ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
3⃣5⃣

THE END

…………………………………………………kamar ana mini tafiyar tsutsa cikin duburata, wani daran bana iya bacci idan abin ya ciyo ni, wato wannan dalilin ya sanya Alh. Shazali yace zan neme shi, bayan komai nawa ya kare zan nemi taimakonsa ko kuma na neme shi ta hakan, amman na dake na daure Wani abu da na kula da shi bayan mun . tare da Murtala shine yana bin wasu turawa suna fita yawon shaye-shayen su, ban amince da wannan rayuwa ba don haka bana binsa, sai ma na fara koKarin janyo hankalinsa akan dainawa, ya amince ya dai na din amman sai ya fara nuna wasu halaye da ban san da su ba, har wani dare ya nuna mini abin da yake buKata tattare da ni, ban yi musu ba na amince domin ina neman mai taimaka mini daman, sannan Murtala shine kusan ke riqe da karatuna,daga nan muka kulle da shi, Murtala ya kasance shine wanda ya ci gaba-da taimaka mini akan karatuna da komai na rayuwata har zuwa lokacin da na sami aikin Tadi ina tabawa, duk da Murtala yana bin wasu ni da shi kadai na ke mu’amala, ban kuma taBa gayawa kowa labarin abin da rayuwata ke ciki ba sai Murtala, har bayan Murtala ya gamakaratu ya amince ya zauna ya Kara har zuwa Masters din sa, ni ma hakan na yi, . mahaifiyata sai dai na tura mata wasiKa ta hannun wani malamin mu ya kai mata sannan ya karanta mata, har zuwa sanda na kammala karatu muka dawo gida, Murtala shi ya shige mini gaba ta dalilin alfannar mahaifinsa na sami aikin da na keyi. Ban Kara bi ta kan Alh Shazali ba domin na san ya riga yayi qarfin da bazan iya yi masa komai ba, idan nace kuma zan tona masa asiri kamar na tonawa kai na ne, don haka na tattarashi na watsar sai dai idan na tina shi na yi Allah ya isa. Abin da muke yi da Murtala yana damuna, don na san illar abin ga addinina amman ya zame mini kamar masifa ya kuma sauya rayuwata gaba daya, bana son komai ba kuma na kallon mace, . watarana da na ji wani wa’azi da ya saka ni kuka akan masifar da ke tatttare da masu aikata irin abin da muke yi na fara nemawa kai na mafita, addu’a na fara dukufa sannan na shiga bincike akan yanda zan rabu da wannan masifa, sai na ga ashe zan iya samun taimako daga asibiti don haka babu bata lokaci na ziyarci likita akan matsalata aka bani shawara da magunguna gami da yi mini flushing aka fitar da dukka abin da ke duburata, na so Murtala ma yayi hakan yace mini shi dai ba zai iya dai nawa ba domin abin ya zame masa masifa, duk yanda na so ganar da shi ya toshe kunnensa har hakan ma ya so haifar mana da matsala, ban damu ba, ban kuma yadda da abin da Murtala yake sanar da ni ba. Tabbas na shiga masifa a wannan lokacin, na ji bana qaunar komai bana mu’amala da kowa amman na danne na hakura, lokacin da Murtala ya fare. neman auran Karima na yi farin ciki domin na yi tsammanin qarshen matsalar Murtala kenan amman har yayi aure bai fasa komai ba, bazan boye miki ba Hasna tabbas na sha wahaia har kuka na sha kwana yi idan masifar ta ciwo ni, hakan ya sanya na maida addua suka zama abin bautata, Lokacin da ki ka shiga cikin rayuwata kin taimaka mini kwarai da gaske gurin dawo da ni dai-dai har zuwa sanda muka yi aure, Hasna lokacin da kika tadda ni da Murtala ya z0 mini cikin damuwa akan yau ya rasa wanda zai nema jikinsa har rawa yake yi, na yi qokarin ya je ga matarsa amman ya Ki yadda ya fara roko na gami da yi mini wani abu da ya saba yi mini, wannan shine abin da ya ja ra’ayina har muka fara abin da ki ka ganmu, amman wallahi tallahi bamu aikata komai ba, ubangiji ya kuButar da ni, Hasna ban yi tuban muzuru ba, amman ba ina fadin haka don kin,yadda Dani ba, a’a ina fada ne don ki sami kwanciyar hankali akan rayuwar ‘yaâ €™yanki, na yadda na yi kuskure, amman saboda ke a yanzu na rabu da kowa har Murtala, kuma ko bayan na rabu da ke bazan koma bayaba na tuba, ki yafe mini, ki dawo ga iyayanki, wallahi na rantse zan miki abin da ki ke so.â€� Hasna tana karanta saKon Abdul tana kuka, ba ta taBa jin tausayin mutum ya shiga ranta kamar na yau ba, me ya sanya ba ta tsaya ta ji wannan labarin ba tun farko, nadama da dana sani suka shigeta, tabbas a labarin da Karima ta gaya mata na Murtala ma sanya shi aka yi shiga wannan harkar da karfi to me ya sanya itaba ta yi tinanin jin yanda mijinta ya fara ba, k0 da ace bar yanzu Abdul yana yi za ta iya yafe masa sannan ta sanya shi a hanyar shiri‘ya balle ma ya dai na. Saita tsinci kanta da nemo wayarta cikin sauri ta kunna su duka, saqonni kala~kala suka dinga shigowa amman wanda ta ke karantawa kawai shine na Abdul, magiya da ban baki yake mata, tun tana iya karantawa har ta kasa, kuka ta ke amman bata son tashin lya Fulani daga bacci, wani saqon Husna da ya shigo wayartata shine ya ja hankalinta, ga abin da ta ce “Ki kwantar da hankalin ki a duk inda kike Husna, Abdul yana gabda mutuwa, domin yau kwanaki uku kenan bai farka ba, zuciyarsa na gab da bugawa ya mutu kamar yanda likitoci suka ce! Wannan shine sakon da Husna ta turo mata, sai ta ji kukanta da damuwar ta sun karu, ta dinga bin sakonnin tana karantawa cikin kuka, sai ta fara neman wayar Husna ta ji halin da Abdul ke‘ ciki amman babu service kiran ya Ki shiga, ta kira wayar Abdul ma bai shiga ba, ta ji cikin jikinta ya tsira daga kanta har zuwa Kafarta ta dafe ciki tana kuka, amman cikin Korarin Boye muryarta kar lya, Fulani ta ji, ta dafe ciki tana jujjuya kai, ubangiji kadaya sanya Abdul ya mutu sai ta ganshi ta tabbatar masa ta yafe masa shi ma ya yafe mata, wannan itace adduâ €™ar da ta ke yi, haka ta kwana a zaune dandaragam. Lokacin da Iya Fulani ta farka da ta tsorata saboda ganin Hasna a zaune Cikin mamaki ta ce “‘Diyar nan ba dai ba ki yi bacci ba Hasna ta daga kai tana fadin Iya da ‘na,idar da sallar asuba zan tafi gida, zan koma.” Duk da kalaman sun zowa iya Fulani a bazata amman sai ta ji rashin,jin dadin tafiyarta. sai ta koma kusa da ita domin jin karin bayanin abin da ya sauya ra’ayinta cikin qankanin iokaci haka, Hasna ta sanar da ita sakon Husna, iya mai fura hankalinta ya ashi, ta ce su tashi suyi sallah sai,su tafl. Mutanan da ke gidan,da Iya Fulani, kasancewar a babban gida ta ke ammn kowa na bangaransa ba su ji dadin taf’lyar Hasna domin sun fara sabawa da ita, ta raba musu kudi suka rabu cikin jin dadi, shatar mota guda suka dauka bayan sun isa babbar tashar garin suka nufi kano kai tsaye, tafiya ce ta awa uku, sai Hasna ke kallon taflyar kamar ta shekara guda, addu’a kawai ta keyi cikin ranta har suka isa, daga kano Adai-daita sahu suka dauka shama‘ har asibitin, ba ta damu da yanayin da ta ke ciki ba. domin sanin halin da mijinta ke ciki yafi muhimmanci a gareta yanzu. Nurse din da ke kan kantab reception ta yi mamakin ganin yanda ta ga Hasna, amman kasancewar tana tambayar mijin ta ne ya sanya ta yi mata bayani, Hasna ta,nufi inda ta nuna mata cikin sauri jikinta yana rawa. A wannan lokancin an samu Abdul ya farfado daga suman da yayl amman allurar bacci kawai aka yi masa domin a samu dai-dai tuwar jininsa da ya hau kamin akai ga zuciyarsa da ake sanya ran yi masa aiki. Haj‘ Fulmata tana zaune akan darduma tuna lazimi wanda ya zAmo mata kamar numfashi a yanzu. idan har ba bacci ta keyi ba bakin ta yana kan ambaton sunan Allah ya baiwa yaronta lafiya. hasna ta turo kofa da sauri ta shiga hade da sallama. Hajiyar Abdul ta jUya da sauri cikin mamaki jin muryar hasna ‘ ta mike cikin saurl tana ambaton sunanta. Hasna kuka kawai ta fashe da shi da ta hango mijinta cikin wani irin hali,mutu kwa-kwai rai kwa- kwai. hajiyar Abdul ta rungumeta a jiki tana fadin “Kl ‘dai na kuka Hasna, ki kwantar da hankalin kl, na ji dadi da kika dawo kafin Abdul ya mutu ya nemi gafararki, Abdul ya kai matakin da ba zai tashi ba Hasna.â€� Hasna ta kada kai tana ci gaba da kuka gami da fadin “Na yafe masa Hajiya, kuma bazai mutu ba, Insha Allahu.â€� Sai a lokacin Hajiya ta kula da iya Fulani, ta karasa kusa da ita suka gaisa, Inna tayi wa Hajiyaya mai jiki,Hajiyar ta kama hannun Hasna ta janyota gefen gadon suka,tsaya suna kallonshi, numfashin sa yana sauka a hankali kamar ba Abdul ba, Hasna ta zauna a gefen gado sannan ta kamo hannun Abdul ta riqe a hannunta tana kuka, gami da ba shi hakuri, Hajiya ta yi ta lallashinta harta samu ta dawo hayyacinta sannan ta fara tambayarta. â €œMahaifanki sun san kin dawo ? Hasna ta girgiza kai alamar a’a, Hajiya Falmata ta kama hannunta ta rike kam kamar zatA qara guduwa ta ci gaba da yi mata magana. “Hasna ki kira iyayanki ki gaya musu ga kin‘ dawo hankalisu yana matuqar tashi akan batan da kikai Hasna ta gyada kai alamar â €� to Hasna ta kira, Husna tana dakinta tana shiryawa.  Husna ta kalli mijinta cikin tsananin farin ciki tana ci gabada magana “Da gaske kike Hansa? Ga ni nan zuwa, don Allah kar ki tafl ko ina.’â€� Ta kashe wayar tana dariya, shima mijin na ta dariyar yakeyi, sai ta fara kiran wayar mahaiflyarsu tana sanar da ita Hasna ta dawo cikin farin ciki, wani irin farin ciki ya cika Haj. Aisha gashi a ranar maigidanta yana gidan abokiyar zamanta, a tsarinta in dai_ yana ‘can gidan ba ta kiransa, amman yau tsananin farin ciki ya sanya ta kira shi, lokacin da ya ga kiran yayi matuKar mamaki ya kalli Kubran yana fadin. “Kubra abin mamaki yau Aisha ke kirana a gidan ki, Allah dai ya sanya laflya.â€� Anty Kubran ba -ta ce komai ba sai murmushi kawai ta keyi, ya danna wayar ya kara a kunncnsa, labarin da’ ta ba shi ya sanya shi miqewa tsaye cikin farin ciki yana Hamdala ga ‘ Allah, ko bai fada ba Anti Kubra ta fahimci abin da ‘ya faru,’ don haka ta taya shi farin ciki a zuciyarta ya kashe wayar yana kallonta cikin farin ciki. ‘ â €œHasna ta dawo‘ tana”asibitl gurin mijinta, yanzu ta yiwa ‘yar’uwarta waya.â€� “Alhamdulillahi, daman na gaya maka Hasna za ta dawo, ba za ta yi abin da zai tayar maka da hankali ba, ba za ta baka kunya ba.â€� Ya gyada kai cikin gamsuwa yana fadin“Na yarda da ke Kubra, ki shirya mu je asibitin yanzu.â€� Yau asibitin ya kasance cikin farin ciki da jin dad‘i saboda zuwan Hasna, abin da ya Kara faranta ran Alh. Sammani da ya ga Hasna ta re da Iya Fulani, hakan ya kwantar da hankalinsa gami da sanya shi jin kunya, domin rabon da ya jeya gayar da lyar tasa har ya manta, bayan sun gaisa sai kuma aka koma hirar yaushe gamo, anan ya tafi ya barsu, duk da ana cikin damuwar halin da Abdul ke ciki amman zuwan Hasna da dawowarta cikin damuwar halin da mijin ta ke ciki ya kwantar musu da hankali kwarai da gaske Haj. Aisha da Husna suma sun tafi da yamma tare da lya Fulani suka bar Hasna da Hajiyar Abdul, sai hasna ta tsinci kanta a tsananin kunyar matar, don tana ganin itace silar shigar halin da danta ke ciki, amman ita Hajiyar ce taci gaba da yi mata nashiha, bayan sallar isha’i ta buqaci Hajiyan ta taf’i gida ta huta za ta kula da shi, hankalin Hajiya Falmata ya kwanta domin tanaji a jikinta laflyar danta tana gab da dawowa, don haka suka tafl da Salmanu. Kamar Hasna jira ta ke su flta sai ta matsa jikin mijinta sosai ta riqe hannuwansa ta Kura masa ido watairin soyayyarsa da tausayisa ya dinga shiga zuciyarta, ya sha wahala cikin rayuwasa, ta sanya hannunta tana shafar kansa, duk sakan daya soyayyarsa na Kara shiga cikin zuciyarta, sai ta kwantar da kanta akan Kirjinsa tana jin kamar ta yi masa magana ta ce ta dawo ya farka, ta jima kanta akan kirjinsa tana jin bugun zuciyarsa har bacci ya fara dauketa ba tare da saninta ba. A cikin baccinsa ya dinga jin wani abu yana shiga ransa, kasancewar Ubangiji shine ke hada zuciyoyi su kasance akan soyayya, numfashin Hasna da bugun zuciyarta suka dinga shiga jikinsa har ya bude idonsa a hankali, bai san inda yake ba, bai san ina yake ba sai da ya gama bude idonsa gaba daya, sai ya ji kansa yayi nauyi ya Karewa dakin kallo cikin mamaki, sai ya ji kamar numfashin Hasna a jikinsa abin da ya jima bai ji ba, ya kalli gurin da idonsa sai ya ga itace zaune a gefensa ta dora kanta akan kirjinsa tana bacci, hannunta kam-kam cikin hannunsa daya, ya kalli daya hannun sai ya ga Karin ruwa ne a jiki. a hankali abin da ya faru ya fara dawowa cikin kwakwarwarsa, amman abin da ya kasa fahimta shine ganin Hasna a kusa da shi, shin ta dawo ne? ta hakura ta yafe masa abin da yayi mata , k0 dai mafarki yake yi, sai ya mayar da idonsa ya lumshe domin ya gano bacci yake cikin dakinsa, amman sai baccin yaqi zuwa ya qara bude idonsa ya kura mata ido daga inda yake, sai ya ji kamar ya fahimci Karin ruwan ya kamo ta jikinsa sosai‘ hakan ma ya isheshi sai ya qara matse hannunsa cikin na ta wani irin abu yana sauka bisa zuciyarsa, Allah shine ke hada zuciyoyi bisa soyayya, tabbas yana son Hasna yana Kaunarta. Kamar wacce aka sanar da ita ya farka itama sai ta farka, ta bude idonta a hankali suka hada ido yana kallonta, ta yi masa murmushi gami da ta shi zaune ya bude bakinsa yana son kiran sunanta amman bakinsa yayi nauyi, ta matsa kusa da shi ta shafi kansa tana murmushi gami da fadin “Kar ka wahalar da kan ka cewa komai, nice Hasnanka na dawo, na gano waye mijina, na yafe maka, na kuma yi alkawarin zama da kai , bazan Kara bari ka shiga wani hali irin wannan ba, ka yafe mini mijina.” ldon ta ya fara zubar da hawaye, shi. kam wani irin farin ciki ya ji yana shigarsa wanda ya jima bai ji irinsa ba, ya kamota da hannun da babu allurar ya kwanlar da kanta dai-dai nasa yana shafa wuyanta yana magana cikin hankali dai-dai kunnenta. “Kiyi haquri Hasna! kalaman da ya fada cikin taushi, Hasna ta fashe da kuka ta Kara KanKameshi suka shiga shafar juna cikin salon farantawa juna, duk da yana fama da cuta amman jikin matarsa yana bashi kwarin gwiwa da Karfafa masa gwiwa, sai ma ta koma ta kwanta a gefensa suka rungume juna, ya shafi cikin da ke jikinta yana magana cikin kunnen ta domin ya fahimci cikin yana nan har lokacin. â €œNagodc Hasna, Allah yayi miki albarka.â€� Wani irin dadi ya ratsa zuciyarta da ruhinta ta qara kankameshi tana shafar bayansa, sai suke jin su kamar basuba ,,         FADAN MASOYA… masu iya magana sukance fadan masoya hutu, to hakance ta kasance ga Abdul da Hasna, domin a washegari sai da kowayayi mamakin halin da Abdul ya kasance, ya farka, sannan yana cikin hayyancinsa, su kansu likitocinsun yi mamakin saurin farfadowar Abdul, har suka fara tsokanar Hasna da babbar likita, Hajiyarsa ba ta iya cewa komai don farin ciki sai sanya albarka kawai da ta dinga yiwa Hasna abin da ke haskaka ran Hasna. Cikin kwana biyu sai ga Abdul har zama yana iyayi da kansa, da aka yi masa awon jinni sai aka tabbatar da jinin ya sauka gaba daya, domin ya sami kwanciyar hankali, kulawar da Hasna ta ke ba shi ta fi wacce ta ke bashi a baya, itace ke yi masa wanka idan ta kama shi suka shiga bandaki, itace ke daura masa alwala itace ke ba shi abinci, ya so ya nuna mata ta huta saboda cikin da ke jikinta wanda ya fara nauyi yanzu, amman ta nuna masa dole yana bukatar kulawa. Zuciyar shi bayan an kara daukar hoton an samu ci gaba na samun saukin wanda har suke ganin ba za a yi masa aikin ba, hankalin kowa ya koma jikinsa. Sati guda da ‘dawowarta aka tabbatar da samun lafiyar Abdul da dorashi akan magananin da zai ci gaba da sha, sannan a washegari za a basu sallama. * ‘ A wannan ranar Murtala yaz0 duba Abdul, abin ya baiwa Abdul mamaki, domin bai yi tsammanin Murtala zai Kara kallon sa ba, Hasna ba ta so zuwan na shi ba, don tana son ya rabu da mijinta har,abada,‘ amman dai tayi Kokarln kawar da kanta ga damuwarsa ta sakar masa fuska suka gaisa, shi kan shi Abdul bai wani saki jiki ba sosai ba, hakan ya sanyayar masa da gwiwa suka gaisa a tsatsaitsaye ya tafi. Washegari tun da safe aka basu sallama Salmanu shi ya dauke su ya kai su gida, domin Hajiyar Abdul ta dai na zuwa ganin ya sami sauqi, abin da ya baiwa Abdul mamaki ganin komai na gidan ya sauya, Hasna ba ta yi mamaki ba domin babanta ya sanar da ita za a yi mata gyaran gida, sai dai yanayin gyaran ya burgeta, Husna ta kyauta mata domin ltace ta zabar mata kalar komai na gidan, Abdul ya dinga kallonta da tuhuma. _ Ta yi dariya tana fadin “Ni fa ba ruwana, Sister ce da Daddy suka yi komai.” Yayi dariya kawai cikin farin ciki. Abdul yana jinsa kamar bai taba ciwo ba, burlnsa kawai ya gaba da rayuwa da matarsa cikin daki. amman ya kula ita wani yanga ta ke ji, don haka ya zuba mata ido kawai yana shirin ya tarfata a daki, amman ‘yan dubiya da suka dinga zuwa gidan ya sanya ya daga mata kafa, Husna anan ta wuni ranar ma Karima ta zo duba Abdul, Hasna ba ta nuna mata komai ba domin tausayinta take ji ta amsheta hannu biyu-biyu sun gaisa suka wuni cikin hira da jin dadi Sai da za ta tafl ne sannan ta ja ta gefe ta sanar da ita sun rabu da Murtala, hankalin Hasna ya tashi ta fara tambayarta garin yaya, ta sanar da itakawai ta yanke shawarar hakura da komai ne Murtala kuma ya bar mata gidan da suke ciki da motocinta da yaran, shi ne kawai yabar gidan, duk da. labarin bai yiwa Hasna dadi ba amman tana ganin hakan ne kawai mafita,a rayuwar Karima, ta bata haquri da lallashinta gami da yi mata alkawarin taimaka mata. ‘ Amman bayan ta koma cikin gida ta kasa samun sukuni saboda tana tinanin wanne irin mutum ne murtala daya gwammaci rabuwa da iyalinsa akan ya daina muguwar rayuwar da yake yi, har Husna sai da ta game halin da ta ke ciki, ta tambayeta mai ya faru rabuwar auran kawai: taâ€�$anar: da ita, Husana taâ €™ ji-‘babu dadi musamman,da ba ta san dalilin rabuwar ta su ba Da daddare Hasna ta Shirya.cikin shigar kayan,barci masu kayatarwa, duk da abin da ya faru w da,Karima yana damunta, har tana ganin kamar itace ke da laifi dari bisa dari, ta tarar da Abdul zaune tsakiyar gado yana danne,danne,a,c omputer din sa tana shiga ya bita da kallo cikin,murmushi, shigar burge shi yana jinsa kamar komai,ya,dawo masa sabone, ya hade hannuwa’yana kallonta ta nufeshi tana rangwada,da,rangaji. har ta isa gareshi, ya yi ajiyar kamshin ta yana shigarsa, rayuwarsa ta .daWo kamar baya, cikin kunnenta yayi mata rada na‘gode Hasna, na ji dadin yadda kika fahimce ni.. . . hasna ta sanya,hannu ta rufe masa baki,tana fadin,‘Nafa gaya maka bana son mu karayin â €œmaganar,nana kai,.daga,yanxu ka haqa rami mai gaba gaba dubu ka binneta, bana son Kara jin ta, abdul ya gyada kai* yana shakar kamshinta yana’jinsa kama,sabuwar halitta ya ce “shike nan Hasna, na daina na bazan Karaba.    ” ‘ Ta yi dan murmushi sannan ta ci gaba da magana “Amman ina son ka mini wani alkawari guda daya mijina.” “Hasna indai mutum zai iya yin abin da ki ke buqata, kuma ni ma zan iya na miki alqaWarin yi miki ko menene.â€� “Ina son ka rabu da Murtala har abada, domin ba mutum ba ne, ya zabi son zuciyarsa fiye da komai, ya rabu da Anti Karima a yanzu, Murtala ba mutum ba ne na gariâ€� muryarta ta fara rawa kamar za ta fasa kuka, Abdul ya qara janta jikinsa cikin kunnenta yake fadin. “Na miki wannan alkawarin Hasna, bazan qara kallon Murtala ba lnsha Allah.â€� Wannan . itace magana mafi soyuwa a gareta, ta ji dadi ya ratsata,har tsakiyar kanta, ta Kara rungumar mijinta. Tun daga wannan rayuwarsu ta zamto abin kwatance, abin da ke,burge Abdul shine har suka yi rikicinsu da Hasna suka gamaba ta taBa baiwa kowa labarinsa ba, wannan shine ke qara mata qima da daraja a zuciyarsa, mutane kuma suna ta mamakin abin da ya faru, amman basu san komai ba. Abin da suka sanya a gaba yanzu shine cikin da ke jikinta, wanda aka shiga tattalinsa kamar shine na fari Ta sha wahala kamin ta haihu domin har an fidda ran haihuwar tata da kanta an yanke shawarar yi mata aiki sai kuma Allah ya qaddara ta haifi yarinyarta mace mai kama da ita, ta dinga kallon yarinyar bayan sun koma gida an kammala shiryata, yarinyar da Ubangiji ya Kaddara sai ta shigo duniyar nan, soyayyar ta na shigarta har tana jin da ta zubar da cikinta da ta sha kuka da takaici, ta yi wa Allah hamdala da godiya. Yarinyar ta ci sunan mahaiflyar Abdul wato Falmata Abduljabar Falmata kenan, Abdul ya kashe kudl gurin sunan Falmata da Anti Karima aka yi komai, a wannan lokacin ne Karimar ke bata labarin nacin da Murtala ke yi akan komawar ‘auransu amman ita taqi yadda da hakan, ta ce ta haqura da shi, tsakanin miji da mata sai Allah shi ya sanya Hasna ba ta zafafawa sai dai ta ce kawai ta ci gaba da addu,a. Kafin Hasna ta yi arba’in labari mafi muni ya zo musu na rashin lafiyar murtala, wani abu ne ya fito masa a duburarsa wanda ko zama baya barinsa yayi ga azabar ciwo ba bacci ba tashi, tun yana Boye abin har ya fi qarfinsa, an yi masa aiki anan qasar amman abin ya kuma fitowa gashi babu mai jinyarsa, tun da iyayansa sun jima da rasuwa, su kuma ‘yanâ €™uwansa kowa yana neman na kansa kuma duk maza ne babu wanda zai zauna a gurinsa, sai masu aiki ke kula da shi, wanda suma ba komai suke yi masaba, zuwan da Karima ta yi duba shi taga halin da yake ciki’ya sanya dole ta tare a gurinsa domin ganin irin halin da ya shiga, bayan wani lokaci suka fita qasar waje domin abin Kara girma yake yi, ko acan din ma basu dace ba, domin da aka yanke abin kafin su dawo ya kuma “fitowa Murtala ya fita daga hayyacinsa duk ya rame yayi baki kamar ba shi ba, kudin dai gasu nan amman babu dadin cin su, domin bai ko iya cin abinci, bs zama babu kwanciya sai dai yayi ta yawo a,gari ga rashin bacci, abin har ya fara taba kwakwalwarsa. Bayan sun dawo Abdul suka je da Hasna duba shi, hankalinsu ya tashi Kwarai da gaske da ganin yanda Murtala ya koma, musamman kalaman da yake fada musu. , “Abdul ka ga yadda na koma k0? Da na yadda na tuba na daina lokacin da ka bani shawara da ban hadu da wannan bala’in ba, yanzu duk abokan mu’amalata sun gujeni, babu wanda yake kula ni sai Karima ce kawai ke kula da ni, ka gode wa Allah Abdul da ya tsallakar da kai.â€� Abdul sai da yayi hawaye, k0 bayan sun bar gurin hanyar da zai taimakawa abokinsa kawai yake nema, daga qarshe ya gano wani maimaganin gargajiya a nijer da aka ce yana aiki cikin ikon Allah a warke kowace irin cutace, domin a asibiti sun sanar da shi gaskiya sai dai ya nemi na gida cutar ba irin ta asibiti bace. Ya zo ya shwaraci Karima suka tattauwan da Murtala yace duk abin da suka yanke shawara dai-dai ne a gareshi, suka shirya suka dauki mota murtala Abdul da Karima suka tafi gaba daya kallonsa kawai maimaganin yayi ya tabbatar musu da cutar daji ce ke damunsa, amman za a yi masa magani, satinsa guda a garin jikin ya danyi sauqi sannan suka dawo da magungunan da aka ba shi. Cikin ikon Allah wata guda Murtala ya samu sauki abin da ya fito masa ya qame ya matse, wannan shine sanadiyyar dawowar shi cikin rayuwa ta gari, tun yana ciwo ya mayar da auranshi da Karima domin lokacin ba ta kammala iddar ta ba, don haka sun koma rayuwar auransu cikin jin dadi da fahimtar juna. ‘ Amman labarin da ya zo musu na Bangaran Alh Shazali bai zamto mai dadi ba, domin bayan cutar Kanjamau da ta jima da shigarsa wai yana ganin tun da yana da kudi ba matsabace ba, sai kuma Allah ya saukar masa,da cutar basir mai tsiro wacce ta ke fita masa a duburarsa ga kuma cutar Gundulau da samesa a gabansa, wannan su ne abubuwan da suka maida shi abin tausayi, ga kudi dai akwai su amman basu da amfani, daman kuma bai taBa haihuwa ba sai mata da dangi suka saka dukiyar a gaba suka fara ci, lokacin da ya fara neman mutuwa da kansa sanda cutar ta Karasa gundule gabansa, a daran kwana yayi yana ihu da suma, duk wani maganin duniyar nan an yi masa, tun da har qasar waje an sha fita da shi amman a banza, haka nan ya cika yana ihu da kururuwa cikin mummunan yanayi. Labarin mutuwar Alh. Shazali ya Kara tayar da hankalin Murtala da duk wasu masu irin halinsa, duniyar kenan, shi dai Dakta Falmata soyayya ce mai Karfi ta qaru tsakaninsa da matarsa wacce suka zamto tamkar tare aka haifesu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button