ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

PAGE
0⃣3⃣

kun manta daniba tayi dan yaqe dajin kunya tace tadai manta dakai ni ai na shiga wankane Ina ganin gajia ke damun mutuniyar taka ya kalli hajia yana dan daria Bari na shiga DA kaina na dubata bayan hakama akwai abinda nakeson gaya mata momy tayi murmushi dajin dadi a ranta tanason soyayyarsu ba ita kadaiba kowama yanaso hasna dake kwance tadan lumshe idanu tana tuno kallon DA abduljabbar yai mata Abba ya shigo ya tsaya a bakin kofa ya kura mata ido DA sha,awarta komai na hasna burgeshi yake ya isa kusa DA ita ya zauna sai a lokacin ta kula dashi ta tashi DA sauri ranta a bace tana tsaki banason dabi,arnan ya Abba ka shigo babu sallama babu kyau KO,a addini fa Abba ya daga kafada kiyi haquri banson damuwarki matata bazan qaraba amman kamar babu komai dun na ganki haka. kefa tawa ce ko.‘.”‘. Ta kau da fuska da takaici. ba ta son ‘kallon fuskarsa yau kwata-kwata, son Dr. Abduljabbar da kamanninsa sun lalata ganinta, har ba ta jin dadin kallon kowa, Ya kura mata ido da tuhuma, “Kamar kina da matsala, kin sauya yau gaba daya”. Tayi yaqe “Matsala kuma gajiya Ce nace ka barni na huta kaKi. na kula ka kuma kanason batamin rai Ya mike da sauri yana daga hannu, ” ’no‘. No Ban san damuwarki matata. ina son tabbatar da ba ciwo ne dake ba amma zan barki yanzu, anjima zan daWo”. ‘ Ta kalle shi da sauri. “Kai baka gajiya da yawo ne, ka bari sai g0be_mana‘?” Ya yi dariya. “Idan a kanki ne bana gajiya. ki shirya tara ta anjima”. Ya juya ya nufi kofar fita, ta bishi da‘ kallo wani malolon baqinciki ya tokare zuciyarta. Abba kyakkyawa ne ajin farko ’ bata taba jinsa a rantaba wani lokacin har gori momy take mata akan wai ya fita kyau DA haduwa Amman hakan bai damunta ta Sani KO kafin ta farajin DR Abduljabbar a ranta Abba bai birgeta don shagwaba DA gatansa sunyi yawa ta juya ta kwanta abinta qarfe takwas na dare ya kuma shigowa bai sametaba don’ ta tilastama kanta barcin qarya ga husna tana tare DA masoyinta kamal hajiyarsu kuma tana sama wurin alhaji ya gama walagiginsa a falo sai DA Yan aiki kawai yakecin Karo ya kuma Kira wayoyinta duk a kashe ya dafe Kai DA damuwa yanason tuno abinda yasa hasna ta fara yin masa haka ya jima yana ganin rashin kula DA soyauyarsa ga hasna Amman bai taba hango kiyayyarsa a idonta kamar yau ba tabbas yau ba komai take nuna masaba illa qiyayyah shi kuma bashi DA buri bayan mallakarta da ya gaji DA saqa da warwara saiya miqe tsam ya nufi dakin nasu ya jingina DA qofa bayan ya bude ya zuba mata ido tabbas bacci takeyi Amman bai yarda ta yi baccin ba don lokacin yinsa bai yiba‘ ‘sai don gudun haduwa da shi kawai. Ya dinga kallonta. soyayyarta na Kara bijiro masa. ya kada kai ya fice. Sai dai a ransa bai ji shawarar komawa gida ba. don ganinta a haka ya tsokano masa sha’awarsa. don haka gwara ya isa ga matansa na titi ya fiye nasa. *** ** ** Yau basu makara gurin shiryawa ba ba. domin bata tsaya bata.lokaci gurin yin kwalliyar ba. ‘ ‘ Suna tafe suna hira. a fuskar Hasna bazaka iya tantance halin da ta ke ciki ba: Husna ta’ kalle ta da tsokana, “Sister ya. ya dai, k0 tunanin yayan nawa ki keyi ne?” Hasna ta ja tsaki tana ci gaba da driven bata kalleta ba. tace”Kin fiye son yin zantuka; marasa kan gado. don Allah ki barni na ji. da damuwata mana”. Husna ta kauda baki wajen windo tana dariyar tsokana‘ciki-ciki. Haushi ya kuma cika: Hasna ta kalle ta a tusace ta taka burki kamar za ta daki bishiyar da ke gab da su, Husna ta juyo a gigice tana kallonta Cike da tsananin mamaki da fargaba. “Lafiya Hasna, me ya faru ne haka?” “Ban sani ba, kin maida ni wata mahaukaciya, har wani dariya ki ke mini k0?” Husna ta Bata rai, “Kin ga don Allah kada ki raina min wayo, kawai don ina dariya sai kice da ke na ke? Ki ja mota mu wuce kada ki sanya mu yin latti malama”. Tana maganar tana qokarin danne dariyar da ke neman kubce mata. Hasna ta kuma hawa har ta kasa cewa komai, ta taka motar ta jata DA gudu Cikin zafin rai ta Ci gaba da tuKi. Kan’ Husna ya bugujikin motar, ta dafe gurin tana dan ihun ‘wasa da fadin. “Don Allah kada ki kassara ni ban ji ba ban gani ba”. ‘ _ ’ Hasna ba ta kulata ba ta ci gaba da tuKin kamar za ta-tashi sama. K0 data ‘shiga cikin makarantar ba ta “sauya ‘tuqinba‘,‘ sai da Husna ta fara rokonta ganin dalibai na daréwa ana kallon motar ‘tasu, ta kuma rage din ne domin ta san illar yin «hakan gare ta. Ta isa gurin da ake ajiye motoci tana qokarin tsayawa kamar ance ta kalli gefenta. sai ta hango Dr. Abduljabbar yana qokarin bude motarsa ya fito. Ta tsaya ‘da sauri jikinta ya dauki rawa ta nuna wa Husna shi. “Sister. kalli Dr. Abduljabbar can yau tare muka shigo, lallai mun shigo da wuri. Bari naje na gaishe shi tun kafin ya shige ofis dinsa”. Ba ta jira jin abin da ‘yar uwar tata za ta ce ba ta bude motar da sauri, Husna ta fara kokarin hanata ta hanyar kiran sunanta da sauri. “Hasna. tsaya don . kada ya wulakanta ki…” Ina Bata saurari jin abin da ‘yar uwar tata ke fadi ba, ta fice cikin sauri ta ke tafiya kamar za ta fadi domin takalminta mai tsananin tsini ne. Tana tafe tana kallon kanta don ta Kara tabbalar da ta yi kyau, sai dai ya , dan yi mata nisa da yake yana da zaf’in nama, komai nashi cikin Karfi da jarumta ya keyi, balle safiya da yake jinsa kamar kasakaryan zaki. Husna ta fito daga gurin zamanta ta zaro makullin ta kulle motar, tabi bayan ‘yar uwarta ‘da jakarta da tata, domin k0 jakarta‘ ba ta iya dauka ba don rudewa. Cikin ikon Allah ya dan tsaya yana magana da Wani dalibi daidai lokacin da ya iso dandazon wasu dalibai. Wannan ya bai wa Hasna damar isowa kusa da shi, daidai lokacin da ya kammala maganar yayi shirin ci gaba da tafiyar, da sauri ta ce. “Malam! Dr. Abduljabbar ya waigo da sauri ya kalle ta, abin da ya dauki hankalin .daliban dake tsaye a gurin. kenan Ya’ yi mata wani duba na tara saura kwata, a wulaqance amma bai ce komai ba. Cikin rawar baki da jin kunyar abin da tayi, ta ce. ” Good morning” Malam’ Ya dan waro ido da mamakin abin da ta ce domin ya yi zaton wani babban dalili ne ya sanya ta yin kiransa. Bai ce da ita komai ba, yaja dogon tsaki ya ci gaba da tafiyarsa. Daliban da ke gurin suka fashe da dariya Suna kallonta daidai ‘lokacin da Husna ta iso gurin. duk abin da ya faru a kan idonta. akai Jikin Hasna ya yi Sanyi, tsananin kunya da fargaba suka rufeta . ba a taBa kunyatar DA ita irin na yau ba tunda ta ke a rayuwarta. Husna ta .kama hannunta ba tare da cewa’komai ba. ita ma ba ta yi musu gurin bin-ta ba, suka wuce har lokacin daliban naci gaba da yin dariyarsu. Har suka isa aji ba wanda ya ceda Kowa komai Husna ta nufi gurin zama ta‘zauna bayan ta saki hannun ’yar uwar tata, abin da ya sanya Hasna tsayawa tana kallon ‘yar uwarta da’ damuwa, ta san Bacin rai ne ’ya hanata yin magana; . Shigowar profesa Ibrahim da, zai musu lakcar deVelopment comunication’ ya sanya ” ta nufa kusa. da ‘yar uwar tata ta zauna, zuciyarta na suya, don» ta ma. rasa abin. daya dace ta yi Husna ta: miqa mata, -jakarta ‘daidai lokacin da Furofesa ya fara ‘zuba, turancinsa,-.~ ajin ya yi tsit kowa hankalinsa yana kan darasim ban da Hasna da ta ke kallon malamin nasu amma ba ta fahimtar komai. hawaye ya cika mata ido sai dai taKi bashi damar fara zubowa. Har suka tashi Husna bata kula ta ba sai ma ta dinga bin wasu qawayensu suka dinga hirarsu da shewa. wannan abin ya qara kona ran hasna wato yau har ’yar uwarta na, gudunta a kan abin da ta aikata. shin ya ya za ta yi da zuciyarta‘.’ da akwai abinda za ta *yi k0 ta sha ta manta da Dr. Abduljabbar da tayi, amma ta kasa k0; daya Bata’ mata rai da zarar lokaci yaja sai taji zuciyarta ta huce ta Ci gaba da tunaninsa. ‘ Yau k0 capteri ta kasa zuwa ta dora kanta bisa tebur din gabanta tana yin. kuka kasa-kasa. duk wanda yazo kanta sai dai ‘ yayi mata sannu, don ‘husna ta ce musu bata jin dadi ne wannan ya hutar da ita tuhumar kowa. KO’a gida ma irin bayanan da Husnar ta yi ‘ a makaranta’ shi ta Kara maimaitawa Hajiyarsu. wacce ta damu kwarai da gaske. ta fara kokarin ‘ kiran likitan gidan yaxo ya dubata. amma HusnA ta Kara dora mata da cewar ai sun je asibitin cikin makaranta an ba ta magani ta sha. Hakan ya sanya Hajiyarsu ta fasa kiran wayar. sai dai ta mike ta nufi diyar tata domin qara ganin yadda jikin Nata yake da yi mata sannu, lokacin Husna ta wuce cikin : dakinsu kai tsaye . “K0 za kici wani abu nasa masu aiki ‘ su dafa miki? Da sauri tace “Na koshi Mommy. ‘ kwanciya kawai nake buqata. idan an jima zan sanya su dafa min “Shi ke nan. ki kwanta. idan kinji jikin ba sauqi kimin magana na Kira DR Abbas yaxo ya dubaki “To Mumny Ta bata amsa ta nufi dakin nasu lokacin. Husna tana ta tube kayan jikinta da alamar wanka take son shiga Hasna ta banko kofar a fusace tana kallonta da takaici. “Malama. wai me kike nufi da qaryar ciwon da ki ka dora min har ki ke sanyawa ana ta wani damuna da sannu‘.’” ‘ Husna ta waigo ranta a bace”Au don na rufa miki asiri ki ke neman gaya min magana? To bayan haka me ki ke son nace musu. k0 kinfison na ce kina bin Wanda bai damu dake bane wanda ya wulakanta ki a gaban bainar jama’a. abin, da ke damunki ke nan k0? eh Ba don kallon da za a yi miki na sakarci zai shafe ni ba wallahi da hakan . zance, ‘to ina gudun abin kunyar da zai danganta sunana da nakine don wasu za suyi‘ zaton Husna aka ce, kin ga dole sunana ya bayyana gurin karin bayani”. _ Cikin kuka tce “Dakata Husna Wai har kin fara gudun alaqanta ki‘da ni kenan? Kina gudun ace ni ‘yar uwarki ce yanxu?” “Tabbas in dai labarin zai danganci bayar da kanki da zubda martabar mata gurin. son maso wani ba, to lallai ba zanqi .yin takaicin sunana ya raBu da nakiba”. Husna ta bata amsa a kausashe ‘ Ta fashe da kuka……………….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button