ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣6⃣

Tana fadin ka fita na tsAneka ganin tsayuwar tasa zata iyar haifar da matsala yasa ya fita da sauri ta bishi yana bita ta kulle kofar gamida sa mata key ta jingina jikin bango tana ci gaba da kuka Ta tani abdul batason ko ganinshi amman t yaya zata iya gaym dunia abinda ta kama mijinta yanayi wazai yarda da ita wazai qarya tata sannan yaya makamar danta zai kasance idan yaji waye mahaifinsa wannan shine yafi damunta sannan yaya mahaifanta zasu dauki wannan wannan babban abin kunyan Ta qr fashewa da kuka gamida fadin aabdul ka cuceni. Kuka takeyi mai ciwo da taba xuciya. Ta qara kwanciya bisa gadonta kamar qaramar yarinya. A ranta ji take dama batasan abdul ba dama bata taba gaaninsaba mai yasanyama ta nace akan saita aureshi shin maiya sanya bata haqura ta auri abba ba shi zina kawai yakeyi amman abdul lwadi yakeyi nan ta qara fashewa da kuka A bangaren abdul yai tsaye a falo cikin tsananin damuwa akn abind ke faruwa har lokacin hannunsa yana dafe da goshinsa saida yaga jini n qoqarin wanke masa fuska sannan ya nufi first aid box dinsa domin yima kansa dressing allah ya sanya ciwon bamai girma bane ya koma ya zauna akan kujera yana naazarin halin daya bar hasna a ciki saiya miqe da sauri ya kunna karatun alqur ani ya karade gidan a ganinsa hakanne zai sanya dukkan saidanun dake kanta su sauka Ya qaraa komawa ya zauna akan kujera ya tsare kofar dakin nata da kallo kamar yana zton zata fito da gudune saiya juya ya kalli dakin mai aikinsu yaji kamar ya shiga ya tsheta ya tambayeta ko tsan wani abu game da matarsa amman sai zuciyarsa ta kwabesa dayin hakan Tun yana zaune hardai ya kishin gida akan kujerar barci barawo ya silalo ya saceshi a wannan lokacin Karatun Alqur,anin kuwa kwana yai yanayi A bangaren hasna kunna karatun da abdul yayi ya qaraa bata mamaki Tace da haka yake yaudarar mutane bayan ya kasance mugu azzalumi mai aikata sabon Allah Amman saiya dinga abu irin na mutane masu gskia byan ya kasance kungurmin mai aikata laifi har bacci ya dauketa itama tana ci gaba da sauraron karatun daya kunna Lol……………….

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣7⃣

Kiran sallar subar farko shiya tayar da abdul daga nannauyan barcin da yake Ya tashi a firgice kasancewar baaiyi addu.a ba kafin ya kwantan Domin tino abinda ya faru yaa kalli Kofar dakin hasna har lokacin a kulle yake. Ya mike ya nufi kofar dakin ya murda sai yaji a kulle take sai ya kada kai yai hanyar dakinsa kawai Yai alwala gamidaa nafila yaai zaune a wajen shiru yana lazimi cikin zuciyarsa abubuwa biyune suka tsaya masa halin da suka rabu da murtala jiya sai kuma halin da matarsa ke ciki sai da Yaji kiran asalatu sannan ya miqe ya nufi masallaci Har qarfe bakwai da rabi naa safe hasna bata fitoba dud da yasan bata daa aikin safe kasancewar tayi na dare jia amman aa qa,idarta yasan tana tashi da wuri a irin wannan lokacin domin tanazar masa breakfast. Saidai har takws bata fitoba ya tsaya kyam yana kallon agogo. Baison ya bata qa.idr ikinsa domin yaanada lecture qarfe takwas da rabi Ya isa kofar dakin nata ya tsaya shiru tsawon lokaci. Saiya fara buga qofar a hankali yana kiran sunanta Tan kwance akn gdo tana jinsa amman taqi amsawa Saima taakaici da baqinciki dake qara shigarta tasa hannu ta toshe kunnent domin jin muryarsa. Take kamar na wani tsohon makiqinta Nasan kinajina hasna ki taimaka ki budemin don allah ki gayamin abinda ya sameki yauce rana ta farko tun bayan aurenmu da zan fita aiki cikin damuwa Don allah ki bude naga halin da kike ciki Harya qaraci magiyarsa bata ko daga kai ta kalli kobar ba Ya kalli agogon hnnunsa ya qara cinye minti goma gabansa ya fadi don bzai iya bita ba tare da yasan halinda hasna ke ciki ba sai dibara ta fado masa ta lekawa ta windon dakin nata kai tsaye ya nufi windon Ya koyi sa,a a dage yake saiya hangota a tsakiyar gado ta nannade gamida toshe kunnuwanta tamkar maaaijin sanyi Hakan ya qar tabbataar masa da lallai wani abu ya sami mataarsa naa tabuwaar tinani yayi dan jim yana kallonta sai yaga dacewar ya fita kawai ya tafi yaje ya dawo Allah ma ya sanya lecture din safe kawai ke gareshi………………

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣8⃣

kawai yake da ita don haKa ya fice cikin hanzari yana duba agogon hannunsa zhasna tanajin fitarsa ta miqe zaune tayi shiru akan gado abindata gama yanke shawara a cikin ranta tun daren jia shine barin gidan saidai idan tabar gidan ina zataje gurinwa zata bata manta da gargadin da mahaifinta yai mata sanda ya amincewa aurenta ba wannan shine abumda ke damunta tun daren jiya batason ta tuna yaddah taga mijinta da murtala batason ko tina abin hawaye ya zubo mata ta hade kai da gwiwa waye zata iya gayama wannan lbrn waye zai taimaka mata wannan shine halin data kasance har tsakiyar rana ta kasa cin abinci ta kasa yin wanka ta kasayin kowai harta mai aikinta saidata lura yau akwai abinda ke damun uwar dakinta………………

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣9⃣

tace hatta mai aikinta saida ta kula yau akwai abinda ke damun uwar dakin tata domin ko falo ta kasa fita abinda ya kamata tayi shine abinda take saqawa cikin ranta tun safe tanason sanar da yar uwarta abinda ya faru amman tana tsoron abinda zai biyo baya wajen qarfe daya da mintina abdull ya iso gida taji qarar shigowar motarsa a harabar cikin gidan don haka ta qara shigewa daki ta kulle kanta ya shigo gidan a sukwane cikin damuwa baida kwanciyar hankali domin duk wanda ke tare dashi a yau saida ya fuskanci da akwai matsala a tattare dashi yaci karo da zulai yarinyace yar shekara sha uku mai masu aiki a falo kan kujera ta samu sakewa yarinyar sosai a gidan domin ta hadu da iyayen gida na kwarai dukda abu mawuyacine ka ganta kai tsaye a falon gidan a koda yaushe tana can bangarenta tana ganin shigowar abdul ta miqe da sauri cikin tsoron abinda zai biyo baya tana gaisheshi amman sam baijiba hankalinsa na kan kofar dakin hasna saiya fuskanci a kulle yake baison yarinyar ta fuskanci komai amman kuma bashi da zabi dole ya tambayeta halin da matarsa ta kasance zulai tai hanyar fita cikin hanzari amman muryar dakta ya tsaidata ya karisa kusa da ita yana qare mata kallo irin na nazari sannan ya fara tambayarta hasna taci abinci kuwa?ya kureta da ido domin baiso tai masa karya cikin sauri yarinyar ta girgiza kai tace a,a uncle batayi girkiba don daman batason ina mata girki da kanta takeyi to naga bata shiga kichin ba don ko faloma bata fitoba ina tsammanin bata da lafiya ne harda abinda bai tambayaba ta bashi amsa don haka ya gamsu basai ya qara tambayarta komai ba ya bata umarnin tafiya cikin sauri tabar falon bayan fitarta ya tsaya gamida kurama kofar dakin hasna ido cikin damuwa yanajin yinwa domin tun safe babu abinda ya sanya a cikinsa bayan ruwan tea amman halin da hasna ke ciki yafi komai tsaya masa cikin ransa domin yinwa bata damesaba yayima kansa alqawarin yin dukkan yaddah zai iya domin shiga cikin dakin nata idan har bata bude masa kofar ba domin ya tabbatarda matarsa ta samu matsala a kwakwalwarta domin hasna bata taba yarda da ta wuni batare data gansa ba kallon fuskokin juna kadai yakan sanyaya musu zukatansu ya nufi kofar ya fara bugawa har e wannan lokacin tana nade a tsakiyar kan gadonta bataima kanta komaiba babu wanka bacin abinci bubu abinda taima kanta shiru tai babu amsa ba magana ya jima yana buga kofar har har haqurinsa ya soma qarewa wayarsa dake cikin aljihunsane ta fara ruri alamun kiransa ake yana dubawa yaga kiran murtala ne yayi dan murmushin jin dadi yasan murtala mutum ne mai saurin fushi amman kuma baida wahalar saukowa a yaddah suka rabu jiya baiyi tsammanin zai iya kiransa a cikin wannan lokacinba har ya huce kenan ya kalli kofar dakin nata sannan ya daga wayar cikin sauri hello yaya akayine abokina ina cikin matsala ina neman taimakonka daga can wajen murtala yadan razana yana fadin meya faru abokina ? cikin damuwa yaci gaba dayi masa bayani hasanace tayi gamo ina tsammanin dai mutanen boyene suka kamata don tun daren jiya na kasa gano kanta duk ta birkice min hasna ta tashi da sauri tana kallon kofar dakin da jiyo muryar mijinta a yanxu ta tsani ko sunan murtala taji an ambata amman wai dashi mijinta ke magana koda yake shimadin kamar yaddah na tsani mutuwata haka na tsaneshi da dukkan wani abu da ya shafeshi ta sanya hannu ta toshe kunnuwanta tana kada kai dakta yaci gaba da wayarsa cikin damuwar halin da matarsa ke ciki ya kashe wayar tasa da alqawarin haduwarsu da abokin na sa wanda shine kalma mafi muni da hasna ta kara saurara daga bakinsa a yau sannan yaci gaba da bugun kofar hasna wlh idan baki bude kofarnan ba zanje na sanar dasu mommy halin da kike ciki don allah ki bude mini kofar bakici komaiba bakiyi komaiba amman ki kulle kanki please ki bude don allah kamar bada ita yake maganar ba domin zuciyarta takai qarshe wajen damuwa don haka ya fara kwada karfinsa wajen ganin ya bude kofar da kansa tana zaune tsakiyar gado tana jiran abinda zai biyo baya koface mai tsada da daraja amman dakta bai damu da hakanba saida ya budeta da qarfinsa ganin yana gab da shigowa dakin yasa tai hanzarin tashi ta fada toilet ta kara kulle kanta domin taima kanta alqawarin bazata sake ganinsaba har abada yanxuma tana zaune a cikin gidansane domin nemarma kanta mafita akan abindaya kamata ace tayi. …. I fall, I rise, I make mistakes, I live, I learn, I’ve been hurt but I’m alive. I’m human, I’m not perfect but I’m thankful……………….

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button