ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
2⃣9⃣

ko a jikin Murtala sai ma gyada kai da yayi yana fadin.” “Wannan shine abin da na yankewa kai na shawara Karima, domin zaman mu zan iya cutar da ke, na yanke shawarar sakin ki je ki auri wanda ya fi dacewa da ke.” Hawaye ya cika idona, domin jin abin da Murtala ya fada, wato da duk barazanar da . zan masa babu amfanin da za ta yi kenan, sai na kawar da kai gefe cikin kuka nace masa, amman kafin ka rabu da ni ina son na gaya maka ina dauke da cikin ka, hankain Murtala gaba daya ya tashi, dadi ya cika shi sai ya rungumoni cikin jin dadi, nasan Murtala yana matukar Kaunar haihuwa don haka zan iya amfani da wanan damar gurin ganin na shawo kansa, don haka na ture shi na tashi nabar dakin. Kwanaki suka kuma ja, amman ba a ji komai daga bakin Murtalaba, sai da akayi wata daya sannan ya Kara samuna akan shawara daya yanke na zai sake ni, amman zai ci gaba da kula da cikin da ke jikina har na haihu, na yi kuka na yi bakin ciki, tashin hankali na daya idan ya sake ni inazan nufa ina zani na zauna, sannan yaya matsayina da darajata za su koma a idon ‘yan’uwana, daga karshe dai na shigo da Abdul cikin matsalar. Abdul yayi Kokarin ganin ya kawo karshen matsalar amman bai iya ba, domin Murtala ya gaya masa hukuncisa kawai, da na ga babu mafita sai na nemi Murtala na ce masaba zan iya rabuwa da shi ba domin ina kaunar zamana tare da shi domin shine jin dadi na kuma shine rayuwata, amman idan ya amince zai daina bin kowa ni zan yi masa dukkan abin da yake buKata, soyayyarsa ta rufe mini idona a wannan lokacin, shi kuma ya ji dadin wannan hukuncin da na yanke ya rungumeni cikin jin dadi yana mini godiya, tun daga wannan lokacin na fara KoKarin biyawa Murtala buqatarsa domin bana son ya bi wasu mazan ‘na banza, amman lokacin da na tashi haihuwa sai na sami matsala yaron da ke cikina yayi kokarin fitowa ta inda bai kamataba hakan ya tayarwa da Murtala hankali amman dai cikin hukuncin Allah na sauka lafiya bayan taimakon da na samu daga hannun likitoci, Murtala ya kara nuna mini irin kaunar da yake mini, domin anyi hidimar suna irin wacce ban taBa gani ba, sannan yayi mini kayan fitar suna irin na manyan mata har da tsarabar mota sabuwa dal, wannan abin ya ruda ‘yan’uwana/ suka dinga santi da taya ni murna, Murtala kuma ya ci gaba da abubuwansa, duk da bai gaya mini ba amman na fahimci ya ci gaba da abin da yake yi, ni kuma na hana shi nemana ta baya domin na fuskanci zai lalata mini rayuwa, ina son rabuwa da Murtala amman idan na tina irin son da na ke yi masa da kuma irin kular da ya mini sai na ji bazan iya ba, dole haka na hakura na zuba masa ido, amman ni na yiwa kai na fada domin gudun samun matsala irin wacce na samu a baya, amman Murtala ya fuskanci ina cikin damuwa don haka ya dai na kawo mini kowa gida na,amman duk da bana so wani lokaci idan ya rasa wanda zai biya masa bukatarsa nice na ke masa dole,,wannan itace rayuwa mafi muni da nake yi da mijina, ba ni da mafita bayan wannan, domin idan ya sake ni ban san inazan je na zauna na ji dadi ba, sannan banson rabuwa da yarana,ba don haka kema ki yi hakuri Hasna, watarana sai labari, Allah ya jarabce mu da wannan masifa babu yanda za mu yi. . . Cikin sauri Hasna ta mike tana fadin “Aa wallahi ni Allah bai dora mini ba, bazan Kara zama da Abdul ba, domin bazan yi biyayya gurin saBawa mahalicci ba, ke kan ki kwadayi ne ya zaunar da ke, da kin mika lamarin ki ga Allah zai fito miki da mafitar da za ki bi, don haka ni rabuwa da Abdul ta zamar mini dole, zan kuma zubar da cikin sa ba zan Kara yadda na Kara haihuwa da irin wadan nan mutanan ba, kema na raina wayon ki Anty Karima, ya kamata ki yiwa kan ki fada, ki daina aikata abin da Allah ya hana saboda son duniya da soyayyar data rufe miki ido, amman ni bazan yadda hakan ta kasance akai na ba, zan shiga ciki ki gaida gida.” Ta juya cikin gaggawa ta yi hanyar dakin baccinta, Karima ta bita da kallo gabanta yana faduwa jikinta yayi sanyi kwarai da gaske, amman ba ta da zaBi bayan tafiyar tata, don haka ta dauki Jakarta ta nufi hanyar fita. KAKA KARA-KAKA KARA Abdul ya wuni cikin OfiS sai ruwan tea kawai yake sha, wayar shi ta fara kara cikin sauri ya dauka ya kara a kunnensa, Murtala ne yace maza ya je yana nemansa. Babu Bata lokaci ya nufl gidan, domin sun yi waya da shi dazu ya sanar da shi Karima tana gidan sa, to a tsammanin shi yanzu ta shawo masa kan Hasna, domin yasan Hasna tana ganin mutuncin ta kwarai da gaske. Amman sanda ya isa gidan sai ya tararda abin da bai yi tsammani ba, domin labarin duk abin da ya faru Karima ta sanar da shi, hankalin sa ya tashi kwarai da gaske har ya kasa motsawa ya dora hannu akansa cikin tashin hankali, tabbas jikinsa ya bashi wani abu ya faru mai kama da haka, amman bai kawo cewar tasan ko ta ganshi da Murtala ba, sai ya ji ya kasa hada ido da Kariman ma, domin ita kanta tana girmamashi, sai yake ji kamar ya nutse a tsakiyar gurin ya huta k0 kuma ya Bace bat kowa ma ya dai na ganinsa, Murtala ne ya dafa kafadarsa yana rarrashin sa bayan ya sallami Karima daga falon, cikin sanyin murya ya fara magana. “Ka yi haquri Abdul tabbas ni ne mutumin da na ja maka wannan matsalar, amman ban yi zaton hakan zai faru ba ka yi hakuri, sannan inamai baka shawara da ka yiwa Hasna irin abin da na yiwa Karima, ka nuna mata zaka rabu da ita kawai, na san zata haqura domin tana son ka kwarai da gaske.” Abdul ya girgiza kai yana fadin “Barazanar saki, koma menene ba zai daga hankalin Hasna ba kwata-kwata, hasalima ta sanar dani tun kafin na san abin da nayi mata ‘ sai na saketa, ta gaya mini ba zata iya kallon idona ta gaya mini abin da na yi mata ba, amman kuma ta matsa na sake ta lallai na shiga uku, wallahi ba tonuwar asirina ne ya fi tayar mini da hankali ba illah rasa Hasna cikin rayuwa ta, da kuma kama ni da ta yi dacin amanar ta, Hasna ta so ni ta guji kowa saboda ni, me ya sanya na yimata haka? Yanda ya ke maganar kamar ba shine Dakta Falmata ba, mutum mai kwarjini da karsashi, yau shine ya koma hakan. tausayinsa ya cika Murtala domin ya tabbatar da Abdul bai taba hada soyayyar Hasna da komai cikin rayuwarsa ba, zai iya rasa ransa akan ta, ya ci gaba da lallashin sa. “Ka je ka yi mata bayani, ka gaya mata komai, ka gaya mata duk abin da ke faruwa da kai Abdul, na tabbatar za ta yi maka uzuri za ta daga maka kafa.” Abdul ya mike jikinsa yayi sanyi kalau yana fadin “Na gaya maka ba zata saurare ni ba ni ma bazan iya kallon ta ba, amman wallahi bazan iya sakin ta ba, bazan iya furta wannan Kalmar gareta ba, zan wuce ni sai mun yi waya.” Yana kaiwa nan yayi hanyar fita cikin sauri’, Murtala ya bishi da kallo cikin damuwa, _ bai san me ya sanya abokinsa ya yadda soyyayyar mace ta yi masa Karfi har haka ba. Kwanaki kusan hudu ana wasan Buya tsakanin Hasna da Abdul, a Bangaransa baya iya wuni .ma kwata-kwata a gidan, domin bai qaunar ya hada ido da ita, bai san da irin kallon da ya kamata ya kalleta ba, itama Hasna a Bangaranta hakan ya fiye mata sauqi, don duk duniyar ta yi mata zafi, bata son komai a wannan karon sai mutuwa. A gurin aiki sun damu da rashin zuwanta aiki, domin Hasna tana daga cikin ma’aikatan da ake kaunar shirin su, amman ta gama yanke shawarar barin aikin, ita fa duk abubuwan rayuwar sun zame mata tamkar Kiyama. Ta rubuta takardar barin aiki ta aika musu wato resignation latter, labarin ya tayar da hankalin Husna wacce wata Kawarsu da suka yi karatu tare suke aiki da Hasna ta buga ta gaya mata, don haka da kanta ta zo gidan, halin da ta ga Hasna a ciki ya firgitata, babu wanka balle kwalliya ta zama wata iri kamar wacce ta sami ciwon tabin hankali, da zummar yin fada ta shigo gidan amman sai ta koma nasiha da lallashi, tasan ko me za ta yi Hasna ba zata gaya mata dalilin barin ta aiki ba, amman fatan ta ta shawo kanta ta hana ta aikata hakan, ta janye barin aiki kamar yanda ofis din na su ke fatan ta janye din, amman babu wata magan mai dadi, haka nan tabar gidan dole, tana son ta sanar da iyayan su halin da Hasnan Ke Ciki amman tana tsoran abin da zai biyo baya, domin za su matsa mata ne akan lallai sai ta fadi laifin mijin na ta wanda ta yi alkawarin ba zata sanar da kowa ba. Haka ta fice daga gidan, ta kira wayar Abdul ta ce masa tana son ganinsa a gidan ta. Hankalin Abdul yayi matukar tashi domin a tsammanin sa Hasna ta sanar da ita abin da ya yi mata, ya ji kamar yace baya gari’ ba zai sami damar zuwa ba, amman sai ya ga bashi da wata mafita bayan zuwa, domin k0 ya je k0 bai je ba abin da zai faru ya riga ya faru din. Da yamma sakaliya ya tafi gidan na ta, kai tsaye aka shiga da shi, da yake daman suna zuwa shi da matar ta shi, basu iya sati daya ba tare da wani ya kaiwa wani ziyara ba, hakan ya sanya mazajansu shaKuwa sannan gidajan su ya zamto musu kamar gidan kowa ba su da shamaki. Bayan sun gaisa Husna ta tsare shi da ido da tambayar da ta dan kwantar masa da hankali, domin tun da ya shigo kan sa a Kasa yake yana tsammanin tasan k0 waye shi a yanzu. “Don Allah Malam ina son ka sanar da ni laifin da ka yi Wa Hasna, gabadaya ta rikice ta ~fita daga cikin kamaninta, yau fa har takardar resigning ta tura ofis din su.” Abdul ya kalleta cikin tsananin mamaki yana fadin “Resigning, Hasna din ce ta yi risgining gurin aiki ba tare da na sa ni ba? “Tabbas kuwa.” Ta bashi amsa sannan ta dora “Bayan barin aiki ma za ta iya aikata komai, shi ya sanya nace gwara mu tattauna da kai wataKila zan iya gano mafita ta abin da zaka gaya mini, bai kamata ace manya sun shiga cikin case din nan ba, amman idan abin yafi Karfina dole su shiga. Don Allah malam ka gaya mini gaskiyar abin da ya hadaka da matar ka.” Yayi shuru gabansa. yana faduwa, a yanda Husna ta ke da matarsa zai iya gaya mata komai na rayuwarsa, amman kuma tsoransa daya yaya Hasna din za ta ji idan har ya fada, domin ita kanta duk irin shakuwarsu da kusancin su bata gaya mata komai ba, me sanya shi zai gaya mata, amman wata zuciyar na gaya masa fadin ne kawai hanyar mafitar shi. ‘ Cikin karfin hali ya fara magana “A gaskiya ban san menene laifin da na aikawatawa Hasna ba, amman nafi zaton ganina data yi da wata budurwa cikin motaba tare da na sani, ba, da na zo gida kuma na musa mata, sai da ta bani tabbaci na yadda, ina zaton shine kawai”Yana magana yana kallonta domin ganin yanda za ta dauki abin, a ranshi yana istigifari ga Allah, tabbas yayi hakan ne domin kare auransa, amman a fili sauraran Husna yake yi. Husna ta yi murmushi mai ciwo tana fadin “Wallahi na yi tsammanin lamari makamancin hakan, Hasna tana da kishi amman ban yi zaton wauta da rashin hankalinta ya kai nan ba, yanzu Dakta yaya kake ganin za mu yi? Abdul ya yi dan jim, a ransa ba shi da wani abu da zai yi, kasancewar baya son mutane su shiga cikin lamarin su ya sanya’ya tabbatar mata da zai dauki mataki da kanshi ta dan ba shi lokaci.Amman da ya fita daga gidan ya shiga cikin motarsa ya hada kai da sitiyari ya rasa me yake masa dadi cikin rayuwarsa, sai ya tsinci kansa da fashe da kuka kamar wani karamin yaro………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button