kuyi tambaya .cikin aji gahan sauran dalibai ‘yan uwanku a’yi muku bayani. k0 kuma ku haKura da shiga dukkan lakca ta wannan shi ne sharadina”. , Yana .kai wa nan ya debi takardunsa da shirgin littattafansa ya nufi? Kofar fita, dalibai suka rude da ihu da dariya. gasu Nana wadanda suka ji kamar qasa ta bude su shige, don Nana ma kasa zama tayi a ajin ta suri jakarta da ‘yar jorter dinta ta yi hanyar waje tana huce da boye fuska don kar daliban suga hawayen dake zuba daga idanun nata Dr Abduljabbar ya. Mata yarfin da harta mutu ba zata manta dashiba sannan yai mata tabon da bazai taba kankaruwa a zuciyartaba gamida mata wulaqancin da ba.a taba mataba tundata fito daga cikin mahaifiyarta………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button