ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣5⃣

Abin duhu3 RANAR BAKIN CIKI HASNA TA KIRA WANNAN RANA Hasna ta isa falon tana dube- dube, ta manta ainihin abin da take nema, domin a rude take, ta gigice gabadaya, don haka ta koma ta zauna shiru, k0 za ta iya tuno abin data flto nema daga cikin bandakin. Can kamar tsikarar kibiya abin ya fado mata, ta flto domin duba P.T Strip abin awon fltsari ne, ta mike cikin gaggawa ta nufi first aid box din su ta fara neman sa, cikin sa a ta hangoshi ta dauka ta nufl bandakin kai tsaye, ta dauko wata Karamar roba ta yi fltsari a cikinta, cikin gaggawa take abun kamar wacce aka sanya a gaba, tana gamawa ta farke ledar P.t strip din ta sanya cikin fltsarin ta cire ta ajiye a gefe ta Kura masa ido tana kallo ba tare da k0 dauke ido ba tamkar wanda zai Bacéwa ganinta, Mintina kusan biyar tana tsaye duk da jiri dake dibarta sama-sama amman ba ta gajiya da tsayuwarba, a hankali jajayen layuka guda biyusuka fara rinewa daga fari zuwa ja, gaban Hasna ya ci gaba da faduwa a duk sanda kalar ta ‘sauya har zuwa lokacin da jajayan layukan guda biyu suka flto sosai, ta ja da baya ta hada bayanta da bangon bandakin ta Kara fashewa da kuka, a fili take fadin na shiga uku na lalace, wayyo ni Hasna, ta zame ta fadi Kasa tana ci gaba da kuka da fadin. “Ka ci amanata Abdul, me ya sanya ka mini haka‘? Me ya sanya ka ci amanar kaunar da na maka, ya Allah ka taimaka . mini ka sanya hakan ya zamto mafarki, Allah kar ka barni da iyawata, Allah ka san ina son mutumin nan, na kuma so shi ba don komai ba sai don kai, Allah ka kawo mini dauki ka tabbatar da abin nan mafarki ne. A tsakiyar bandakin take kuka bata tina da komai na daga kazantar bandaki ba, burin ta kawai ta farka daga mafarkin da ta ke yi mafi muni. A Bangaran su Abdul suna tsaka da ’aikata abin da ‘suka yi niyya, wanda Murtala shine jigon neman, domin shine ke neman Abdul ya biya masa bukata bisa abin da zuciyar sa ke buKata, kamar Abdul ya tina wani abu sai ya mike zumbur gami da hankade Murtala daga jikinsa, Murtala ya bi Abdul da kallo cikin tsananin mamaki da wata irin kasala kamar zai fasa kuka, Abdul bai kalli inda yake ba kai tsaye ya wuce gurin da kayan sa suke ya fara Kokari daukowa ya sanya a jikinsa. Murtala ya bishi da kallo cikin matsanancin takaici yana fadin “Menene haka Abdul, yaya kake irin wannan abin, aure fa ba hauka ba ne, bai kamata ka manta da kan ka da bukatarka akan matar ka ba ‘ Abdul bai ‘kalleshi ba ya ci gaba da sanya kayan da yake yi yana Magana “Lokacin da ya kamata na dauko Hasna daga ofls yayi, ka tashi kawai ka fita, na gaya maka Murtala na dai na, mai ya sanya kake son maidani ruwa ne, bana son ganinkaka tashi ka fita kawai! Murtala ya mike zaune cikin takaici yana ci gaba da kallon Abdul kamar zai fasa kuka “Me ya sanya Abdul! Kasan bani da kowa ban san kowa ba sai kai, na dai na bin kowa a yanzu, bazan iya tonawa kai na asiri ba, gurin wa kake son na je bayan kai! Abdul ba tare da ya kalleshi ba ya ci gaba da Magana “Ka je gurin kowa ma Ni _‘ na fita.” Yayi hanyar fita cikin gaggawa bayan ya dauki wayarsa ya kunna ta, ga mamakinsa sai ya ga miscall na kiran ‘ Hasna yana ta shigowa wayarsa, hakan ya ; sanya ya karasa ficewaa cikin azama. “ Murtala ya bishi da kallo kamar zai sanya kuka, me ya sanya Abdul ke yi masa haka, matsalar su daya ce, lalurarsu daya, _bukatarsu daya ce me ya sanya ba zai. fahimce shi ba, Dakta ya kammala shirinsa yayi hanyar fita. Cikin damuwa Murtala ya ci gaba da magana “Wai da gaske taflya zaka‘ yi ka barni Abdul? Abdul bai juya ba bai kuma kara Magana baya flce daga dakin. Murtala cikin rawar jiki ya mike ya fara kokarin sanya kayansa ransa a bace. A harabar gidan Dakta ya shiga motarsa ya yi mata key sannan yayi hanyar flta kai tsaye, Maigadi ya tashi cikin sauri ya fara qokarin bude masa kofar flta yana daga masa hannu. Dakta ya sanya motar” a waje zai fita amman bai kammala fitarba sai ya tsayar da motar ya kalli Maigaadin da, ke tsaye ya yaflto shi da hannuWansa, Maigadin ya nufeshi cikin rawar jiki da ladabi. “Barka -da dare yallabai.” . Dakta ya daga kai gami da fadin “Yauwa, zan flta ne daukar hajiya, yanzu Murtala zai flto, ‘ sai na dawo.” Ya fara kokarin taka totir ya ‘ wuce. Maigadi ya dan zabura cikin ladabi yana Magana “Ranka’ya dade ‘na ji kamar kana cewa Hajiya zaka je daukowa k0? “Eh, ya aka yi? Dakta ya tambaya cikin mamaki yana kallon Maigadi, ganin kamar akwai Magana a bakinsa. “Eh hajiyar ce ta shigo tun dazu, ina zaton bata jin dadi ne, domin kamar motar gurin aikin su ce ma ta shigo da ita.” Mamaki ya bayyana akan fuskarsa cikin fargaba yace “Ka ce kamar ba ta da laflya? , “Eh ranka ya dade” Maigadi ya bashi amsa cikin gaggawa. ‘ Dakta bai kawo kamai aikin ransa ba, sai ya gyada kai gami da kokarin yin ribas, maigadi ya bishi da kallo har ya koma ciki ya gyara parking din matar ta sa ya fita ya rufe motar, ya nufi cikin gidan kai tsaye sai ya’ hango Murtala ya nufo Kofar cikin damuwa, kamar ya wuce sai kuma ya tsaya yana kallon Murtala har ya Karaso kusa da shi, Murtala bai kula shi ba ya wuce kai tsaye ya nufi motarsa, Abdul ya bishi cikin sauri ya sha gabansa, Murtala ya daga kai ya kalleshi cikin Bacin rai. “Me kuma kake son gaya mini? Murtala ya fadi cikin takaici. ‘ “Ina zaka je daga nan? Abdul ya wurga masa tambayar,‘ Murtala ya kauda kansa gefe yana tsaki. “Meye kuma ya dame ka da inda zan taf’1 yanzu, ka barni na je ko ina ne mana.” Yana huci yake fadin hakan. Abdul ya gyada kansa ta hanyar koKarin rarrashin Murtala’ “Kar ka je ko’ina Murtala, ka tafi gida, matar ka tana can tana jiranka, za ta iya yi maka komai, itace halaliyar ka, itaCe‘ ,mallakin ka, abin da zuciyar ka ke gaga maka yanzu bai kamata ba, mun yi wa kan mu alkawarin mun tuba, mun fada da bakunan mu ba zamu Kara aikatawa ba, me ya sanya muke shirin komawa ruwa.” Murtala ya kalleshi kamar ya yadda da maganar shi, amman cikin zuciyarsa wutar ba ta mutu ba, abin da ya yadda kawai zai je gida, zai je matar sa ta yi masa abin da Abdul ya kasa yi masa, tasan bukatar sa ita, ta na son sa, ba za ta Ki yi masaba, k0 kuma ya nemi wani daga cikin abokansa, don haka ya wuce kawai ba tare da yace da Abdul komai ba, Abdul ya bishi da kallo har ya shiga motarsa ya nufl hanyar fita daga giden a fusace,‘ kamar zai buge maigadi sanda ya bude kofar ya flce a sukwane, Abdul ya gyada-kai yayi hanyar cikin gidan kai tsaye. A cikin falon ya hango jaka da gyalan Hasna ajiye, ya dan tsaya turus cikin mamaki ya kalli jakar, ya daga kai ya kalli agogon bango wanda ya nuna shabiyu saura minti uku na dare, sai ya nufi dakin baccinta kai tsaye, ya karewa dakin kallo ba tare da ganin ta ba, daga cikin bandaki ya dinga jiyo sautin kukanta yana flta, hankalinsa a tashe yayi hanyar bandakin ya tura Kofar, sai ya hango Hasna kwance male-male tana kuka, hankalinsa ya kara tashi ya nufeta cikin gaggawa. “Hasna 1af1ya? Me ya faru? Me ya same ki? Ya fara Kokarin kamata, Hasna ta mike a fusace cikin sauri ta doka matsa tsawa. “Kar ka taBa ni. . .kar ka taBani Abdul! Ya tsaya sororo cikin mamaki yana kallonta, sai ya kalli gefe da gefensa a tinaninsa da wani take ba da shi ba domin yasan ya rabu da matarsa lafiya, da ya tabbatar shi kadai ne cikin bandakin sai ya nufeta kai tsaye yana kokarin fara lallashinta. “Hasna me ya faru ne? me ya same ki, ko kuma. . .? ‘ Ba ta son jin komai daga bakinsa don haka ta mike cikin sauri ta. yi hanyar flta, ya bita da kallo, ya kasa yadda da abin da yake gani, sai ya bi ta cikin sauri shima. Kai tsaye gefen gadonta ta je ta zauna tana jijjiga kai kamar wacce za ta hau iska tana cije lebe, wannan ya tabbatar masa da lallai ba laflya ba, bai taBa ganin ta cikin wannan halin ba, ya matsa kusa da ita karo na biyu, amman Sai ta mike tana ja da baya tana ci gaba da kuka. “Nace maka kar ka zo kusa da ni, ka ‘ fita daga gurina, bana son ganinka Abdul, na tSane ka? Abdul ya bude baki da mamaki, kwata—kwata tinanin sa bai kawo komai ba, domin bai taBa tsammanin za ta je Bangaransa ba, k0 da ta je ya san dakinsa a kulle yake ba zata iya budewa ba, don haka wannan tinanin bai ZO masaba sai ma wani daban, abin da ya zo ransa shine matarsa ta gamu da iskokai, tabbas aljanu: sun taBata cikin daran nan, don haka ya taimaka mata shine abinda ya kamata, sai ya kara matsawa gabanta a hankali yana Magana cikin lallashi. “Hasna kar ki tayar da hankali, please ki gaya mini menene ya faru, me ya same“ ki? Hasna ta dinga kallonsa da wani irin duba irin na tsana da takaici wanda hakan ke Kara tabbatar masa da abin da yake tinani din cikin ransa, yana tinkararta yana ci gaba da Magana “Ban son ki sami matsala, ki mini bayanin abin da ya same Takaici da haushi suka qara kasheta, ji take yi kamar ta kulle dakin ta banka musu wuta su mutu .su duka su huta, don haka ta fara dibar dukkan abin da ya je hannunta tana cilla masa tana i‘hu da kuka gami da fadin “Ka flta daga dakina, bana son ka‘ Abdul na tsane ka. . .ka fita. . .ka flta! Ta maka masa bed side lamp ta ya fada goshinsa da Karfl ta fasa masa goshi ya dafe gurin cikin tsananin azabar zafI, jini ya fallatsa yayi sama ya sanya hannu ya dafe gurin, amman har lokacin hankalinsa yana kan Hasna ganin abin da take yi, ba ta damu da abin da ta yi masaba illah ci gaba da take yi da ihu da jifansa gami da fadin Hmmmmmm ana rikici………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button