ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣1⃣

“Babu daya. amma bai dace mu zauna‘ . ni daya mace ba…” . , Yara guda biyu suka: zagayo daga; bayan gidan da gudu suna tsere sukai cikin gida Ta bisu .da kallo har lokacin‘ yana kallonta ya’harde hannaye a kirjinsa.Kin aminta gidan mai iyalaine nan ko ” Ta yi dan murmushi. “Ni fa ba ‘wai. Qin yarda nayi da kai naiba. Taba shi amsa. ; “Kin yi daidai. har kimarki ta kuma Karuwa a idona. mu shiga Karima nata jiranki daman”. Ya wuce gaba tana biye da shi a baya suka nufi cikin gidan. ‘ Duk da cikin kudi da gata ta tashi amman tsarin gidan Murtala ya burge ta kwarai da gaske lafiyayyen falone kusan guda uku. Hotonsa dana matar‘sa ne kala-kala suna yi wa juna dariya. sai’ da suka ‘isa falo na uku sannan suka zauna. Suna zama Karima da Murtala suka fito Karima cikin’ Shigar alfarma tana fadin “oyoyo matarmu”. ‘ Mace kyakkyawa mai tsananin fara’a; tafi kama da jinsin sadaka yalla. Ta isa kusa da Hasna ta zauna tana ci gaba da yi mata sannu da zuwa. Hasna ta saki jikinta tana amsawa. ranta ya yi Wasai don tana son mutane irinta masu faram faram “‘Yau dai gani ga wacce Abdul keso. Abin dana jima ina addu’ar Allah nuna mini”. Karimu ta kuma “Lallai kam, Allah ya so ki da kallon soyawa mai tsada, bai wuce ki ba Ai ni na sha kallo”. Murtala ya fada da tsokana. Hasna dariyar kawai ta keyi, sai ta manta da dukkan damuwarta ma, Abdul ya ce “Matsala ta da ku shegen surutu, shi ya sanya ban son zuwa gidan ku wallahi’ Hasna ta kalle shi, “Ni kuwa na ji dadi dan zuwan da na yi”. , . ;‘ Karima ta doka hannu “Shi kenan na ci gari tunda mai ranka ba a kushe mu ba, Hasna ya ya gida da karatu da kuma fama da wannan rigimammen?” Ta nuna Abdul da ke murmushi. “Duka Alhamdu lillahi, ya yara?” Hasna ta ba ta amsa gami da tata tambayar. Karima ta ce, “Yara suna nan kalau, yanzu suka shigo daga kwallo suna gurin mai aiki tana musu wanka ne…” “Don Allah ku bar mu haka kuna cinyé mana lokaci ba mu yi‘ abin da ya kawo mu ba”. Abdul ya fadi Cikin tsokana. Karima ta mike; WaIIahi ba don kai zamu tafiba, dOn Hasna kawai, za mu tafl, Dee ~ taso mu shige Ciki Murtala ya mike, “Lallai kam ya ci darajar Hasna, bakuwa kuma salaha”.‘ . Suka ‘yi dariya gaba dayansu, Abdul na fadin, “Na ji aje dai sarakan xance”. Suka Wuce suna dariya, ya dafe kai yana ajiyar zuciya. “Wadannan mutane akwai zance kamar cakwaikwaiwa. Ta yi dariya. “Ni kuwa sun burge ni wallahi, ina son iyalai irin haka”. “Kwantar da hankalinki gidanmu sai yaf1 wannan dadi, na gaya miki”. Ta kada kai ba ta ce komai ba, domin ya famo mata ciwon da ke ranta, ta ce. “Wacce — shawara ka yanke a kan matsalarmu ne Malam, Daddy yana da kafiya, sannan suna tsananin ji da‘Abba cikin family dinmu, babu wanda zai bani goyon baya a kanka, ina fargabar rabuwa da kai”. Tayi narai—narai kamar za ta fashe da kuka ya yi shiru yana tunanin abin da ya dace ya ce mata. ya kada kai ya ce “Saura kwanaki nawa ku fara jarabawa, na ji an kafa muku timetable k0?” Ta dinga dubanshi ‘da mamaki kafin ta‘ yi magana. “Ya ya muna magana mai muhimmanci za ka sako wannan Malam‘? “Wannan ma mai muhimmanci ne, ba ni amsa kafin ki ji abin da nake son cewa”. Ta rangwadar da kai, “Saura kwanaki :- shida mu fara”. Ya gyara zama, “Yauwa’ abin da na ke son ji ke nan, kin Bata Tsawon shekaru kina karatunki bai kamata kiyi asararsa a lokaci daya ba”. “Kamar ya ya? Ban fahinta ba Tana kallonsa ta ke maganar. “Idan ki ka matsa da maganata a , wannan lokacin za ki iya asarar karatunki, ‘ domin mahaifinki ya san ni malaminku ne, sannan matsala zata miki yawa har ta hana ki yin karatun da za ki iya cinye jarabawa, don haka ki kwantar da hankalinki ki yi kamar Kin haqura dani. ki bari har ki kammala jarabawarki. a sannan ya dace muyi komai Ta yi ajiyar zuciya da damuwa, “Amma baka ganin hakan zai iya janyo matsala. ya ya kuma zan yi da rashin ganinka‘?” “Shi ne maganin matsalarmu, ganina kuma koyaushe xa mu hadu a makaranta, idan kuma ranar karshen sati ne sai mu hadu a nan, ina ganin hakan shi ne mafita”. Husna ta yiru tana juya zancensa, ita fa ba ta Ki ta rasa kamai a kan ta rasa shi ba, amma ba ta son ya. fahinci tana da gaddama k0 musu don haka ta bar maganar kawai. shi ne ya yi kokarin sauya hirar domin mantar da ita damuwar da ta ke ciki. A nan ta yi sallar isha’i sukaci abinci tare da Karima, shi kuma da Murtala. Sai ta ji Karima ta shiga ranta lokaci guda. sanda za su rabu sai da ta ji kamar kada ta tafl. A can gidansu Abba har ya gaji da jiranta, ga shi duk wayoyinta a rufe suke ya ishi Husna da tamhayar kwakwaf har sai da ta gudu ta bar masu falon. Hajiyarsu ma nan ta bar‘shi. sun gaisa cikin mutunci duk da a ranta ba ta jin Kaunar auransa da na diyarta, amma tana kokarin Boye hakan cikin ranta ba ta son ya fahinta, don haka. har hira sai da suka yi kafin ta shiga ciki ta bar shi a nan. HaSna ta ma manta da shi sam, farin ciki ya cika ranta, domin har Kofar gida Abdul ya rakota cikin motarsa, ita ma tana tafe a tata ‘ sannan suka rabu, don haka kai tsaye ta shigo falon, hargowarsa ce ta, sanar da ita yana nan. ” ‘ ‘ “Hasna, daga inai’kike? Kin san‘awanni ‘ hudu kenan ina zaman jiranki?” Ta waiga ta kalle shi yana nufota ransa a Bace. ta yamutsa fuska. “An sanya mini takunkumi ke nan ban sani ba k0?” Ganin yadda ta Bata rai ya sanya shi saurin saukowa ya ce “Na ga alama fada kikeji yau. to ni ba shi ya kawo ni ba hira na zo mu Yi mai dadi ta tabe baki. “Hira kuma‘? Kaga malam don allah Ka shafamin lafiya, baCCi ke shan kaina sai da safe”. Ta kada kai ta wuce. Ya sha gabanta da sauri yana huci. “Haba Hasna: wai me ki ke son mayar da ni ne don Allah ya jarrabe ni da sonki sai kiyi ta wulaqanta ni? Ki kalle ni da kyau mene ne wanda ki ke kulawar ya fi ni? Kyau k0 kudi;ko ilimi? Mene ne ya ke da shi ba ni da shi iyee?” “Nagarta Ta ba shi amsa a gadarance. Ta ci gaba da magana. “K0 da ka fishi komai da ance ya fi ka nagarta. Ka ga ya yi maka fintinkau k0?” “Karya ki ke yi wallahi, babu wani abu da ya f1 ni, kalle ni da kyau”. Kamar ta fashe da dariya ganin yadda ya ke wani hankoro kamar zai doke ta, Sai kawai ta yi murmushi ta kada kai ta zagaye ta wuce. Ya bi ta da kallo kamarya bi ta ya finciko ta, amma ya daure’ya juya a fusace da nufi motarsa ya bar gidan, don idan akwai abin da ya tsana bai wuce maganar Abdul ba, dole zai dauki mataki a kan hakan. *** *** *** Kwanaki sun ‘ja har sun fara gabatar da jarrabawarsu, Hasna tayi kokarin kwantar da hankalinta tana karatu sosai, domin idan ba ta tare da masoyinta a waya, to tana tare da shi a makaranta, k0 kuma gidan Murtala, har kowa ya gano abin da ke tsakaninta da Abdul, ina wuta ‘yan matan jami’ar da ke kaunar Abdul su jefa ta, k0 wucewa ta yi sai an yi zundenta, amma ita kam k0 a jikinta ba ta damu ba, domin ta ji ta gani a kan son Abdul ba, tana gama takardarta ta Karshe ofis din Abdull ta nufa sai dai ba ta same shi a Ciki ba. dolé: ta kira wayarshi. Mintina kadan ya iso ya bude kofar ofis din suka shiga tare, ta yi tsaye tana kallonsa yana kokarin zama ya waiga ya kalle ta da mamaki. “Ya ya ki zauna mana”. Ya fada yana kallonta ganinta tsaye Kikam. Ta karkata kai, “Ba lokacin zama ba ne yanzu, ina sauri ina son mu yi maganar da ya kamata yanzu na wuce”. Ya yi» ‘dan murmushi‘ ya qarasa kusa da ita ya tsaya yana kallonta. , “To ya ya aka yi ‘yammata?” “Ka bar wasa don Allah Abdul, mu yi maganar da ta dace, mun kammala jarabawa yau”. Ya yi doguwar ajiyar zuciya yana ci gaba da kallonta. . “Wannan shi ne abin da ke damuna tun da ,ku ka fara jarabawa, kina ganina kamar cikin farin ciki ‘amma ba haka ba ne, na rasa me ke damuna Ta kasa cewa komai sai kada kai kamar kadangaruwa tana kallonsa, Ya yi dan gaba kadan hannuwansa cikin aljihu yana shirya abin da ya dace ya gaya mata. ’ Lokacin da ake gudu akan auran dole ya wuce Hasna, lokacin da a ke bore a fada rijiya’ mai gaBa dubu ya wuce. Ilimi da Wayewa sun ‘wadata, don haka ba mu da sauran abin yi bayan addu’a”. Ya waigo ya kalle ta domin yaga yadda ta dauki abin. “Addu’a ita ce abar da muke bukata‘ Hasna”. Ya sake nanatawa yana kallonta. Ta yi doguwar ajiyar zuciya. “Tabbas muna buKatar addu’a, amma sai mun hada da kokarinmu. Ina ganin zan yi fito-na-fit0 da kowa a yanzu game da abin, ba zan iya jure rashinka ba”. “K0 me za ki yi ki yi a sannu, ka’ da ki yi abin da zai bata‘ ranmu, ina son zuwa na tunkari Daddy din ma kai tsaye, amma ya ya ki ka gani‘?” Fuskarta ta fadada da farin ciki. , “Wannan shi ne abin da za ka yi, zan ‘yi ta nazarinsa daga yau zuwa jibi zan sanar da kai lokacin da ya f1 dacewa ka Shiga, har‘ na ji na‘ zama taka ma in dai ka yi hakan”. Ya harareta a wasandare. “Waye ya ce miki da ni ragoo ne? Ba zan ji tsoron k0 harbi ba ne in dai a kanki ne”. ” “Kar dai ka cikabaki, ka‘bari na ga iyakacin jarumtar’ taka tukunna”. Ta ba shi amsa. “Kin ga Zauna mu yi hira sosai ban son tsayuwar nan kamar masu tirenin’din soja”. Ya fada yana kallonta da tsokana. “Sauri nake yi, na. san Husna na can na nemana, sai mun hadu a waya anjima”. Ta juya ta tura Kofar fita, ya bi ta‘ da kallo yana murmushi da kada kai, sannan ya koma‘ya zauna ya dafe kanshi. Allah ya sani yana tsananin kaunar Hasna, bai san ya’ya zai kasance ba idan ya rasata ba, dole ya; dage da’ addu’a amma Ubangiji zai amsa ‘addu ar tawamakuwa bayan ‘na kasance mai babban laifi‘? Hawaye ya fara zub0wa daga idonsa, bai Son ya dinga tuno abin, amma ya” shige ” cikin ,rayuwarsa,‘ dole: ya dinga tuna shi,’sai kawai ya mike ya nufi bandakin’“ da ’ke cikin ofis din domin dauro alwala, duk da lokacin bai kamata a yi sallar nafila ba, tunda la’asar ta Wuce yana da damar yin lazimi da tasbihi, wataqila Allah zai ji qansa ya yafe masa. Shin wannan wanne irin laifine? ya za,ai na iya sani muje zuwa Suna zau‘ne a falo suna kallo Hasna tana zaune a kan kujera’ta harde qafafuwanta tana ‘shan kankaha da . kecikin, faranti, Hajiyarsu da Husna. suna ta tattaunawa a kan. film din da suke’kallo, tana jinsu kawai taKi sannya musu baki, don ~hankalinta bai tare .da‘ su yana can wata duniya. Mahaifinsu ya shigo. ‘ Mamaki ya kama su gabadaya, domin yau a gidan Anti Kubra ya ke- bai Shigowa irin wannan lokacin, Hasna da;husna suka yi masa sannu da zuwa, ‘ gami da qokarin . mikewa su bar falon,’yakallesu su’da sauri. “A’a, ku zauna da ku zan yi- magana ai“. Hajiya Aisha ‘ta‘Kara hade fuska domin tana fushi da shi, ga shi kuma ‘yau yana gidan’ , Antin da ba ta son k0 jin sunanta, don haka da Kyar ta iya yi masa sannu da‘ zuwa. . _ Ya amsa shi‘ ma fuskarsa ba a sakeba,’ sannan ya kalli su HUsna wadanda ‘suka zauna”a* tsorace, ya fara magana. ” ‘ ” “Gobe ki‘ sanar da Hashim” ya turO magabatan nasa tunda an kammala karatun gabadaya, ina son kafin ku tafi bautar kasa kuna dakunanku”. Hajiya Aisha ta tabe baki. “Akan Wannan maganar ka fiti cikin wannan ‘daren Alhaji? Idan ka bari ma ai gobema ranace ko. ” ” ‘ “Haka kike ‘gani, amma~ba. zan’ iya bacci idan ban‘ aiwatar da hakan ba, Kubra ke sanar da ‘ni sun kammala karatu yau, mai ya sanya ba ki sanar dani ba?” Ta kuma ‘hasala, “Tunda ‘ita ta gaya maka ba dole sai na ‘gaya maka ba ni-ai”. ‘ Kamar zai yi magana sai ya fasa‘ya yi shiru kawai, amma duk da haka ba’ta huce ba- ta ci gaba da‘magana. “Har za kace wani ban gaya maka halin da’ suke cikiba, ka damu da mu ne yanzu? Inda ka damu da da ka sani din ai da ka sani k0”. ’ . ,, Ya yi murmushi ya kau da kai gefeya kalli‘ Hasna da ta~yi qui-qui tana kallonsa ya’ fara mata magana. Ke kuma Hasna ki zauna» cikin shiri lokacin da iyayen mijin Husna din suka sanya shi ne lokacin bikinki da Abba idan Allah ya so . Ya mike tsaye ba tare da kula da yanayin da ta shiga ba, ya kalli Hajiya Aisha ya gama kai ta karshe, ya ce. ’ “Zan wuce ni sai da safe kenan?” Tsakanin matar tashi da yaran aka rasa wanda zai iya ce masa sai da safe har ya sanya R Kafa ya fice, sai binshi da suka yi da kallo. . Hakan ya dan taBa ransa amma ya dake bai juyo ba ya wuce kawai Yana fita Hasna ta fashe da kuka tana surutai. ‘ “Shi ke nan don ni kadai aka tsana za a yi wa auren dole, kamar ni ba mutumba ba za,a barni na zabi son raina ba, Momy kuma kina kalla kin kasa cewa komai…” Ta kuma rushewa da kuka. Hajiya‘Aisha ta mike ta nufe ta ta janyo ta jikinta tana lallashi. ” “Kin ga ki yi shiru ki bar ni da shi kawai, muddin ina gidan nan auran nan ba zai yiwu ba, abin da ba a taBa yi wa wani ba, ba Za a fara yinshi a kanki ba. Ki kwantar da hankalinki”. Sai a lokacin ta dan sami sauki cikin ranta ta rage kukan, mahaifiyar tata‘ ta jima tana rarrashinta kafin ta samu ta yi shiru, ta kama ta kamar wata karamar yarinya ta raka ta dakinsu. Hajiya Aisha tana fita kiran wayar Abdul ya shigo ta, gage ido ta dauko wayar ta ‘danna tare da kafa: wa a kunnenta. Husna ta yi – murmushi ta; kwanta ta ja kanta ta rufe. “Ya ya kaiyi ne na ji ki cool?” Abdul ya faramagana. Sai hawaye ya; sake Ballewa kamar da bakin kwarya, ta kasa furta komai. Yana kwance sai‘ ya mike zaune da sauri, domin’ya fara jiyo shesshekar kukanta. Yaci gaba da magama. “Look Hasna, ki bar kuka ki mini bayani don Allah, me ya sake faruwa kuma?” Sai ta fashe’ da kuka kamar daman jira ta ke yi, wannan ya iara daga‘hankalinsa, ya durgo daga gadon yana sauraran fitar sautin kukan nata kamar ‘zubar ruwan zafi a kan zuciyarshi. _ “Hasna, kukanki ci gaban” tashin hankalina ne kowace daKiKa,’ don Allah ki yi shiru ki sanar da ni abin da kefaruwa”. ‘ ‘ Har lokacin ‘ta kasa ceWa komai sai kukan ya dan fara‘ hasala “Ki kashe wayar, gani nan ~ zan‘ zo gidan, komai zai ‘faru ya f1 mini wannan kukan dadi”. ‘ “Kar ka zo don Allah Sai a sannan ta iya’yin magana’.. Ya yi kWafa,””Ya’ ya za ki saka mini kuka a waya ki Ki sanar da ni abin da ke ‘faruwa, ki Ce ka da na zo.Hasna-ko kina son zuciyata ta buga ne na’ mutu?” ‘ ‘ Cikin shesshekar’ kuka: tace “‘A’a’, daman Daddy; ne~yace ‘maganar aurena da ,Abba daidai lokacin~ da ‘iyayen saurayin Sister suka sanya ne,‘ kuma- yadda ya fadi maganar babu wani Wasa k0 alamun SaSsauci’ a ciki‘ Bansan’ya’ ‘ya‘ zan’yi ba…” ‘Kukan ya kuma kwace’ mata. Ya dafe kai a fusace yana‘ hUci-. “0hh my god kin ga kwantar ‘da hankalinki don Allah, ki bari gobe zan zo na tadda Daddyn naku”. Ta dan sassauta kukan tana kokarin yin magana. “Ina ganin kamar zuwan naka zai iya janyo wata matsalar, Daddy ba shi da sauKi”. “Zuwan shi ne mafita, zan gabatar da kaina gare shi a Amai neman aurenki, ba zan damu ba k0 da zai doke nine “Kadai dakata mu ji yadda Momy za ta ce, don tace na bata .lokaci zata’yi masa magana”. “Shi kenan, ‘amma Hasna ki yi addu’a ki daina kuka, ki ~raya dare da roqon Ubangiji, hakan ne kadai mafitarmu. “Zan yi yadda ka ce din insha Allahu, amma ya kamata gobe mu hadu gidan Murtala”. ’Ba ya gari shi da Karima din, ba zan so kai ki gidan kowa ba”. Ta ka‘da kai. “Shi ke nan mu yi waya goben”’ Ta kashe wayar tana satar kallon Husna da ke gefenta a kwance; k0 ta ji abin da ta ce na‘ad‘uwar tasu, ga mamakinta sai‘ta ga ta bar gurin, sai ta jiyo muryarta a can falo tana dariya. Duk yadda aka yi waya ta keyi da masoyinta, ita kam ta huta,_ ba ta .da matsalar komai. Ta koma gado ta kwanta lamo kamar ‘yar mage tana tunanin abin da ya dace ta yi, amma dai dole za ta dage da addu’ar kamar yadda yace Kwanaki biyu -hasna yadda ta ga rana haka ta ke ganin dare, don ma dai ba‘ zaman banza ta ke yi ba, sallah da addu’a ta ke yi akan Allah ya kawo mata sauki. Yau k0 da gari ya waye kasa tashi ta yi da wuri, Husna da ta tashi ta ga ba ta ‘da niyyar tashi ta yi wanka ta fice falo don cin abinci. A teburin cin abincin ne Baban nasu ya ga ba ta ziba ita, da farko ya share kamar bai damu ba, can ya kalli Husna. “Ina ‘yar uwar taki ta shiga ne?” Husna ta kai loma bakinta, sannan ta Ce “Daddy‘ ba ta tashi daga bacci ba har yanxu”~ ‘ Hajiya kuwa kwafa ta yi don ba ta da abin fadi. ya kalle ta bai ce komai ba, har suka kammala cin abincin, har rana ta daga wajen sha biyu Hasna ba ta fito ba, mahaifin nasu yana zaune a falo yana kallo, amma gaBadaya hankalinsa yana Kofar sashinsu, burinshi bai wuce ganin ta fito din ba. Hajiya tana kula da duk halin da ya ke ciki, amma a zuciyarta cewa ta ke yi, kamar gaske Sanda karfe daya ta buga ya mike ransa a Bace ya nufi sashin nasu, Hajiya ta bi shi da kallon mamaki, sai taji kamar ta‘bi shi amma dai ta dake ta kyale shi. Husna tana falonsu tana ta rubuce- rubuce bisa wata ‘yar takarda’ ya shiga da sallama. Ta daga kai da mamaki, don ta manta rabon da ta ga mahaifinsu a dakinsu. Ta mike tsaye da mamaki. Ya ce. “Koma zauna ki ci gaba da aikinki, ina Hasna neko har yanzu ba ta tashi daga baccin ba?” Ta yi dam jim sannan ta ce “Ta tashi Daddy har ma ta’ yi wanka. nayi na yi da ita ta fita ta Ci abinci ta ce ba ta ci, da na matsa mata ma kamar za mu yi fada shi ne na rabu da ita, don tace fatanta bai wuce? yunwa ta illatata ba”. . , Ya kada kai, “Shi ke nan Ci gaba da abin da ke gabanki”. Ya nufi dakin baccin nasu kai tsaye Husna ta bi shi da kallo da: mamaki da kuma fargaba har ya bude Kofar. Hasna tana kwance a kan gado ta yi rigingine ta kura wa silirn ido ta jiyo sallamar mahaifinta kamar daga sama. Ta mike firgigit da fargaba ta kalle shi, yana tsaye ‘bakin kofar ya nade hannuwa a kirji yana kallonta ya fara magana. ‘ “Me ya hana ki fita ki ci abinai da: safe Hasna?”. Ta kau da kai gefe idonta ya cika da jwalla ta ce. “Ba na jin yunwa ne”. Ya dan yi taku kadan ya Shiga cikin dakin yana ci gaba da kallonta. ya ce “Ba kya jin yunwa? Me ki ka ci da ya hana ki jin yunwa? ‘Yar uwarki ta ce mini k0 abincin dare ma ba ki ci ba, haka ne?” Ta yi shiru ba ta ce komai ba, sai idonta da ke ci gaba da zubo da hawaye. Cikin daga murya da fada ya ce “Ba magana nake miki ba, me ki ka ci da ya hana ki jin yunwa?” Ta fashe da kuka sosai, jikinta yana rawa ta Ce. . “Babu komai; ba na jin yunwar ne kawai Ya kada kai yana huci “Hasna, ki ~ sani k0 da yunwa za ta halaka ki kamar yadda ki ke fata maganar auranki da Abba ba za ta sauya ba,” shi ne mijinki, shi na zaBa miki don haka ki kWantar da hankalinki ki sanya nutsuwa cikin zuciyarki shi ne abin da ‘yafi dacewa da ke, ba auren dole zan miki ba, auran zumunci ne zan miki, domin dan uwana ya fi karfin komai a gurina, sannan kece ki ka nuna amincewa da shi, tun farko ba ki taBa cemin ba ki son shi ba har sai da kowa cikin dangi ya aminta da soyayyarku sannan zaki bijiromin da wannan lamarin toki sani na rantse da allah koda sama da qasa zata hade saina daura aurenki da abba inkuwa kikaga hakan bai faruba to ina mai tabbatar miki da bana numfashi a doron qasane Hmmmmmm Mu hade a next page………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button