ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

PAGE
0⃣7⃣

mu koma gida dan Allah. na gaji da jin wannan kulaman naki .masu kama dana mai wasiyyar mutuwa”. Ta fara tafiya. Husna ta bi ta da kalli tana kada kai da damuwa. Lallai ban da tare suke kwana da kuma tashi da ‘yar uwar tata da sai tace lallai ta fara shaye-shaye ne, amma tabbas ta yarda kwakwalwar .’yar uwarta ta dan sami matsala. don mai hankali da nutsuwa ba zai yi irin abin da ta yi ba. Ta kada kai ta bi ta don ba ta da zaBi baya ga binta din. *** *** *** Dukkan abin da “ya dace likitoci sun yi a: kan Dr. Abduljabbar sunyi daqar suka samo shi da saboda dogon ,suman da ya yi, abokinsa Murtala yaqi sanar mada hajiyarsa , don ya san halin da zata shiga idan ya shiga irin wannan halin. sai dai‘tun da magriba ta yi ta fara damuwa. don ta san danta bai wuce wannan lokacin bai dawo gida va,’k0 da yana da abin da zai yi ya kan dawo .gida ya sake yin wanka, “ya shirya sannan ya Kara fita. Saida akai sallar isha’i ta kuma Shiga rudani ta zagaya bayan gidan. dakin Salmanu ta kwala masu kira. Salmanu ya fito daga cikin dakinsa da sauri ya nufeta “Hajiya lafiya. me ya faru?” Ta mika masa wayarta dake hannunta. “Amshi nan. kira mini yayanka ka ji ina ya shiga ne. har yanzu fa bai dawo ba”. Salmanu ya yi dan murmushi. “Hajiya kenan. na yi zaton wani abin ne ma ya faru. Yaya Abdul ai ba zai Bata ba, watakila yana wani aikin ne shi ya sanya bai dawo ba.. “Ka Ci gidanku. bar mini dogon turanci, amshi nan ka kira shi. Ai ka san bai kai wa wannan lokaci. idan kuma ya kai ma, yana kirana ya sanar da ni abin da ya sanya ya yi daren. Kirawo shi dai na ji me ya sanya bai dawo ba’?” Salmanu yana dariya ya amshi Karamar wayar ya daddana ya kara a kunnensa. har ta Karaci kararta ba a daga ba. Hajiya ta Kara matsawa gaba ta dan fara rikicewa, “ka gani k0, bai daga‘ ba‘?” Shi ma jikinsa ya dan fara sanyi, ya daga matakai. “Amma ina zaton bai kusa ne. bari na sake kira mu gani”. Ya Kara danna lambar cikin sauri, nan ma ta kuma yin Burarin har ta yanke ba a daga ba.wannan karon shi ne ya fara yin magana. “To Hajiya yaya bai daga kiran ba,_ bai qin daga kira har sau biyu”. Idon Hajiya ya fara yin kwal-kwal‘kamar ta fashe da ihu. tana fadin. “Nemo min lumbar Murtala ka kira shi. wata qila ya san inda ya ke. Ina jin tsoron k0 ciwonsa ne ya tashi. ban son faruwar hakan. kira shi don Allah”. Salman ya “fara neman layin Murtala. cikin sa’a bugu daya. ya daga. Salman ya yi ajiyar zuciya da jin dadi kafin ya fara magana”Alhaji Murtala. Hajiya ke neman Yaya don har yanxu bai dawo gida va”. Murtala ya danyi shiru da damuwa yana kallon Abduljabbar dake kwance yana bacci. Hajiya ta kalli salman cikin damuwa ta ce. “Ya ya me’.’ Me yace’ ‘ Salmanu ya daga mata hannu alamar tayi shiru. sannan ya Ci gaba da sauraron Murtala da ke bayani. ‘ “Kana ji salman, dazu ya fadi a makaranta yana Kokarin shiga mota, amma yanzu jikin da sauqi, don ga shi nan yana bacci a asibiti”. Ya yi ajiyar zuciya yana kallon Hajiya, “To shi ke nan zan yi mata wannan bayanin”. Hajiya ta kalle shi lokacin da ya ke kashe wayar. “Ya ya me ya same shi. yana ina‘?” Salman ya faraa cikin kwantar da murya. “Ba wani abu neba Hajiya. ciwon kai ne yasameshi amma yae da suuki…:.” “Karya ka keyi Salman. ka gaya mini gaskiya. na san ciwonsa ne ya tashi, jikina ya bani hakan. ka tambayeshi yana wani aibiti ne Sulman ya kuma kwantur da murya, “Ki yi hukuri Hajiya. zamuje zuwa gobe insha…” “Ban son gardama. Ba zan iya zama har Gobe ba bansan halin da yake cikiba mu tafi kawai tai saurin juyawa cikin gida yayindsma salman yai shiru cikin damuwa sannan ya juya domin dauko makullin mota ’ A bangaren Husna kuwa tunda suku dawo gida taci gaba da ayyukan gabanta. a kokarinta na ganin ta manta da komoi. amma zuciyarta ta kasu yarda da hakan. maganganun ‘yar uwar-ta suna ta mata yawo a kanta. Tabbas idan Dr. Abduljabbar Fulmata ya rasu itace sanadi. k0 kowa ‘bai sani ba ina zata kai dumbin zunubin idan Allah ya kamata‘.’Amma dai bata son a zargi wani abu, don haka take basarwa kawai don kada ta gane, ‘ ‘ Hajiya Falmata tana gaban gadon Dr. Abduljabbar ta zuba masa ido. Tana zubda hawaye tana’kada kai. “Allah kasan ‘bani ‘da kowa bayan wannan ‘yaron Allah kai Ka jarrabe‘ shi da Wannan ciwon da muka rasa maganinsa muka kuma rasa shawo kansa. Ya Ubangiji‘Ka kamo Karshensa ka tashi kafadarsa murtala yana gefe yace ki kwantar da hankalinki hajia jikin yayi sauqi zai iya farkawa daga yanxu zuwa ko wanne lokaci likita ya tabbatar mana da hakan murtala towai meya sameshinema nasan ciwon bai tashi sai ranshi ya baci ko wani abu akai masa ne ? Murtala yace wlh ban saniba ina ofis akaimin waya wai ya fadi a makaranta amman dai tunda ya samu sauqi kibar maganar kawai hajia zai tashi insha allahu Hasna tana kwance a gado ta kasa barci sai juyi kawai takeyi ta bude ido ta kalli agogo qarfe biyu da rabi na dare abinda yafi tayar mata da hankali bai wuce rashin sanin halin da DR Abduljabbar yake ciki ba shin ya mutune ko yana raye waye zai bata wannan amsar?ta miqe zaune tayi zaman gefen gado ta hada uban ta gumi ta dan Ta juya ta kalli husna daketa sharar Baccinta. Ta yunkura ta miqe ta nufi bandaki ta dauro alwala. Ta soma nafilar sallah. Sai gata tana kuku cikin ruku’u da naiman taimako gurin ubangiji a akan ya raya, Dr. Abduljabbar. kada Ya dauki rayuwarsa ta ‘sanadinta. Idan hakan ta kasannce ta shiga uku. kusan haka ta raya daren tana Sanar da Ubangiji damuwarta‘. ; Da safe kam kasa yin kwalliyar data saba tayi. har Mumy dinsu tayi mamaki sanda taga ta iso ta kalle ta tana fadin. “Hasna’ yau lafiya na ganki haka da dogon hijab ‘kamar matar “liman’ Suka yi dariya. Hasna tana kallon kanta. “Kawai dai nayi sha’awarsa ne Hajiya Aisha ta gyada kai. “‘Da haka kike shiga kinfi kyau wallahi”. Husna tana kallonta tana dariya. “Nima na gaya mata haka amman ta dinga wannan kwalliyar kamar aljana Hasna ta daure rai. “Na san haushi ki keji dun na fiki kyau Husna ta tuntsire da daria: ai ni bani shafe-shafe irin naki. don haka dole a ganni a natural beauty”; “Ko nayi kwalliya ko ban yi ba ni mai kyau ce Mumy dake ta ‘kwasar dariya ta’daga musu hannu. “Ya isa haka dan Allah. koma dai meye ai kamarku guda ce babu bambanci…” Hasna ta katse ta. “Amma wallahi‘Momy kowa yafi son fatata don irin ta mutanen Etofia”; ce Momy ta kuma tuntsirewa da dariya. idan da sabo ta saba da shiriritar yaran nata da kishi tun suna Kananu. Ta daga musu‘kai, “Wallahi yau zaku rasa lakcar safe. ku. bari idan kun daWo saiku ci gaba— ,da gWada kyan Da wannan aka rufe chapter suka nufi mukaranta. ‘ Suna isa Hasna ta nufi- can wani bangare ba Bangarensu ba. Husna ta bita da kallon mamako “I‘na kuma zaki ne? “Zan gaya miki idan na dawo kai tsaye office: din; Dr: Abduljabbar ta nufa.-tayi;tsaye daga nesa tana qarema office din kallo babu alamar akWai .mutum da~ aciki daman ,bataga.m0tarshi ba. .yau a inda ‘ya.;saba ‘ajiyewa Ta shiga, :tsananin damuwa: da tashin , ~hankali,: ta jima a—tsaye :tana sakawa. Da kwancewa bata san wanda,-zai gaya. mata halin’ da ,yake ’Ciki ‘ ba.-; bata san wanda: zata tambaya shin :yana ‘raye ne koya; rasu ,ba ..Hakanan ta kada kai ..:ta bar‘gurin da tsananinsa :damuwa da ‘ sarewa. 2m k0,; data:isa hall din nasu da za suyi lakcar wasu’ da dama sunyi mamakin ganinta haka‘ yau. Hasna sarkin gayu. sarkin kyale‘kyale,da kwalliya‘itace’ yau da dogon hijab K0 :da xa a.musu lakca ma babu’ Wani abu da tanke fahimta. domin hankalinta bai .tare’da ita. wuni ta yi sintiri a;,gurin amma bata sami komai game da abin da take son sumu ba. *** *** *** Dr. Abduljabbar ya farka da safe lokacin Murtala ya yi musu sallama don komawa gida shirin tafiya gurin aikinsa. Hajiya tana’gabansa ta zuba masa ido. shi ma Salmanu baya nan. ya tafi samo musu abin kari. Yana juyi ta mike ta isa kurinsa tana yi masa sannu. Mamaki ya cika shi ganinshi a gadon asibiti a kwance. ya kalli Hajiya da duk ta rame ta a dare daya. cikin sauri da hanzari Kwakwalwarsa ta fara tunasar da shi abin da ya faru. da lokacin da ya yi yunkurin sanya mukulli ya bude motarshi amma ya kasa. ya yi kokarin kakaro murmushi don kwantar wada mahaifiyarshi hankali. ‘ikin tausayawa da tsananin soyayya taci gaba da magana. “Sannu Abdul. sannu. ya ya jikin‘.’ Me ya keyi maka ciwo yanzu?” ‘ Ya yi murmushin ,dai yana kokarin mikewa zaune. Ta jingina masa filo a hayansa ya dan runtse ido ya bude Babu komai hajia babu abinda ke mini ciwo fuskarta cike da murmushi tace alhamdulillah haka nakesonji banyi bacci cikin kwanciyar hankaliba sam na kwana cikin tunanin yaddah za,ai ka rabu da wannan ciwonne ciwon dake neman rabani dakai ya kaika lahira kiyi haquri hajia zai daina watarana ki daina tashin hankalinki don alllah idonta ya ciko da kwalla yaya kakeson nayi kaikadai ka ragemin idan na rasaka bansan ya zanyiba hawaye ya fara zubo mata ta juya gefe don kada ya gani yayi shiru cike da damuwa duk sanda mahaifiyarsa ke wannan maganar sai yaji sai yaji tashin hankali ya cikashi dama zai iya cika mata burinta da yayi mata amman bazai iyaba bazai iyayin aureba har abada mai yasa yaxa,ai na sani muje zuwa cikin sanyin murya yace kiyi haquri hajia watarana zanyi Tadan qara fusata ba zakayiba abdul da zakayi da tuni kayi maika rasa a rayuwarka wanda zai hanaka aure kanada lfy kanada dumbin dukiya kanada gida mai zai hanaka aure yayi shiru gamida lumshe idansa shi kadai yasan abinda ke damunsa bazai taba sanar da kowaba har abada amman yana tsananin tausayin mahaifiyarsa da gaske batada kowa sai shi mai zai sanya baxai iya kyautata mata ba ganin yayi shiru yadan tayar mata da hankali don tasan baison damuwa musamman a yanxu da yake cikin wannaN yanayin don haka cikin sauri ta gyara fuska zuwaga lallashi da murmushi shi kenan ka kwantar da hankalinka yi addu,a tausayinta ya kuma cikashi tanasonshi batason damuwarshi dama zai iyayin aure dama zai iya kyautata mata da yayi daidai lokacin salman yai sallama ya shigo da flask da wani dan kwando na kaba dake cike da kayan marmari a hannunsa. “Yauwa Sulmanu. kawo nan. Ta amsa ta jera akan yar lokar da ake jera kaya ta kalli DR Abduljabbar zaka iya zuwa kayi wanka kayi sallah da wanke baki ko kuma sai salman ya taimaka maka Ya yunkura ya mike. “Ba na jin komai, yanxu zan iya”. .. Ya nufi bandakin ta bishi da kalo tana dan kada kai da farin cikin ganin yaddaya yi din. ** *** *** Kwanaki suna taja. rayuwa na sauyawa ga kowa banda’ Hasna data,.ke Cikin. damuwa. duk ta rame ta zabge. zuwa yanxu ta tabbatar da Abdul’bai mutu ba._*amma kuma bai da‘laf’iya. yana ‘Cikin mummunan hali. duk da labarin ma a bakin jama‘a takeji Husna ta tattarata ‘ta watsar,domin ta gaji da tambaya da lallashi. ta bar lamarin a“ alhakin Abba da shi ma yaketa naci a kanta ta ‘ Qi sauraronsa harya shiga damuwa Satin DR Abduljabbar daya a asibiti ya samu sallama ya koma gida saidai zuciyarshi ta kasa samun nutsuwa gameda abinda hasna tai masa daya juya ita yake gani lokacin da take masa wannan cin zarafin dunda yake ba,a taba masa hakaba ya rasa mema zai mata wanda zai zama fansa ga abinda tai masa idanma korar tata yai bai birgeba domin tayi zaton hakan yafi dacewa yai wani abin sabanin tunaninta zaidai bari yadan qara samun sauqine sannan yaje da ramuwarsa gareta Mai gadi yana zaune yaji anata horn kamar za,a kashe dodon kunnensa ya miqe da sauri ya bede yar qaramar kofar da yake leqawa don ganin ko wanene sai yaga baisan baqonba amman da alamar yanada girma da daraja koda bai barshi ya shigoba ya kamata ya saurareshi yaji abinda ya kawo shi don haka ya bude kofar ya fita ya qarasa gamida masa sallama barkadai ranka ya dade gurin wa kaxo ne? Bakoqon hasna neni tasan da zuwana jika sanar mata ya bashi amsa mai gadi ya daga kai da gamsuwa sannan ya nufa kofar ya bude gamida bude masa babban gate din gidan ya shigo bayan ya rufe ya nufi cikin gidan da sauri kasancewar ranar asabarce babu makaranta kuma yammacine yan matan da mahaifiyarsu suna babban falo suna kallon wani sabon film a tashar arewa24 mai gadi ya iso ya tsaya daga bakin qofa yana sallama hajia ta kalli kofar shigo mana malam habu Mai gadin ya shigo cikin girmamawa ya gaisheda hajia aisha hankalin yan matan nakan plasma din dake manne a jikin bango suna kallon wani shiri mai taken. Mu kula dasu mai gadi ya qara kwantar da kai da girmamawa ranki ya dade hasna kece da baqo hankalinsu yayi kansa da sauri suka dubeshi cikin mamaki hasna ce ta fara Magana hasna kodai husna baba mai gadi? Yadan gyara tsayuwa hajia ke dindai yacema kinsan da zuwansa domin kunyi dashi zaizo Nasan da zuwansa to waye wannan kai karyane bansan da zuwansa ba kaje kace bansanshiba a,a baza,ai hakaba hasna ki tashi kije kiga ko waye wata qila babban baqo kikai husna ta fada da tsokana Hasna ta dalla mata harara da takaici tace bazanje dinba aiba neman kasuwa nakeba malam habu kaje kace masa kawai ya tafi ban sanshi ba yi haquri autata tashi kije ko gaisawa kawai kuyi ki dawo wulaqanci babu kyau hajia aisha ta fadi tana dauri dariyar dake fuskarta din kada ta qara tunzurata malam habu ya juya yana dan murmushi hasna ta tashi tana dan kukkumbura baki da fushi ta dauki wani gyale dake kan kujera ta nufi kofa tana ci gaba da zumburo baki Da yake doguwar rigace mai kwalliyar duwatsu a jikinta. Suka bita da kallo suna dariya har ta fice. Hajia ta waiga ga Husna da ke dariya. Tace “Kinataa dariya. Allah ya sanya har su gama su dawo rigimammen nan bai zoba Abba”. Husna ta kada kai, “Ba zai zoba insha Allah. kin san ma bazata dade ba zata dawo, don ma kin matsa ta fita ne”. Hasna ta fito tana hangen sabuwar motar dal data tsaya a harabar gidan nasu don daga ganin motar ba,a dade da baretaba‘da rashin sanin motar. cikin ranta tama fadinn, k0 wane dan iskanne yayi qaryar saninta zatai maganinsa yanxun nan. Ta tsaya kyam daga inda take taqi motsawa, don tasan kowaye cikin motar yana hango ta Ta rike qugu tana murguda baki ganin na cikin motar bai fitoba a ranta ta ba shi wasu mintina ne da zarar bai fito ba zata juya abinta. Shi kuwa daga cikin motar Kare mata Kallo yakeyi yana kada kai dukkan kudirinsa da burinsa a dan kankanin lokaci wannan yarinyar tayi nasarar wargazasu yadai daure ya ziro kafarsa domin qoqarin fitowa hasna ta kuma motar ido har zuwa sanda na cikin motar ya kammala fitowa ta waro ido cikin mamaki da fargaba sanda fuskarsa ta bayyana cikin wani irin sauti mai kama dana shidewa tace DR Abduljabbar Falmata me yaxoyi gidanmu ? Yadan tsaya yana kallonta da murmushinsa dake bata tsoro har ga sauran dalibaima jikinta yadau rawa domin tasan meya kawoshi gidansu ko ya kawo mmata takardar sammaci daga kotu ne tayi tsaye ta rasa abinyi ya nufeta kai tsaye hannunsa cikin aljihu yana ci gaba da murmushi duk takunsa daya gareta kamar ana tsikararta da mashine a qahon zuciya ya isa ta tsaya a gabanta har lokacin murmushin kan fuskarsa bai dauke ba. ya ce. “Na yi zatin jarumar gaske ce ke daga ganina a gidanku sai gashi duk kin “wani rikice Ta yi ajiyar zuciya tana kokarin daWo da nutsuwarta. amma ta kasa cewa komai don har lokacin tana Cikin kidimarr ganima. Ya kara gyara tsayuwa. “KWantar da, hankalinki, ba daukar fansa ya kawo ni ba, sulhu da ban hakuri na zo nema. don na yarda ni ne mara gaskiya. ‘ ‘ ‘ Sai a lokacin ta sami damar yin magana bayan doguwar ajiyar zuciya da ta yi. “Ka ga don Allah idan ma ka zo cin zarafina ne ba a nan ne ya dace ba sai ka bari idan na je makaranta’kayi dukkan .abin da za kayi” “Waye ya gaya miki haka. ai k0 .da na rasa raina ba ki daukar laifin balle da na rayu. bubu sauran fada. Ki taimaka dai ki bani gurin zama kafin na fadi kin san har yanzu patient ne ni wani nannauyan ajiyar zuciyat qara ajiyewa a ranta tace Shin wai-mafarki, nakeyi ne k0 kuma gaske………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button