ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

Na
FAUZIYYA D SULAIMAN

PAGE
3⃣3⃣

“Shike nan ‘komai ya wuce, maza tashi ka tafi gurin aikin ka, amman ka yi kokarin sanyaya fuskarka, ka dai na barin abin da kezuciyarka yana fita har ya sauka akan. fuskarka, kowa ya ganka yasan kana cikin damuwa a yanzu. ya yadda da abin da ta fada ya fahimci dalilin da ya sanya dalibai ke daridari’ da shi, sai yayi murmushi yana gyada kai .alamar to, ya tashi yayi mata sallama ya fltatana sanya masa albarka. Yau girkin Haj. Aisha ne macce ce ita da ke son burge mijinta da girkuna da kulawarta muddin yana gidanta, shi ya sanya idan bai tare da ita take kishi kwarai da gaske, don haka da ta idar da sallar asuba ta ke shiga kicin da kanta ta shiryawa mijinta abin da zai bukata kafin ya fita gurin harkokinsa, yau ma tun asubar tana kicin tana hada-hadar hada masa girkin mai aikinta na taya ta. Da a baya ne sai ta taso Hasna ta taya ta, domin komai da yaranta take yi, musamman idan suna gida ba su da makaranta, amman yanzu tausayin Hasna din ta keyi saboda. halin da ta ke ciki na damuwa da kuma cikin da ke jikinta, don haka idan tana bacci ba ta flye damun ta ba. Amman shigowar Hasna cikin shiri ya bata mamaki, a yanzu ta sauya rayuwarta k0 hoda bata sanyawa balle kwalliya idan ta yi wanka man shafawa kawai ta ke sakawa, ko dankunne ba ta sakawa, sai ta zura dogayen ‘riguna kayan ta kenan yanzu, domin takanas ta sanya Husna ta siyo mata su kusan kala ashirin su take shiga ta ke flta, ta zamto kamar wata mai takaba. Yanzun ma haka ta bayyana, Haj. Aisha ta kalleta tana murmushi sanda ta ke gayar da ita tana fadin “har kin tashi Hasna? “Na tashi Momy ina son na je asibitine, jiya na kwana cikina yana ciwo Haj‘Aisha ta tsareta -da ido akwai alamun bata yadda da abinda ta fada ba, Hasna ta yi dariyar basarwa. “Allah Momy da gaske na ke, babu inda zan je.”Haj. Aisha ta yi dariya tana gyada kai. “Ba yadda ne ban yi ba, sai dai ina tsoron kar ki aikata abin da kika yi niyya tun da farko.” ne Ranta. ya dan sosu, a zuciyarta ta ambata Husna munafuka, wato ita bata da sirri komai sai ta gayawa Momy ne, wallahi za ta gamu da ita, a fili kuwa shuru ta yi ta sunkuyar da kanta kasa. Haj. Aisha ta matsa ta dafa kafadarta tana magana cikin Kasa da murya “Hasna kada ki yiwa Allah butulci bisa baiwar da yayi miki, ni da mahaifin ki da abokiyar zamana ya kamata mu zamto miki darasi, tun bayan ku har yau Allah bai Kara bani haihuwa ba, ita kuwa abokiyar zamana har yau bata k0 taba yin Bari ba, duk inda mahaiflnku yasan ana bayar da wani abu don a haihu ya je amman Allah bai bashi ba, yayan mahaifinku kuwa tun bayan Abba har yanzu bai Kara samun k0 rabin mutum ba, hakan yana nuna muku zuri’ar ku ba masu yawan haihuwa ba ne, sai Allah ya taimake ki ya kai ki inda suke da yawan haihuwa, duk da Abdul shi daya mahaiflyarsa da mahaifinsa suka Haifa ke kuma sai gashi rahamar Allah ta sauka akan ki ta haihuwa, shin ba za ki yi godiya ga Allah ba Hasna? K0 da Abdul yayi miki laifi bai kamata ki yi fishi k0 ki huce takaicin akan baiwar Allah ba, ita baiwar Allah rungumarta ake yi da godiya da tasbihi.” Jikin Hasna yayi sanyi gaba daya, sai ta ji duk abin da ta kudurce a ranta ya zuba .komai ya fita daga kanta na shirinta “yanayin fuskarta ya nuna ta amshi nasihar: mahaifiyarta, Haj Aisha ta ci gaba da magana “Su‘ yaya rahama ne k0 da kin rabu da mahaiflnsu kin sake sabuwar rayuwa zasu zame miki gata watarana, ki duba ga ni , duk sanda mahaifin ku ya Bata mini rai idan na kalleku sai na ji farin ciki ya cika raina takaicina ya ragu, da ban haife ku bai da na shiga uku Hasna.” Ta daga kai da sauri ta kalli mahaifiyarta “Allah Momy na fasa, zan je. kawai a duba ni ne saboda ciwon cikin da na ke yi.” Haj.Aisha ta daga kai cikin gamsuwa tana fadin “Na ji dadin hakan, amma za ki iya tuqi kuwa da kan ki‘? Hasna ta daga kai cikin sauri “Me zai hana zan iya mana Momy.” A’a ban yadda ba, bari na kira driver ya zo ya kai ki, ki jira ni a falo yanzu.” Hasna ta yi kamar za ta yi magana amman Haj. Aisha ta daga mata hannu wanda ya sanya dole ta yi shuru, Haj. Aisha ta yi hanyar fita tana mata magana. “Kula mini da funkason nan bari na shiga na sanar da baban ki kada ya yi ta fada.” Bata jira jin abin da za ta ceba ta fice, Hasna ta bi ta da kallo harta fice sannan ta ci gaba da juya funkason, lokuta da dama idan ta tina Abdul da abin da yayi mata sai ta ji kuka ya cika idonta, yanzu‘ ma tana suyar fuskanson nan shi ta tina, .yana matukar son duk irin wadan nan abubuwan na gargajiya, hawaye ya zubo a idonta, daga Karshe dai Abdul ya ci nasara akanta, shi zai ci gaba da ‘ rayuwarsa yadda yake so ita kuma ta zama abar tausayi, ba ta komai na jin dadin rayuwa domin komai ba ya burgeta, ta daina kunna Ipad dinta, ta dai na whatsapp ta daina instgram ta dai na facebook ta dai na twitter kai komai ma ta dai na sai kwanciya kawai da tagumi, shike nan ita haka za ta Kare? Har kicin din mahaifinta ya shiga ya duba ta yayi mata sannu, sannan ya tambaye ta k0 ta sanar da mijinta za ta flta, ta kalli mahaifiyarta sannan ta kalli baban na ta cikin tsoro, da ta sanar da Abdul za ta je asibiti gwara ta hakura da ciwon ya kasheta, kamar ya fahimci abin da take ciki sai ya wayance yana fadin. “Shike nan, ki bari kawai zan sanar da shi, ga Amadun can yana jiran ki a waje.” Ta ji dadin abin da yace har ta yi murmushi, ta flce da gaggawa tana rike da ‘yar Jakarta, suka bita da kallo, sannan Haj. Aisha ta dubi Alh.Sammani tana magana. “Alhaji yarinyar nan fa ba ta da niyyar sauka, shike nan haka za mu zuba mata ido? Alh. Sammani ya kada kai yana fadin “A’a akwai abin da na ke shiryawa, jiya ma mun yi magana da Alh. Auwal, ki kwantar da hankalin ki, komai ya kusa, wucewa Insha Allah; Ambaton yayansa ya sanya ta ji wani Bacin rai cikin zuciyarta, yanzu shike nan matarsa ta ji halin da rayuwar ‘ya’yanta ke ciki? Amman ba ta so hakan ba, sai dai babu yanda za ta yi. A titi suna tsaka da taflya sai motar su ta fara jacking daga karshe ma ta fara kokarin mutuwa a tsakiyar titi, hakan ya sanya direban ya nufi agefen hanya, Hasna da ta yi tana cikin tinani ta farka flrgigit cikin mamakin dallin . tsayawarsu, ta fara tambayarsa; “Yaya dai Amadu me ya faru? Ba tare da ya kalleta ba ya fara bata. amsa. “Wallahi Hajiya ban san abin daya faru ba, lafiya Kalau na dauko motar nan, amman kin ga tsiyar Karfen nasara. Ya kammala parking ya fara Kokarin fita “Bari na dubata na gani.” Ya flce daga cikin motar ta bishi da kallo ba tare da ta ce komai ba sai ma jingina bayanta da ta yi jikin kujerar motar ta yi ajiyar zuciya. Kusan minti ashrin suka kwashe ba tare da yace mata komai ba, hakan ya. sanya ta bude motar ta fita tana tambayarsa. “Yaya Amadu har yanzu baka gano kan mOtar nan ba ne? Ya daga kai alamar eh “Wallahi ban gano ba Hajiya, na yi duk yanda zan yi amman na kasa ganowa, ina zaton dole sai mun kira bakanike.” Ta waro ido waje “Da wa? Ina bazan iya tsayawa ba, bari zan Karasa cikin Adaidaita sahu, ka je ka dauke ni idan kagama gyaran, bani nambar da kake amfani da ita yanzu.” Ta Ciro waya daga jaka ta fara Kokarin sanya lambar da ya ke gaya mata, sannan ta wuce da sauri ta fara qokarin tsayar da Adai-daitan. Suna isa asibtin dai-dai lokacin da Abba ya shigo asibitin cikin hadaddiyar motarsa, tari ne yake damunsa tsahon lokaci har yayi tsammanin tarin Tb ne amman Allah ya takaita masa wahala ba shi ba ne, amman an tabbatar masa da dai sai ya kula, wannan asibitin’ shéne asibitin gaba daya iyalansu kowa nan ya ke zuwa. Yana koqarin parkin sai ya hango wata kamar Hasna tana biyan mai Adai-daita sahu, mamaki ya kamashi ya fara Kokarin yin parking amman hankalinsa yana kan ta, Hasna dake Kakarin sauka daga motar haya, me ya sami mijinta da bai kula da ita har haka, ya fltO cikin gaggawa dai-dai lokacin da ta nufi hanyar asibitin, itace dai duk da ya kula tana cikin damuwa da rashin lafiya amman kamaninta ba za su sauya ba, sai ya bi ta da gaggawa yana kiran sunanta. Da farko ba ta yi zaton ita Hasnan ake kira ba, amman muryar da ta ji ta tabbatar~ mata da lallai da ita ake, k0 daga bacci ta tashi muryaI Abba ba za ta bace mata ba, shine, ta tsaya cak ta kasa waigawa sannan kuma ta kasa tafiya, Abba ya Karaso ya tsaya a gabanta yana dan haki yana kallonta. “Hasna…kece da gaske? Ta daga kai ta kalleshi da wani duba, Abba ya rame ya fita daga kamaninnsa kamar ba shi ba, gayun nan na sa duk babu, komai ya zame masa lami, ta yi kokarin Kakaro murmushi ta amsa da. “Eh ni ce, Yaya Abba ina kwana? Ba gaisuwar tata ya ke buqata ba. jin abin da yake damunta ya fi damunsa, don haka ya Kara wurga mata tambayar. “Me yake damun ki? Yaya kuma na ganki cikin motar haya, ina mijin na ki? Ta kasa cewa komai sai idonta da ya cika da kwalla, wai yau Abba ke tambayar mijinta, yanayinsa ya nuna matukar damuwa, har yanzu Abba yana kaunarta kenan, sai tayi Kokarin kakaro murmushi tana fadin. “Kar ka damu, babu komai direba ne ya dauko ni motar ta sami matsala, bari na karasa ciki.” Sai ta wuce da sauri, ya bita da kallo kamar ya fasa kuka, gabadaya Hasna ta lalace ‘ta jeme kamar ba itaba, me yake damun rayuwarta ne, tun da ta yi aure bai Kara ganinta ba sai yau, k0 gidan su ya je ba sa haduwa, k0 wata sabga ake yi cikin family ba ya bari su hadu, amman lokacin da Husna ta haihu har gida ya je mata barka bayan an watse zaman bakwai domin kar ya ga Hasna, rayuwarsa ta sauya gaba daya saboda’tunda suka rabu da ita, babu abin yayakeiyiai neman mata, wanda a yanzu ya daina boyema kowa a cewarsa tundaya rasa Hasna me zai boye kuma, babansa yana ‘cikin takaici da ’ bakin ciki musamman lokacin da ya gano mahaifiyarsa ta taka rawa gurin shigar da shi halin da yake ciki, don haka ya tattarasu ya watsar. Har ta Bacewa ganinsa yana tsaye° sai ya ji babu dadi cikin ransa, shin zai bita ne ya tsaya ta kammala k0 kuma zai je a duba shi sannan ya tarar da ita. ne Daga karshe ya yanke shawarar gwara ya fara zuwa ya ga likitan domin ya gargadeshi. akan kada yayi sakaci da zuwa ganin likita, cikin hanzari ya nufi gurin. Hasna ta na hangen Abba ya dade tsaye yana tinani, hakan ya tabbatar mata da yana son ta kammala ne yace zai maidata gida, ta roki Nurse din a dubata, ta kuma yi ~sa a babu layi da yake babban asibitin kudi ne kuma akwai likitoci da yawa da suke duba marasa Iafiya. A can gida Alh. Sammani ya kira Abdul kamar yanda ya fada ya sanar shi Hasna ta tatafi asibiti gaban Abdul ya fadI ya ji kamar yace ta jira ya. zoya kai ta, amman sai Alhajin ya gaya masa ya hada ta da direba, suka rabu yana godiya. A lokacin yana kan computer yana ta danne-danne sai ya ji ya kasa yin komai, yana son k0 fuskar matarsa ya kalla ya ji dadi, sai kawai ya ga gwara ya tafi asibitin da kansa, ya mike ya rufe ya nufi hanyar flta. Hasna ta kammala cikin sa’a ta fICe daga asibitin tana waigen motar Abba da ke fake, ta jima ba ta sami Adai-daita sahu ba, kasancewar asibitin yana cikin unguwar masu kudi,ne ababan haya ba su flye shigowa ba. Abba ya fito daga bangaran da ya shiga ya nufi Bangaran da Hasna ta ke ya fara nemanta amman bai ganta ba, daga karshe yayi tambayar ko ta tafl suka sanar da shita dan jima da tafia, cikin gaggawa ya fita. Cikin sa a ta hango wani Adai-daita ya nufo gurin ta tsayar da shi da hanzarce, da ‘ kyar ya tsaya, yana tsayawa ta shige cikin gaggawa. Irin ‘yan Adai-daitan nan ne ‘yan gadagada don haka cikin muryar qauraye yace Hajiya “Ina za a kai ki? Tana waigen waje ta sanar da shi inda zai kaita, yace sai dubu daya, kafin ta bashi amsa sai ta hango Motar Abdul ta doso asibitin amman ta daya Bangaran, gabanta ya fadl, ta tabbatar ita ya biyo babanta ya sanar da shi tana asibiti kenan, cikin fargaba ta fara magana. ~ ‘ “Malam mu je mana! “Ya za ki ce muje, bayan na ce miki dubu daya ba kice ~komai ba? “Muje k0 nawa ne zan baka! Ta fadi dai-dai lokacin da ta ga Abdul ya shige cikin ‘ asibitin. Abdul ya shigo cikin asibitin yana kokarin parking ya hango Abba yana waigewaige cikin asibitin, sai kuma ya ga ya nufi motarsa ya shiga, mamaki ya kamashi, kawai , sai zuciyar shi ta ba shi tare suke da Hasna, yana nan tsaye har Abba ya tayar da motarsa yayi hanyar fita, ya bi motar da kallo yana son ya gano wanda ke cikin motar amman bai iya gani ba, domin motar an rufeta da baqaqen gilasai. Zuciyarsa ta yi baqi ya ji wani kishi ya cika shi, mai ya sanya Hasna za ta yi masa haka, duk da ya yi mata laifi amman tana nannade da auransa bai kamata ta yi masa abin da ba ya so ba, sai ya kasa yin gaba balle baya, bai san lokacin da ya dauka cikin motar ta sa a zaune’ ba, ya dai tsinci kansa da kokarin tuka motar ya nufl gidan shi, ko ya koma makaranta ya san babu abin da zai iya aikatawa, k0 ya isa gidan ma sai dai ya Boye kansa, amman kafln ya tafl sai da ya kara gwada kiranta ba ta shiga ba kamar k0 da yaushe Abba yana barin asibiti kai tsaye gidan su ya nufa ya tarar da mahaifiyarsa zaune a falo tana kallo, yanda ta ganshi ya bata tsoro ta kalleshi tana magana. “Abba yaya aka yi na ganka haka? Laf‘iya, me ya faru ~ ‘ ‘ Abba ya zauna a kusa da ita cikin damuwa yana’ magana ~“Momy me ya yake faruwa da Hasna ne? ~ ” :Ranta ya: Baci jin ya ambaci sunan Hasna ta kalle‘shi da takaici tana fadin “Me ya faru ‘ka ke mini wannan’tambayar ?“Yanzu na ganta‘ a asibiti cikin wani i irin hali, yarinyar tana cikin damuwa, a cikin Adai-daita sahu fa na ganta Momy? Ta qara fusata “To sai meye don ka ganta cikin Adai-daita sahu, me ya sa ka ke son sanyakanka cikin abin da bai kamata bane? ” :“Momy Hasna Ce fa, Kanwata ce.. ya kamata idan ba ta’ jin dadin auran nan a raba, ko kuma a zaunar da ita aji abin da yake damunta.” -‘ Hajiyarsa ta yi tsaki “Don Allah ka raba ni da maganar mutanan nan, halin su ne ke bin su, ‘yanzu .haka tana gida tsahon lokaci domin auranta yana gab da mutuwa.” Abba ya waro ido waje cikin damuwa kamar wanda~ aka sanar da shi labarin mutuwa yana fadin “Momy Hasna tana gida? Duk kaunar da ta yi wa Abdul amman zai sake ta? “Ba laifln sa bane, kasan su ‘ya’yan mai ne, abin da suke buqata shi suke yi cikin rayuwarsu, sun sami daurin gindi daga gurin mahaiflyarsu, ita ce ta matsa akan sai ya sake ta, haka na ji baban ka‘yana fada.” Ta bashi amsa. “Wallahi Momy Hasna ba za ta nemi ‘ Abdul ya saketa idan har bai aikata mata wani mummunan laifl ba, na san Hasna na san ra’ayinta, ba ta yin sakaci ga komai na rayuwarta, amman zan shiga cikin maganar dole ne a kwatar mata‘ yancin ta. Yanayin yanda yake magana ke fusata mahaiflyarsa ta dalla masa harara tana fadin. “Kai yanzu ko kunya baka ji, ka gigice akan yarinyar da ta nunaba ta qaunar ka sai wani bare, me ya sa baka kishin kanka ne Abba? “Momy ba Iaifin ta ba ne, ni ne mai laifi, da na kasance irin yanda ya kamata da Hasna za ta iya kaunata watarana, amman zan taya ta kwatar ‘yancinta ba zan yadda a cutar da itaba.” Ya mike tsaye kamar wanda zai yi fada yana ci gaba da mita. . “Kai ba na son haukan banza, ban yadda ka sanya bakin ka cikin lamarin nan ba, idan ka yi Kokarin aikata hakan wallahi ranka zai Baci, idan kai baka san ciwon kan ka ba ni na sani, sakarai kawai.” Yanda ta yi maganar sai ya sanyayar masa da gwiwa ya kasa cewa komai, amman dai cikin ransa wannan kudirin yana nan bai kau ba, yayi alKawarin taimakawa Hasna, ba zai yadda bakin ciki ya kashe ta kamar yanda ya ganta dazu ba. Yayi hanyar fita, Hajiyar ta sa ta bishi da kallo tana tsaki da mita. “Haka kawai Aisha ta asirice mini da ta mallake mini shi, ni ban taBa ganin jaraba irin wannan ba, yarinyar nan ta yi aure amman ya kasa samun nutsuwa yayiwa rayuwasa abin da ya kamata, to wallahi ba zai yuwu ba dole na Kara daukar mataki akanta. . ABIN DA YA GAGARI KWANDILA… Bayan sallar La’ asar Haj. Aisha tana zaune da Alh. Sammani a falo ” yana kallon labaran C ..N N da glass a idonsa, , haj. Aisha tana gefensa hankalinta ba ya tare . da abin da yake yi, ta karkata ga tinanin ” makomar rayuwar diyarta, yanayin yanda Hasna ke kara shiga ya fara bata tsoro, damin abin na neman wuce hankali, yarinyar “ta zamto kamar wata mai tabin hankali, lokuta da dama takan kamata tana kuka da wasu irin surutai ga shi duk yanda za ta yi ta san abin da ke faruwa hakan ya gagara, tana son mmmdan na ta ya ta kalli mai gidan nata da alamar yin magana sukajiyo sallama kalli bakin Kofar shigowa dakin, Hajiya Falmata ce tana rike da hannun Sadik wanda aka gyarashi gwanin sha’awa. Haj. Aisha ta mike da sauri cikin jin dadi tana mummushi. “A’a Hajiya sannu da zuwa, lale marhabin.” Hajiya Falmata tana murmushi cikin jin dadi ta amsa, shi ma Alhaji Sammani yana murmushi yake mata sannu da zuwa, Haj . Aisha ta suri yaron tana dariya gami da tsokanarshi. “Maigidan da babu cefane balle zanin sallah.” . Suka gaisa ~gaba dayansu, Hajiya Aisha ta nuna mata kujera tana fadin “Bisimillah hajiya zauna mana.” Hajiya Falmata ta zauna tana murmushi, Alh.Sammani ya .dan zame daga kujerar da yake ya gayar da Haj. Falmata, duk da ta girmeshi amman sai ta ji nauyin yanda yayi mata, darajar gidan ta Kara karuwa cikin ranta ta amsa itama a mutunce, page 87 is missing plz kuyi haquri zuwa wannan lokacin ba mu san abin da ya hada yaran nan ba, anan gurin na lura da ‘ su, akan su sanar da ni abin da ya ke faruwa tsakanin su amman yaran nan sun qekashe kasa sun Ki fadin komai, ba na son na ji din ma yanzu, domin akwai sirrin da ya kamata ace na ma’aurata ne su kadai wannan bai shiga ba, shi ya sanya ban matsa musu akan lallai sai sun sanar da mu ba, muna fatan Allah ya dai-daita lamarin.” “Amin summa amin Haj.Falmata ta amshe ta dora da roqo. » “Idan da hali ina son ganin Hasna din.” “Me zai hana, hajiya kira mata ita mana.”Alh. Sammani ya fada yana kallon Haj. Aisha, ta yi saurin mikewa, suka ci gaba da tattaunawa da Haj. Falmata da Alhaji sammani. ‘ ‘ Wannan karon tana zaune akan sallaya tanata lazumi ba ta san adadin abin da ta ambata na sunan Allah h ba a yau, domin ta ta kula iyayanta ba su da niyyar amincewa ‘ rabuwarta da Abdul. Haj.Aisha ta shigo dakin, ta jima tSaye akanta tana kallonta sannan ta yi mata magana. “Hasna! Hasna ta jiyo da sauri ta kalli mahaiflyarta tana kakaro murmushi na Kokarin nuna bata cikin damuwa kamar yanda ta saba, sai dai abin da ba ta sani ba, ko ramar da ta ke yi kadai ta isa ta bayyana hakan. , “Hajiyar Abdul ta zo tana falo, tana son ganin ki sai ki tashi ki je.” . Gaban Hasna ya fadi, Haj. Aisha ba ta saurari jin abin da Hasnan za ta ce ba ta fiCe, Hasna ta ji kamar ta fasa kuka, domin tana jin matuqar nauyin sirikarta, ta jima kafin ta yunkura ta flta daga dakin cikin fargabar abin ‘ da zai faru. Ta tadda su suna ta hirarsu, ta Karasa ta zauna tunda ta fito Haj. Falmata ke kallonta har ta karasa ta durqusa ta gaishe, ta ta amsa cikin sakin fuska, Sadik ya tashi da gudu ya nufl Hasna ya zauna akan cinyarta yana mata gwarancinsa. Gaban Haj. Falmata ya fadi kwarai da gaske saboda ganin yanda Hasna ta koma, sai ta rasa me zata ce domin kunya ta baibayeta bi sa ganin laifin dan ta muraran, ta tabbatar da wasu iyayan ne da tini sun kashe wannan auran, amman da yake dattawan arziqine suke bin abin sannu a hankali, sai da ta jima sannan ta fara magana. “Hasna na zo na baki haquri ba don Abduljabar ba, sai don darajar zuri’ar da kuka fara Tarawa,_ bana son na ji abin da ya hadaki da shi, amman na miki alkawarin k0 me ya faru ba zai Kara faruwa ba Insha Allahu.” Tausayin Haj. Falmata ya cika zuciyar Hasna sai ta fashe da kuka, ba ta san waye dan ta ba shi ya sanya ta amince da shi dan’ bi sa dari, me ya sanya Abdul ya cutar da wadan da suka yadda da shi suka amince da shi, lallai idan Haj. Falmata ta ji abin da danta ke aikatawa zuciyatta za ta buga ta mutu. Haj. Falmata ta ci gaba da roKon Hasna da tausasan kalamai amman Hasna ta kasa cewa komai, Sadik sai shafe hawayen mahaifiyar ta sa ya ke yi yana gwaranci da surutai, hakan’ya Kara karya zuciyar Hasna da duk wadan da ke. falon. Alh. Sammani ne ya daga mata hannu yana fadin “Hajiya ya isa haka, Hasna za ta koma gidan Abdul Insha Allahu, ku yi hakuri.” , Wannan kalaman sune suka sanyaya mata rai, amman a Bangaran Hasna kuka sukakuma saka ta, domin ta yiwa kanta alqawari ba za ta koma gidan Abdul ha har abada, sannan ba za ta iya musu da mahaifanta ba, Haj. Falmata ta ci gaba da lallashinta har ta taji ranta babu dadi, sai da Alh. Sammani ya tabbatar mata da ‘gobe Hasna za ta koma gidan mijinta Insha Allahu kar ta damu, sannan ta yi sallama ta tafi amman zuciyarta ta mutu, anan tabar Sadik domin ya fara bacci, Haj. aisha ta kai shi dakinta. Bayan ta koma gida ta kira Abdul a waya tan son ganinsa, bayan ya je gidan ta kare masa tanadi tsaf, shi dai ya yadda ya amshi komai, fatan shi Hasna ta -koma gidansa ta saurari bayanin da zai mata k0 da ba ta yadda da shi ba yana son ya wanke kan ._ shi ta dai na kallonsa da irin kallon da ta ke y i masa a yanzu, don haka haquri kawai yayi ta baiwa mahaiflyar ta sa. A gidan su Abba tsare mahaifinsa ya yi da maganar Hasna, abin ya baiwa Alh. Auwal mamaki, amman ya san soyayyar da Abban _ ke yi wa Hasna ce ta kawo hakan, ya kuma ji dadi don haka yace ya ta shi su tafi gidan su Hasnan, daman yau zai ga dan’uwan na sa. Sun isa gidan lokacin Alh.Sammani shi -.daya ne a falon, Haj.Aisha ta shige dakin ta suna ta waya da Husna. Alh. Sammani yayi mamakin zuwan yayansa domin ba su jima da yin Waya ya tambaye shi inda yake ba, musamman da ya gansu tare da Abba, bayan sun gaisa Alh, Auwalu ya fara tambayarsa halin da ake ciki game da matsalar Hasna. Alh.Sammani yayi masa bayanin komai har zuwan Haj.Falmata da shawarar da ya yanke yanzu saboda ganin halin da mahaifiyarsa ta shiga. Alh.AuwaI ya yaba kwarai da gaske da hukuncin da dan’uwansaya yanke ya dora da cewar shima abin da ke ransa kenan. Abba hankalinsa ya tashi ya kallesu cikin ladabi, domn duk halinsa yana matukar girmama iyayan na sa ya fara magana. . “Baffa don Allah idan dahali zan ce wani abu.” Gaba daya suka kalleshi da mamakin jin abin da yake son fada, Alh. Sammam’ yace “Muna jinka Abba, menene abin da zaka fada? Abba ya gyara zama yana ci gaba da magana “Baffa bai kamata saboda damuwar wasu a matsawa Hasna ta koma gidan gayen nan ba, ya kamata a tsaya aji abin da yayi mata tana da matsalafa Hasna ni na ganta na kuma ga halin da ta ke ciki, kar ku yi haka don Allah Baffa.” Alh.Auwal ya amshe cikin Bacin rai “Ka ji sakarai da bai san menene rayuwa ba, kasan illar da mutuwar aure ke haifarwa ma’aurata musamman Hasna da ta kasance mace me dauke da ciki qarami, kasan illar da hakan za haifar ga rayuwarta? Jin kalaman ciki da Hasna ta ke da shi ya fadar da gaban Abba,daman cikene da ita, duk da haka bai kamata ace an tilasata mata ta yi abin da ba ta Kaunar yi ba, amma fin karfinsa da iyayan suka yi ya sanya yayi shuru da bakinsa, domin babu yanda zai yi. Alhaji Auwal ya sanya aka kira masa Hasna yayi mata fada gami da nasiha akan abin da ya faru, ita dai sauraran su kawai ta ke yi amman zuciyarta kwata-kwata ba ta tattare da su har suka kammala nasiharsu, fatanta dai ta koma dakinta ta samarwa kanta mafita. ‘ Tun da ta shigo Abba ke kallonta, da akwai abin ,da zai iya yi don ganin ya f1tar da Hasna daga wannan kangin da yayi, a zuciyarsa yana jin ciwon halin da ta ke ciki matuka, ita kuwa tun bayan gaisuwa ba ta Kara daga kai ta kalli kowa ba a gurin, a gabanta mahaifinta ya kira Abdul ya sanar da , shi gobe da safe ya shigo ya dauketa sannan suka bata damar tafiya. . , Da ta shiga dakinta sai ta ji kamar ta rataye kanta ta huta, k0 dai za ta koma ta sanar da mahaifanta abin da Abdul ya aikata mata, tabbas tonuwar asirin Abdul ne kadai abin da zai fitar da ita daga masifar komawa gidansa, sai ta ji ta aminta da shawarar da zuciyarta ta sanar da ita, don haka ta nufi hanyar flta cikin gaggawa,domin da ta yadda ta koma gidan Abdul gwara ta aikata komai. Har‘ lokacin Alhaji Auwal bai tafl ba yana nan suna tattaunawa da dan’uwansa, ta sanya kai za ta shiga falon kai tsaye sai ta ji kamar an kwala mata kira daga bayanta, ta waiga da sauri tana waige-waige faduwar gabanta ta Karu sai ta ji kamar tana shirin aikata wani mummunan abu ne da zai shafi rayuwarta, ta tina Abba ma yana gurin, ya , kamata ta sanar da su abin da Abdul ke yi? Idan sun yadda sun kashe’auransu yaya kuma za su kalli ‘ya’yanta da cikin da ke jikinta, sai ‘ ta ji ba za ta iya ba, ta juya da sauri tabar ‘gurin ta koma dakinta, abin mamaki mahaiflyarta ta tarar a gefen gadonta, gabanta ya yanke ya fadi, amman haka ta daure ta Karasa ta zauna. “Ina ki ka shiga ne Hasna? Tambayar da mahaifiyarta ta yi mata kenan, ta kasa bata amsa sai zama kawai da ta yi, ba ta Kara yi mata wata tambayar ba ta shiga lallashinta da ba ta baki, kusan abin da mahaifanta da yayansa suka fada shi mahaifiyar tata ta kara fadi don haka ba ta ji komai ya shiga ranta ba bayan irin abin da taji a dazun, sun jima tana lallashinta da sanar da ita labaruka kala-kala na wasu ma’auratan ga yanda suka ji dadin auransu bayan sun yi haKuri, a cikin ranta take fadin ba za su gane ba, da wani abu Abdul ya aikata ba wannan ba za ta iya hakuri amman wannan kam ba za ta iya ba. Yanayin yanda mahaiflyarta ke magana sai ya dinga darsa mata wani abu a cikin ranta, tana jin kamar suna sallamar bankwana ne, don tana ji a jikinta kamar karshen rayuwarta ne ya zo KOWA YABAR GIDA… da safe Haj.Aisha ba ta damu da shiga gurin diyarta ba sai shirya mata kayan da za ta tafl gidan mijinta, dasu take: Alh.Sammani ya tanadi abubuwan da damana burgewa. A Bangaran Abdul kasa bacci yayi sai gyaran gida da tsaftace ko’ina yake yi, duk da baya wata shararriyar murna da dawowar matar ta sa, domin yana matuqar jin kunyarta. amman yana jin dadi a ransa yanda ta rufa masa asiri duk da irin siradin da ta shiga, don haka kafin gari ya waye gidan ya fita fes-fes, bai son yi musu sammako don haka ya dan shiga makaranta domin ya Karae da wasu lokutan acan. ‘ Husna ta zo wajan goma na safe da shirin raka ‘yar’uwarta gidan mijinta, sai da suka fara kebewa da mahaiflyarsu suka tattauna sannan ta nufl dakin Hasnan. Ba ta dakin amman bandakin a kulle yake hakan ya tabbatar mata da tana ciki, ta fara karewa dakin kallo cikin takaici da mamakin yanda Hasna ta koma, komai ya fita daga kanta, wai wannan ne dakin Hasna ba gyara babu qamshi, sai ta fara addu’a cikin ranta da rokon Allah ya sanyaya zuciyar ‘yar’uwarta, ta jima zaune tana jiranta amman har mintina kusan goma suka Kare ba ta ji ta fito ba, sai ta mike tana kwala mata kira ta nufi bandakin ta tura Kofar bandakin sai ta ganta a bude kuma babu kowa, gabanta ya fadi ta juya da sauri ta bar dakin ta nufl Bangaran mahaiflyarsu tana tambayarta inda Hasnan ta tafl, Haj. Aisha ta mike cike da mamaki tana tabbatar mata da tana cikin dakin, Husnan ta sanar da itaba ta nan, sai suka dunguma suka kara komawa cikin dukin, duk duban da suka yi ba su ganta ba hankalin su ya tashi su ka fara nemanta da kiran wayarta, amman dukkan wayoyin ba sa shiga, Husna ta duba gun’ da Hasna ke ajiye kayanta amman babu rigunan da ta siyo mata, ta kalli mahaifiyar su cikin tsoro tana fadin. “Momy kar fa ace Hasna guduwa ta Kinga babu kayan da na sai mata, sannan kuma wayoyinta da ipad din ta duk ba su dakin nan, anan gurin ta ke ajiyewa gashi babu komai na ta.” Hankalin Haj. Aisha ya Kara tashi ta yi hanyar fita cikin damuwa ba tare da ta ce komai ba, Husna ta bi ta da kallo sai ta Kara danna wayar hannunta, abin da ake fada tun da fari shi ake ci gaba da fada ta tafa: hannu cikin damuwa tana salati. “Innalillahi’ wa ’inna ilaihi raji’ un, ina kika shiga Hasna ina ki ka je, kar ki cutar da rayuwarki da cikin jikinki don Allah? Sai ta fashe da kuka. Haj.Aisha ta tura kai dakin Alh. Sammani wanda ke aiki akan computer din sa, yanayin yanda ta shiga babu k0 sallama ya ja hankalinsa ya kalleta da mamaki yana magana “Yaya dai Aisha laflya? “Ta gudu! Ta gudu tabar gidan Alhaji? Ya mike cike da mamaki amman bai fahimci abin da ta ke son gaya masaba, don haka ya mayar mata da tambaya a rude. “Wacece ta gudu Aisha? “Hasna mana, ta gudu tabar gidan, shi ya sanya nace kar a matsawa yarinyar nan, Allah ya sani hukuncin da aka yanke bai mini ba, amman anfi Karfina na ne kawai.” “Kin ga kwantar da hankalin ki Hasna ba za ta yi haka ba, ba za ta gudu tabar gidan nan ba, watakila ta tafl wani guri ne, bari na kira wayarta.” Sai ya fara daddanawa wayarsa alamar kiran Hasna, Haj.Aisha ta bishi da kallo kawai tana kada kai cikin takaici domin ta tabbatar Hasna ta gudu, har ya kammala kiran wayar ba ta shiga ba, hakan ya daga masa hankali ya fice da sauri daga dakin, ta bishi da kallo cikin takaici. Abu kamar wasa sai karamar magana ta fara neman zama babba, duk inda suke tinanin Hasna za ta je sun buga waya amman ba a same ta ba, wannan shine abu mafi muni da ya taba faruwa cikin rayuwar Alh. Sammani, me ya sanya Hansa ta gudu daga gidan shi, k0 lokacin da zai mata aure da Abba bata gudu ba amman . me ya sanya ta gudu yanzu? Shine abin da yake ta tambayar kansa, Husna kam ta kasa zaune ta kasa tsaye, sai kawai ta fada dakin ta ta fara binkice k0 za ta gawani abu, abin mamaki sai ga takadda akan receiver da ke cikin dakin ta dauka da sauri ta bude, rubutu layi hudu ne a takardar amman me tayar da hankali.‘ “Ban bar gida don na bakanta muku ba, sai don na baku damar yadda da abin da ke cikin raina na rabuwa da Abdul, idan kun amince zan dawo! Shike nan abin da ta rubuta, Husna ta fice da gaggawa tana kwalawa mamansu kira, a falo suka ci karo Haj. Aisha na shirin fitowa ta mika mata takaddar, haj Aisha ta karanta ta fara yiwa Alh. Sammani bayani wanda ya Kagu ya ji wani abu ganin yanda Husna ta shigo a gigice. LoL INA HASNA TAJE ?? OHO MUJE ZUWA ASHA KARATU LFY………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button