ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
3⃣2⃣

gaba daya ta karye, ita kanta Husna sai ta sami kanta da damuwa kamar za ta fasa kukan, wato laifin dan’uwa shafar mai inji masu iya magana. Dukkan jijiyoyin jikin Abdul sun yi sanyi, yana jin kamar zai fasa zuwan, domin tabbas yasan idan aka. matsawa Hasna za ta iya tona masa asiri, yaya zai ji idan wannan labarin ya bayyana gaban mahaifin Hasna, wacce irin kunya zai ji? Ya yi ta saqawa da kwancewa, tun da yake bai taBa shiga bala’i irin wannan ba, tabbas yasan abin da ya shuka shine Allah ya sanya yake girba yanzu, me ya sanya bai yi hakuri ba, mai ya sanya bai kawar da kai ba Salati da salallami yayi bai san adadin da yayi ba, har sai da miyan bakinsa ya qafe kaf ya rasa na hadiya sai Kanqani. KARO DA MAZA.. .wannan shine abin da yake ta fada cikin ransa har lokacin daya isa ta shiga, ba ta yi zaton mahaifanta za su yi mata haka ba, duk da tana sane da abin da baban na ta ya fada mata, amman ta yi tsammanin za su tausayawa rayuwarta. Husna kallon ta kawai ta ke cikin tausayawa, tun da suka shigo dakin ta ke rarrashin ta amman ba ta ce mata komai ba, har yanzu ma da aka gaya mata sakon mahaifin na ta ba ta ce komai din ba sai kallo kawai, Haj. Aisha ta kula da hakan, ta karasa ta rungume ta jikinta, kamar jiran hakan ta ke sai ta Kara fashewa da kuka cikin wata irin murya da ta fara dashewa saboda wahala da azabar kukan da ta sha, tana goga kanta jikin mahaifiyarta tana magana. “Momy kar ku bari ku rasa ni…don‘ Allah kar ku yadda zuciyata ta buga…na gaya muku bana son Abdul…bana kaunar k0 kallonsa…kada ku mayar da ni gidan sa don Allah… Haj. Aisha ta kasa cewa kamai sai shafa kanta kawai ta ke yi cikin rarrarshi zuciyarta gidan, tsakiyar ranace domin wajan Karfe daya ne na rana, mafi muni cikin tarihin rayuwarsa. Kai tsaye ya shige gidan babu ko iso, a babban falon gidan ya tarar da Alh. Sammani suka gaisa cikin girmamawa, sai dai abin da ya bashi mamaki bai ga komai akan fuskar sirikin na sa ba, sai ma jansa da yayi da hira, cikin dar-dar yake amsawa jikinsa yayi sanyi. Bayan tsahon lokaci Haj. Aisha ta iso falon dauke da abinci, yau mijin na ta bashi da niyyar flta gurin harkokinsa, ya zauna a gida domin kashe gobarar da ta ta so a gidan na sa. Cikin ladabi amman kansa yana Kasa Abdul ya gayar da Haj. Aisha, ta amsa babu yabbo babu fallasa, ta juya tabar falon, abin da ya Kara tayar da hankalinsa da Alh. Sammani ya buKaci su ci abinci tare, bai taBa cin abinci da sirikin na sa ba, don haka sai ya ji abin wani iri. Amman ba zai iya kin ci din ba, domin bai kasance daga cikin jahilai ba, hakan ne ya sanya ma sirikin na sa ya roqe shi da ci din, ya sanya hannu yana ci, Alh. Sammani wayayyan mutum ne da ya san takan duniya, ya kula sarai da yanda sirikin na sa yake jin nauyinsa, amman yana kokarin kwantar masa da hankali. ‘ ‘ Abin da ya baiwa Abdul Kwarin gwiwa shine yanayin hirar da Alh. Sammanin ke masa ta matsalolin da kaSa ke ciki, kasancewarsa malamin jami’a da ya san komai na rayuwa ya ji dadin hirar domin ya na sanar da sirikin na sa abubuwan da shi bai sani ba game da yanayin da qasa ke ciki, musamman da ya kasance dan jarida. Sai da suka kammala cin abincin sannan Alh. Sammani yayiwa Haj. Aisha waya yace ta fito masa da Hasna yana son ‘ganinta. Hankalin Hasna idan yayi dubu ya tashi, domin ta yi wa kanta alkawarin ba za ta gayawa kowa labarin ta ba, amman tana jin yanzu idan mahaifinta ya matsa mata akan ta koma gidan Abdul za ta iya sanar da shi komai ko domin ta samu a rabata da auran da ya zame mata alakaliai, kafin kuma ta koma kan cikin da shima ta ke kiransa da hakan. Ta iso falon kanta yana kasa ba ta son k0 kallon fuskar Abdul, amman duk da haka ta hango gefen da yake zaune ta gefen idonta, ta kuma can wani Bangare ba inda yake ba ta zauna ta tankwashe Kafafunwanta. Tun da ta fito Abdul yake satar kallonta, gaba daya ta rame ta fita daga hayyacinta, wanan shine abin da yafi daga masa hankali, sai dai ramar da ta yi ta sanya cikin da ke jikinta ya bayyana a yanzu domin yana dan iya gano yanda cikinta ya daga kafin ta zauna. Sun zauna shuru kowa da abin da yake sakawa a cikin ransa, Alh.Sammani ne ya katse Shirun ta hanyar fara magana. “Abdul na ji wani labari mara dadi wanda ya tayar mini da hankali. Abdul ya daga kai cikin fargaba ya kulleshi a ransa yana fadin shike nan ta faru ta qare, amman a fili shuru yayi cikin tsoro. Alh. Sammani ya ci gaba da magana “Lokacin da na fara ganin ka a wanda Hasna ke so na ji farin cikin cikar kamalarka~ da hankaiinka, duk da a wancan lokacin ban amince zan baka itaba, amman na ji dadin da ‘ ya sanya diya ta ta ke mu’amala da mutum irin ka mai ilimi, lokacin da auran ta ya tabbata akan ka na yi matukar farin ciki, domi daga baya na gano ina shirin kai ta gidan da ni da ita ba za mu yi kuka watarana ba, duk da Abba da na ne, amman na san Hasna ba za ji dadin auran sa baba saboda abu biyu, na farko bata son sa, na biyu kuma yana da wani hali mara kyau, hakan yaya sanya bayan auran ku naji kamar an daukemini dukmatsalolin darayuwar ‘ya’yana za ta iyashiga k0 ta fuskanta cikin auransu, nakuma sami hakan kusan shekaru biyu da wani abu da yin auran na ku, amman yau kuma sai na ji wani abu saBanin hakan.” Yayi dan shuru yana nazarin su, Abdul gaba daya ya flta da ga tinaninsa, jira kawai yake Alh Sammani ya kai karshen zancensa ya sanar da shi abin da Hasna ta gaya masa ya nemi afuwa gami da sanar da shi dalilinsa, Hasna kuma kuka take yi Kasa-kasa cikin . damuwa, Haj. Aisha tana gefenta tana kallonta kawai. Alh. Sammani ya ci gaba da bayaninsa “Ba ta sanar da ni komai ba, ta ce mini baka yi mata komai ba Abdul ya daga ido cikin sauri ya kaili Hasna wacce ke sheshekar kuka,‘ a yau ya tabbatar Hasna tana kaunar shi fiye da soyayyar da yake zato tana yi masa a baya, duk da halin da ta ke ciki amman har yanzu ta kasa yadda ta sanar da wani abin da ya aikata mata, to me ya sanya Hasna taqi fadin wannan labarin ne? Maganar Alh. Sammani ’ta katse masa tinaninsa “Ga ni gaka ga ku.ma Hasna ka , sanar da mu gaskiyar abinda ya faru, domin ta karyata labarin da ka baiwa Husna, me ya hadaka da matarka? Abdul ya goge gumin da ke karyo masa, idan har Hasna ta yi Kokarin rike sirrinsa, mai ya sanya shi zai yi mata Kazafl akan abin da ba ta sani ba wanda ke koqarin hukuntata da laifin da ba ta ji ba bata gani ba, ya gyara zama idon sa yana Kasa ya fara magana. “Tabbas Baba abin da Hasna ta fada shine gaskiya.” Mamaki ya kama Haj. Aisha ta kalli Abduljabbar cikin mamaki, amman me ya ‘ sanya ka fadawa Husna wani labari daban ba wannan ba, sai dai ci gaba da bayanin da yayi ya bata amsar tambayarta. “ Baba na wayi gari Hasna ta shiga cikin wani hali, duk abin nayi za to ya zamto ba haka bane nayi zaton ko aljanune harbeta ashe ba haka ba ne, sannan na yi zaton k0 ta ganni da wata lacture da na dauko wacce muka flta wata unguwa daga ofis shima na tabbatar ba haka ba nne daga karshe Baba ni kai na ban san menene laifin da na yi wa Hasna ba, ban kuma san dalilin da, ya sanya ta keson ta rabu da ni ba.” Yana kaiwa nan ya ja bakinsa ya tsuke, a karo na farko Hasna ta kalli inda yake cikin sauri tana jin kamar ta tashi ta rufe shi da duka, yaya zai ce bai san abin da yayi mata ba‘? Wannan shine rainin wayo mafi muni da wani ya taba yi mata, da ma za ta iya da ta fada yanzu da bakinta. Alh.Sammani ya girgiza kai cikin gamsuwa da bayanan Abduljabar sannan ya fara magana “Daga qarshe na fahimci wani abu a zamantakewar ka da matarka, kuma na ji dadin hakan, na fuskanci kun yi wa juna laifi amman bakwa son kowa ya san menene a cikin rayuwar auran ku, wannan abin yayi mini dadi kwarai da gaske, don haka ina amfani da wannan damar gurin baku haquri.” Hasna ta kalli mahaifinta da sauri da faduwar gaba a ranta tana addu’ar Allah ka da ya sanya yace ta koma gidan Abdul, amman ina aikin gama yagama. Ya ci gaba bayaninsa “Ki tashi ki bi mijin ki ki koma dakin ki, kamar yanda kuka san matsalarku ku kadai ku warware ta ku kadai, Allah yayi muku albarkaa .. Kuka da gunjin Hasna ya katse masa maganarsa ya kalleta da sauri cikin mamaki irin ihun da ta ke yi kamar wacce za ta hau bori, Hankalin Abdul idan yayi dubu ya tashi ya zura mata ido shi ma, Haj. Aisha ce ta yi kokarin daka mata tsawa cikin Bacin rai. “Menene haka Hasna Me ki ke aikatawa? Hasna tana ja da baya tana ci gaba da kuka, amman ta rage ihun da ta ke yi sai jijjiga kai. kuyi haquri plz page 56 is missing bansan ya akai ba komai zai zama daidai, ka je ka ci gaba da addu’a kawai.” Abdul ya ji dadin hakan, domin bai son a matsawa Hasna har ta kai ga ta aikata abin da kowa zai yi da ya sani, don haka cikin Karfin gwiwa ya amsa da to, yayi sallama da surukan na sa ya wuce. Alh. Sammani ya mike shima yana kallon Haj. Aisha “Zan dan fita ni, idan na dawo za mu yi magana.” Cikin sanyin murya ta yi masa a dawo lafiya, sai dai ta kasa tashi daga in da ta ke saboda damuwa. ‘ABU KAMAR WASA… sati guda ya tafi ba tare da gano ‘ komai na matsalar ma’auranta ba, a Bangaran gidan su Hasna sun tattara sun zuba mata ido babu wanda ya Kara yi mata maganar komawanta gidan mijinta, yayin da a na shi Bangaran Abdul shima ya zuba IdO, amman yana kiran Alh. Sammani ya na gaisheshi da kuma tattauwana halin da Hasnan ke ciki da Husna, ya fahimci babu wani ci gaba, domin a zaman da ya yi da Hasna ya san mutum ce ita mai wani irin hali da ake wuyar tankwara. Daga Karshe Zulai me aikinsu gidan Husna din ya kai ta ta zauna, kafin uwar dakin ta ta dawo, domin ya fahimci zaman yarinyar ita kadai a gidan kamar yana damunta. Daga ya sallamawa komai, donyana ganin wani ikon Allah ne kadai zai iya mayar da auransu, amman ba dabararsa k0 wani wayon sa ba. . Rayuwa ta yi masa zafl, ya saba da Hasna da rayuwarsu ta farin ciki da jin dadi kasance baya yin komai sai da ita, baya cin abinci sai na ta baya komai sai tare da ita, ammaan a yanzu babu ita a kusa da shi, gidan ya masa girma Shi Ya sanya bai shigarsa sai da‘ kwanciya, bacci kawai. A Bangare guda kuma yana jin kewar Murtala, ko babu komai Murtala shine abokin sa kwaya daya tal a wannan duniya, shine . wanda yake iya gayawa abin da ke damunsa, da shi suke saqawa kuma suke binnewa, yayi mamakin irin flshin da yayi da shi haka mai zafl, lokuta da dama Murtala yana yin fishi da shi amman fishin bai zuwa ko ina suke shiryawa, sai dai yanzu ya kula abin ya yi zafl har yafi ko yaushe, hakan ya sanya ya fara jinsa kamar shi kadai yake rayuwa a wannan duniyar, gurin hajiyarsa kawai ya ke jin dadi sai dai itama ta sanya masa ido Kwarai da gaske akan yanayin da ya sauya, amman ba ta takura da tambayarsa abin da kedamunsa ba, shima ya ja baki yayi shuru bai ce mata komai ba. Abokansa da Dalibansa ma sun fuskanci malamin na su yana cikin matsala, domin babu wuya yanzu ya balbale dalibi da fada k0 cin zarafinsa, hakan ya sanya suke taka tsantsan da shi. Yau ba Shi da lacture din safe, don haka ya ga shigarsa makarantar kamar zai zame masa takura, tunda bai san zaman ofis din, don haka bayan ya flta daga gida gurin Hajiyarsa kawai ya wuce, Hajiya tana cikin daki saboda yanayin sanyi da ake yi a garin ta jiyo Shi a falo suna gaisawa da mai aikinta, ta fito cikin murmushi tana kallonsa, ya kalli inda ta ke sai ya Karasa ya durqusa a gabanta cikin gaggawa yana gaisheta, ta amsa cikin sakin fuska sannan ta baiwa Laraba umarnin ta kawo masa sauran dumaman tuwo da kunun gyadar da ta dama mata. Ba ta tambayi ra’ayin sa ba, domin tasan yana son irin wannan abincin, duk da bai damu da cin abu me nauyi da safe ba. Shi ya fara tambayarta Sadik, ta sanar da shi har lokacin ya na bacci da yake bai kwanta da wuri ba jiyan, suka ci gaba da hiran Sadik har Laraba ta kawo masa abincin, ya gyara zama ya fara ci, yanayin yanda yake cin abincin ya bata mamaki, domin ta jima rabon da ta ga ya ci abinci irin haka, shi kuwa yunwa ce ta yi masa karo, domin ba shi da abinci bayan ya dafa Indomie k0 ya sha wasu abubuwa na ruwa ko na gwangwani. Har ya kammala cin abincin hirar Sadik kawai suke yi, sai da ya kammala ya wanke hannunsa a kwanon da Laraba ta ajiye masa ya matsar da kayan gaba sannan Hajiya Falmata ta fara tambayarsa. “Abdul me ya ke damunka da ka ke Boye mini ne, acan baya baka da abokiyar sirri da gayawa abubuwan da yake damun ka sai ni, amman yanzu ka Ki sanar da ni komai, na yi shuru na yi shuru amman har yanzu ka ki sanar dani komai.” Ta yi shuru tana kallonsa, ya dukar da . kansa Kasa bai ce mata komai ba, ta ci gaba da magana. “‘Ko da ba zaka sanar da ni komai ba inasonka gaya mini me ya sanya Hasna bata gidan ka har zuwa wannan lokacin? “K0 Karyace ka gaya mini kamar yanda ka gaya mini a baya sanda na ga goshinka a fashe kuce mini faduwa ka yi, tabbas na san ba gaskiya ka gaya mini ba, amman na ji dadi daka yi mini bayani, ba zan so ka gaya mini komai tsakaninka da matar ka ba, ammun ka sanar da ni dalilin barinta gidanka k0 da ba gaskiya ba ne ba.” Yayi shuru cikin tsananin tashin hankali, mahaifiiyarsa mace ce da ta san abin da ta keyi, ya sani ko ya gaya mata karya tana iya ganewa, amman takan yi kokarin nuna masa kamar ba ta san menene ya faru ba domin ba ta son takura masa a lokuta da dama, amman me ya kamata yayi ya ci gaba da yi mata karya da Boye mata abin da ya faru da shi a rayuwarsa kamar yanda ya sa ba yi mata don samun kwanciyar hankalinta, ko Ma ya gaya mata gaskiya wacce bai san abin da fadar ta zai janyo masaba. Amman ba shi da zaBi bayan fadar gaskiya, ya Kara gyara zama ya daga kai ya Kalmar, abu ne me nauyi da ba zai iya fada ba, sai hawaye kawai yake flta daga idonsa. Hajiyar ta fuskanci ko me ya yi mataba qarami ba ne, sannan kuma wani sirrin ne tsakaninsu da auran su, ko da ta matsa ta ji ba zai kasar da ita komai ba, don haka ta daga masa hannu sanda yake Kokarin fadi ya kasa. “Ya isa Abduljabar, na fahimci komai na, kuma ji dadi da Allah ya sanya kai ne -ka yiwa Hasna laifl ba ita ce ta yi maka ba.” Ya Kara kallonta da mamakin jin abin da ta fada, bai fahimci me take nufl da hakan ba. “Da ace itace ta yi maka laifl kuma ta fasa maka goshi, sannan ta tayar maka da hankali da ba zan yafe mata ba, amman da ya kasance kai ne ka yi mata harka fusata ta fasa maka goshi ban ga laifin ta ba.” Yanayin yanda ta ke magana shine ke qara tayar masa da hankali, har ya ji kamar Kasa ta tsage ya shige, tun mahaiflyar‘sa ba ta san abin da ya aikata ba kunyarta ta kama shi, to idan ta’ ji abin da yayi ya za ta ji a jikinta da rayuwarta? “Ka tashi ka tafl aiki kar ka yi latti, zan yi abin da zan yi domin ganin na mayar maka da Hasna gidan ka, sai dai k0 bayan ta koma ka kiyaye aikata abin da zai Kara fusata tabar gidan ka, kar ka zamto daga cikin mazan da ke azabtar da matansu, kar zamo daga maza azzulumai irin mahaifinka, idan har ka kasance haka baka yi mini adalci ba, baka kuma taya ni baKin ciki bisa abinda namiji yayi mini ba Abduljabar, dalilin da ya sanya na saka maka suna Abduljabar domin ka zamto namiji irinsa, mai kyawun hali da nagarta, ba wai ka zamto daga cikin mazan da ke cutar da matan su ba.” Cikin rawar baki ya yi magana “Ki yi hakuri hajiya…bazan Kara ba…na yadda na yi laifi, amman na miki alqawari indai har Hasna ta amincewa komawa gidana ba za ta qara samuna da irin abin data sameni da shi ba, ki yi hakuri.”………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button