ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

PAGE
0⃣6⃣

Wasu samari suka kuma binta da ihu da fito na tsokana dukda abinda yayi yama hasna dadi amman bataji dadin ihun da ake musu ba ta kalli husna da sanyin jiki banji dadin abinda yayiba sister husna ta vata fuska gamida fadin hakane daidai ga ma,abota shishshigi da karambani tashi mu bishi a kan maganarki ta dauki jakarta tai hanyar fita jikin hasna yai sanyi sai take ganin kamar da ita yar uwar taya take amman saita dake ta dauki jakarta ta rufa mata baya a office din DR Abduljabbar suka tsaya daga bakin kofa suna kwankwasawa daga ciki suka jiyoshi yana yes come in husna ta kalli hasna kafin ta tura kofar tace saiki shiga cikin nutsuwarki naga sai wani rawar jiki kike kindaifi kowa sanin halin mutuminnan Kunya ya kamata ganin yar uwar tata ta gano abinda ke zuciyarta sai tayi kokarin gayyato dakiya da dauriya ta sanya ma zuciyarta husna ce a gaba don haka ita ta tura kofar suka isa ciki yanata danne danne akan laptop dinsa bai daga kai ya kallesuba husna ce tai karfin halin yin magana sannu da aiki malam Yauwa ya amsa a takaice yaci gaba da danne dannensa suna tsaye kusan minti biyu sannan ya dago sorry ina dan saving din wani aikine idan na bari zai iya bata wannab karon ma husna ce tai magaba babu damuwa malam kuna buqatar wani abune ?ya katse zancen ta hanyar tsaresu da fararen idanuwansa daradara wadanda ke firgita yanmata kai harma da samarin malam daman akan maganar sister dina da mukai dakai ranar da mukai gwajin test ne wacce nace maka bata da lfy Ya daga kafada to na tuna amman ita bata magana ne? Yana maganar yana qarema hasna kallo wacce duk ta dimauce cikin hanzari tace a,a malam ina magana yayi dan murmushi kamar bashiba yace ok yanxu yaya kukeso ayi?suka kalli juna da mamaki sannan hasna tace a,a malam ai duk yaddah kace ayi haka za,ai yace ok keda kikai kwajin zaki iya tafiya ke kuma da bakiyiba zaki iya komawa ajin ki bada sanarwa ga duk wanda baiyiba ya shirya nanda minti goma zan iso nai muku idan babu malamin dazai shigo muku wani irin dadi ya cikasu har suke ganin kamar bashiba ya maida kansa yaci gaba da danne dannensa hakan ya basu damar ficewa a waje husna tace sister kodai kin shiga offis din mutuminnan da wani fahamine bansaniba Cikin farin ciki hasna tace wlh ban shiga da komai ba saidai ko kwalliyatace ta tafi dashi husna ta kada kai banajin haka donda hakane da dazun baimasu …..wulaqanciba amman dai mubar wannan maganar yi maxa kije ki bada sanarwar tun dalibai basu gama watsewa ba ta dau hanyar tafiya hasna tai tsaye dajin dadin abinda ya faru wacce irin sa,a ce da wannan rana ta yau amman dai bari naje na sanar kada daliban su gama watsewa Kowa yai mamakin maganar tata aka dinga juya maganar da mamaki wadanda sukai a baya basu sami maki da yawaba suka sake zama wai dole su sami maki da yawa ana cikin haka ya shigo ya qarema ajin kallo sannan yace dukkan wanda yasan yayi waccen Basaiya sake yin wata ba. don idan na ga lamba iri daya sau biyu kayi asarar dukkan makin har na jarahawa ma. don haka wanda ya san ya yi ya fice salin‘alin”. Daya bayan daya.da1iban suka dinga ficewa, sai ga su basu wuce su goma sha shida ba, ya yi murmushi. sannan ya juya ya fara ruhutu jikin farin allon dA makarsa. A yau kam har wanda suka fara rubutu kafin ya bada umarni ya gani, amma bai yi kora ba sai gargadi kawai da ya yi musu. wannan abin ya bawa daliban mamaki mutum sai ka ce mai mutanen boye yanzu Ya gama bori yanzu kuma yazo yana abin arziqi, da alama yana da aljanune, abin da wasu dalibai suka dinga fade: ke nan. ga hasna cikin farin ciki da jin dadi ta‘yi gwaji (test) dinta. tana kuma da qarfin gwiwa da yakinin zata Hakan kuwa aka yi, bayan ga raba makin gwajin ta samu irin makin da take bukatar samu. tana gani ma ta fara samun shiga da matsayi mai girma a zuciyar Dr. Abduljuhhar. duk da bai taba nuna ya ganeta k0 ambaton sunantaba Amman dan abinda yai mata ya sanyata jin dadi Kwanaki sun tafi kamar gudun tsere su hasna harsun fara jarabawar zango na farko wanda ya rage musu sauran jarabawar zango daya su kammala karatun nasu wanda baida spill over ya sanya ran tafiya bautar qasa wanda kuma yake dashi ya tsayaya gyara harya samu yaci hasna tana daya daga cikin dalibai masu fata da buri domin ta karantu a wannan zangon musamman a course din DR Abduljabbar tanasaran zata sami point masu yawa sanda aka qare makin jarabawa jikinta har rawa yake akan taje ta duba duk ta isa yar uwarta da mita akan su isa makaranta da wuri domin suje su duba wajen ya cika da dalibai sai dubawa ake masu murna nayi masu cizon yatsa nayi Husna ta gano nata ta fasa ihu gamida rumgume yar uwar tata da murna hasnama dadi ya cikata domin tasan duk abinda yar uwar tata zataci sai nata yafi don kowa yasan tafi husna kokari “Dan Allah ki sake ni karki kayar dani. ki bari na duba nawa mana”. ‘ Ta yi’ wa husna magana ‘dake Kokarin kayar da ita. Husna ta sake; tana fadin. “Dadi ne ya yi mini yawa, bari na taya ki duba miki Suka cigaba da laluben lambar kasancewar kowa ya san lambar kowa. Husna ce ta gano ta nuna mata da hannu Laaa ga lambar nan”, Sukaci gaba dabin. ayyukan ahankali cikin murna da jin dadi. kamar yadda tayi hasashe hakan ceta faru sai dai me Suna zuwa kan darasin Dr. Abduljabbar suka tsaya turus cike da mamaki da fargaba. Hasna Ce ta fara magana da fargaba. “Sister. duba min point din nan. haka ne yadda nake gani k0 kuma ida nuna ne ke mini gizo”. Husna ta janyo hannunta tana fadin Zo Muje muje ina ki tsaya kimin batani mana hankalin daliban ya fara dawowa kansu abinda ya sanya husna ta janyeta da qarfi kenan tana tirjewa haba hasna me kikeson jama kanki cikin dalibaine kina ganin kowa yaga nasa jan bakinsa yake yai shiru sai kece za aji kanki ammanfa point dindaya bani na qaryane yayama za,ai yaimin haka yana nufin na sami carry over course dinsa kenan dukkan karatunda nayishi shikenan ya tashi a banza kenan husna ta rirriqeta tana qoqarin toshe mata baki haba sister kibi a sannu ba qarshen rayuwarki kenan ba ta kubce daga riqon datai mata cikin qarfi idonta ya fara zubda hawaye ranta ya gama baci tace koba qarshen rayuwataba kenan qarshen farincikinane maiya sanya zaisanyamin haka don ko,a C.A dina yafi abinda ya sanyamin wlh bazan yardaba gwara nayi asarar karatun gaba daya mai ya sanya ya tsanenine mai nayi masa Husnu ta Kara matsawa gabanta da lallashi. Tana son qara ruko hannuwanta “Ki kula hasna bake kadai ya tsanaba, watakila ma‘bai san kebace ba. dan Allah ki‘ dawo. .cikin nutsuwarki”. . “Ba zan dawo ba idan har ban sami Dr. Abduljahbar na gaya: masa abin da ke raina ba mutuwa zanyi. jinina ya hau fiye da yadda ya hau a baya. ki bammrni kawai”.., Ta juya da sauri ta nufi hanyar Ofis din Dr. Abduljabbar. Husna ta bita tana lallashinta amma ina sam taqi saurarenta har suka isa bakin kofar ofiss din. Husna ta riqota da sauri Cike da fargaba. “Hasna. kin san me kike; shirin yi kuwa‘.’ Kin san abin da zaki janyo wa kanki’.”’ “Na sani mana. Za a ce an koreni a makaramar nan. k0 kuma an dakatar da ni. Hakan yafi min sauKi da a ce na mutu da ciWon zuciyar tsanar= abinda malamin nan ya yi mini Ki sake ni nayi hakan idan ba hakaba Zan mutu sister Yaddah take kuka wiwi ne ya firgita yar uwar tata ya sanya ta saketa gara ace tayi asarar digreen nata da ace tayi asarar ta Tana kallonta ta nufi ofis din a fusace ta banka kofar va tare da ko sallamaba , Dr. Abduljabbar yanata danne-danne a kan laptop dinsa yaji an bankado kofarsa babu ko sallama a ka’idarsa k0 vice; chancello ne zau‘shigo sai ya nemi izni. ,Ya mike a fusace da karaji. . “Wane.mara mutuncinne haka MAmaki ” da‘ takaici ya Kara cika fuskarshi sanda Hasna ta bayyana cikin gadara da Bacin, rai tace nice nan Ya kada kai da mamaki. “Lafiyarki? Kokinyi hauka ne ki shigo min ‘office babu sallama balle neman izini Wacece ke?” “Ni mutum ce wacce ubangiji ya karrama ta bashi amsa a taqaice Meya sanya zaki shigomin office haka kai tsaye Ya kuma fadi da Bacin rai. Ta yamusa fusku. Tace “Don jin dalilin ‘daya sanya ka tsane ni hara kayar dani a course dinda da jama a da dana suka tahbatar da naci. Amma da yake‘ kai macuci ne. Azzalumi. mugu ka kayar -dani “Ke yarinya ki gyara bakinki. ki kula da: abinda kike fadi kin Sam wayeni kuwa‘.” Ya fadi a fusace yana huci kamar zai hauta da duka “K0 waye kai baka da abinda zaka iya mini baya da kasanya a koreni idan kuwa har bakai hakan ba kai ba dan halak bane na dainajin tsoron mutum azzalumu macuci irinka . Tana maganar tana, kuka tana wurga hannaye tamkar zata kamo shi ta rufe shi da duka Ya yi kasaqe yana kallonta yama rasa me ya dace yayi mata;shi’ba ’abin ya rufe ta da duka ba bazai iyaba macece. amma amman yayi qoqarin nuna mata qofa ” Please get out Ta kuma rushewa da kuka baxan fitava saika sanar dani dalilin tanarka gareni Ka gaya mini mai nayi maka ka tsananeni Ya gyada kai yana huci kamar wandn yayi tseren gudu. “OK zanbar miki offis dinni. Amma ki sani baki yi min rashin kunya-a banza ba ; zaki san “wa kika xaga. Sannan zaki biya dukkan abin daya salwantu cikin’ offis din nan”. Ya hada kayansa da nufin barin Offis din. Itama ta durkushe a gurin tana gunjin kuka kamur ranta zai~ fita harya kammala hada kayansa ya nufu kofar fita ransa a bace bai Kara kallon inda ta keba. Ta bishi da kallon bakincikin rashin kula ta din da baiyiba ta kuma fashewa da kukan Husnu dake bakin Kofar a tsaye cike da tashin hankali tana jiyo duk abinda ke faruw ta dafe kanta tana zubda hawaye ta shiga uku itakan da halin ‘yar uwar nan tata. “ – Dr Abduljubbar ya fito daga offis din a fusace yana huci bai kula da Husna da ke tsaye ba ya wuce Yana wucewa Husna ta fada ofiis din da sauri. jikinta yana rawa. Ta tadda Hasna durkushe tana kuka. Ta kamo ta da sauri. “Tashi mu tafi. kin fadi abin da ya dace ki fada daina kukan haka”. Babu musu ta miqe suka nufi kofar fita tana kokarin rage kukanta. Suna fita Husna ta janyo kofar ofis din sannan ta nufi gurin Hasna dake tsaye ta kalleta da mumaki ganin tana murmushi tana kada kai. “Murmushin me ki keyi Hasna. kokin fara samun matsa a kwakwalwarki’.ne Ta Kara kada kai, “K0 daya, naji dadi cikin raina ne kawai. domin na rama dumbin baqin cikin daya jima yana sanya nine‘ Bani da sauran haushi ko yau na bar mukarantar nan burina ya cika”, Husna ta kada kai. Tace”Amma baki wani abu zai furu idan wannan maganar ta kai gusu Daddy ba?” Hasna tai shiru tana kada kai ta kasa cewa komai domin ta fara dawowa hayyacinta “Ba xan fadi komai a kan dukkan abin da ya faru ba zan rufa miki asiri sai dai zan kasance cikin baqin ciki idan akace kin rasa karatun da muka jima muna yi. dare da rana safe da yamma.. Amma kumai ya tashi a banxa Husna ke magana cikin sanyin murya. idanta yana zubda hawayen baqin ciki ganin hasna batace komaiba Ganin Hasna bataa da niyyar yin komai ya sanya Husna ta kama hannunta suku fara tafiya kamar makauniya da’yar jagora. “Z0 mu tafi”. Kai tsayea Bangarensu suka nufa a hanyar shiga suka ci karo da Fatima ta fito a gigice suka kalle ta da mamaki da fargaha. Husna ‘ce tayi kokarin yin magana. “Ya ya dai Fatima. me ke faruwa ne na ganki a gigice Fatima tayi ajiyar zuciya tana yarfe hannuwa. ‘ ‘ Bakuji abinda ya farubava DR Abduljabbar ne ya fadi kunsan ance yanada matsala a zuciyarsa idan ransa ya baci yakan fadine gaba daya suka waro ido da fargaba Husna ce ta kuma yin magana. “Subhanaklahi: yana ina yanxu?” “Can zan karasa inda akace yake. kuzo muje hasna ta dage tana kallonsu. “Ni kam babu inda zani sai kun dawo Suka kalle ta kamar su myi magana. sai kuma suka fasa suka nufu gurin da sauri. Sanda suka isa ana ta kokarin sanya shi cikin ambulance. babu alamar numfashi a jikinsa. Hankalin husna ya kara tashi. daliban kuwa sai ‘yan Surutansy suke yi. wasu na cewa. Allah ya ba shi lafiya. wasu kuma na fadin. “Allah ya kara, Ubangiji ya sanya ya tafi kenan, yau ai ya ji kamun Allah. Ita dai Husna sai zare ido ta keyi, har lokacin da ta ga tashin motar. Ta juya a gigice ta Nufi inda tabar Hasna. Can gefen wata hall ta hango ta tana zaune ta hada kai da gwiwa. da alamun tayi zurfi a tunani. Ta isa kusa da ita da sauri ta kamo hannunta. kasancewar, gurin akwai mutane da ke zaune a gefe wasu kuma na kaiwa da komowa. Hasna ta bita babu musu tamkar rakumi da akala har suka isa can baya inda babu wadatar dalibai sannan ta sake ta, tana huci kamar wacce tayi tseren ‘gudu ta fara magana “Husna kin san abin da ya faru kuwa? Kin san abin da kike Shirin ja mana‘.’ Wallahi idan Abduljabbar ya mutu ba keba hatta ni na shiga’ uku. Yana can, babu alamun numfashi a tattare da shi. ina jin tsoron faruwar wani abu”. ‘ Hasna ta yi yake wanda aka: ce yafi kuka ciwo. Tana fadin, “Ban damu da kome_ ya same shi ba, dukkan halin da ya shiga ‘nima na shiga irinsa. Shi bai ma san na shiga ba. ‘ni kuwa na sani, don haka can ta matse masa tunda na san bani na kashe shiba………………

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button