ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣3⃣

Tace gaskia shawararki tana buqatar nazari don banajin zan iyama dana asiri tace ahto ki tsaya wasa ayi baki amman lallai ya kamata kiyi wani abu domin ganin bayan auuran nan Ga Abba hadad‘diyar motarshi ya shiga, yana cikc da nishadi, burinshi bai wucc riskar Hasna ba. duk da kwanaki biyu da ya ke zuwa gidan bai samun ganinta amman yau dai ya yi wa kansa alkawari k0 mai zai faru dole sai ya ganta. Ya sami Hajiya Aisha a falo tana kallo, .Husna kuma ha.ta gidan da alama ta fice wani gurin’ .dabanne hasna dai tana can daki kamar ‘yadda’ ta daukarwa; kanta’, lokuta da dama _ hira suke da Abduljabbari yanar gizo-gizo a wayarta, wannan ke dan rage musu damuwa da kunci. Abba ya tsaya gurin Hajiya suka gaisa, duk da ha ta wani maraba da zuwansa, amma ba ta bari hakan ya bayyana a kan fuskarta ba, ta amshe shi da farin ciki. Bayan sun taBa hira ya mike yana fadin. , “Bari na shiga mu gaisa da rigimammiyar can”. Momy ta bi shi da kallo kawai ba ta ce komai ba, amma ta’ San a-halin da diyar tata ke‘ ciki ba lallai ne su wanye laflya ba, amma dai gani ya kori ji in ji masu iya magana. . Tana zaune‘ a gefen gado ta dora Kafafuwan’ta a kan gadon ta‘ dan ‘jingina bayanta jikin filo tana ta chatting da Abduljabbar‘, rarrashinta da ba ta magana ya kc yi, domin yau ma sun hadu gidan Murtala, da kuka‘suka ‘rabu‘don‘ta kasa ,sabawa da kalaman‘mahaifinta‘ har zuwa wannan lokacin. ~~Ya ‘shig0“da sallama ya tokare a bakin kofa kirjiinta.ya buga, rantaya Baci sanda ta jiyo muryarsa, amma dai ta amsa sallamar ba tareda ta ‘kalle shi ba ta ci gaba da abin da ta- ‘ keyi. Ya jima a tsaye yana kallonta da sakawa da kwancewa yana tunanin ta ina ya kamata ya‘ fara ne? Sai ya dake kawai ya isa kusa da ita ya zauna daga gefen gadon. Ta yi saurin janyc kafafunta ba ta yi masa‘magana ba har lokacin. Ya kura mata ido yana magaha cikin sanyin murya. ‘ “Hasna, ba za ki dago ido ki kalle ni ba ma bare na sami k0 gaisuwa ba?” ‘ ‘ ‘ Tayi masa banza tamkar yana magana da dutse, chatting dinta kawai “takeyi ’haushi ya ishe shi, ya miqa hannu ya warce Wayarda ke hannunta, abin da ya sanya ta saurin kallonsa kc nan a fusace, ranta a’ Bace ta miqa masa hannu da fadin. “Ba ni wayata Malam!” “Na Ki na ba ki,din don na kula ita ce ta dauke miki hankali ‘har ki ka kasa kallona da idon rahama”. ‘Cikin tsiWa ta ce. ‘ “K0 babu waya ba ka cancanci‘wannan .- kallon ba. mutum mai naci da son ‘kanshi ya.fi dacewa da yi-masa banza, don ba shi da abin fadi bayan surutu mara kan-gado'”. _ “Ni ki kc gaya Wa haka ‘Hasna‘?” Ya nuna kunshi ‘da yatsa cike da takaici. Tace waye kai daba xa a gaya maka hakan .ba’.’ ka bani, Wayata kaj’i’ k0 Malam”; Ya gyara zaman da takaici; yace bari naga abin da ki kcyi, Ta yi murmushin .mugunta,taci gaba da kallonsa kawai ba ta’ yi wani yunkuri nakwacéwa ba sam. Ya fara kunna wayar ‘yana bin abin da :sukc tattaunawa itada Abduljabb’ar, ‘W’ani irin malolon’ bakin’ ciki ne ya_ fara cika ransa don kusan ‘duk hirar tasu a kanshi’ ne, tana ta sanar daAbduljabbar irin kin da take yi masa, shi kuma yana rarrashinta. ’ Farin ciki ya cika Hasna. don ta san sai ya kusa hadiyar zuciya yau, Ta dinga murmushin jin dadi kamar ta zuba ruwa a kasa ta sha don dad’i Abba ya dago idonshi a fusace ya kalleta. Wanda ya sau‘ya launi zuwa jawur. Cikin tsananin takaici yace “Hasna’ni’ dan uwanki nc fa, me ya sanya ki ka sanar da wani ba ki kaunata?” “Saboda ita ce gaskiyar magana, ba na qaunarka,-ba kuma Zan taBa Kaunarka ba har abada .na gaya maka, w‘allahi Abba k0 ka yi nasarar aurena ba za ka sa’mi komai daga gare ni ba sai‘ baqin Ciki biyyya kawai Zan yi wa Daddy na’ aurc ka, amma za ka auri’ ganga‘r jikinae. kaWai, so. na da” zuciyata har abada suna’ga‘Abduljabbar’ Wani irin_takaici Ya‘k‘uma takire shi’ har ya ji kamar ya’ Shaketa ya yita duka. kallon da ya kc mata kaWai ya isa ya bayyana mata abin ‘da kc zuciyarsa. tun suna yara ta sanhalin Abba idan ya yi zucia duka ya kc kai Wa amma yanzu addu’u ne ke Cikin A ranta Al’lah ya sanya ya’dokc ta wannan kadai ya isheta samun babbar hujjar‘da zata fara kafa‘wa iyaycnta; ‘ ” ’ Kamar ya‘ san me ta kc sakawa cikin ranta, ya ka’da kanshi kawai yana huci ya ce “0k ba da wannan “ki ke samun damar zagina ba yanzu zan raba ki da ita wallahi”. Ya daga wayar- ya maka ta da Kasa yana huci, sai dai ga mamakinsa sai yaga Hasna ko motsi ba ta yi ba balleta yi KOKarin hana shi . Tana ,kallonsa kawai tana riqc ‘da kugu tana murmushi, hakan yakara kular‘da shi ya bi wayar yaci gaba da taka ta da kafarsa tana ta kara .ratattakcwa.-:”H.asna ta’ fashe da dariya ganin yadda ya keyi kamar ya sami Kato yana duka, ta ce ‘Ka san ‘mc?.Wallahi k0 a takalmina, don a yanzu na hau kan wani gurin ‘zan ci gaba da cartin da masoyina, in ce ka manta abin’ ba a kan_wayar ya kc .ba, kan yanar gixo yake wahalar’da kanka kawai; .kake amma ~ charting da Waya da Abduljabbar yanzu na’”-faré yinshi ‘ci’kin Rayuwata k0 da za,a zarge ni da igiyoyin aurankane “Karya kikc yi, shi din banza‘.’ wallahi dana sanya an batar da shi a duniyar nan, k0 ba ki san waye ni ba?” Yana huci yar kc maganar kamar zai shaqeTa. Ta daga kafada, “Koma me zaka yi masa hakan ba zai sanya na daina sonshi ba. Wallahi k0 kushewar Abdul ta fika a gurina, soko kawai…” Yadaga hannu kamar zai kai mata duka. amma sai ya fasa Cikin sauri saboda wani kashedi da zuciyarshi ta yi masa cikin gaggawa. Cikin tsiwa ta ce. “Ka dake ni mana. don Allah ka dakc ni ka gani babu wani abu da ya iya na soyayya sai fadan banza da fushi”. Ya yarfe hannuwansa yana huci ya kada kai. “Za ki ganckurcnki, wallahi k0 zan yafe miki komai ba zan yafc miki wannan maganar ba, dole watarana saikinyi dana sanin amhatonta… Dole ne”. Ya nufi kofa a fusace yana huci. Tabi shi da kallo tana dariyar tura haushi. k0 ba komoi ta kai shi inda ta kc buqata. Ba ita kadai za ta yi ta fama da ciWon zuciya da bakin Ciki ba. dole shi ma ya dandana. Ta nufi wayar da sauri ta dauka ta zare Slmcard din duka. Ta dauko wata sabuwar waya Cikin kwalinta ta maida layukan tayi updating din komai a kan sabuwar wayar Cikin ‘yan mimuna ta yi mata yadda ta kc buqata. ta hayc bisa gado ta fara lalubar Abduljabbar. ya sake turo mata sakonni Sun f1 goma yana tambayar yaya dai, lafiya. ina ta shiga’.’ ‘ Ta fara’ba shi labarin abi‘n’d‘a ya faru, ransa ya dinga zafi yana kara jin haushin Abba cikin ranshi. sakarai kawai. yadda ya kc taqama da kanshi bai kamata ya nunama: mace na wulakanta shi kamar haka’ba. Shi kuwa Abba daganan a fusace ya fice daga gidan cikin motarsa kai .tsaye barikinsa ya wuce don nan zuciyarsa ke saqa masa ya tafi . koya samu sauqi cikin zuciyarsa can tsakoyar sabon gari gurin gurin da sukc shqe ayarsu yana shiga abokansa da yakeyiwa Barin kudi suka taso suna ihu da shcwa suka nufeshi amma hankalinsa yana kan yarinyarsa Ruma baby. wacce kc kallonsa da kallo irin nasu na ‘yan iska. Ya isa gurinta da sauri ya kamo ta yana murmushi suka fara aikata abin da suka saba. Har wajcn karfc daya na dare suna tare. ya manta da damuwar da Hasna ta haddasa masa sam. domin ya sha kayan mayensa ya yi tatil, ga kuma Ruma da kc taya shi nishadi. ba kuma su rabu daga nan barikin ba ya’daukcta a mota Suka wuce can gidansu, kasancewar sashinsa daban, yana‘ shigar shi da ‘yammata k0 mai gadi bai sani ba, domin glass din motar tasa baka ce kuma k0 da yaushc a dage ya kc, don haka’sai ya shiga har su kammala abin da suke yi babu wanda ya sani. Yau ma hakan ya yi, suka kwana suna shashancinsu da Ruma, sai dai tunda Alhaji Auwal mahaifinsa ya dawo daga sallar asuha ya tsinci wayarsa a yashe a kasa kusa da motarsa, don ya yar da ta ne sanda ya kc kokarin kama Ruma da ta kusa fadiwa Abin ya ba wa mahaifin nasa mamaki matuka. amma ya bari idan sun hudu a masallaci ya ba shi, ya kuma tambaye shi dalilin yar da ita, k0 bai sani ba ne. Duk da Abba yana yin dukkan abin da ya so na badala da shakiyanci, amma yana kOkari gurin yin sallah har ta asuba, musamman da ya ke ya san mahaifin$a bai son wasa da sallah. hakan ya sanya ta zauna a jikinsa, har sallar asu’ba ba ta wuce shi. amma yau kam bai ma san an yi kiran ba. domin ya sha kayan mayen da suka fi qarfin kwakwalwarsa ya bugu da yawa. ‘ Alhaji Auwal ya yi» mamakin rashin ganin Abba a masallaci, har aka dar da sallah. Ya jima yana lazimi k0 zai ,ga shigowarsa amma shiru bai ganshi ba. har ya gaji da jira ya’miqe ya nufi gidansa. A harabar gidan ya yanke shawarar biyawa ta sashin dan nasa ya gani k0 lafiya, k0 makara ce ya yi don haka kai tsayc ya wucc sashin nasa. Gida ne guda shi ma mai zaman kansa, don suna ji da Abba sun yi masa komai na jin dadin rayuwa. kayanshi ma duk a kasashen wajc ya aka zo dasu ga mamakinsa sai ya ga kofar da zata sada shi da Bangarcn nasa a budc. don haka kai tsaye ya shigc da sallama. Ya tsaya a falonshi na farko yana ta sallama, amma karar talabijin tana ta yi daga falonshi na ciki. wanda hakan ke nuna masa kallo .ya kwana yana yi kcnan. wata qila shi ya sanya ya maka‘ra. don haka ya nufi falon tsakiyar. ya kama kofar ya bude yana yin sallama. idonshi ya hango masa mugun abin da bai taBa tsammanin zai gani ba. Cikin tashin hankali ya zabga salati. domin Ruma da Abba ne baje a tsakiyar falon bisa kafet suna hacci. duk sun gaji. Ruma daga ita sai sikct da ta ja shi kirjinta. shi kuma gajeran wando ne a jikinsa, sai yajuya da sauri ya fice. Salalin da Alhaji Auwal ya sane ya farkar da Abba daga nauyayycn haccin da ya daukc shi. sai ya ji kamar muryar mahaifinsa ya ji ‘cikin mafarki. amma kuma ya jiyo kamar numfashi a falonshi na farko. don haka da sauri Nufi“ falon ya budc kofa. Saiya hango mahaifinnasa yana fita da sauri yana ta sallallami. hankalinsa ya yi mugun tashi ya dafe kai yana hango mahaifin nasa. duk son da mahaifinsa kc yi masa ya san bai son ya dinga aikata irin wadannan abubuwan. zai iya yi masa komai. . Ya koma cikin dakin da sauri a rude. ya nufi Ruma ya fara daka mata duka cikin kagauta. Ta farka firgigit da mamaki tana kallonsa, ta Ce “Ya ya dai mutumina. k0 har yanzu Kwayar ba ta sake ka ba ne?” ‘ Cikin rawar baki ya kc fadin,“ “Daddyna… Babana… Ta kallc shi da mamaki tacw “Kai kuwa lafiyarka Abba. me: ye haka ne “Kc da Allah. Daddyna ne ya sbigo nan da kansa ya ganmu. jiya ba na cikin hayyacina na manta na bar kofar a bude ban rufc ba. Ya gan mu… Tashi maza na maida kc…” “Amma dai ka bari k0 wanka na yi k0?“ “Wane irin wanka. kc fa wani lokuci tamkar jaka ki kc, ba kya fahintar karamin bayani. Ya ya baban nawa ya ganki a nan sannan ki ce zaki tsaya yin wanka, idan zuwa ya yi ya dauko makami da zai karya ki kuma fa?” Sai ta rude tace. “Kuma fa haka ne Nan da nan ta fara dibar kayanta tana sakawa jikinta yana rawa. sai da ya kai ta har bakin titi cikin ‘motarshi, sannan ya dawo gidan. Kai tsaye Bangarcn iyayen nasa ya dosa. don su yi masa abin da suka ga dama, ya San dai yau mai raba shi da Babansa sai Allah, da ma mahaiflyarsa’ ce ta ganshi za ta iya jan bakinta ta yi Shiru kawai. Alhaji Auwal yana falo yana ta bala’i, hajiya Aimana tana zaune tana jinsa. Jikinta ya yi sanyi, ranta a Bace don babu abin da ta tsana a duniya bayan a Ce yau danta ya yi Laifi tasan yana yawon bariki da ‘yan shaye- shayc tabbas,‘ amma ba ta yi zaton yana shigo da mata gidan ba. don tana yi masa fada sosai a kann ya daina wannan din ma, amma fadan da .-alhajin ya ke ya yi yawa. sai ka ce zai tsine wa dan nasa. . Abba ya turo kofa ya shigo da sanyin jiki. Alhaji ya kalle shi da sauri da. Bacin rai. yana fadin “Mutumin banza mutumin w’Ofi. wato shukiyanci da iskancin naka ya kai har ka shigo Cikin gidana kana yi k0. wanda ka ke yi a can titi bai ishc ka ba sai ka kawo mini mata Cikin gida don ka janyo mini tsinuwar Allah da zagin mutane To wallahi ba ka isa ba, zaka iya bar min gida a kan wannan abin”. Hajiya ta kwantar da murya tana fadin. “Ka yi hakuri Alhaji Kuruciya .ce ta kai shi ga aikata hakan, amma da ya yi aure zaiyi hankali Cikin fushi ya kuma katse ta. “Uban waye zai ba shi auran yana yin wannan abin‘.’ Tsaya ka ji na gaya maka babu kai habu auran Hasna, zan sami dan uwana na sanar da shi dukkan abin da ka kc aikalaWa… Ba za a yi auren nan ba”. ‘ Duk cikin kalaman d‘a, mahaifin nasa ke fadi. wannan ce taf1 yi masa ciwo da tayar da hankali, don haka ya dinga kallon mahaifinsa da faduwar gaba idonsa a waje, ita ;kam Hajiya Aimana jin dadi da farin ciki. Ne ya cika ta. ‘ wannan shi ne abin da, ta jima tana nema, ga- shi nan Allah ya kawo mata Cikin ruWan sanyi, ‘sai ta‘ji kamar ta‘ zuba ruwa a kasa‘ ta sha don dadi da farin ciki. ‘ Ta inda ‘Alhaji Auwal yake shiga .ba’ta nan ya ke fitaba, sai da yai mai isarsa sannan ya fice yana huci, Abba ya’kalli ’mahaifiyarshi idonshi ya Sauya kala,’ya Ce. ‘ ‘ ‘ “Mom, kina jin abin da Alhaji yace amma ba ki-ce komai ba, kin f1 kowa sanin irin .yadda .n’a ke son Hasna, me ‘ki. ke tsammani zai faru idan na- rasata? Ta daka masa harara; “Yafi kyau ka rasata, daman.,can bana son auran nan naku; kai ba ka jin kunya a‘ Ce kana» son yarinyarda ita~,ko~sunanka batason taji me ta ke da shi’.’ da zata iya yimaka haka?’, Ya Kara marairaicewa yace ‘Haji’ya wai baki San meye, so bane baki’S’an yadda na kc son Hasna ba‘? Wallahi’ zan‘iya rasa hankalina idan na rasa ta nasan ba za ki‘bari hakan ta ka-Sance daniba don Allah ” kiyi wani abu akai haushi ma ya–kara. bata yanzu ta karaamincewa da . asiri;,aka yima danta do wannan ba, ”ba ‘soyayyar Allah da Manzonsa bace Aman komai yaxo karshe D‘ukkan abin; ; da: ; ‘ Abba; ya“gaya wa mahaifiyarsa ta yi kunnen uwar shégu dashi na zuwa roqon abban sa taKi sauraransa,‘hakan ya sanya abba cikin damuWa Kwanaki kusan uku yana ~fama da abu guda, sai bin: kan mahaifins‘a ya ké a kan ya yi haKuri amma ya Ki sauraranshi da ya kc ‘mahaifiyarshir-tana ta zuga shi, abin da ta ke nunawa shine. kada . “a yi auran nan zumuncinshi da’ danuwansa zai ‘lalacene Maganin kar a yi to kar a soma, ’duk da yana sau’raran ‘magananan amma ba. haka ne abin ya kc fata ya kasance ba, sai don idan habu Yadda zai yi; ’ Yau yana zaune a office yana ta, aiki, Abba‘ ya turo kofa ya~ shigo da sallama, ya ganc muryar tasa don baka kai k0 daga kai: ya kalle shi.ba ya amsa, Abba ya ja’kujera- ya zauna da damuwa da tashin hankali ya fara” magana. . “Alhaji ina wuni‘?” Ya amsa bai kalle shi ba. Abba ya Ci gaba damagana. , .“.Don Allah Alhaji ka .yi haku‘ri, wallahi- ‘ na yi nadamar abin da na aikata, ba kuma zan ‘ Kara ba, ka yi mini afuwa bana fatan;na rasa Hasna, don ko Allah ya san ina sonta‘da gaske”; Ya kwantar da murya ya dinga lallashin mahaifin nasa kamar‘zai fashe da kuka. Alhaji Auwal yana sauraransa har ya ji zuciyarshitayi sanyi, da man wannan ya ke fatan ji’ daga bakin dan nasa. Ya daga, kanshi ya kallc shi yana girgiza kai, yace “Abi‘n da: ka aikata- ya Bata mini rai‘ kwarai da gaske, amma wannan maganarda ka fada ta sanya ‘zuciyata yin sanyi. har na ji zan iya janyc kudirina. amma akwai sharad‘i guda daya. a yanxu saura sati uku bikinka da Hasna. dun haka cikin wannan lokacin zan Kara sanya maka ido na ga ka sauya k0 ba ka ‘sauya ha. Idan har ba ka sauya ba nima ba zan fasa da kudirinaba nason raba,ka da ita ba tashi ka ba ni guri”. . Sai a sannan ya ji dadi cikin zuciyarshi, sannan ta hakan ya gane bai sanar da qanin nashi komai ba, don haka ya sami’ damar zuwa ga Hasna a yau. Sai dai bai tarar da ita a gidan ba ta fita unguwa, ya zauna zaman jiranta. A Bangaren Hasna tana‘ tare da Abduljabbar a gidan Murtala yana: rarrashinta da bata baki kamar- yadda ya saba don ya gama sarcwa ya sani ya rasa Hasna zuwa Wannan lokacin. ya’rage saura sati biyu a kammala shirye-shirycn komai. don an kawo kayan lefe da dukkan wani abu na aurc. gidan iyayensa sai shiryc-shiryc sukc yi. dukkan yadda Husna ta so lallas‘hin Hasna akan ta yi hakuri ta kwantar da hankalinta su je rahon katin biki abinya faskara. don cewa ta kc yi babu inda zata , auran da ake farin ciki da shi akc yi wa gayya ba irin nata ba na dole, dolc ta hakura ta kyalc ta ta kc rabonta ita kadai. Abba kam ya‘shafa wa kansa lafiya, ya daina tunkarar Hasna, yana zuwa gidan amma bai ce mata’ko uffan sai dai ya yi hirarshi da Husna k0 Hajiya Aisha k0 kuma Alhaji Sammani, a ranshi ya hakura da tunkararta har sai ran da ta zama tashi. “A Bangarcnta kuwa tana cikin damuwa da tashin hankali, don ta gama fidda rai da samun Abduljabbar, .mutumin da ta sha wuya kafin ta samu amincewar sOyayyarsa, amma ta rasa shi lakaci guda, dukkan abin da ya kamata ta yi d0n samunshi ta yi amma Allah bai Kadddara shi. ne mijinta ba, sai dai cikin ranta ta kudurci babu wani farin ciki k0 kwanciyar hankali da Abba zai samucikin ransa. Lokacin dabikiya rage saura sati guda sai Hasna ta ke jin kamar ta gudu ta bar garin’, dukkan wani abuda ake yi wa amare an _ zo yi mata amma taqi yarda da hakan, sai Husna kawai akc yi wa, Husna ce ta sanarwa da Hajiyan‘su taqi yarda Lili ‘yar Nijar din ta yi mata gyaran gashi. da kuma jiki. Hajiya Aisha ta shiga dakin nasu a tusace tana fada gami da fad’in “Ya kamala ki maida komai hannun Uhangiji, Allah ya Kaddara Abba ne mijinki sai ‘ki‘ yi haKuri, dukkan kaddarar da Allah ya yi :Wa bawa amsarta ya ke yi da hannu biyu”. Hasna ta fashe da kukan baqin ‘ciki, da me. za’ta jine wai‘? Tausayinta ya cika Hajiya Aisha kuma, saita nufe ta ta kamata tana rarrashinta da ba ta baki da nasiha gami da nuna mata irin abubuwan da*.;,.Allah ya tanadarwa ‘mutane masu hakuri, sai da ta samu ta sha kanta ta amince zata yarda a yi mata gyaran jikin Lili ta dinga tausarta da ba ta baki da nasiha, har sai da ta ji’ ranta ya yi, Sanyi‘. .Tsa’won, kwanaki’ hudu ‘da’suka kasance tare d’a Lili’gurin gyaran jikih ta ji sanyi da kwanCiyar hankali kadan duk da son Abduljahbar ya kasa barin ranta. ‘ Kwanaki suku suka rage ga bikin nasu, wanda suka zama tamkar ~ranar‘mutuwa ga Hasna da, .Abduljabbar, da kullum suke haduwa don jajantawa juna, Ga Abba kuma ya manta da lamarin Hasna ya Ci… gaba da mu’amalarshi da Ruma don ba zai iya rayuwa babu kadangarun bariki ba. _ .. Yau gidan a cikc ya ke da mutane, don yau cc ranar kamun amare, sai dai ‘tunda safe Hasna taficw daga gidan kai tsaye ofis din Abduljabbar ta nufa, don ta gaji da zuwa gidan su Karima. Ta tarar- da ,,shi cikin damuwa, yana ganintaya mike da sauri don tunaninta ya kc, yi cikin ransa ta shig0._ ,. Ta tsaya cak‘tsakiyar ofis din ta kasa motsi. Ya isa kusa da ita da sauri yana fadin. “Hasna lafiya?” ‘ Ta Sunkuyar da idanunta Kasa wadanda ke zubda hawaye’ cikin sanyin murya‘ta ce ‘ “Na’zo nc mu yi sallama, don yau ce ranar da za’a sanya ni a lalle Gaban Abduljabbar ya yanke .ya fadi, ya sanya hannuwa cikin aljihunsa’ da‘sanyin jiki yanakada kai. ya ce. ‘ “Ban yi zaton irin wannan ranar cikin ranakun haihuwata ba! Ban taBa son mace ba sai kc. ban taba tunanin aure ba sai a kanki Hasna! Ina sonki Hasna, sai dai lokacin da zan barki ya yi dole Hasna!” Hawaye ya Ci gaba da wanke idon Hasna, amma ta kasa daga kai ta kalli Abduljabbar wanda ke fadin kalaman da ke Kara kashe mata zuciya, ta dago kai ta kalle shi saboda kalmar da ya fada ta Karshe wacce ya ce. ” “Ina sonki Hasna!! Ina sonkii!” Sai ta ji kamar ta rungume: shi k0 ta ji dadi da sanyi cikin ranta. Shi ma hakan ya dinga ji cikin ransa, sai dai bai taBa samun fuskar yin hakan daga Hasna ba, lallai ‘yammatan da suke shiga jami.’a suna yin soyayya mai muni fiye da ‘runguma ma, amma bai taBa jin hakan a kan Hasna ba,. don ba ta taBa nuna masa wata alama ba, bugun zuciyarshi da shaidan suka dinga ba shi umarni da yin hakan. amma yana dannewa da ambatun Allah. Sai dai kamo hannunta da ya yi na dama, abin da’ya fadar da gabanta da sauri jikinta ya dauki rawa, ta kura masa ido, ga mamakinta sai ta ga ya Ciro zobe a dayan hannunsa ya sanya mata cikin yatsanta, sannan ya saki hannun yana ja da baya a hankali. Ta kalli hannun nata idonta na zubda hawaye wani zobe ne na azurfa mai kyan gaske, ba ta taBa ganin kira mai kyan wannan ba, sai ta jiyo muryarshi yana fadin. “Ina sonki Hasna! Zan ci gaba da rayuwa da sonki ba zan kara kallon wata mace da sunan s0 ba, Sai watarana Hasssssna!ya karashe maganar da sheshsheqar kuka ” Ita ce kalmarshi ta karshe a gare ta, ta kasa jure jin kalaman ta fice daga ofis din da gudu tana wani irin kukan dake tafe da daskararren baqinciki Shi kenan ta rabu da masoyinta ta rabu da Abduljabbar. Wayyo allah ina zansa raina ni hasna Eyyyah i feel sorry to those two lovers Aradu dukda ban taba soyayyah ba saida naji tausayinsu ya bani………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button