ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
2⃣8⃣

tabbas gWara ace ta auri mazinaci da ace dan luwadi ta aura irin Abduljabar. Kamar daga sama ta ji an turo dakin an shigo, ta waiga cikin mamakin ganin wanda ya banko mata Kofa sai ta yi ido hudu‘ da Abdul, tsanar sa ta kara shigarta ta doka masa tsawa. “Me ya kawo ka dakina, na‘ce ka fitar mini daga daki, ka fita daga rayuwata! “Bazan fita daga rayuwar ki ba Hasna, bazan bar ki ki aikata abin da ba shi da kyau cikin addinin ki ba, na fahimci zuciyar ki ta qekashe ba ki tsoran Allah! Mamaki ya cikata, wannan shine mai bunu a gindi na shirin kai gudumawar gobara, cikin karfin hali ta fara bashi amsa. “Au nice wacce ba na tsoran Allah Abdul? Har kana da Karfin gwiwar kirana da wannan kalaman yanzu? Cikin Kwarin gwiwa yace “Haka ne, bari na gaya miki dukkan abin da kike aikatawa na sani, kina kokarin zubar mini da ciki bisa wasu banzayen hujjojin ki da ban sani ba, to bari na gaya miki, wallahi duk son da na ke miki zan iya daukar mataki akan ke ta mini haddina, idan kin shirya gaya mini abin da ke ranki ina maraba da shi, idan kuma baki shirya ba ki yi ta zama da abin ki, amman dai na Kara gaya miki wallahi bazan lamunci zubar da ciki ba! Yanda yake maganarr cikin masifa da hakikancewa shine abin da ke bata matukar mamaki har ta kasa cewa komai ta barshi yana ta zubar sa, sai dai ganin yana kokarin zakewa bisa abin da ta ke ganin borin kunya ne, ya sanya ta fara kokarin taka masa birki ta hanyar magana itama cikin tsawa. “Kai Malam dakata, ya kamata ka tsaya iyakacin matsayinka, kada garin kokarin ganin ka raya kanka da irin son kan ka Barowa rayuwarka matsala. .. Bai bari ta qarasa bayanin ba ya kuma katseta “Matsala ai kece matsalata, kece ke kokarin zame mini matsala, domin tsahon kwanaki biyu ban sami nutsuwa ba, ban huta ba, amman hakan ba yana nufin na sakar miki komai ba, ina son ki amman soyayyar ki ba zata rufe mini ido har na yadda ki yi abin da zai shafi mutuncina ba.” Takaici ya sanya Hasna fashewa da dariya, wai Abdul ke kiran kansa da mai mutunci, yanayin dariyar da ta ke ya sanya shakku cikin ransa, wanda ya sanya shi tsayawa cak yana kallonta, anya kuwa matarsa ba ta sami tabin hankalin da gaske ba, ya kasa furta komai sai kallo kawai da yake mata harta yi dariyar ta gama sannan ta kalleshi tana magana. “Akwai wani abu tattare da kai wanda ya qarar da mutuncin ka tun tini, tun kafin ni na karar maka da shi, amman sannu a hankali zan sanar da kai wannan abin, sai dai ina son ka sani kai ne mutum na farko da na taba mu’amala da shi da ya kasance mai tsananin saBawa Allah, sannan kai ne mutumin da na taBa dana sanin sani ciki rayuwata, na gaya maka na tsaneka bana Kaunar ka har abada.” Kalaman suka dinga dukan ransa kamar zubar ruwan dalma, amman sanyin da jikinsa yayi ya sanya shi kasa furta komai, tabbas akwai wani abu da Hasna ta ji game da shi, k0 wani ya gaya mata mummunan labari akansa, anya kuwa Alh. Shazali bai shigo cikin sabgar iyalinsa ba, kamar yanda yake sanar da shi hakan tun tini cewar idan bai yadda sun ci gaba da mu’amal irin ta bayaba sai ya Bata masa sunansa, wannan tinanin ne ya sanya shi Yin shuru cikin fargaba. Ganin bashi da abin fada ya sanya tabar gurin cikin sauri ta nufi bandaki, d0min zuwa yanzu ta fadi wani abu da zai taka masa burki bisa abin da ta gani da ldonta, ba ta san ta yanda za ta sanar da shi ba ne, domin tana jin kamar duk sanda ta zata fadi abin da bakinta zata iya hadiyar zuciyarta ta mutu. Abdul ya bita da kallo a fili da ransa yana fadin Innalilahi wa’inna ilaihi raji’un. Bai taBa jin faduwar gaba da tashin hankali kamar irin na yau ba tunda yake cikin rayuwarsa, yana jin kamar ya dafa hannuwansa duka biyu akansa yayi ta kwarzaba ihu, to me ya rage masa ne yanzu, ya gama gano komai, abin da kawai ya rage Hasna ta fada da bakinta. Ya zauna jabar a gefen gado kamar mai tsohon ciki, kukan Hasna ya fara dawo da shi duniyar sa, domin ya shige duniyar tinani, ya dinga jiyo kukan ta, babu abin kukan ke bayyana masa sai irin tsananin dana sani da damuwa cikin muryarta, waye ya sanar da Hasna mugun labari game shi, shine abin da yake buKatar sani a yanzu. Me ya sanya ba a bari ya gaya mata da bakin sa ba, jin ba ta da niyyar dai na kukan ya sanya ya mike yabar dakin cikin sauri, bai Kaunar zaman gidan, komai na gidan ma baya bukatar kallo, don haka ya fice kai tsaye ya shige motarsa babu wanka balle gyaran jiki, kai tsaye Makarantarsu ya nufa, ya shige ofis din sa ya kullo Kofa, ya rasa me ya kamata yayi, abin da ya dace yanzu gareshi shine ya shiga aji ya bayar da lacture ga dalibansa, amman ba zai iya ba, ya zauna akan kujera ya hada kai da tebur kawai. Yana ta jin ana buga kofarsa daga waje, amma bai mayar da hankali gurin sanin su wayeke bugawar ba, domin ya san ba zai bude ba, bai san lokacin da ya kwashe a hakan ba. Acan gida Hasna tana kwance akan gado ta dinga jiyo sallama daga falonta, hankalinta ya tashi domin ta gane muryar Hajiyar Abdul ce, bata son k0 kallon wani abu da ya shafi Abdul, amman ba zata iya wulakanta tsohuwar nan ba, don tana jinta tarnkar mahaifiyarta. A falon dai ,ta jiyo muryar Sadik yana gwaranci, gabanta ya fadi domin jiyo muryar yaron, kafin ta yanke shawarar abin tafiyarsa dago-dago. Ta tsaya tana kallonsa yana surutai yana nufarta cikin farin ciki har yana Kokarin faduwa, a baya idan ta ji muryarsa takan gigice ta nufeshi ta daukeshi ta rungumeshi, amman yanzu sai ta tsinci kanta ga kasa hakan, domin kamanin Abdul ne ke bayyana akan yaronta, har ya isa ya rike rigarta yana ci gaba da gwaranci ba ta motsaba, ya kwantar da kansa jikin kafarta yana ci gaba da gwaranci. Sai zuciyarta ta karye ta daga yaron gami da rungumeshi ta fashe da kuka, ba ta taBa zaton ko kallon Sadik za ta iya yi ba, ta dauka ko a hanya ta ganshi za ta wuce ta barshi, amman ta kasa yanzu, soyayyar uwa da da ba zata barta ta aikata hakan ba. yaron bai san me take yi ba, dariyarsa kawai yake yi cikin murna ya na ci gaba da gwalan-gwalantinsa. Cikin ranta tana fadin “Na cuceka Sadik, na haifeka a gidan da bai da ce ba, kawo ka zuri’ar da bai kamata ba, ka yafe mini.” Muryar Hajiyar Abdul ta dinga dukan dodon kunnenta tana fadin “K0 gidan babu kowa ne? Zulai kina ina ne? Sai ta kasa jurewa, ta nufi hanyar fita cikin sauri ta tadda Hajiya a tsaye cikin damuwa, tana fita Hajiya ta bita da kallo baki bude ganin yanayin da ta ke. “Sannu da zuwa hajiya.” Hajiyar Abdul ta na kallon Hasna ta ke amsawa cikin sakin fuska da Kokarin gano halin da take ciki tana fadin “Yauwa Hasna yaya jiki, gidan shuru? Hasna ta amsa cikin sakin fuska gami da fadin “Eh na kwanta ne, ita kuma Zulai na aiketa, bari na kawo miki lemo.” Hajiya da ta fara Kokarin zama ta daga mata hannu tana fadin “A’a yi zaman ki Hasna a Koshe na ke.” Hasna ta zauna tana rungume da Sadik Wanda har lokacin bai bar gwarancin da ya ke yi ba, tana dan biye masa amman cikin jin nauyin hajiyar. “Abduljabar ne ya sanarda ni ba ki da lafiya, shine nace bari na shigo na ga jikin na ki, amman dai ba kya cin abinci k0? Domin duk kin lalace gaba daya Hasna ta sunkuyar da kai ba ta ce komai ba, ba ta da abin fada din, Hajiyan ta ci gaba da yi mata magana cikin kulawa, tana jin dadin irin yanda Hajiyar Abdul ta damu da ita a baya, hakan ya sanya take alfaharin kasancewarta sirikarta, amman a yau sai ta tsinci kanta a jin maganarta kamar busar sarewa, tana tausayin ta akan halin dan ta, da ta san irin rayuwar da dan ta ke yi da ta yi ta kuka, gata mace ta gari mai kirki, amman dan ta’ watsatstse, dama za ta iya da ta gaya mata waye dan ta, watakila ta dauki mataki akansa, amman ba za ta iya ba. Da wuya Hajiyar Abdul idan ta zo gidan ta dade, domin mace ce dattijuwa ba ta zuwa gidan ma sai da kwakkwaran dalili,-don haka yau din ma ba ta jima ba ta fara qoqarin tafiya, ta miqa mata jakar ledar ta zo da ita mai cike da kayayyakin marmari tana fadin “Hasna ga wannan kya dan taba, ni zan wuce, Allah ya Kara lafiya” Hasna ta amsa cikin qokarin kaqaqaro murmushi tana godiya, Hajiyan Abdul ta mike tsaye, tana tashi sadik ya mike shima cikin rigima yabar wasan da yake yi, Hajiya ta bishi da kallo tana dariya. “Au ba zaka zauna gurin mama ba? Sadik ya noqe kafada alamar a’a ya nufeta, ta kama shi tana dariya ta dauke shi, Hasna ta bita da kallo cikin murmushi kawai, koda hajiyar za ta bar mata dan ba za ta amince ba, domin zai iya hanata aiwatar da abin da ta yi niyyar aiwatatwa. Hajiyan Abdul ta kula akwai wani abu da yake damun Hasnan bayan matsalar ciki, amman da yake wayayyiyar macece ya sanya ba ta matsa da tambaya ba, tasan zaman aure dole akwai samun saBani. Ta yi hanyar fita da jikanta a hannunta, Hasna ta dan taka mata zuwa harabar gida. Direban hajiya na fita da ita cikin mota, Karima ta danno da hancin motar ta cikin gidan, abin da ya baiwa Hasna damar juyawa dai-dai lokacin da take koKarin komawa cikin gidan, ganin sabuwar motar da bata taBa gani ba ya sanyata tsayawa domin tabbatar da wanda ya shigo gidan. Kwarai da gaske motar ta bata sha’awa, za ta iya cewa ma ba ta taBa ganin irin ta ba, Fitowar Karima daga cikin motar ya bata mamaki gami da sanya gabanta faduwa, domin tana ganinta mijinta ne kawai ya fado mata, amman sai ta dake kawai. Karima ta nufeta cikin fara’a tana sanye da shigar alfarma ta zuba gwalagwalai wuya da hannu, duk wanda ya kalli Karima yasan tana tsananin jin dadin gidan mijinta, Murtala yana da kudi yana kuma sakar mata, macece mai fantamawa iyakacin rayuwarta, duk da unguwa daya suke zaune amma yanayin ginin gidan Murtala ya fi na su, balle motocin da suke hawa, k0 da yake ba ta taBa damuwa da kasancewar hakan ba, don tasan mijinta ma’aikacin gwamnati ne yayin da da Murtala ya kasance shararran dan kasuwa mai juya naira, kuma wanda ya fito daga babban gida. Karima ta Karasa suka yiwa juna murmushi, na fuskar Hasna dai Karfin hali ne sannan suka Karasa cikin gidan Karima na zolayarta. Karima mace ce mai matukar mutunci da kirki don haka sun shaku, k0 da tana cikin damuwa ba za ta iya wulakantata ba, don haka ta biye mata suka isa falo, suna shiga Zulai ta dawo daga aiken da Ta yi mata ta .sanya ta kawo mata abubuwan motsa baki. Karima ta kalleta sama da kasa tana dan murmushi tace “Kawata kin ga yanda kika koma kuwa, gabadaya kamanninin ki da yanayin ki ya sauya, anya baki takurawa kan ki da yawaba? Hasna ta yi yake tana fadin “Babu komai, ina jin dadin kasancewata a haka, koda bana cikin farin ciki ina cikin nutsuwata, ki sha lemo mana.” Ta sauya hirar ta hanyar nuna mata abubwaun da Zulai ta ajiye mata a gabanta Karima ta ‘dauki lemo ta cire masa kai kasancewarsa irin na kwali sannan ta tsiyaya ta Kurba ta ajiye, ta dubi Hasna wacce ta jingina jikin kujera. “Hasna ban ji dadin abin da ki ke shirin aikatawa ba, duk laifin da mijin ki yayi miki bai kamata ya shafi abin da Allah ya baki ba, kefa macece mai ilimi da wayewa, yaya ki ke shirin aikata irin wannan aiki na jahilai? . Ran Hasna ya kara baci mai ya sanya mutumin nan yake mata haka, sai Kara turo mata mutane yake yi, ita ya kamata ace takarar shi, amman ba ta yi ba sai shi yake ta yamadidi da ita da rayuwarta, haushi ya sanya ta kasa cewa komai. Karima ta ci gaba da magana “Kiyi hakuri Hasna Abdul yana son ki, bai ma taBa son wata mace bayan keba, halin da kike ciki ya sanya shi zama tamkar qaramin mahaukaci, jiya da na ganshi wallahi sai da na tsorata, don Allah ki kwantar da hankalin ki, na san dai ba zai wuce maganar kishi ba, amman ki sanya a ran ki Abdul ke daya ya taBa so, kuma ke zai ci gaba da so har abada.” Yanda Karima ke magana cike da Kwarin gwiwa sai ya fara bata tausayi, domin ta kula bata san halin da auranta da mijinta ke ciki ba, ba ta san waye mijin ta ba da itama hakan za ta yi, amman sai ta kasa cewa komai, sai da ta lura da Kariman bata da niyyar tsayawa a nasihar tata sannan ta fara yin magana. “Anty Karima kiyi hakuri ina ganin mutuncin ki kwarai da gaske shi ya sanya na tsaya na saurare ki. amman ina gaya miki wata magana da zaki gayawa Abdul ka da ya kara zuwa miki da magana ta, bana son shi, bazan kara son saba, na tsane shi, sannan na yi nadamar auransa, ayau na gwammace da ma dan’uwana na aura wanda soyayyar da ta rufe mini ido ta Abdul ta sanya na barshi cikin damuwa da ciwon zuciya. . .” Sai ta fashe da kuka amman tana ci gaba da magana, Karima tana kallon ta cikin matukar mamaki, tafi kowa sanin irin son da Hasna ke yiwa Abdul, domin tasan irin halin da ta shiga lokacin da aka ce ba za su auri juna ba, don haka jin maganganun Hasna din a yanzu ya tayar mata da hankali kwarai da gaske. Hasna ta ci gaba da magana tana kuka “Koda mun rage mu kadai ne a wannan duniya aure tsakanina da Abdul ya haramta, bazan iya fadawa kowa abin da yayi mini ba, amman bazan kara kallon sa a matsayin miji ba, ki taimaka ki rokeshi ya sake ni don Allah.. Karima ta mike da sauri ta matsa kusu da Hasna ta zauna ta rungumota cikin rarrashi tana magana “Yi hakuri Hasna, don Allah ki kwantar da hankalin ki, tubbas na san damuwa da fishi ne ya sanya ki fadin komai, amman na tabbatar a duniyar nan ba za ki qara samun miji kamar Abdul ba, yana son ki yana kula da ke, don Allah ki yafe masa abin da ya aikata miki, kuma nasan ke ma kina son shi. . . Hasna ta zame jikinta da sauri tana fadin “Waye ya gaya miki? Na gaya miki a yanzu ba na son shi na tsane shi, wallahi da za a halatta mini kisan mutum daya yanzu a duniya Abdul zan kashe, domin hakan ne kawai zai wanke mini zuciyata bisa cin amanar da yayi mini.” Karima ta ci gaba da kallonta cikin tsoro kamar taga dodo, amman maganarta ta Karshe ta daki ranta har ta haddasa mata kokwanto cikin zuciyarta. Hasna ta ci gaba da magana “Don Allah ki gaya masa ya sake ni…kar ya Kara kallona. . .kar ya Kara zuwa inda na ke Jin abin da Karima ke fada ya sanyata tsayawa da kukan ta tana kallonta. “Bai kamata abin da Abdul ya aikata ya sanya ki hauka haka ba Hasna, ki tina kina da sauran damammaki, sannan kina son mijin ki, shin soyayyar sa ashe ba zata sanya ki rufa masa asiri ba? Hasna ta yi murmsuhi cikin dacin rai tana fadin “Baki san me Abdul ya aikata ba abin da ya aikata ba irin shine ake yafewa mutum ba, ba kuma irin shine ake haqura a zauna da aure ba, da wani laifin Abdul ya aikata zan iya kawar da kai na zauna da shi, amman wannan laifi ba zai yafu ba, kamar yanda na fada miki bazan iya gayawa kowa ba, da zan iya da na gaya miki, wanda idan kika ji ke kan ki zaki yadda na rabu da shi, rabuwa kuma ta har abada babu yafiya.” Karima ta yi murmushi tana ci gaba da kallon ta tace “Hasna k0 kin gaya mini k0 baki gaya mini ba na san abin da Abdul ya yi miki domin kalaman ki sun sanya na fahimci komai, amman idan ki ka yi haquri komai zai wuce. .. “Komai ba zai wuce ba, kuma ba ki san k0 menene ba! Hasna ta Kara mayar mata da amsa cikin karaji. Karima k0 dar babu a jikinta tana kallon Hasna cikin ido ta ci gaba da magana “Na sani, wata Kila kin kama Abdul yana luwadi da wani ne, kuma wanin ma nasan ba zai wuce Murtala ba ko! Yanayin bugun zuciyar Hasna ya , sauya lokaci guda ta dinga kallon Karima kamar taga wata sabuwar halitta, mamakin abin da ta fada ya baibayeta’ amman bai ‘hanata nufar ta da sauri jikinta har rawa yake ta zauna a kusa da ita , ta dafa cinyarta cikin rawar murya tana fadin “Anti Karima kin san Murtala yana luwadi? daman Kin san yana neman maza amman HMMMMM LOL
Matan………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button