ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
1⃣4⃣

Da kyar ta ‘ iya .tuka kanta ta isa gidansu, ta tadda jama’a cike a gidan don haka bandaki kawai ta shige ta rufo kanta ta yi’ kukanta ta more; An‘yi kamu kamar yadda aka saba da yamma an sha shagali da kade-kade, amma babu farin ciki k0 daya a kan fuskar Hasna, hasalima haushin dukkan wanda ya zo bikin ta ke ji. Da daddarc suna cikin dakinsu ana ta hira ana shcwa, ’yammata da ‘yan uwansu wadanda suka kasance sa’anninsu ita kam zuciyarta suya ta kc yi, sai kawai ta dauki mukullin mota ta fice babu’wanda ya ganta. Ta yi ta zagaya garin ba ta san ina za ta je ba, har zuwa sanda ta samu gefen hanya ta yi fakin ta hade kai da sitiyari tana kuka. Kamar an ce ta daga kanta, sai wata mota ta wuce ta da gudu, ta bi motar da kallo cikin hasken f’ltilar da’yahaske titin, sai ta ga lambobin motocin Abba ne a jiki, ta yi tsam tana tunanin ina Abba zaije kuma yanzu? Sai ta hango motar ta tsaya bakin wani qaton gurin‘ shakatawa daga can nesa da ita,‘ sai ta ji zuciyarta tana bata umarnin ta je ta ga me zai yi? Ta kunna motarta ta nufi gurin, daidai 10kacin da ya fito yana rungume da Ruma suka nufi gurin. Ta waro ido da tsoro da bakin ciki, wannan shi ne ake so ta aura‘wai, namiji mai bin mata? Tana nan tana sakawa da kwancewa ta ga sun fito daga gurin dauke da kwalaye da alama na giya ne sun sanya cikin mota suka shi‘ga suka tada motar suka wuce, ta kunna motarta ta bi su a hankali-. Abin da ya ‘ba ta tsoro da takaici shi ne gidansu inda za su tare ita da Abba suka shiga, gidan da aka yi mata jeran komai satin da ya wuce, ashe nan ya ke kai matan banza tun ba ta tare ba? Har ‘ suka shiga gidan Tana k‘all0nsu da bakin ciki da takaici. da kyar ta iya komawa gida tana kukan zuciya,,amma dole zata sanar da Mominta. A gidan’ma anataci gaba da shiryc- shirycn biki ‘Hasna‘ta shigo ta nufl gurin mahaifiyarta da ke zaune‘ta rada mata wata magana, suka mike .suka shige’ dakinta. Akwai wata ~ab0kiyar wasan su Alhaji Sammani. wacce ‘ta kasancc amintacciyar Hajiya Aimana ce. ta tashi ta bi su don daman kusan zaman tsurku ta keyi cikin gidan ta lcbe Hasna tana kuka ta ce. “Momy kin ,san abin ‘da Abba keyi kuwa‘.’ Har yau fabai bar bariki ba…,” Hajiya Aisha ta harare ta, tace. “Uban waye‘ya gaya mi‘ki‘.’ K0 ma me ye Iokaci ya kurc Hasna‘ don Allah ki yi hakuri ki kau da kanki daga wannan abin…’.‘ Cikin kuka ta Ce, ‘Haba Mome, sai na auri ‘dan iska mai kai. mini mata’ gidana…” “Gidanki ‘kuma a ina?” Hajiya Aisha ta katseta ‘ Ta kwaShe‘ labarin dukkan’abin da, ya faru ta sanar da ita, hankalin hajiya Aisha ya yi mugun tashi. Ta kada kai tace Shi .ke nan jcki;kWantar da «hankalinki ina zuwa”. K0 da ta fita daga nangurin mahaifin su Hasnan ta nufa; An yi sa‘a babu kowa sai shi daya cikin falon nashi. Ya kalleta‘da mamakin yadda ranta kcbacc ya ce “Ya ya dai. lafiya‘?” Ta sami guri ta zauna ta Ce “Da sauqi dai‘ Alhaji”; Ta kwaShc dukkan abin da ya faru ta sanar da shi, ta dora da cewar‘.‘ ‘ “Alhaji na’gaya maka tun farko Abba bai kamaCi auran. yarinyar nan ba ka’ dage, ka runtse idonka. Yanzu wannan Shi ne mijin?” ‘ Jikin Alhaji Sammani ya yi sanyi, amma babu yadda ya iya bayan rarra’shi da ban haquri, abin da ya kular da” Hajiya AiSha – kc nan’ta fiCE daga falon a fusace. “Allah ya sani zuwa wannan lokacin aUran ya flt’a daga ranshi gabad‘aya, don‘kullum ‘addu’a ya kc yi, amma bai jin ‘abin na zama ‘a ranSa ba ya dinga kai Wa’ da’ komowa da baKin ciki,‘ba;’zai iya yin abin da zai saba wa dan uwansa ba, da wani ne wallahi a yau zai ce an fasa auran nan. ‘ ‘** “** ** Abba bai taba tunanin komai ba. don yana cikin farin ciki da nishad‘l sai dai ya boye wa Ruma zancen auransa don tana bala’in sonsa, cewa ya,yi,sab0n gidansa ne kawai, don Bangarenshi ya’kai ta.. Suna ta shaye-shayensu aka banko Kofa aka ‘shigo, mahaifinshi neda mahaifiyarshi don‘bayan. Mairo munafukar Hajiya Aiména ta ji komai ta je ta sanar .da ita, wannan abin ya: yi Wa, Hajiya Aimana dadi, ta kira Alhaji ‘tacc ya zo ya- gani da idonshi. Suna Lafe a mota tana- kara yi masa famfoda cewar,‘maganin kar a yi to kar a ‘soma. ida’n har baso ka kc abba ya watsa zumuncinka da dan uwankaba a, haka suka isa’gidan Abban .Da yake ‘maigadi yasan Alhaji y’a bude ‘musu *gidan’, ~kai ~_tsaye Suka” wuce Bangaren Abba, Kofar a bude.~.take.suka‘shiga da sauri. Abba da Ruma ba su ankara ba suna soyayyar su Alhaji ya shigo’.”~Abba ya mike da sauri da rawar jiki. Abba ya ji kamarkasa ta tsagc ya shigc don kunya‘ da takaici, ita kuwa Ruma Wuqi—wuki ta yi cikin ranta tana ganin wannan mutumin ‘ya takura wa dansa ya hana shi sakewa‘ sam. Alhaji Auwal ya. ,gyada kai ya juya da *sauri, Hajiya. Aimana ta bi shi. ita ma da sauri. Bai ce mata uffan ba sai dai daga ‘yanayin tukinda ya ke yi ta .san yana cikin tsananin- damuwa da.tashin“hankali. Yana son Abba. yana son shiriyarsa, amma ba zai cutar da diyar dan uwansa ba, dole ya dauki mataki a kai. Ita kumaHajiya Aimana dadi ne fal a ranta da. farin ciki. Abba ya k0ma. ya zauna a kujera ya dafe kai yana’ huci yama rasa me zai yi, Ruma ta isa kusa da shi da kwarkwasa ta kama Shi tana fadin. “Darling ka manta da wannan tsohon..,” , Ya hankad‘c ta a fusace ya mike yana fadin. “Shcgiya. karuwar banza sake ni, kin ja min masifa daga yau babu ni babu kc. ki fita daga hanya ta”. ‘ ~ Ta bi shi da kallon mamaki, k0 ya yi hauka ne’.’ Amma sai ta kula damuwa cc kawai, don haka takara yunkurin lallashinsa amma ya birkice mata har da kai duka, yana fadin. “Na fa gaya miki ki fice min daga gida. ban son k0 Kara kallonki, don kin yaudare ni, kina gab da sanya-ni cikin bakin ciki”. Da dai ta ,ga abin nashi da gaskc ne yana nufin nakasata ta ‘suri jakarta da takalminta ta fice a guje, don zai iya halakata idan ta biyc masa tana mamakin irin halin da ya shiga bata san irin abin da ya ke ji ba sai ya kasa barin gidan ya zauna da damuw’a bai san abin da zai faru ba. ‘ Haka zuciyoyin kowa suka kwana cikin baqin ‘ciki da Bacin rai matuka. Sai karfc bakwai na safe Alhaji ‘AUWal ya ‘Isa gidan Kaninsa abin ya bai wa Alhaji Sammani mamaki, amma dai ya amshe shi hannu biyu suka gaisa. Bayan sun gama gaisawa Alhaji Auwal ya ce a kirawo masa Hasna da Hajiya Aisha, don a gabansu Za a yi komai. Alhaji Sammani ya dinga tambayar yayan nashi laflya, me ya faru’? Amma yace ya bari sai sun z0 kawai. Bayan sun iso sun zauna kowacce da mamakin abin’ da ya kawo Alhaji Auwal da sassafen nan, ya fara bayani kamar haka. “Sammani, kai dan uwana ne da muka flto ciki daya, :da na so mu kulla zumunci, sanda Abba ya. sanar da ni yana son Hasna ban nazo da maganar auranta don tsananin son da nakc yi masa ba, sai don ganin kamar ya sami shiriya, duk da na ji labarin akwai wanda yarinyar nan ta ke so. amma muka rufe idonmu muka yi nufin aura mata Abba. Sai dai daga jiya na gano Abba ba’ abokin auran HaSna bane, ha don ba zai gyaru ba. na san ni nc na rinka shagwaba Abba allah ya sani ina Kokarina a kan kada‘ya lalace, abin da ban sani ba ashe yalalace irin lalacewar da bazan iya tankwara shiba don haka maganar auranshi da .‘ Hasna yanzubabu ita…” ‘ , Wani irin farin ciki da’ jin dadi ya kama .Hasna har ya gaza Boyuwa ta daga ido. tana kallon iyayen. nata Duk da Alhaji ‘ Sammani ya dan ji dadin hakan, amma sai ya ke ganin kamar hukuncin da yayan nasa ya dauka kamar ya yi tsauri. Ya bude baki da zummar yin magana, Alhaji Auwal ya katse shi da sauri yana fadin Kadaka ce .komai wannan hukuncin ya tabbata, da ma mahaifiyarsa ta; jima tana mini kashcdi naqiji, amma ma godc wa Allah. daya sanya ba a daura ba. Za a daura auran Hasna jibi amma ba da Abbaba”. Ya kalli Hasna da sauri. “Ba ni lambar wannan yaron da kike so, ina son ganinshi yanzu‘ Kasancewar ta haddace lambar, a kanta ta fara karanto masa yana san yawa Gikin layinshi ha‘r ta‘ :gama. Ya kirawo lambar bugu daya’Abduljabbar ya dauka. Alhaji ya ce.‘ ‘ “Sunana *‘- ‘Alhaji Auwal, yayan Sammani mahaifin Hasna. Ina son ganinka yanzu a gidan su hasnan”; ‘ ’Mamaki ya cika Dr. Abduljabbar, har ya gaza Boyuwa ya ce. ‘Laflya dai k0 Alhaji?” Ya ce, “Lafiya kalau, ka dai zo kawai yanzu“. ‘ Ya. Katse wayar ya kalle’ su. “Zaku iya tafiya ku”; ‘Suka miqe kowacce da tsananin‘ mamaki d3 A murna, gwara ita Hajiya Aisha ta yi kokarin boyewa, amma Hasna kam ta gaza Boyewa. Ta isa dakinsu da‘gudu tana ihu da murna, Husna da sauran kawayensu suka dinga kallonta da ‘mamaki Kwarai da gaske. Ta kwashe labarin dukkan abin da ya faruta sanar da su, amma Husna ba ta yarda ba ta ce “Sister k0 dai mafarki ne ki ke yi?” Ta dalla mata harara tana fadin. “Bari idan ya iso gidan kya tabbalar da gaske na ke yi”. . Shi kanshi Dr. Abduljabbar da mamaki fal ya iso gidan, aka yi masa iso falon Alhaji Sammani. Yadda ya tadda su zaune a tare gabansa ya fadi ya durkusa cikin ladabi ya gaida su, suka nuna masa guri ya zauna. Bayan ya zauna Alhaji Auwal ya fara yi masa bayani. “Kamar yadda ka ji sunana a baya, nine yayan’ Alhaji Sammani da muke uwa daya uba daya, kuma da dana Hasna za ta aura amma a yau na ganokai ne ka f1 dacewa da ita, don haka nakeson ka gaya mini sunanka da asalinka”. _ Abduljabbar ya dinga jin abin kamar almara, amma dai k0 mafarki ne wannan ai mai dadi ne, don haka ya kamata ya ci gaba da bai wa mafarkin hadin kai. Ya ce, “Sunana Abduljabbar Falmata”. Mamaki ya kama su har Alhaji ya ce “What sunan mace na ji ka fada, kana’nufin ba ka da mahaifi ke nan?” Abdul ya girgiza kai yana fadin. “K0 daya, ina da mahaifi sai dai dawainiyar da mahaifiyata ta yi da ni ne ya sanya na ga ya f1 dacewa na yi amfani da sunanta a mazaunin na uba, amma idan har kun bukaci ganin dangin mahaiflna zan ‘ kawo muku su, k0 kuma na sanar da ku inda suke ku je ku yi bincike a kansu da ni kaina. ‘ Sannan sana’ata koyarwa a jami’ar Bayero ta Kano”; Alhaji Auwal ya gyada kai ya ce, “Kana ganin idan aka ce jibi ka kawo sadaki a dauna maka aure da Hasna za ka iya‘?” Abdul ya yi murmushi, ya~ ce, “Wannan shi ne abin da ya f1 komai sauqi da farin ciki a gare ni Alhaji, wallahi k0 yanzu a shiryc na ke da bayar da sadakin Hasna”. ‘ ” Alhaji Auwal ya gyada kai, ya ce. ‘Shi kc nan, ka je ka Ci gaba da shiri, jibi idan’ Allah ya kai mu ka iso da waliyyanka za ka auri Hasna. amma ka fara turo mana danginka a gobe sa’nnan za mu Kara yin bincike a kanka, shi ke nan za ka iya taf1ya”. Ya kasa motsawa daga inda ya ke, don bai son motsawa ya farka daga ‘wannan mafarki da ya ke yi mai tsananin dadi. Sai dai maganar da Alhaji Auwal ya kuma yi masa ce ta tabbatar masa ba mafarki yakc yi ba, inda ya ce “Ka gode wa Allah, daman can kai ne‘ mijin Hasna muke ta bulayinmu, Allah ya sanya alkhairi a ciki, ka tashi ka je abinka don ka fara shiri”. Ya mike da tsananin farin ciki yana godiya ga Allah a cikin zuciyarshi, ya nuf1 kofa. Alhaji Sammani ya kalli dan uwansa ya ce. ‘ “Amma Alhaji ya ka ke zaton Abba zai ji, wanne irin hali zai shiga‘.’” “Shi ya sani, ya shiga k0 ma mene nc babu ruwana. son da na nuna masa ne ya ke ba ni tukwicinsa ai. idan ya ga dama ya rungumi wuta k0 ya fada rijiya mai gaba dubu ba ni da damuwa”. Ya mike yana Ci gaba da fada. “Zan je na ci gaba da shiri, shi kuma kayansa a tattara masa abinsa ku ajiye, sanda ya shirya sai ya zo ya dauka, na wuce ni”. . Abin kamar shirin’ film, k0 almara cikin kwana daya maganar aure ta sauya daga nan: gidan su‘ Hasna Abdul kai tsaye gidan Murtala ya je ya sanar da shi dukkan abin da ya faru. Suka dinga tauna maganar da mamaki da farin ciki, sannan suka wuce‘ gurin mahaifiyar Abdul suka sanar da ita. Dadi ya cikata tace “Allah baya bacci, lallai ya amshi addu’ata, don kwana nake ina yin kuka da sanar masa, ‘yanzu maza ku garzaya can Kauye ku ksanar da dangi, ku taho da wasu. Yanzu ni ma zan sanar da abokan arziki da kawayena nan su z0 mu fara shiri, don ma Allah ya sanya na yi tanadin wannan lokacin, na jima ina ajiye abubuwan da zan yi amfani da su gurin aurenka, sai ga shi Allah ya nuna mini, Allah na gode maka da wannan baiwa”. Haka nan suka wuce can kauyen su Abdul. A gidan Alhaji Sammani biki ya sauya, Hasna sai waya ta. ke *yi wa mai gyaran jikinta a kan ta dawo ta ma manta da neman angon nata. Shi kam Abba’ bayan ya. gama takaicin da safe ya nufo gidansu, mahaifiyarshi kawai‘ya ta’rar ya zauna yana mata kuka da magiya, amma ta ce ba ruwanta ya bari mahaifinsa ya dawo ba ta sanmatakin da ya dauka ba sam. Suna nan zaune sai ga Alhaji Auwal ya shigo ransa a Bace, bai k0 kalli inda suke ba ya wuce yana shirin shiga sashinsa ne Hajiya Aimana ta yi masa magana. “Alhaji ga fa yaron nan ya z0 neman afuwa, ya ce wai ba zai kara ba”. Maganar iyakacinta a bakinta amma cikin ranta murna ta ke yi. domin Mairo ta sanar da ita dukkan abin da ya faru ta waya. Alhaji Auwal ya waigo a fisace ya cc. “Ai kuma sai dai ya bi wani‘ Sarkin, amma maganar auranshi da Hasna babu ita, don yanzu haka har mun gamamagana da yaron da ta ke so, ya kc sonta, dan mutumci ba irinka ba”. Abba ya dafe kai da rudu ya ce. “Alhaji wai kana nufin an fasa aurena da Hasna kenan?” Alhaji Auwal yace, “Ka cire kalmar wai an fasa, idem har kana son na yi maka aure sai ka kawo wannan lalatacciyar yarinyar da kake watsewa da ita na hada ku aure ….. Da ita kai itama zaka aura dolenka Murnara Hajiya Aimana ta koma ciki, ta mike a fusa‘ce tace “Haba Alhaji, me zai yi da karuwa kuma‘ ka bar shi dai Allah ya hada shi da ta gari wacce ya ke so ta ke sonshi dai, amma ba wannan karuwar ba”. Alhaji Auwal ya cc, “Da ya kc ita ba diya ba ce ba k0? Danki shi ne da k0. k0 ma dai mc ye bai shafc ni ba, ya je ya yi dukkan abin da ya ga dama, amma batun aurc shi da Hasna babu shi har abada”. Ya kada kai ya wucc. Abba sai ya fashe da kuka. ya rasa mai ya kamata ya yi yanzu duk burikan da ya ci a kan‘Hasna ba matarshi ba ce ba wani ne can zai aure ta. Gaskiya an cuce‘ shi matuka. Sai a wannan lokacin Hajiya Aimana ta ji tausayin dan nata ya tsirga mata. don ta jima ba ta ganshi yana kuka kamar haka ba. amma dai ta san komai mai Wucewa ne, ‘da asirin da aka yi masa ya karye zai ci gaba da rayuwarshi kamar baya. Za kuma ta samo masa matar data f1 Hasna komai da komai. Da wannan ta fara lallashinsa da kwantar masa da hankali. ‘ *** *** *** Abu kamar wasa karamar magana sai ta zamto babba, domin yau ga shi bar an daura auren Hasna da Abduljabbar, Husna kuma da Hashim. Aure _mai cike da ban mamaki, an yi shagulgula irin na masu hali da kuma ‘ya’ya ‘yan gata. Husna aka fara .kai wa domin Abduljabbar yace a ba ‘shi sati biyu ya kammala gyara inda zai ajiye amaryar tasa da kuma hada kayan lefenta tunda aUran :ya zo ne Bagatantam don ma Allah ya taimake shi ya kammala ginin gidanshi, abubuwa‘ kadan suka ragemasa‘unguwa daya suke da Murtala amman kuma yana da kudade cikin akawum dinsa kuma amininsa ‘Murtala ya yi masa komai, don shi ne ya kawo akwatina da takalma da jakunkuna har da saitin gwal da sarka da sauran kayan lefe Akwati goma sha biyu, shi Abduljabbar kayan ciki kawai zai siya, mutane ba su yi mamaki ba domin abotarsu ta wuce nan. Har da ita aka kai Husna. amma a motar Abduljabbar ta lafe, domin ya ce bai yarda matarshi ta dinga yawo ita daya k0 da wasu kartan ba. Bayan an shiga da Husna kowa ya sanya albarka aka ce .za a. wuce gida. Nan fa rigima‘ ta Barke‘, domin da ” Hasna da Husna kankame‘juna suka yi suna kuka a kan’ ba za su rabu ba, don tunda aka haifc su ba a taBa raba musu‘ko da daki ba ballc a ce su kwana ba tare” ba. Da kyar aka Samu aka lallaBa su suka rabu, amma sai da suka sanya kowa‘zubda hawaye Hasna tana kuka ta iso ta bude motar Abduljabb‘ar ta shiga, ta hade kai da gwiwa tana kuka kamar karamar yarinya. Ba sai an yi masa bayani ba ya san abin ta kc yi wa kuka, rabuWa da “yar uwarta “ne da suka shaku. Ganin mutane sun fara baibaye’motar da sunan‘ rarrashinta ya sanya ya kunna motar’ya bar gurin, can wata- hanya daban ya dauka ba wacce suka b‘iyo ba. Ya sami gcfen tiri cikin Wata duhuwa ya tsaida motar, har lokacin Hasna tana kuka, babu zato ba tsammani sai kawai ta ji ya rungume ta,tsoro da fargaba suka kamata, abin da ya sanya kukan nata Saurin ,daukewa, kenan ya dinga shafarta ,kama’r. Wata mage ‘yana’ magana cikin’kunnuwanta “”Hasna idan kin rabu’ da ‘HUsna da ni fa Za ki ci gaba da rayuwa, k0 ba kya sona ne? Bari na gwada’ miki yadda na ke sonki Hasna”. Ya dinga gaya mata wasu irin kalamai da bai taba fadi ba, ba ta ma san ya iya su ba. Duk kunya ta kamata, tun tana kOKarin kwacewa har ta sakar masa komai domin sai yanzu’ta game: tana tsananin buqatar‘namiji ‘ kamar Abduljabbar kusa da ita. Sun jima Cikin wannan halin da suka manta kansu da komai, sai da ta ga‘ yana nufin wuce makadi da rawa sannan ta fara – Kokarin zamewa tanayi masa ‘nuni da titi ne‘, kUma cikin‘mota ne Da kyar ya’ sake ‘ta ya maida kanshi ya jingina jikin kujera yana maida numfashi da kyar, idonshi a lumshe. Tana gyara rigarta da ya zame gabadaya tace. “Dakta mu wuce gida don Allah dare ya yi… kuma…” Ya bude ido yana kallonta wanda ya sauya launi zuwa jawur, yace “‘Kuma me?” Ta kauda kai da sauri ganin irin kallon da ya ke mata, cike da kunya. Ya kada kai ‘kawai ya *tada motar suka Ci gaba da taflya, amma kowa da abin da ya ke sakawa cikin ranshi. A kofar gidan su ma sai ‘da yayi abin da’ya so son ranshi, sannan ya barta Duk da dai bai samu gamsuwar da ya ke fatan samu ba a; tattare da shi, haka nan ya kunna . motarshi ya wuce ‘da sake sake kala-kala cikiin ranshi da zuciyarshi. Ita kuwa .daren ranar kwana ta yi mafarkin mijinta, musamman da ya ke babu abokiya’r kwanan nata, cikin dakin ita daya ta kwana cike da kewa da tunanin halin da Husna kc ciki, don ta San a jaraba irin ~ta Hashim ba zai barta ba, mutumin da tun a gida ya so gamaw‘a da ita don dai ta dagc nc ta nuna masa ba ta So ya sanya dole ya hakura har aka yi auran. ‘ Abduljabbar ya dage maimakon sati biyu da ya ce cikin ‘kwana tara’ ya kammala komai. ya buqaci matarsa‘aka tartare‘ maSa. iyayenta suka kai’masa ‘abarsaa wani da‘re mai dumbin tarihi cikin rayuwarsa, daren ‘da ba zai manta da shi ba. Ya iso ya tadda Hasna zaunc tsakiyar gado an “nade ta da wata lafiyayyar laiffayamai ruwan gwal, sai kamshi ke fita daga jikinta; Ya haye tsakiyar gado ya kamo ta ya rungume yana mata rada da zolaya, daqar ya iya ‘Cin ‘yar kazar amarcin suka yi’ sallah, don ya kagu ya isa ga-matarshi. ” Ita kuma ta ba shi hadin kai dari bisa dari, sun raya darensu da soyayya duk da ta dan ji jiki kasancewarta farin shigar ginin aure; sai dai yadda Abduljabbar ya dinga gwada mata soyayya ya sanya ta shanye dukkan irin azabar da ta sha. Da safe shi ne ya shiryata, Karima ta aiko musu da komai tun kafin su farka, don haka suna tashi suka amsa gurin maigadi suka hau ci cikin farin ciki da annashuwa suna hira. Wannan shi ne irin lokacin da suka jima suna jira a rayuwarsu. Ina labarin Abba? Tun randa mahaifinsa ya sanar da shi fasa auransa da Hasna da ya fiCe bariki bai dawo ba sai da ya yi sati guda, yana can tare da Ruma. Wannan abin ya kara daga hankalin‘ mahaifnsa, amma ita Hajiya Aimana ko a jikinta, don tana ganin ta wannan hanyar ne kadai zai samu ya rabu da damuwar da ke damun zuciyarsa, don haka ko da ya dawo mahaiflnsa yana fadan hakuri’ ta dinga bayarwa da nuna masa yanzu dan nasu lallashi ya ke so ba fada ba, amma Shir ya kasa ganewa. Daga karshe dai ya yarda dole ya rarrashi dan nasa da yi maSa addu’a, domin ya fi zalon abin da ya yi masa zai sanya shi ya gyaru. amma sai ya kara Baci ma, don haka addu’a kawai ya ke bukata. *** *** *** Rayuwar Hasna da mijinta rayuwa ce mai ban sha’awa da tsananin soyayya, har mutane sun sallama musu,’ sannan Hajiyar Abduljabbar tana bala’in son Hasna kamar ta lashe ta, musamman da ta fahinci bayan watanni hudu da’ yin bikin Hasna na dauke da ciki, duk da su basu gane ba, amma ita ta gano, ta kuma sanar da danta. ‘ Dad‘i ya cika shi, ya dauki matarsa sai ’ asibiti. Gwajin farko likita ya tabbatar masa da gaskiyar abin da Hajiyarsa ta fada, saboda . jin ‘ dadi bai san lokacin da ya rungume ta ba gaban likitan ba. K0 da suka dawo gida ma wata sabuwar murnar cc, wannan Ciki shi ne (dan soyayya da gata, haka nan aka dinga lelensa da tattalinsa har ya girma. ‘Watarana lokacin cikin ya tsufa Abduljabbar ya dauki Hasna don zuWa sabon kantin nan na ‘yan gayu da aka bude don Kara yi wa dan cikin nasu siyayya. Sun kammala siyayyar kayan masu yawa suna fitowa cikin farin ciki sukaci karo da Alhaji Shazali mafia, sam Abduljabbar bai ganshi ba, amma shi ya ganshi. Da tsananin mamaki ya ce. “Wa na ke gani kamar Abduljabbar Falmata?” K0 cikin mafarki Abduljabbar ya ji muryar Alhaji Shazali Mafia zai gane, don haka a kidime ya kalle shi lokaci guda yanayinsa ya sauya zuwa damuwa da bacim rai. Alhaji Shazali ya kalli abokansa guda biyu da ke tare da shi, ya ce. “Wannan shi ne yaron da na jima ina ba ku labari, Abduljabbar”. Dr. Abduljabbar ya Kara had‘e rai ya kama hannun Husna‘ da ta tsaya tana kallonsu,hankalin Alhaji Shazali ya kai kan Hasna, Ya yi murmushi yace “Ba dai matarka ba ce wannan’.’ lkon Allah ga ta nan kuma har da ciki, Abdul ina ka buyane?” Abduljabbar bai ce k0 uffan ba ya fara jan Hasna alamar su taf1. Alhaji Shazali ya ci gaba da magana. “Haba Abduljabbar, ya ya za ka yi mini haka? Ka tsaya mu yi maganar da ta dace mana, na jima ina nemanka wallahi, don Allah ka saurare ni”. Abduljabbar bai tsaya ba balle ya . saurare shi. Alhaji Shazali ya yi nufln binsa, amma daya daga cikin abokan nasa ya ruko shi yana fadin “Ba ka ga tare ya ke da iyalinsa ba? Ka bari mu nemesa lokaci daban ba irin wannan lokacin ba”. Abduljabbar yana hangensu ya sanya matarshi a mota ya kunna ya fice a fusace. Hasna kallonsa kawai ta kc yi da tsananin mamaki, daga karshe dai ta kasa haquri sai da ta ce masa. “Dakta, wai wayc wannan din na ga daga ganinsa ka shiga ‘ damuwa lokaci guda?” Abduljabbar ya goge, gumi duk da sanyin A.C din da ke cikin motar yace “Ki bar maganarshi kawai, ba alkhairi ba ce Haka nan dole ta hakura ba don ta so ba. ,Allah ya sauke ta laflya. an sami namiji, dan soyayya ke nan don kowa ya yi murnar samin Sadik, wanda ya ci suna ba na kowa ba. ‘ Sai da Sadik ya yi wata hudu sannan ita ma Husna ta haihu. ita ma namiji ta haifa aka sha suna cikin farin‘ ciki. ‘ Watan Sadik sha daya- ‘Hajiyar Abduljabbar ta daukc shi domin tunda ya fara cin abinci kUSa da ita yake yini, sun shaqu domin iyaycnsa kullum suna yawon aiki. dun haka ba su damu sosai ba. Ranar wata laraba da Hasna takira baqar rana a arayuwarta. ta tafi na dare da ta saba. domin ta sami aikin gidan radiyo ne, amma tunda ta je ciwon kai da amai ya takuramata, dole wani ya amshe ta, ta dinga kiran wayar Abduljabbar a kan ya z0 ya dauke ta, amma wayar tashi a rufe, dole haka ta hakura ta hau motar ofls don ya saba sai sha biyu ya ke zuwa daukarta, yau kuma tun karfe takwas ta taho, aka sauke ta a qofar gidan ta shiga. Tun daga harabar gidan ta ga motar Murtala tayi murmushi kawai ta nufi cikin gidan, sai dai ga mamakinta babu su a falon farko, ta wuce na tsakiya ma ba sa nan. Sai ta wuce dakin’ baccin Abdul. da fargaba . domin tana. jiyo numfarfashin mutane. Ta tura kofar a hankali cike da fargaba. Me zata gani? Mijintane da abokinsa- Murtala ta gani suna shafe-shafe irin wanda ma’aurata mace da namiji ke yi, sam ba su ganta ba, domin hankalinsu ba ya tare da su, don haka ta saki kofar da sauri ta juya da gudu dakinta bakinta a toshe. Tana isa dakinta ta fasa ihu da dafe kai tana zagaya cikin dakin, me za ta gani’.’ Daman mijinta dan luwadi ne dan mai neman maza ne? Innalillahi wa inna ilaihirraji un Abduljabbar yacuce ta, ya yaudare ta’ bai taba ba ta wata ‘yar kofa k0 damar da za ta zarge shi ba, shi ya sanya ashe shakuwarsu da Murtala ta yi yawa. Sai kawai ta fara sauko da akwatunanta tana hada kayanta tana kuka, tabbas yau auranta da shi ya kare tunda ABIN DUHU ya bayyana, da ma Abba ta aura don shi mata kawai ya ke bi ba maza ba. Kaiconta! Kaicon wannan rayuwa! Tana tsaka da hada kayan Sai amai nan ya taSo mata. Ta fada bandaki da gudu ta fara kelayawa tana kuka,-tana jin kamar zuciyarta ta fado k0 ta huta Sai da ta amayar da duk abin da ta Ci sannan ta samu sa’ida ta koma tana numfashi da Kyar. Tana zaune a tsakiyar bandakin, can wani tunani ya fade mata na k0 ciki ne da ita? Don aman nan ya yi yawa, sai ta ji hankalinta ya Kara tashi, ta dafe kirji ta fashe da kuka tana fadin. “Allah ka da ka sanya ya zamto ina da ciki, don dayanma da na haifa ina da na sani da shi”. ‘ Sai ta mike a gigice ta yi falo… Wohoho wato ana rikici a book dinnan Daman abdujabbar dandandandan ne lol………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button