ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
2⃣6⃣

Zulai da ta yi kasake cikin dakinta’ a wunin yau saboda abin da ke faruwa, ta jiyo kiran Hasna ta mike cikin azama ta nufeta. Hasna tana tsaye a kofar kicin din, ta karasa cikin ladabi tana fadin “Gani Anty! “Ina neman sauran lemon tsamin da na ajiye cikin fridge ne ban ganshi ba.” Zulai ta matsa gaba cikin sauri tana Magana “Ba ri na dauko miki shi Anty, yana cikin firijin.” Ta nufi firijin da sauri ta fara Kokarin nemo abin da ta tambayeta, Hasna tana tsaye tana kallonta har ta fito da shi ta mika mata, ta amsa gami da kallonta tana fadin. “Shike nan je ki abinki.” Zulai ta fice cikin sauri domin bata son abin da zai sanya ta Kara yiwa uwardakin na ta laifl, Hasna ta bita da kallo har ta fice sannan ta fara Kokarin yin abin da za ta yi, lemon tsami guda hudu ne ta yanka shi ta matse a cikin kofi, sannan ta debo gishiri mai yawa ta sanya cikin ruwan lemon tsamin ta juya. Ta taba jin wasu ‘yan mata suna hira akan layin ATM yanda daya ta zubar da Cikin nata , tana gayawa dayar cewar lemon” tsami da gishiri’ ta hada ta sha kawai sai jini ya Balle mata, Wannan shine abinda take shirin aikatawa itama. Ta daga kofln ta kafa shi a bakinta ta fara sha, duk da rashin dadi da jin hadin kamar yana shirin dakatar mata da numfashin ta ne hakan bai sanya ta yi tinanin dakatawa da shan ba, sai da ta shanye tsaf ta ajiye kofin Abin kamar sihiri tana dire kofin cikinta ya fara hautsinewa ta dafe shi, sai ta dinga jin wani abu kamar zuciyarta za ta fito, ta lallaBa da kokarinta na komawa dakinta sai dai bata sami damar hakan ba ta durkushe cikin falon tana rike da cikinta, sai amai ya kwace mata, ta fara aman, dukkan abin da ta sha sai da ya fita daga cikinta,’ sai ta fara wani irin nishi. har ta daina fahimtar komai ta zube a falon sumammiya. Zulai taji kamar alamun motsin mutum cikin babban falon gidan, amman taqi fitowa domin tayi zaton ko masu gidan ne suke wani abin sai data daina.jin motsi motsin sannan ta yi Kokarin fitowa, tana fitowa idon ta ya fada kan Hasna da ke kwance a sume, ta gigiceta nufeta cikin tashin hankali tana jijjigata da ambaton sunanta. UWA MA BADA MAMA Haj. Aisha ta yi mamakin jin abin da Dakta ke sanar da ita game da diyarta, hankalinta yayi matukar tashi, amman saboda surukantaka ya sanya ta yi Kokarin boye damuwar ta, amma hankalinta ya tashi. Abdul yayi zaune ya kasa motsawa duk da Haj. Aishan ta sanar da shi za ta sanar da mahaifinta idan ya shigo, amman sai ta ‘ga bashi da niyyyar ta shi. Ta gyara zama sannan ta fara Magana “Ka kwantar da hankalin ka Abduljabbar da zarar Alhaji ya shigo zan sanar da shi tabbas wannan ba maganar wasaba ce ba, anjima za mu zo.” Wannan maganar itace ta kwantar da hankalin Abduljabbar suka yi mata godiya shi da Murtala, sannan suka yi mata sallama suka fara kokarin tafiya, suka barta cikin damuwa. ‘ Suna tafiya cikin mota wayar shi ta fara Kara, mamaki ya kamashi domin ganin kiran daga Hasna ne, ya kalli Murtala cikin mamaki. Murtala ya fahimci wani abu ya; faru don haka cikin Kaguwa yace masa.“lafiya me ya faru? “Hasna ce ta kira ni.” Ya bashi amsa cikin sauri‘ sannan ya danna wayar ya kara a kunnensa gami da yin sallama. Amman muryar da ya ji cikin wayar shine abin da ya tayar masa da hankali, kafin ya kai ga cewa komai ya jiyo muryar Zulai cikin kuka tana fadin “Alhaji Anti ta mutu…! A rude ya furta “Ke me kike cewa,ne kina nufin kice Hasna ta mutu? . HMMMMMMMMM Akwai chakwakiya kenan………………

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
2⃣7⃣

Zulai ta Kara maimaitawa cikin kuka “Eh ta mutu. . .kazooo ka gani. . . Gumi ya karyowa Abdul ya fara salati cikin karfi da rudewa, Murtala ya kalleshi cikin sauri. “Yaya dai me ya faru? Cikin wata irin murya da bai san me yake furtawa ba yace “Hasna ta mutu, Zulai ce ta yo mini waya yanzu! Kaga abin da na ke gaya maka k0? Ashe Hasna mutuwa za ta yi! “Ta mutul Murtala ya shima a gigice gami da Kara speed din motar yana ci gaba da Magana. “Kwantar da hankalin ka, ina zaton maganar ba gaskiya bace,bari mu Karasa gidan mu gani.” Yana Maganar ne cikin lallashi ganin yanda abokin na sa ya fita daga hayyacinsa gaba daya, Allah ya taimaka sun kusa isa gidan ma. Suna isa Kofar gidan Murtala ya saki horn, amman Abduljabbar bai ‘ iya. jiran Maigadi ya isa ba ya bude motar cikin gaggawa ya fice, Murtala ya bishi da kallo cikin mamakin yanda ya fice, dai-dai batason mutuwar Antin tata domin tana matukar kula da ita A harabar gidan ya ci kuro da Murtala wanda ke kokarin shiga gidan, yana ganinsa ya iso dauke da hasna ya juya ya nufi motar da sauri ya bude bayan motar. Abdul ya isa ya sanyata a bayan motar sannan suka koma gaban motar cikin sauri suka shiga suka tafl. asibiti bayan an amsheta karin ruwa aka fara kokarin sanya mata domin ruwan jikinta ya ja baya, gashi ta kwana ta wuni bata ci komai ba, sannan ga aman da ta sha dukkan karfin jikinta ya Kare gaba daya. Sai .da ya ga ta dawo cikin hayyacinta bacci ya dauketa sannan ya sami nustuwa, duk da sauran sakamakon bai kammala bayyana ba, amman a Kalla ya sami kaso ‘ saba’in na kwanciyar hankali. A lokacin ya tina ko sallar magariba ba su yi ba, gashi har an yi sallar isha’I, suka juya suka nufi masallaci domin bayar da farali. Bayan sun fito daga masallacinne ya fito’ da wayarsa daga aljihunsa, sai ya tararda miscall wajan guda bakwai na mahaifin Hasna, sai a lokacin ya tina wayar shi a silent ya barta, don haka cikin gaggawa ya kira Alh. Musa, cikin ladabi yayi masa bayanin abin da ya faru da asibitin da suke, a lokacin ya fahimci suna gidan sa domin duba jikin Hasna amman ance musu tana asibiti. Bayan sun kammala wayar suka nufi dakin kai tsaye, lokacin Hasna ta farka daga baccin tana karewa dakin kallo cikin damuwa, tun da ta farka ta fahimci tana cikin asibitine, a lokacin abubuwan da suka faru suka fara dawo mata cikin kanta, to waye ya kawota asibiti, me ya same ta har aka kawo ta asibiti? Tana tsaka da yiwa kanta tambayoyin Abdul ya shigo dakin Murtala yana biye da shi, ganin su’ya sanya zuciyarta wani irin bugu da tashin hankali, domin duk sanda ta gansu tare abin data gani daran nan shine ke dawo mata, shi kuma take kara gani tattare da su, sai ta yi saurin dauke kanta zuwa wani Bangare. Abdul ya kalli Murtala suka hada ido, Murtala yayi masa alamu da ido akan su Karasa, suka nufeta kai tsaye suka tsaya akanta. Murtala ne ya fara kokarin yin Magana “Sannu Madam yaya jikin? Ba ta kalle su ba kuma ba ta yi Magana ba, suka Kara kallon juna cikin damuwa, amman sai Murtala ya ci gaba da Magana. “Madam k0 kin zamakurma ne, na kula ko kallon mu ba kya son yi, ayi hakuri idan wani laifin muka yi ” Nan ma babu Magana babu kuma kallon su, hakan ya kara tayar musu da hankali. Murtala ya ci gaba da magana, sai dai ba ta ce masa komai ba, abin da ya kai matuka gurin bata ran Murtalan har hakan ya bayyana akan fuskarsa. Ya juya ya kalli abokinsa yana dan yaqe “Zan wuce ni Dakta Allah ya bata lafiya.” Abdul ya fahimci halin da abokinsa ya shiga, sai dai babu yanda zai yi sai ya gyada kai yana fadin “0k muje na dan taka maka mana.” Suka nufi hanyar fita kai tsaye, Hasna ~ tana jin abin da ke faruwa, ranta na ci gaba da suya idonta na zubar da hawaye, tana jin » kamar ta tsige karin ruwan da aka yi mata tabar asibitin, sai a lokacin tinanin abin da ya faru tun farko ya kara fado mata, wato akan zubar da cikin data yi Kokarin yi ne ta sanya hannunta da babu karin ruwan ta Shafi cikinta a hankali, ba za ta iya gane cikin yana nan k0 baya nan ba, wannan shine abin da ya Kara daga mata hankali. A waje Murtala ya kalli Abdul cikin damuwa yana fadin “Abokina na fara zargin wani abu bayan wanda kake zargi. .. Dai~dai lokacin Alh. Sammani da Haj. Aisha suka iso gurin, Alh. _ Sammanine yayi musu sallama, suka waiga gaba daya suka kalleshi, sai suka fara kokarin gaishesu cikin ladabi, bayan sun kammala gaisawa Murtala yayi musu sallama ya wuce, Abdul ya ji kamar ya bishi domin su karasa akan abin da suka_tsaya, amman sai ya dake domin bai kamata ya bar sirikan na sa ba, hankalinsa ya Kara tashi, domin bai san abin da abokin na sa ke son fada ba. Hasna tana jin muryar mahaifanta ta mayar da kanta gurin su, suna hada ido da mamanta sai ta fashe da kuka, Haj. Aisha ta karasa kusa da ita da sauri ta kamata a jikinta cikin tausayawa. Cikin Kuka Hasna ke fadin “Mutuwa zan yi Momy! Ki taimaka mini don Allah. . .zan mutu..gwara na mutu na huta.” Alh. Sammani yana kusa da su a tsaye hankalin sa ya tashi shima kwarai da gaske, Abduljabar kuwa ya kasa Karasawa kusa da su, ya tsaya daga baya-baya yana kallonsu cikin fargabar abin da ke faruwa. Haj. Aisha tana shafa kanta cikin rarrashi tana magana. “Kwantar da hankalin ki Hasna, ciwo ba mutuwa ba ne ba, za ki warke, za ki dawo cikin hayyacinki, kiyi hakuri.” Maganganun mahaifiyar tata suka dan kwantar mata da hankali ta rage kukan da ta ke yi. “Hasna, Allah zai ba ki lafiya, ki kwantar da hankalin ki.” Maganar Alh. Sammani ta Kara ratsa kunnenta, ta daga ido ta kalleshi a kokarinta na son yin murmushi duk da abin da ke damun zuciyarta. “Nagode Daddy.” Ta furta cikin jin dadi, dai-dai lokacin Husna ta shigo dakin a gigice, domin suna hanyar tahowa mahaifiyarsu ta yi musu waya ta sanar da ita halin da Hasna ke ciki, tare suke da maigidanta, kai tsaye Husna kusa da su ta wuce, sai dai ganin Hasna a kwance ido biyu ya sanya ta ji kaso saba’in daga cikin ‘ damuwar da take ciki ya ragu Maigidanta ya tsaya suna gaisawa da Abduljabbar, sannan ya Karasa kusa da Hasna yana yi mata yaya jiki. “Wai me yake damunta ne Abduljabbar? Alh. Sammani ya wurga masa tambaya. Hasna ta Karahade ranta ta kasa cewa komai, amman shi Abduljabbar damuwarsa ce ta qaru domin bai san komai akan ciwon na ta ba, amman da kunya ace bai san abin! da ya ke damun ta ba, don haka cikin qarfin hali ya fara bayani. “Eh da yake daman kusan .kwanaki biyu ba ta jin dadi, dazu kuma bayan na dawo daga ofis mun dan fita ni da Murtala, muna hanya Zulai ta kira mu ta sanar da mu halin da ta ke ciki, amman nafi ‘tsammanin aman da ta yi ne ya haddasa komai.” Ambaton sunan murtala ga mijin na ta sai ta ji kamar zubar ruwan dalma ne cikin ranta, amman da yake bata kallon inda ya shi ya sanya bai fahimci komai ba ya ci gaba da bayaninsa. “Sai dai Likitan ya tabbatar mana da babu wata matsala, yawaitan aman da ta yine ya sanya ta faduwa.” Alh. Sammani ya jijjiga kansa cikin gamsuwa, ita kuwa Haj. Aisha tini ta gano matsalar da ke damun diyarta, domin ance ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ne. “Babu damuwa, ina son na ganka minti daya yanzu Abdul.” Alh. Sammani ya buKaci hakan, gaban Abdul ya Kara faduwa fiye da farko, amman dai ya dake ya amsa dada To Baba, babu damuwa.” ‘ Suka yi hanyar waje tare, bayan fitar su Auwal yakalli matarsa wacce ta kalleshi . adai-dai lokacin yana fadin. “Husna zan dan fita waje kadan, idan kin kammala sai ki kirani a waya mu wuce. Husna ta daga kai tana fadin “Babu damuwa. Sannan ya Kara kallon Haj. Aisha yana fadin “Momy ni zan wuce Allah ya bata lafiya.” Haj. Aisha ta amsa da amin sannan ya wuce, suka mayar da duban su ga Hasna gaba daya, Husna ce ta yafito maman su tana fadin. “Momy zo ki ji.” Babu musu Haj. Aisha ta mike ta nufi gurin da Husna take Hasna ta bi su da kallo cikin mamakin abin da suke shirin aikatawa suka dan tsaya daga nesa da ita. Amman sai ta nuna kamar ba ta damu ba, bayan sun keBe Husna ta saci kallon Hasna sai ta ga ta kauda kanta gefe‘ guda, sannan ta mayar da dubanta ga mahaifiyarsu ta Kura mata ido ta fara magana. “Momy ni fa ina ganin matsalar Hasna ba ta asibiti bace ba, k0 baki kula da yanda ta ke wani kallon mutane da wani irin dubabane ”’Haj. Asiha ta kalli Bangaran Hasnan itama sannan taci gaba da magana “’Da zu da yamma’ mijinta ya je da abokinsa sun sanar da ni komai, ki na ganin hakan ne kema? ‘ “Haka ne Momy! Ta bata amsa cikin gaggawa ta dora da cewar “Momy maganganun Hasna da abubwaun da ta ke aikatawa basu yi kama da irin na mutane masu hankali ba, ya kamata ayi ‘wani abu akai.” Haj. Aisha ta gyada kanta cikin gamsuwa gami da dafa kafadar Husna tana fadin “Kar ki damu zamu tattauna yanzu da Baban ku, zo muje kar ta yi tsammanin wani abu ne.” Suka nufe ta kai tsaye, dai-dai lokacin da Alh. Sammani da Abdul suka shigo dakin, Haj. Aisha da Husna suka zauna kusa da ita, Hasna ba ta kula da shigowar mijin ‘ na ta da mahaifin ta ba ta fara magana. ‘ “Momy Husna ta gaya miki cewar kamar na sami matsala cikin kwakwalwata, k0 kuma aljanu sun taba ni k0? Gaba daya suka kalli juna cikin tsananin mamakin jin abin da ta fada, amman kowa ya kasa cewa komai. Hasna ta ci gaba da magana “Momy wallahi kar ku wahalar da kan ku, ba ni da komai, ba ni da aljanu, babu abin da yake damuna, kawai dai ina bukatar na rayu ni kadai ne yanzu.” Suka Kara kallon juna, maganar da ta fada mai harshen damo ce, don haka ba su fahimci abin da ta ke nufi ba kai tsaye, daga Husna sai Abdul ne suka fahimci hakan. Haj. Aisha ta kalli Abdul da mijin ta sannan ta fara magana “Ni fa bace mini ta yi kina da aljanu ba, ki kwantar da hankalin ki, komai zai zamto da sauki.” “Haka ta gaya miki, wallahi momy ba ni da komai, ki kalle ni da kyau mana, idan ba ku yadda ba ku kira malamai su yi mini ruqiyya k0 kuma ku fara karanta ayoyin sihiri da fitar aljanu ku gani.” “an gaya miki ya isa kibar maganar haka.” Ta kalli mijinta “Ya kamata mu wuce k0 Alhaji? Sai a lokacin Hasna ta fahimci sun shigo dakin amman ba ta ji ko dar a jikin ta ba, domin iyakacin gaskiyar abin da yake. ranta ta fada. ‘ Alh. Sammani ya Karasa kusa da ita ya fara magana cikin rarrashi.“Hasna na ji duk abin da ki ka fada, amman mijin ki yace mana dabi’un ki da komai na ki ya sauya, hakan ya sanya ya ke zaton akwai wani abu a tattare da ke. Ta kada kai tana fadin “Babu komai Daddy, momy za ta yi maka bayanin komai, akwai wani lokaci da mace ta ke shiga irin wannan yanayin, na ji kawai bana son komai da kowa ne, amman yanzu kam komai ya wuce, kar ku sanya damuwa a ranku, babu abin da ke damuna.” Alh. Sammani ya girgizva kai yana fadin “Na yadda Hasna, Masha Allah, ubangiji ya Kara miki laliya.” .Haj. Aisha murmushi ta yi domin ta gamsu da abin da diyar tata ta fada, ta kuma yadda ciki ne ya sanya ta yin abin da ta yi, a haka suka yi sallama suka wuce, sanda suka fara kokarin fita Abdul ya bi su domin rakiya, Husna kuwa Kara matsawa ta yi gaban ‘yar’uwarta domin ta tabbatar da abin da ta ke fada gaske ne k0 kuma wata sabuwar yaudarar ce daban. Cikin sanyin murya ta ambaci sunan ta, Hasna ta amsa gami da daga kai ta kalleta tana murmushi ta ce. “Abdul ya gaya miki na haukace, k0 kuma aljanu sun shige ni ko, irin haka ya je ya gayawa su Momy, duk abin da kuke fada da momy na jiyo, amman ina son ki sani bani da aljanu, duk abin da na ke yi ina yin shi cikin hankali na, ke ‘yar’uwata ce da ya kamata ace na gaya miki komai, na tsani Abdul bana son shi, domin na kama shi da laifin da bazan yafe masa ba, kar ki tambaye ni me yayi mini, amman ki sanya a ranki duk abin da na ke yi saboda abin da ya aikata mini ne, kuma babu makawa zan rabu da shi koda zai mutu ni ma zan mutu, abu na biyu shine na keson gaya miki, dalilin wannan’ cutar tawa saboda Kokarin zubar da cikin jiki na ne da na yi, domin bazan yadda na Kara haihuwa da Abdul ba, abin da na Haifa ma a baya na tsane shi! Tun data fara magana hankalin Husna ya tashi, yanzu kam ta tabbatar ‘yar’uwarta tana cikin hayyyacin ta, amman menene wannan ya faru mai zafi da ba za ta iya gaya mataba, me mijinta ya aikata gareta wanda har ya sanya ta fasa masa goshi ta tsane shi haka. Ta bude baki da zummar yin magana amman Hasna ta dakatar da ita ta hanyar ci gaba da magana “Kar ki ce za ki kara ba ni hakuri’ na gaya miki! Bana buKatarsa, sannan kar ki tambayeni kome game da abin da Abdul yayi mini domin bazan fada ba, kawai ki yadda ki goya mini baya kuma ki taimaka mini akan ganin na rabu da shi.” Husna ta girgiza kai gami da fadin “Bazan iya goyan bayanki akan abin da ba ni da hujja akai ba, ban san me mijin ki yayi miki ba balle na sanya lamarin bisa sikeli na aunashi na’ ga ya kamata na taimaka miki gurin ganin kun rabu k0 kuma sasantawa ne ya kama ce ku kiyi hakuri shine abin da zan gaya miki ‘ Wayar Husna da ta fara ringing da ke Jakarta, ta kalli Hasna kamar za ta Kara yin magana, amman sai ta sanya hannu cikin. Jakarta ta dauko wayar da sauri ta kara a kunnenta tana fadin. ‘ “Hello Abban Halifa? Ta yi dan jim sai ta mike tsaye cikin sauri “0k yi hakuri gani nan zuwa.” Ta kashe wayar sannan ta kalli Hasna “Zan wuce ni, domin Halifa ya tashi a cikin mota yana ta yi masa rigima, sai gobe zan shigo.” “Kar ki shigo domin ba za ki tadda ni ba.” Hasna ta bata amsa. “Bazan tadda ke ba kamar yaya? Husna ta fadi tana kallonta cikin mamakin abin da ta fada. Hasna ba ta Kara yin magana ba ta kauda kanta gefe, Husna ta yi dan jim kamar za ta Kara yin magana amman sai ta fasa ta fice da sauri, Hasna ta bi hanyar da ta fita da kallo cikin ranta tana fadin. “Sai dai kiyi hakuri Sister babu yanda zan yi ne, bazan iya gaya miki ba, na bar ‘wannan ya zamto sirrin rayuwata, saboda darajar dana Sadik.” _ Dakta yana waje cikin damuwa kowa ya watse cikin asibitin gari ya fara yin shuru, domin dare ya fara yi, yana son shiga cikin dakin amman yana shakka, da Hasna ta fada gaban iyayanta ya tayar da hankalinsa, ya jima yana saKawa da ~kwancewa amman magan. daji Karshé dole ya yadda ya amince zai shiga, a zaton shi na lokacin ta yi bacci, a hankali ya tura Kofar ya shiga ya maidata ya rufe‘ ya nufi kujerar da masu ziyara ke zama ya zauna, har lokacin bayanta yana juye tana kallon bango. Ya Kura mata ido daga bayanta yana kallonta, soyayyarta da tausayinta suna shigar shi, duk da yana jin damuwa bisa abin da ta keson aikatawa amman yana tausaya mata, sai dai yana bukatar su yi magana yanzu, kamar yanda ta yi bayani a gaban iyayanta shi ma ya amince cewar ba ta da komai illah wani abu da ya aikata mata da bai sani ba, don haka yanzu ne lokacin da ya kamata ya tunkare ta, sai dai~ wani Bangare na zuciyarsa ya lallasheshi akan ya bari‘su koma gida jikin ta ya Kara warwarewa. Hasna kam idon biyu, kuma tun da ya shigo tatai alamun shigoWarsa, ba tatauqatar shi a kusa da ita, amman tataaya zata ce ya bar ta domin ba tason kara yi masa magana, babu mafita bayan maganar, cikin kausashshiyar murya ta fara yi masa magana amman har lokacin ba ta waigo ba. “Da zaka taimaka ka fita daga dakin nan da yafi Mamakin jin abin ‘da ta fada ya kamashi tsammanin shi ta yi bacci, sai ya mike tsam ya nufeta yana magana. “Hasna please ki saurara mu yi magana don Allah… Cikin kara da kururuwa ta ci gaba da magana -“ Na gaya maka ka fice, idan ba haka ba ni zan fita na bar maka dakin, ka fita ka bani guri! Yanayin yanda ta ke magana Ya tsoratashi domin cikin kururuwa ta ke yi, ya ji kamar yace‘wani abu amman halin da ta shiga kamar na mai shirin tayar da iska ya tsorashi, don haka ya fice daga dakin cikin gaggawa_ Yana fita Hasna ta feshewa da kukan bakin ciki, k0 fuskar Abdul ba ta kaunar Kara gani. Dakta Abdul yayi zaune cikin reception cikin tashin hankali, ya rasa meye yake damun matarsa, kawai sai maganar da Murtala ya fada masa ta fado masa, ya zaro wayarsa da sauri ya daddana ya fara neman layin Murtala, amman sai aka ce masa layin a rufe yake, ya kalli agogon reception din wanda ya nuna shabiyu da rabi, takaici ya cika shi ya koma ya jingina jikin kujera. Ba zai iya tafliya yabar Hasna a asibitin ita daya ba, sannan kuma ba zai iya shiga dakin na ta ba, don haka dole sai dai ya kwana anan din yana ganin ta, haka ya zauna nan rabi baccinsa rabi da. Sai asuba sannan Abdul ya mike ya nufi masallaci domin bayar da farali, amman kafi ya wuce sai da ya lekata ya ga tana bacci sannan ya wuce. Bayan ya idar da sallah sai ya ga dacewar ya tafi gida yayi wanka, ya kawo mata koda tea ne sannan ya debo wasu abubuwan bukata. ‘ Tun kafin nurse din da ke kula da ita ta shigo ta farka, ta kalli Karin ruwan da ke hannunta wanda ya kusa Karewa, gaba daya ruwan da zaman asibittin ya isheta, don haka bukatarta kawai a cire mata. Tana sakawa da kwancewa Nurse din ta shigo, cikin fara’a ta fara gayar da Hasna, Hasna ta amsa babu yabo babu fallasa ta dora da buKatar ta cire mata Karin ruwan tana son ta yi sallah. Nurse din ta cire mata ta taimaka mata ta tashi zaune, sai ta ji jikin ta yayi kwari ba kamar jiya ba, tun da ta tashi a ranta Abdul ne ya fado mata sai kuma take tinanin to ina ya kwana gida ya tafi ya barta, maganar da Nurse din ke yi ce ta katse mata tinani. “Jiya Maigidan ki a reception ya kwana, muka yi da shi ya tafi gida, ko kuma ya shigo nan daki ya kwanta amman ya ki yin k0 daya daga ciki, sai yanzu ya fita cikin mota, gaskiya wannan mijin na ki yana ji da ke.” . Maimakon maganar ta sanyaya ranta sai ma ta kara kona ranta, ta Bata fuska ba ta ce komai ba ta nufl bandaki, ganin yanda ta yi ya sanya Nurse din ta fahimci ba ta son maganar don haka ta juya ta fice lokacin data ke kokarin shigewa bandakin. Acan gida har dankali da kwai ya sanya Zulai ta soya mata, ya harhada ‘yan abubuwa ya nufi asibitin, sai dai sanda ya isa dakin ya tarar babu kowa akan gadon sai ‘yan kayayyakin da aka yi amfani da shi jiya, bai kawo komai a ransa ba yayi tsammanin ta na bandaki, ya zauna gabansa yana faduwa akan abin da zai iya faruwa, ya zauna shuru tsahon lokaci yana mamakin kansa da abin da ya zama, ya rasa irin son da yake yiwa Hasna da ya sanya kasa baiyana mata tishinsa akan abin da ta yi masa zaman ya isheshi har ya fara saka wani abu cikin ransa, sai ya mike kawai ya nufi bandakin ga mamakinsa sai ya gan shi a bude, ya tura a hankali Kofar ta bude, ya leka babu kowa, gabansa ya Kara faduwa, to ina ta shiga? Shine abin daya tambayi kansa, ya fita a rude ya nufi reception. Ya fara tambayar mai zama a, reception din ko ta ga inda Hasna ta shiga, tace masa tabbas ta ga ta fita, amman ba ta yi tsammanin nisa ta yi ba domin tasan ba a sallame ta ba, suna cikin tattaunawa Nurse din da ke kula da ita ta Karaso tana tambayarsu abin da ya faru, mai zama a reception din ce ta yi mata bayani. Mamaki ya kamata ta zaro ido tana fadin “Au sai da ta tafi kenan? “Kamar yaya sai da ta tafi, daman ta ce za ta tafi ne? Abduljabbar ya wurga mata tambaya. Ta daga masa kai alamar eh tana ci gaba da magana “Eh ta ce mini na sallameta, na ce mataba ni da ikon sallamarta, dole sai likita ya Karaso, sai ta kama masifa na fice na bar mata dakin, yanzu da likitan ya shigo na yi masa bayani ya ce zai shiga ya duba ta, ashe ta tafi ma, gaskiya ba ta kyau ta ba, ta karya mana tsarin asibiti.” Abdul ya rasa abin da ya kamata yace don takaici, me hasna ta ke shirin mayar da shi da kanta ne, sai kawai ya nufi ofls din likitan, daman yana jiran jin sakamakon abin da ya sameta, suka bishi da kallo har ya wuce. Dakta Buba yana zaune yana rubuce rubucc Abdul ya kwankwasa Kofar, ya bashi damar shiga ya shiga da sallama, bayan sun gaisa Dakta ya nuna masa kujera da bashi umarnin ya zauna, amman sai Abdul yace. “A’a Dakta ba sai na zauna ba, domin . ina sauri ne na koma gida na ga k0 ta tafi can, domin ance ta fice ba tare da kun bata sallama.” Dakta Buba ya mike cikin mamaki yana fadin “Ta fita kamar yaya? Cikin haushi Abduljabbar ya bashi amsa. “Na iso da kayan break fast ban tarar da itaba, na Shigo ne domin jin sakamakon rashin lafiyarta, domin na san ta yanda ya kamata na Bullowa lamarin, menene yake; damun ta likita? Dakta Buba ya koma ya zauna yana kokarin lalubo takadda ya mikawa Abduljabbar yana yi masa bayani. “Kamar yanda na yi maka bayani tun da farko matarka ta zo asibitin nan da zummar a zubar mata da ciki amman ba’a yi mata ba, to ta kara kokarin zubarwa da kanta ta hanyar shan wasu abubuwa masu ‘ Karfi ne…. Abdul ya zaro ido a rude yana fadin “Likita yanzu yaya cikin ya zube kenan? “Anyi sa’a bai zube ba, amman idan har ta ci gaba da shan irin abin da ta sha komai zai iya faruwa gareta, abin tsoran ma ba Cikin kadai ne zai zube ba, har kayan cikinta zai iya tabawa.” “Kar ka damu likita, zan yi qokarin daukar mataki yau ba sai gobe ba, nagode, yunzu akwai wani abu da za a yi ne? Abdul ya karashe maganar tasa da tambaya. Dakta Buba ya daga kai “Kwarai da gaske, zan rubuta mata magani sai ka amsa anan pharmarcy idan ka flta” Ya dauko takadda ya fara rubutu, ya mikawa Abdul. A hanyarsa ta komowa gida kiran Murtala ya shiga wayarsa, da sauri ya dauki wayar ya danna ya kara a kunnesa. “Hello Dakta Falmata yaya aka yi ne, yaya mai jikin? “Babu sauki Murtala abubuwa sun Kara rikicewa, Hasna ta yi Kokarin zubar da ciki, shine dalilin ciwonta, sannan ta gudu daga asibitin yanzu…’ Cikin mamaki Murtala yace “What! Anya kuwa yarinyar nan ba ta yi hauka ba Abdul? Ran Dakta ya Kara Baci cikin karaji yace “Babu wani hauka, iskanci ne kawai, akwai abin da na game a yanzu, haihuwa ce ba ta buKata shine dalilinta na aikata komai, amman yanzu zan je na sameta, bazan kara yadda ta raina mini hankali ba, komai ya zo karshe wallahi sai na mata mugun rashin mutunci, ta tsayar mini da rayuwata da al’amura na cikin kwanakin nan, bazan yadda hakan ta kara faruwa ba.” Murtala yayi ‘yar dariya yana fadin “Ka ji shi kamar gaske, idan ka isa gaban Hasna fa komai rikice maka yake, ka bari zan tura Karima ta taya ta zama ta kuma lallabar mana ita, tunda mutuniyar ta ce.” “wallahi da gaske na keyi, kasan zan iya daukar komai amman banda asarar zuri’a, bazan yadda ta zubar mini da ciki ba, abin da ya sanya na kyaleta da farko ma ina tsammanin aljanu ne, amman tun da na fahimci ba hakan ba ne wallahi bazan yadda ba.” ‘ .Wata mota ta taho a guje ta kusa gOgawa Abdul da ke waya, Abdul ya kauce cikin sauri ya kusa taba na kusa da shi, amman Allah ya tsare, Murtala dada can Bangaransa ya ji abin da ya faru, don haka cikin sauri yace na ji kamar zaka gogawa wani mota, bari na barka, sai ka koma gida za mu yi waya. Abdul ya gyada kai yana fadin “Ba damuwa sai mun yi waya.” IDAN TA YI DAGA-DAGA. .. Hasna ta zamto tamkar mahauciyar da ta rasa gurin tsugunnawa, tun da ta dawo gida cikin Adai-daita sahu maigadi ya ganta ya Kara rudewa, cikin ransa ya dinga tambayar kansa abin da ke damun matar nan, amman dai bai da amsar tambayar sa, don haka ya dinga kallonta har ta shige. Ta rasa me ya ke damunta da raYuwarta, har ta na jin kamar ta kashe kanta ta huta, musamman da ta tabbatar da Cikin jikinta bai zube ba, wai shin me ya Sanya ba ta auri Abba ba ne tun farko, HMMM Lol. asha karatu lafia………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button