ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
3⃣1⃣

Murtala ya ci guba da neman Wayar Abdul amman bai same shi ba sai ma ya ji an kashe ta, jikinsa ya yi sanyi hankalinsa ya tashi kwarai da gaske sai ya fara kokarin mikewa cikin sauri, kayanbacci ne kawai sanye a jikinsa ya dauki makullin motarsa yayi hanyar fita, dai-dai lokacin Karima ta fito daga ciki tana yauqi ta sha kayan bacci, domin cikin wannan lokacin ta fara samun kan mijinta, tun bayan faruWar abin da ya faru a gidan abokinna sa ya dan shiga damuwa har ya fara komawa cikin hayyacinsa, kwanaki biyu k0 abokanai bai kawowa gidan, sannan daya dawo daga harkokinsa zai kasance a gida tare da ita da yaransa su yi kallo su yi hira’rsu, yanzu ma suna tsaka da hira ne ta tashi kwantar da yara daga nan ta ga ya dace ta dan sauya shigarta domin samo zuciyar maigidan na ta, sai dai kuma ta na fltowa ta hango shi zai fita daga gidan. cikin mamaki da daga murya ta kira shi “Dee! Yaya dai? Murtala ya juya da sauri ya kalleta daidai lokacin da ya fara kokarin bude kofar fita. ta nufeshi cikin gaggawa. “Yaya dai ina kuma zaka je a daran nan? cikin kokarin kwantar mata da hankali yayi magana “Yanzu zan dawo kar ki damu.” Kafin ta Kara fadin wani abu ya fice da gaggawa. ta bishi da kallo ta kasa~cewa komai a ranta tunani kala-kala ne ke yawo, babu abin da zuciyarta ke gaya mata sai dai abin nasa ya ciyo shi, ya fita don neman biyan buqatarsa ne kawai, sai ta ji damuwa ta qara baibayeta, ta fada kan kujera ta fashe da kuka‘ anya kuwa ba za ta yi irin abin da Hasna ta yi ba, ba zata daukarwa kanta mataki ba, shike nan haka za ta yi ta zama tana kallon mijinta yana aikata wannan abin? Hawaye ya fara wanke idonta mai ciwoda daci, meye amfanin rayuwarta da auranta ne?sai ta fashe da kuka. ABOKlN BARAWO! Abdul yana zaune akan kujera mai cin mutum uku ya dafce kansa da tafukan hannunwansa yana kallon kafet, dare ya fara ja amman babu alamun bacci cikin idonsa ya ji an buga Kofar babban falon gidan wanda shine zai sadaka da ainihin cikin gidan, k0 ba a gaya masaba yasan waye, domin mutum daya ne maigadi zai bashi damar shiga gidan sa a irin wannan lokacin, amman me ya zo yi masa, bai da abin da zai gaya masa, don haka bai k0 yi koKarin tashi ba balle ya bude. Murtala ya ci gaba da buga gidan yana magana “Kar ka mini haka bokina, ka bude don Allah, wallahi akwai maganar da na ke son mu yi, idan baka bude ba bazan bar gurin nan ba.” Yanda Murtala ke magiya ya sanya ya bude kofar cikin sauri, ran shi yana tina masa wata rayuwa da suka taBa yi da murtala ta taimakon juna da rufawa juna asiri. Bai kalli inda Murtalan yake ba ya koma ya zauna akan kujera ya dafe kansa kamar farko, Murtala ya isa ya zauna kusa da shi ya kura masa ido tausayinsa ya cika ransa, wai mutum kamar Abduljabar namiji mai cike da izza da kwarjini ne ya koma haka kamar wani sakarai, lallai ya yadda babu abin da soyayya ba ta bayarwa, babu kuma abin da bata sanyawa, watarana ta kai mutum ‘ kololuwar farin ciki, watarana kuma ta sanya shi cikin kuttun bakin cikin da ko motsi ba zai iya ba, kamar yanda ta sanya abokin sa yanzu ciki. Cikin kwantar da murya ganin yanda abokin nasa yake: nishi ya fara magana “Wallahi ba ni na ba shi lambar kaba Abdul! Abuduljabar ya daga kai da sauri ya.da. kalleshi, babu ja yayadda da. abin daya fada Murtala ya fada, bai Karya k0 shakka akan duk abin da zai aikata k0 , wani irin mutum ne shi da ake kira wawaye masu fadar komai gaba gadi Amman tambayar da ke ran Abdul wacce Murtala ya fahimta akan fuskarsa cewar to waye ya bashi lambarsa, murtala ya ci gaba da magana. “Kamar yanda ka sani Alh. Shazali ya sha neman hadin kai na, amman ban taba kallon shi a mutumin da ya kamata na kula ba, musamman idan na tuno waye shi a gurinka, ya tadda ni har ofis dina lokacin muna tare da Barista Saddam, a gabansa yayi kokarin na bashi lambarka ko na gaya masa wani abu daga gareka, amman bai sami hadin kai na ba, karshe ma mun rabu da shi cikin ~bacin rai, domin na gaya masa ya fita daga harkata, sai dai wani abu da na kula tun da Alh. Shazali ya shigo akwai alaqa tsakanin sa da Barista to ina tsammanin bayan na bar Barista cikin ofis din ya dauki lamabar cikin wayata ya aika masa, wannan shine kawai abin da nai tinani.” Abdul ya dalla masa harara cikin Bacin rai yana ci gaba magana cikin fada “Amman meye hadin ka da Barista Saddam, na gaya maka dukkan mutane irin wadan nan masu neman duniya bai kamata ka dinga hulda da su ba, idan har zaka yi mu’amala da Barista me zai hana ka yi da Alh. Shazali domin ba su da wani banbanci k0 daya ni a gurina! Yanda yake maganar cikin zafl bai dami Murtala ba sai ma murmushi kawai da yayi, a ganinsa Abdul kawai yana kishi ne amman a fili sai ya fara magana. “Abdul idan har kai da muka kasance tare tsahon lokaci zaka iya guduna, zaka iya juya mini baya akan wata mace me zai hana ba zan bi kowa ba, na gaya maka ka kuma sani halina da naka ba iri daya ba neba, ni mutum ne mai matukar bukata.. “Shut-up Murtala, please leave my house!! A yandayayi maganar ta girgiza Murtala kwarai da gaske ya saki baki yana kallonsa, amman bai motsaba ya ci gaba da magana cikin Bacin rai shima. “Kar ka Kara mini tsawa, kasan ko waye ni, kasan matsayina da darajata, akan me zaka dinga treating dina tamkar wani yaron ka? Meye ban yi maka ba, meye ban baka ba, domin ka haukace zaka gaya mini maganar banza! A hankali yake zaro maganar kamar ba daga bakinsa ta ke futowa ba, matuka ta fusata Abdul amman bai kamata ace shi yayi fada da Murtala ba, Murtala ya zame masa komai a sanda ya rasa komai, don haka yayi shuru kawai yana huci, dama wani ne ya gaya masa wannan ba shi ba da yayi maganinsa a yanzu.” Murtala ya mike a fusace yana huci yana kallon Abdul yana ci gaba da magana “Don kaga ina binka kamar wani yaron ka, k0 kuma raqumi da akala shi ya sanya kake mini haka, amman ka sani daga yau na barka, na bar rayuwarka, bazan kara k0 kwada nasan wani mutum mai sunan ka ba, kar ka Kara tinanin kai ma ka sanni! Yana fadin haka yayi hanyar fita cikin sauri ransa a Bace. Abdul bai yi kokarin ba shi haKuri ba, bai kuma yi yunkurin ce masa komai ba, ya bishi da kallo har ya fice, a cikin ransa yana fadin meye zai dame shi don wani ya rabu da shi, tun da Hasna ta rabu da shi bai damu da kowa ma ya rabu da shi ba, ya Kara fadawa . kan kujera. A Bangaran Hasna kwance kawai ta yi akan gado ta kasa yin komai, ta rufe idonta kwata-kwata domin cikin kwananin nan idan ta rufe ido sai ta dinga ganin Abdul da Murtala a halin da ta gansu, hakan ya sanya ta ke fargabar rufe idonta sai dai bacci Barawo da ya Iallabo. ya sace ta. KOWA YA DEBO DA ZAFI.. gari hantse, a Bangaran Abdul yaya ga dacewar yaya. tafi. aikinsa bai. kamata ya yadda matsalar kansa ta shafl aikin sa ba, amman kafin ya wuce sai da ya fara biyawa ya gayar da mahaiflyarsa, duk da ta kula akwai abin da yake damunsa amman ya nuna mata babu wani abu, idonsa a rufe yake da glass sai dai yanayin yanda yake magana kadai ya isa tona asirin halin da yake ciki, domin bai sami bacci ba kwata-kwata. A yau duk .daliban da basu san waye shi ba Sun fahimta sun kuma gano dalilin kiransa da sunan da ake masa lakabi a baya kafin Hasna ta shiga rayuwarsa ya sauya, yana sanye da bakin glass wanda ya flto da suffarsa ta boss sosai, lokacin shi yana shiga ya fada ajin, ya kuma bar kofar a bude, sai dai duk dalibi ko dalibar da ta yi kokarin shiga sai ta gane kurenta, har gaban daliban’ ya dinga fadawa, turanci yake zubowa kamar bakon America babu sauKi a idonsa, akwai ‘yan mata da dama da ke masa yanga da rangwada wanda bai taBa kallonsu a komai ba, yana nuna bai san suna yi ba, amman yau duk wacce ta nuna ita yar yangace da yauqi sai yayi waje da ita, hakan ya sanya daliban shiga taitayinsu, minti guda bai qara ba a lokacin sa ya fice cikin azama dauke da kayansa, kamar jira daliban suke ya flta aka fara hirarsa, wasu suna cewa kawai don yana cikin matsala sai ya huce akan su, kowa da abin da yake fadi, shi dai bai san suna yi ba. . A ofis dinsa yayi shuru tun jiya yake jiran kiran mahaifan Hasna amman ba’a kira shi ba, shi yana son ya kira amman yana shakka, sai dai a yanzu ya fara shiga damuwar anya kuwa gida ta wuce, don haka yaga dacewar taBa wayar mamansu, amman kunya da tsoro suna damunsa, daga Karshe ya yanke shawarar kiran Husna. Tana kan hanya tana tuqi kiran wayar Abdul ya shigo wayarta, ta dauka da sauri ta dannan ta kara a kunnenta. “Assalamu alaikum, malam an tashi laflya? Cikin fargaba ya amasa da “Lafiya lau Husna, daman na bugone na ji k0. .. Husna ta katse shi cikin sauri domin tasan abin da yake son fada yake in-ina “Ka kwantar da hankalin ka Malam, yanzu haka ina kan hanyar zuwa gida ne, tun jiya mun yi waya da Momy ta gaya mini komai, dole yau za ta dawo gidan ta, ka rabu da ita kar ka kulata, idan takamarta iskanci da rashin mutunci wallahi mun fita, don taga ana lallaBata ne, zan kira ka anjima.” Cikin sanyin jiki ya amsa da “Shike nan babu damuwa sai na jikii” Ya kashe wayar yana kallonta, kalaman da ta fada sun yi tsauri, sun kuma tabbatar masa da lallai idan suka bi ta wannan hanyar babu abin da zai hana Hasna ta fadi komai, tabbas za ta sanar da su waye shi, waye zai Kara kallonsa da mutunci idan wannan magana ta bayyana, dama bai kira wayar tata ba, dama yayi shuru da bakinsa, dama bai sanar da ita komai ba, dama-dama ta cika zuciyarsa har tana shirin fasata. Cikin lokacin nan zuciyarsa ta yi nauyi har ta fara gaza daukar wasu abubuwan, abin da yafi bashi mamaki ma da ciwonsa har yanzu bai tashi ba, a baya kananan abubuwa sukan tayar da ciwon nasa, amman a yanzu yana jinsa kamar ba shi ba domin ya kamata ace ciwonsa ya tashi a yanzu, ko da yake tun bayan auransa da Hasna farin ciki da kwanciyar hankalin da ya shiga aka tabbatar masa da cutar da take damun zuciyarsa ‘ a kaso dari an sami rangwame casa’in; yana tsammanin wannan ya sanya har yanzu bai girgiza ba. Hasna ta yi shuru a daki tun da ta idar da sallar asuba bata tashi daga kan sallayar da ta ke ba, tana ta lazumi da addu’a, addur Allah ya rabata da cikin da ke jikinta sannan ya sanya Abdul ya saketa cikin ruwan sanyi ba tare da ya matsa harta tona masa asiri ba. Haj. Aisha ta gaji da jiranta a cikin falo sai ta bita dakin ta tarar da ita zaune akan dardumar, a zuciyarta ta fara fadln kamar gaske anyi sallah ana addu’a amman an kasa zaman lafiya da miji, ko da yake ita kanta tana zargin irin kishinta Hasna ta dauka, amman ita ai kishin na ta bai sanya tabarwa wata mijinta ba, tana zaune a gidanta ana turzawa, me ya sanya ita Hasnan za ta yi irin wannan shiriritar. Cikin kakkausar murya ta kira sunanta, Hasna a juya a firgice domin kwata‘kwata bata san ta zo dakin ba, cikin kokarin boye damuwarta ta fara gayar da mahaifiyarta ta dora da fadin‘ “Ban san kin tashi ba Mumy da na shigo na gaisheki, ina kwana“ “Yaya za ki san na tashi tun da baki duba agogo kin gani ki taso ki yi break fast.“ ba ta qarasa maganar da bata umarni. Hasna ta hade rai, cikin kwanakin nan ta dauki abinci tamkar makiyinta. bata son k0 ambatonsa ayi. cikin kokari ta daga kai ta ce “Momy ba na jin yunwa ni.“ “Ai daman wani lokacin ba don yunwa aka cin abinci ba‘ don ya kamata aci din, ki taso tun kafin na bata miki rai.“ Haj. Aisha ta bata umarni dole ya sanya. ta tashi tsam ta nufi waje. a cikin abincin bata kaunar k0 sha‘awar komai, Haj. Aisha tana kula da ita yanda ta dinga jujjuya cokali cikin abinci bata ci wani na kirki ba. amman dai tasha ruwan shayi da dama momyn nasu ta shiga ciki domin yin wanka. da ta fito sai ta tarda ita: ainda ta barta bata da niyyar tashi bare ta gyara jikinta. Hasna ‘yar gayu da Kyale-kyale ace ta kasa yin wanka ma balle bukatar sake kaya. Ta yi tsam tana kallonta har ta ji a jikinta ana kallonta ta daga kanta ta kalli bangara da mahaifiyarta ke tsaye, sai ta Kakaro murmushi, amman bata san ta riga ta hango hawayen da ta ke zubarwa ba Dai~dai lokacin Husna ta shigo gidan tana rike da Jakarta, kai tsaye ta nufesu tana gayar da mahaifiyarta, Haj. Aisha ta amsa cikin sakin fuska sannan ta ja kujerar dinning din ta zauna, bata k0 kalli Inda Hasna ta ke ba, itama Hasna bata damu da kallon inda ta ke ba, amman ta san zuwan Husna din nata ne, don haka ta hade rai, ta shirya gaya mata abin data ga dama, domin ba ta ga dalilin da ya sanya za ta yi kane-kane cikin rayuwar ta da auranta ba. Haj. Aisha ta Kurawa Hasna ido wacce ta kauda kan ta gefe kamar bata san suna gurin ba, Cikin kakkausar murya ta fara yi mata magana. “Gani gaki ga ‘yar’uwarki ina son ki gaya mana dalilin da ya sanya ki ke shaawar rabuwada mijin ki Hasna? Hasna ta daga ido ta kallesu wanda ya sauya lokaci guda kamar ta fasa kuka cikin rawar murya ta fara magana “Momy ina tsammanin mun kammala maganar nan tun jiya, yaya za ki kasa fahimtata, wallahi bana kaunar Abdul a yanzu, bazan iya ci gaba da zama da shi ba, idan kuka matsa mini komai zai iya faruwa. “Rufe mini baki sakarya shashasha babu abin da zai faru kawai dai zakiyiwa yiwa kan ki asarar da har abada ba za ki iya mayar da itabane Haj. Aisha ta fadi a fusace kamar za ta rufe Hasna da duka sannan ta ci gaba da fada. “Sakarya baki san irin baqin jinin da na dauka akan auran ki ba, kin manta irin gumurzun ‘ da muka yi da baban ki da danginsa, shine yau ki ke son saka mini da wannan! To wallahi baki isaba Hasna, ba za ki sanya maqiya su mini dariya ba. Hasna ta fashe da kuka cikin Bacin rai tana fadin “Momy karki yanke hukunci bisa bacin rai, wallahi na tsani Abdul, karki yanke hukunci akan abinda ba ku sani ba “Meye ba mu sani ba, mun san komai, k0 ba kin yanke shawara rabuwa da mijin na ki saboda kawai kin ganshi da wata cikin motarsa bane, ba wannan ne dalilin na ki? Haj. Aisha ta katseta da tambayar da ta sanya ta kalli Husna, tasan ba wani ne ya bayar da wannan labarin ba sai Hasna, kallon da ta ke yiwa Husna na takaici kamar za ta rufe ta da duka ya kara sata su, Husna ta doka mata tsawa. “Menene ki ke kallo na, ai kin riga kin san wannan maganar ni ma na santa, akan kishin banza kin hana kowa kwanciyar hankali, kin hanawa kan ki jin dadin rayuwa! Husna ta fada hakan a fusace. Hasna ta kawar da kanta gefe, dama za ta iya gaya musu abin da ya faru, da sai sun tabbatar ta yanke hukuncin da ya kamata, amman ba za ta iya ba, don haka ba ta san da menene. za ta iya kare kanta ba. Tsawar da Haj. Aisha ta doka mata ne ya sanya ta dawowa cikin hayyancinta “Ko ba haka bane ki ka yi shuru, mara kunya! Babu tsoro ta ci gaba da magana “Ba haka bane Mamy Wallahi tallahi ba haka baneba, ban san wannan maganar ba Suka kalli juna cikin mamaki da tsoron jin abinda tace, hankalin Haj. Aisha ya kara tashi ta dinga nuna hasna da yatsa tana kadashi hasna akan son ki kare kanki zaki rantse da karya mai ya sanya kikeson sauya halayenki daga masu kyau zuwa marasa kyau allah yana kallonki shine kike rantsewa dashi don kawai ki kare kanki hasna ta kuma marairaicewa tanaci gaba da kuka ki yarda dani momy wallahi tallai baansan da wannan labarinba kuma ki kira abdul ya fadi hakan a gabana sannan ya rantse da hakan idan har yayi na yarda zan amshi laifin amman walli mommy ba haka bane suka kara kallon juna cikin mamakin maganganunta daga sama suka jiyo muryar Alh sammani yana magana “Make furuwa ne a gidan? Suka juya gaba daya suka kalleshi, ran Haj. Aisha ya Kara Baci domin ba ta so ya zo ya ji matsalar bata so ace sai ta sasanta komai sannan zai ji yaran kuwa wuqii-wuqi suka yi suna kallon sa cikin fargaba, yana ci gaba da doso su yana Kara tambaya. “Na ce menene ke faruwa, na ganku haka carko-carko? Ya tsaresu da ido yana jiran jin amsar su, amman sun kasa cewa komai, ya kara doka tsawa cikin Bacin rai. Husna ce ta yi karfln halin yin magana “Daddy Hasna ce suka sami matsala da mijinta…shine …shine… “Shine me? Ya Kara fadi a fusace yana ci gaba da kallonsu, hanjin cikin Husna ya qara kadawa, ita kuwa Hasna ji take yi kamar ta zura da gudu, Haj. Aisha k0 dar, sai ma haushin tambayar ta ke ji. “Daddy shine ta taho gida tun jiya tace ba za ta koma ba.”Husna ta karasa a rude. wannan karon be .iya cewa komai ba sai kallon Hasna kawai da yayi cikin nazarin yanayin yanda ta ke kuka ya sanya jikinsa yin sanyi. Sai ya wuce ya nufl falo yana bayar da umamin su bishi, babu musu suka tashi suka bishi. A qasan kafet yaran suka zauna, Alh. Sammani ya zauna akan kujera, Haj. Aisha ta zauna ne sa da shi, ya kalli Haj. Aisha cikin Bacin rai, yama. rasa abin da zai ce mata, amman dole ya magantu domin shine kawai mafita. “Me ya sanya baki sanar da ni abin da yake faruwa ba tun jiya Aisha? Ya tsareta da ido domin Jin amsar da za ta ba shi. Babu ko dar saBanin‘ ya’ yan na tata fara magana “Me ya sanya zan gaya maka bayan baka gidan? “Me ya sanya ki ke mini haka Aisha? Duk abin da zai faru bazan sani ba sai daga baya, idan kuma na yi magana kice bana gidan, yanzu kenan ko mutuwa wani yayi cikin iyalina ba zaki sanar da ni idan bana gidan nan ba kenan? “Don Allah kar ka Bata mini rai Alhaji, wannan tsohuwar magana ce da muka jima da yin ta, kasan dai bana kiran ka idan kana gidan matar ka ko? Abin da ta fada ya Kara hasalashi, amman ya kula idan ya biye mata za su raba hali gaban yaran, domin ita akan kishinta tana iya aikata komai, don haka ya maida kallon sa ga Hasna cikin kokarin ya manta da abin ‘ da Haj. Aishan ta aikata masa ya ci gaba da magana. “Hasna menene dalilin da ya sanya ki ka dawo gida harki ka kwana ba tare da kin sanar da ni ba? Hasna ta sunkuyar da kanta domin ba ta da amsar. da Zata gaya masa, ya ci gaba da kallonta yana magana. “Ki gaya mini menene ya .hadaki da mijin ki? Ya Kara wurga mata tambayar da ta sanya cikin ta kadawa, Baban ta ba irin muhaifiyar ta bane, yaya zai fahimci abin da za ta gaya masa, yanda ya tsare ta da ido .ya sanya dole ta magantau. Cikin sheshsekar kuka ta fara magana da inda-inda “Ni bana son shi Daddy…don Allah ka yi haquri bi sa abin da na aikata maka a baya, na yadda yanzu zan auri’ ko waye kake so, ka yi haquri.” Mamakin abin da ta ke fada ya cika shi amman sai ya bar abin cikin ransa ya sauya da wata tambayar “chan naji ki sanar dani abin da ya hadaki da mijin ki ba maganar abin da ya gabata ba, ki sanar dani abin da yayi miki da ki keson rabuwa da shi? “Ba Abin da yayi mini Daddy kawaidai na gaji da zama da shi ne, na kuma gano ba irin mijin da ya kamata na aura ba ne, ka taima mini don Allah Daddy! Kukan da ta ke yi da magiya shine ke Kara sanya shi cikin tsananin mamaki, ya Kura mata ido domin kokarin gano wani abu amman ya kasa,don haka yaba su umarnin tafiya. “Shike nan ta shi ki je, zan neme ku daga buya.” ‘ Kamar jira take ya ambaci hakan ta mike cikin gaggawa ta yi hanyar dakin da ta ke zauna husna ta bi ta da sauri itama, Haj. Aisha ta mike itama za ta bar gurin amman Alh. Sammani bai bata damar da hakan ba. “Aisha ki zauna ina son yin magana da ke Ta yi tsaye kamar ba za ta zauna ba, amman yananyin yanda yayi maganar cikin rarrashi ya sanya ta yanke shawarar zaman ta koma ta zaUna ba tare da ta kalli inda yake ba. Ya kalleta yanadan yaqe haka take duk sanda ya baro gidan amaryarsa yakan jima kafin ta saki. jiki da shi h amman idan. aka. wuni sai kuma. komai ya wuce “Bayan zuwanta mijin na ta bai zo k0 ya bugo wayaba? Alh.Sammani ya Kara tamaya. “Ni dai bai bugo mini ba, amman ban sani ba k0 ita ya buga mataba, sai dai Husna ta ce mini yanzu tana kan hanyar zuwa gidan nan ya kirata a waya cikin tashin hankali.” Ya girgiza kai alamar gamsuwa da abin da ta fada sannan ya sanya hannu cikin aljihun rigarsa ya dauko karamar wayarsa ya fara daddanawa ya kara a kunnensa. Abdul yana zaune shuru akan kujera yayi tagumi wayar shi ta fara Kara, kamar mai jira ya miKa hannu da gaggawa ya dauka yana ganin sunan mahaifin Hasna ne gabansa ya fadi wanda bai taBa yin irin sa ba tun da yake cikin rayuwarsa, cikin rawar hannu ya ‘ danna amsawa ya kara a kunnensa. Shi ne ya fara gayar da sirikin na sa cikin ladabi, Alh. Sammani ya amsa cikin yanayin da Abdul bai gane ba sannan ya dora da fadin “ldan kana da lokaci ka zo gida yanzu ina son ganin ka Abduljabbar.” Cikin gaggAwa ya amsa da “To Baba gani nan zuwu yanzu insha Allah.” Alh.Sammani ya kashe wayar sannan’ ya Kara kallon Haj. Aisha “Ki je kice ta shirya, yanzu mijinta zai zo su wuce gidan su.” Haj. Aisha ta kalleshi cikin tsananin tsoro da mamakin jin abin da ya fada “Alhaji kaji abin da kace kuwa? “eh haka nace, ta shirya su tafl da _ mijinta, k0 kina ganin akwai wani abu ne bayan haka Aisha? “Eh da an bi abin a sannu, wataqila akwai wani abu da suke Boye mana.” Ta bashi amsa cikin damuwa. “Hakan yasa nace ta shirya tabi mijinta, idan har tace tana son rabuwa da mijinta ba tare da wani dalili ba sannan shima ya kasa sanar da kowa komai, kina ganin za mu iya yadda mu raba auran da ba mu muka hada shi ba, ita ta ganshi ta ce tana son shi, ta kuma yadda za ta aure shi a kowanne hali, meye dalilinta na kashe auranta yanzu kuma ta hannun mu, Aisha ki kula wadan nan sune kadai ‘ya’yan mu, barin .rayuwarsu ta tagayyara ko kuma goya musu baya akan kowanne sakarci kamar ‘ lalata rayuwarsu ce.” Maganganunsa suka sanya jikin Haj. Aisha yin sanyi, tabbas gaskiya ya fada, amman ita a Kasan ranta tana ganin idan har aka matsawa Hasna ta koma komai zai iya faruwaSai dai bata da zabi bayan isar da sakon mijin na ta ta mike tsam kawai tabar ‘ falon. AIh. Sammani yayi shiru cikin damuwa, wato dukwanda Allah ya baiwa ‘ya’ya mata yana cikin jarrabawa ko mai girman su kuwa. Lokacin da Haj. Aisha ta gayawa Hasna “saqon mahaifinta ta girgiza kwarai da gaske, har ta kasa cewa komai saboda shock din da ……………….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button