ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
3⃣0⃣

bai san lokacin da ya kwashe agurin yana kuka ba, tun bayan da ya girma ya fahimci rayuwa yayi wa kansa alkawarin dai na yin kuka akan kananan abubuwa, domin lokacin da ya kamata yayi kuka tini ya wuce, amman b zama dole yau yayi kuka. Husna tana hangensa ta wundo tana kallonsa da duk abin da ke faruwa, tausayin Abdul ya cikbata, ya jima agun kafin ya ja ‘motarsa yabar gurin a hankali kamar wanda ke tafiya bi sa kan mutane. Takaici da Bacin rai ya kuma cikata kamar jira ta ke yabar gurin ta dauko wayarta ta daddana ta kara a kunnenta, kiran farko ta shiga, sai dai ba a daga daga can Bangaran ba, bata damu ba, domin cikin kwanakin nan sai ka kira wayar Hasna sau biyar da kyar za ta dauka sau daya, amman ta yi sa a yau bugu biyu ta daga, ba ta ce komai ba sai alamun daukar ne ya fahimtar da Husna ta daga. Husna ta fara masifa cikin Bacin rai “Wallahi kin bani mamaki Hasna, ashe hauka da .rashin hankalin ki har ya kai nan, k0 da ace ganin mijinki ki ka yi turmi da taBarya akan gado bai kamata ki dauki irin wannan matakin na tsayar da farin ciki da al’amuran rayuwar kowa ba, balle kawai ganin sa ki ka yi da mace cikin mota, ya kamata ki sanyawa zuciyar ki salama, ki sani ke musulma ce kuma kishiyama Uwarki tana da ita.” Hasna ta yi yaqe qasan ranta tana fadin rashin sani yafi dare duhu, amman a fili sai ta ce “Wai waye ya zo ya baki labarin nan Sister? “Mijin ki ne ya bani labarin komai, yanzu yabar gida na wallahi bari na gaya miki bazaki kashe mu a banza ba idan har baki dai.dai ta lamarin kiba wallahi sai na gayawa Daddy da Momy sakarya mai kishin banza.” Ta kashe wayar tata cikin bacin rai Ran Hasna ya Baci ta yi zaune a inda take tana sakawa da kwancewa, har Abdul yana da bakin bin ‘yan‘uwana yana irin wadanan maganganun. lallai ta yadda namiji dan kunama ne. amman za ta nuna masa Shi karamin mara kunya ne. don ya ga ta daga masa kafa shi ya sanya ya aikata mata hakan. To wai da me za ta ji ne a rayuwarta, cikin da ke jikinta yaqi fita, duk abin da ta aikata ta yi amman ya ki, kuka ne kawai sana’ar ta a wannan lokacin. Tn jima zaune tana jiran jin zuwansa, dare yayi sosai kafin ya dawo gidan, domin bai iya shigowu yanzu sai ta yi bacci, sannan ya fice da sassafe ba tare da sanin ta ba, yau din ma hakan yayi, amman bai san ta yi kwantan Sauna bane Ya shiga wanka ya fito yana Iazimi bayan ya yi sallar shafa’i da wuturi ya ji an banko kofar dakinta, ya daga kai da mamaki ya kalli bakin kofar, tsoro da fargaba ya kama Abdui saboda ganin Hasna, sai ya mike cikin sauri jikinsa yana karkarwa. Ba ta kalleshi ba, domin ba ta son hada ido da shi, ta fara magana.“Na fahimci kai namijine mai halin Dan’ akuya kuma bunsuru dan’ uwan kare kana yin wasu abubuwa kamar irin na masu ilimi, amman kai takadirin jahili ne, to bari na gaya maka koka sake ni k0 baka sake ni ba yau zan bar maka gidan nan, don haka idan ka shirya zaka iya bina gidan mahaifina da takaddatar saki, sannan abinda nakeson ka sani, kin yin abin da nake buqata kamar hanyar budewar asirin kace gaba daya, domin bazan yadda ka Ialata mini rayuwa a banza ba, ina jiran sakon ka Domin ina fatan yauce ranata ta qarshe da zan kara ganin wannan azzulamar fuskar ta ka Ta juya a fusace za ta bar dakin, sai ya yunkura cikin sauri ya mike yana magana “Hasna k0 da zaki tafi don Allah ki tsaya kiji abin da zan gaya miki koda ba zaki yadda da ni ba ‘ta waiga a fusace ta kalleshi “Magana daga bakin ka? To bari na gaya maka bazan qara saurarankaba macuci azzalumi! Tana fadin haka ta bude kofar ta fita da gudu tana kuka, ya dafe kai cikin tashin hankali yana Ambaton Allah cikin ransa, sai ya ji kamar ya bita da gudu ya rikota amman babu halin yin hakan Yana tsaye daga inda yake ya kasa zama ya jiyo karar fitar motarta, cikin gaggawa ya nufl wundo ya leka ya hangota tana horn Maigadi na kokarin bude kofar a gigice, yana budewa ta fice a fusace, ya Kara komawa ya zauna cikin damuwa ba shi da abin yi, a yanzu kansa yake zargin da Kin fada mata labarinsa, da ya gaya mata watakila da ya sami mafaka ta kuma yadda da shi bi sa abin da ya same shi na kaddarar rayuwa. Amman ya riga ya. makara, bashi da wani abu da zai yi a yanzu da zai kare kansa. KOWA YA DEBO DA ZAFI BA kowa a falon kasancewar ana ta sallar magariba, Hasna ta shigo ita kadai babu komai a tattare da ita sai hijabin sallah da ta sanya da doguwar riga, ta fara yin sallama cikin sanyin murya Hajia AiSha ta fito daga cikin daki ta idar da sallah, tana sanye da Hijabb da carbi a hannunta alamun ta idar da sallah lazimi ta ke yi, ta hango Hasna zaune akan kafet ta Jingina jikinta da kujera, mamaki ya kamata domin Hasna bata taBa zuwa ta zauna a qasa kamar wata bakuwa ba, kai tsaye take wucewa dakinta, ta nufeta da murna. hankalin Hasna yayi nisa ta kurawa talabijin din bango da ke kashe ido, Haj.Aisha ta karasa ta tabata sannan ta ambaci Sunanta. “Hasna! Hasna ta daga kant cikin sauri ta kalli mahaifiyarta, sai ta maida kanta qasa ba tare da ta amsa ba, hakan ya tabbatarwa da mahaifiyar tata lallai ‘akwai matsala, don haka ta zauna a kusa da ita ta ci gaba da magana. “Yaya dai Hasna lafi ya?me ya faru?Hasna ta yi shuru ba tace komai ba, Haj. Aisha ta Kara shiga damuwa ta ci gaba da magana. “Yaya ina miki magana. za ki mini kunnen uwara shegu Hasna, ki mini magana mana, menene yake damun ki? Me ya faru? Hasna ta sanya hannu ta na goge idonta da ke fidda hawaye sannan ta fara magana “Ki yi hakuri Momy…na dawo gida gabadaya…bazan Kara zaman aure da Abdul ba.” Haj. Aisha ta waro ido cikin fargaba da damuwa, idan akwai wani abu da ke tayar da hankalin mahaiflya bai wuce jin diyarta da ke aure tana cikin matsala wacce har ta ke yi wa kanta fatan rabuwar aure ba, amman sai ta “Kamar yaya ba za ki Kara zama da Abdul ba, me ya faru, me ya hada ku? “Babu komai Momy, kawai dai bana son zama da shi ne, na gaji da zaman, don Allah ki taimaka mini Momy… Sai ta fashe da kuka, mamaki ya qara cika Haj. Aisha, wacce irin magana ce wannan, yaya mace za ta ce tana son rabuwa da mijinta ba tare da wani dalili ba, tabbas wannan ba maganar da kunne zai kamata ba ce, don haka ta qara gyara zama. “Hasna maganar ki ba gaskiya ba ce, kin auri Abduljabar ne saboda kina son shi, haka kawaidare daya kice kin gaji da zama da shi, kunne zai yadda da jin magana be, tun kwananakin baya na kula akwai wani abu dake damun ki da kike. boyemini, bazan matsa miki akan dole sai kin sanar da niba amman. ki sani babu wanda zai goya miki baya akan wannan. shirmen idan ba wata. hujja ce dakeba Hankalin Hasna ya qara tashi ta kalli mahaifiyarta kamar idonta zai fadi kasa don kuka, ta fara rokonta. “Momy yanzu ashe ba za ku iya taimaka mini ba, nice fa na kawo Abduljabbar nace ina son shi, yanzu kuma don na ce ba na son shi sai kuce ba zai yuwu ba, wallahi da gaske na ke Momy bana son shi.” Haj. Aisha ta yi yaKe tana kada kai “Yaro man kaza, Hasna me ki ka dauki aure ne, da ace haka jama’a suke yiwa aure duk ‘ sanda suka so suce suna so sanda kuma suka ga dama suce sun gaji da tini ke kan ki ba ki ~ kawo yanzu cikin kwanciyar hankali ba, bari na gaya miki shi aure bautar Allah ne, don haka ki yi hakuri da dukkan abin da ke damun zuciyarki, ki tattara ki koma gidan mijin ki. . . ‘ Ta kara fashewa da kuka cikin karaji wanda ya fadar da gaban Haj. Aisha ta bita da kallo baki a bude da nufin yin magana, amman ta katseta da fadin. “A’a Momy don Allah kada ki ce na koma, idan na koma zan mutu…bana son shi.” Ta mike tsaye ta fara jada baya tana magana “Momy na tsani Abdul, a yanzu na amince zan auri Abba, ki taimaka mini aurena ya mutu na auri Abba.” Haj. Aisha ta dinga yi mata kallon hauka da tabuwar hankali, gaba daya yarinyar ta rame ta flta daga hayyacinta kamar wacce ta yi cutar shekaru goma, ganin tana shirin faduwa saboda kuka ya sanya ta ‘ nufeta da sauri ta rikota tana lallashinta. “Kin ga ya isa, kwantar da hankalin ki, yanzu dai shiga mu je ciki kiyi sallah ki ci abinci, yi hakuri ki kwantar da hankalin ki.” Kalaman mahaiflyarta suka dan kwantar mata da hankali ta bi ta kamar yanda ta bukata. Bayan ta yi sallah wacce ta yi da kyar saboda juwa da ke. dibarta, Haj. Aisha ta kawo mata abinci, an yi sa’a akwai laflyayyan abinci a gidan, ta ajiye a gabanta ta tsare ta da ido. “Dauki ki ci Hasna.” Hasna ta kalli abincin sannan ta kalli fuskar mahaif’lyarta kamar za ta fasa kuka, rabon da ta ci cikakken abinci tun ranar da ta ga abin da ya faru ga mijinta, irin yanda Hajiyarta ta tsareta da ido ya sanya ta zura hannu ta fara tsakurar abincin tana ci, bata jin dadin komai, dan ruwan shayi daMaltina kawai ta ke sha, don haka bata jin dadin abincin a yanzu. Haj. Aisha ta tsare ta da ido don haka babu yanda za ta yi dole taci abincin, ta dai samu ta tura kadan da Kyar, ta daga kai ta kalli mahaifiyar tata cikin marairaice tana magana “Momy na Koshi… Haj. Aisha ta yi yake tana ci gaba da kallonta. “Kin ci da yawa, amman dai ki daure ki dan Kara ko kadan ne.” Hasna ta Kara marairaice murya “Allah Momy na koshi, idan na Kara zan iya ‘yin amai.” . Haj.Aisha ta daga mata hannu da sauri “A’a ya isa, kar ki yi mini amai.”Suka yi shuru kowa da abin da yake sakawa cikin ransa, Hasna ta daga ido ta kalli mahaiflyarta tana fadin “Momy yau ba a nan Daddy yake bane? Haj. Aisha ta Bata fuska, domin bata son k0 maganar kishiyarta ayi mata, amman sai ta gyada kai “Haka ne, yana can, shi ya sanya na ke tinanin abin da ya kamata na yi akan ki, yanzu da za ki taimaka mini da kin yadda na raka ki dakin ki Hansa… Cikin sauri da fargaba ta kalli mahaifyarta gabanta yana faduwa tace “Momy na gaya miki fa, ko kina son na mutun ne? Haj. Aisha ta kada kai da sauri tana fadin “A’a, kinga shike nan, ki zauna kafin baban na ki ya zo, amman ni dai. Ta yi dan shuru tana kada kai Shike ‘ nan dai.” Sai ta mike ta nufi dakinta kai tsaye. ‘ ‘ Hasna ta bi ta da kallo cikin damuwa, amman ta kudurce a ranta komai zai faru sai dai ya faru, amman ita da gidan Abduljabbar har abada, ta mike da kwanikan abinci da ta ci ta fara kokarin kaiwa kicin, bayan ta kammala ta nufl dakin da suke kwana idan sun zo gidan k0 wani abu ya tashi, wanda tun dakin su ne suna ‘yan mata ba a cire komai ba. Hansa ta yi kwance akan gado ta qurawa silin ido tinanin duniya ya cika ta, labarin Karima ya tsaya cikin ranta, tabbas ta jima tana jin labarai masu ban mamaki, amman ba ta taBa cin karo da irin na Karima ba, yanzu shike nan mace sai ta ci gaba da zama da mijin da yana saBawa Allah saboda biyan bukatar rayuwarta, wannan shine abin da ya dami tinanin ta. A Bangaran Haj. Aisha data shiga daki wayar‘ Husna ta kira suka jima suna tattaunawa matsalar Hasna, daga Karshe suka yanke shawarar gobe Husna din za ta zo gidan, amman Husna ta sanar da mahaiflyarsu duk abin daya faru a iyakacin saninta, ran Haj. Aisha ya Baci kwarai da gaske da jin dalilin da ya sanya Hasna ke son abuwa da mijinta, ta kuma so ta korata gidanta, amman Husna ta ce ta barta ta kwana k0 zuwa gobe ne, domin ko ma babu bin da zai .faru sai Bacin rai, da wannan suka yi sallama. Abdul kam’ya zagaye falon gidan shi da dakunan baccinsa yafi sau dari, har sai da kafafuwansa suka fara yin zafl sannan ya sami guri ya zauna kamar mai ciwon basir, ya kalli agogon da ke jikin bango wanda ya nuna Karfe sha daya na dare, yana son ya kira Husna amman yana shakkar hakan, bai kamata ya kira matar aure a irin wanna” lokacin ba, to me zai yi? Shi ne abin da bai sani ba, amman yasan yau k0 bacci Barawo bai isa ya sace shi ba, yana jin kamar ya fita yabar gidan ya huta. Ya Kurawa wayarsa ido kamar wanda aka tsikara sai ya kai hannu da sauri ya dauka yafara daddanawa, layin Hasna yake kira, koda ba za ta dauka ba amman gwara ya kira k0 ya huta, sai ya ji ma kiran yaqi shiga, akwai alamun ta yi Bloking kiransa ma gaba daya, ya dafe kai cikin kunar zuciya. Kiran wayar da ya shigo wayarsa ya sanya shi kallon wayar da sauri, ga mamakin sai ya ga bakuwar lambace da bai san ta ba, kamar ba zai dauka ba amman sai ya ga rashin dacewar hakan, don haka da ya danna .ya kara a kunnensa, muryar da ya ji cikin wayar ta tayar da hankalin sa gami da firgitashi, yayi kasaqe cikin takaici ya kasa cewa komai, amman yana jin muryar da ke magana daga wayar kamar ihun ibilisai. Daga can bangaran Alh. Shazali ya ci gaba da maganganunsa na banza, a zatonsa Abdul yana Saurara ne domin suna burgeshi har da mahaukaciyar dariya yakeyi. Ran Abdul kuna da suya_kawai yake yi, ya tsani wannan mutumin shine silar lalacewar rayuwarsa, shine ya haddasa masa dukkan masifan da ke bibiyarsa a yanzu, Meye amfanin ci gaba da sauraransa. Maganar da ya fada ta karshe ta doki kunnensa domin cewa yayi “Abdul kar ka kashe_wayar ka, a wannan karon zan iya bin kowacce irin hanya don ganin na same ka, ni nafi kowa sanin waye kai.” Ya kashe wayar da sauri yana huci da me zai ji, tashin hankalinsa ya Kara karuwa, waye ya baiwa Alh. Shazali lambarsa a irin wannan lokacin, cikin sauri wani tinani ya fado masa sai ya fara danna wayarsa da sauri ya kafa a kunnensa. Bugu daya Murtala ya dauka da alamun kallo ya keyi, domin daga inda Abdul yake yana jiyo Karar talabijin din da Murtala ya ke kallo. Ya miKe ya fara magana a fusace cikin Bacin rai “Yaya zaka mini haka Murtala, kafi kowa sanin Matsalar da na ke ciki, me ya sanya zaka baiwa wannan banzan mutumin lambata, haba Murtala yaya ka ke son mayar da rayuwata ne, kuna shirin kashe ni kai da Alh Shazali, kun raba ni da komai na farin cikina, yaya kake son na yi ne da rayuwata? Hankalin Murtala ya tashi daga Bangaran da yake ya fara kokarin kare kansa “Dakata Abokina, ka saurare ni. Abdul ya Kara fusata “Babu abin da zaka gaya mini, domin ka kammala lalata mini rayuwa, Hasna ta barni tabar gidana, ka sanya rayuwa kasa kasha Murlata! Ya kashe wayar a fusace yana huci, yana kashewa kiran Murtala na Kara shigowa cikin wayar sa, ya kalli wayar yana jin kamar ya fasata da Kasa amman kuma yana ganin hakan almubazarranci ne, sai ya fasa ya kashe kawai ya wurgata kan kujera ya rike qugu yana huci cike da bakin ciki………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button