ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
2⃣0⃣

ya shigo dakin ikin sauri yana hakin wahalar bude dakin da yayi hankalinsa yakai kan ban daki ko tantama babu tana ciki kusan yanda kofar dakin take da qarfi da kwari haka itama ta toilet din take ya tsaya yana nishi damaki abin ya fara wuce tunaninsa shin itama ballata zaiyi domin ganin halin da matarsa take ciki ko yaya ko kuma kyaleta zaiyi ta rayu cikin halin da take ciki bai ankaraba sai kawai ya farajin kakarinta a cikin ban daki abin ya daga masa hankali tunda ta shiga bandaki amai ya taso mata gashi ba abinci a cikinta don haka sai kakari kawai takeyi dakta ya isa ban dakin ya tsaya shiru cikin damuwa tabbas wannan abin yafi karfinsa amman bayason sanar da iyayen hasna baison sanya kowa cikin damuwa yaji kamar ya kira mahaifiyarsa ya sanar da ita halin da ake ciki sai yaga hakan ma wani babban qalubalene a gareshi husna itace ta fado masa a rai yasan husna zata iya taimaka masa domin itace tasan hasna fiye da kowa a rayuwarta saiya koma falo cikin gaggawa inda ya aje wayar hannunsa ya fara kokarin kiran number husna tana tsaka da aiki taga kiran wayar dakta abdull falmata mamaki ya kamata tana yawan gaisawa dashi amman bai fiye kiranta a irin wannan lokacinba amman. saita daga wayar xikin sauri daga yanayin dataji muryarsa tasan ba lfy ba amman saita danne ta barshi ya fara fadin abinda ke ransa domin bai taba kiranta ya sanar da ita wani abu game da matarsa ba bayanma farin ciki dajin dadi abdull yadanyi dan dimm baison sanar da kowa halin dA suke ciki da hasna yaso ya warware matsalar shi daya amman babu yaddah zai iya dole saiya sanar da husna maganartaxe ta katse shi da fadin dakta an yini lfy yaya gidan da madam din? yayi dan yaqe kamar tana gabansa domin ya lura data fahimci yana cikin damuwa ya daure sannan ya fara magana lfy lau husna akwai matsala ne a gidan tun daren jiya mutumiyar taki tana cikin dako bansan abinda ke damuntaba saidai kamar lamarin yafi kama dana wanda ya sami matsala da aljanu …… aljanu dakta ta fadi hakan a firgice gamida miqewa cikin sauri kafin ya bata amsa taci gaba da magana hasna bata da aljanu domin bata wani abu dayai kama da hakan ba kodai kun sami wata matsalar ne da ita yace ko daya domin jia da safe muna cikin farin ciki da kwanciyar hankali harta tafi gurin aikinta lfy muka rabu da lokacin tashinta yayi zanje daukota shine mai gadi ke fadamin ai ta jima da dawowa wai batajin dadi hakanne ya tabbatarmin da ko menene a wajen aikin ta hadu dashi cikin damuwa ya sanar da ita halin da suke ciki nan take hankalin husna ya tashi dukda tana kan aiki a offis dinta domin itama tana aiki da wani sabon gidan talabijin nandanan ta fara hada kaya domin zuwa ganin halin da yar uwarta ke ciki tunda suka taso basu son wani abu ya taba daya daga cikinsu hakan yasa idan abu ya samu daya to dayan bai samun kwanciyar hankali abdul yana zaune a falo yayi tagumi cikin damuwa husna ta shigo cikin tsananin mamako ya daga kai ya kalleta domin tsakanin kammala wayar tasu izuwa yAnxu bai wuce minti ashirin ba cikin gaggawa ta fara gaisheshi tana kallon goshinsa cikin damuwa tace ita taji maka wannan ciwon? ya shafa gurin yana yake karki damu samun lfyarta yafi komai husna ta kada kai sannan ta kalli kofar dakin barcin hasna,bata buqatar qarin bayani akan halin da yar uwarta ke ciki amman tana shakkar abinda ya fada mata din cikin qasa da murya ta fara masa magana tana cikin dakinne? ta tambaya cikin qaguwa eh tana ciki tun daren jiya data kulle kanta a ciki bata fitoba ya bata Amsa a takaice ganin kartama kanta illa yasa na bude dakin da qaefin tsiya amman saita koma ban daki ki taimakamin husna banson wani abu ya sami hasna don allah cikin rawar baki yake rokonta tayi masa yaqe wanda baikai cikin zuciyarta,ba tana fadin tace karka damu dakta bari na ganta ka saurara anan ina,zuwa cikin sauri ya amsa da to ya bita da kallo sanda ta nufi hanyar dakin. ji yake kamar ya bita amman baison ya bata lamarin kamar yaddah ta buqata fatansa dai allah esa ta kula yar uwar tata ya fara kaiwa da komowa a tsakiyar falon husna ta shiga dakin a hankali tana kare masa kallo gabanta ya,fara fadiwa domin maganar dakta tana neman tabbata hasna mai tsabtace batason ko kyalle ya fadi a tsakiyar,dakinta amman saiga shirgin kaya akan gado a hargitse komai baya cikin hayyacinsa a dakin natA amman a qasan ranta fata take allah yasa ba hakan bane daga can cikin bandakin hasna ta miqe zubur domin jiyo muryar yar uwar tata taxo bakin kofar amman taqi budewa ki bude hasna nice yar uwarki husna ko baki gane muryata bace tace na gane mana amman ki fadamin gaskia keda waye a cikin dakin ?hasna ta kalli cikin dakin sannan ta kalli kofar tace ni dayace babu kowa a ciki hasna ta bude kofar a hankali har izuwa sanda suka hada ido mamaki ya fara kama husna ganin yaddah taga kayan hasna sunyi datti sunyi kaca kaca hasna ce haka ta fada cikin ranta amman a fili saita wayence tai murmushi gamida kama hannunta hasna lfy meke damunki kika shiga cikin ban daki kika boye haka? meye akai miki?tana maganar tana qara nazarin yar uwar tata a tsanake hasna ta ware idanu ta nufi gefen gado kai tsaye ta zauna tayi shiru cikin damuwa husna ta zauna a kusa da ita tana kare mata kallo abubuwafa suna neman su zamto gaskia ta qara kura mata ido tana ci gaba da tambayarta ki gayamin menene yake damunki tun daren jiya kinqi fadawa mijinki kikazo kika jefeshi da fitila kika fasa masa kai ki fadamin meke damunki ne? hasna ta kalli husna a cikin idanunta da babu ko dar a ciki ta fara magana na fasa masa kai tabbas kuma ina sane sannan idan har bai rabu daniba zanyi masa abinda yafi haka, domin na yanke shawarar rabuwa dashi ….. husna ta kalleta cikin tsananin mamaki lallai ta tabbatar da abinda abdul ya fada mata gaskia ne amman cikin lallashi tace kin yanke shawarar rabuwa da abdul akan me , me yayi miki da kika yanke wannan shawarar??………………

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
2⃣1⃣

hasna ta kauda kai idonta ya cika da kwallah tayi alqawarin bazata gayawa kowa wannan maganar ba har abada zata rufama abdul asiri hatta shi kamsa ba zata gaya masa komai ba zata bar abin cikin ranta domin kare martabar danta domin fadar tamkar kururuwa tai ta dabama kanta wuqa bazata iya fadaba saita. juyo ta kalli husna tana kokarin hadiye hawayen dake zubo mata tace kawai naji na gaji da zama dashi ne bana fatan ko sake kallonsa na tsanesa bana sonsa ta kamo hannun husna hawayen dake kokarin zubowa suka subuce mata tanaci gaba da magana ki taimaka mini kece kadai zaki fahimceni don allah karda ki sake tambayata komai kawai wayar gari nayi naji na tsani abdull idan har naci gaba da zama dashi komai zai iya faruwa dani ki gayamin hanyar da zanbi na rabi dashi kawai husna ,, husna ta amince da lallai aljanu sun taba yar uwar tata amman ta yaya zata sanar da ita domin idan bamai shafar aljanuba babu wanda zai aikata wannan abun data aikataamman lallashi da kwantar da hankali kawai hasna ke buqata a halin yanxu don haka cikin lallashi take mata magana ko menene ya sameki hasna ki cire maganar rabuwa tsakaninki da dakta domin bani da abinda zan iyayi akan rabuwarku hasalima zanfi kowa zamtowa cikin baqin cikin mutuwar auren yar uwata dakta mutum ne na gari da allah ya baki ko kin manta irin siradin da kika taka domin mallakarsa ne? kamar fama ciwo maganar ta zamto ma hasna wai dakta ne mutumin kirki badon alqawarin dana daukarma kaina dana sanar miki da waye shi ni kaina a baya nayi tsammanin haka amman a yanxu nasan ko waye abduljabbar falmata plz………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button