ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????

PAGE
0⃣8⃣

ne amma dai ya kamata ta kai shi gurin da zai zauna. k0 me zai faru ya kasance cikin sirri. Ta fara tafiya tana fadin “Zo mu karasa dakin baki”. Bai yi musu ba ya bi ta zungwi-zungwi tamkar rakumi da jela,yana ci gaba da kare mata kallo hatta tafiyarta ma daban ce da ta sau’ran mata. Ita kam duk ta tsargu. sauri ta ke yi su isa inda‘ya dace ya zauna. har suka isa ta bude kofar ta shiga ta nuna masa kujera. “Ka zauna a nan ina zuwa” Ta nufi wata Kofa da sauri, ya bita da kallo yana kada kai, ya kula har yanzu bata fita daga shock ba. ya dan fara karewa falon kallo Ginin gidan masu hali ne. kuma ‘yan boko, hotunan Hasna da Husna da ya cika falon neya» tabbatar masa da .su kadai‘ne a gurin mahaifansu, sai kuma babansu da mahaifiyarsu‘. ya dinga kallon komai da sha’awa da nishadi. Hasna ta shiga’ falon ta wata kofa ba wacce ta fita ba da gaggawa. mahaifiyarta da Husna suka bi ta da kallo kamar zata yi magana sai kuma ta fasa ta figi hannun Husna dake da sauri. suka nufi dakinsu. Hajiya Aisha ta kada kai tana fadin, “Munafurcin ‘yan biyun ne ya motsa ke nan? To idan ta yi wari maji”. Ta ci gaba da kallonta. Sai da Hasna ta sanya mukulli sannan ta ‘ sami nutsuwar kallon Husna da ke ta kallonta da mamaki da alamar tambaya. fara magana cikin qaguwa, “Sister lafiyarki kuwa, kin ga yadda duk ki ka wani birkice kamar kinyo kisan kai?” Cikin rawar baki ta ce, “Sister kin san“ waye yazo gurina‘? A,a saikin fada Abduljabbar ne fa”.. ‘ Ita ma Husnar saida tadan shiga rudani amman tai qarfin halin cewa “‘ “Waye ke nan, me wannan sunan?” Hasna ta riqo hannunta, “Dr. Abduljabbar na makarantarmu, lakcaranmu“. Mamaki ya kama Husna‘ amman ta kuna zagulo tambayar “Wai kina “nufin dan gidan Falmata‘? “Shi… shi ne Wallahi. kawai na fita hala’in ko waye sai namai rashin mutunci kawai na hango shi ya fito daga cikin mota wallahi saura kadan na suma a tsaye”. . Husna jijjiga kai, “To me ya ce miki ya kawo shi Kar dai kararki ya kawo wa Daddy. lallai da mun shiga ukun mu” Ta yarfa ,hannaye ‘bayan ta saki hannun Husna. “Cemin yai wai sulhu ;da..ban .haquri ne‘ ya kawo shi. ammana kasa gamsuwa da‘ hakan, ina jin kamar yaxo daukar fansa ne. kin san halin mutumin nan sister shaidani ne na karshe Husna ta yi nmrmushim‘ ~.Ki kwantar da hankalinki wata qila fatsarki ce ta cafko kifin da ‘yammatan bayaro kaf Suka kasa kamowa,lallai ’ kina cikin masu sa’a sister”. “Don Allah’ki daina fadin haka na jima da cire ran samunsa kuma shi ma nasan ba hakan ce ta kawo shi ba”. Hasna ta maida mata da amsa “Komadai meye jeki saurareshi sister ni kuma zan dinga duba agogo da zarar awa daya ta wuce nasan ciniki ya fada saina bullo da kayan tande-tande dana motsa baki Ta karasa maganar da zolaya da tsokana. Hasna ta bata rai, “Kina da matsala wallahi, ana maganar nutsuwa sai ki dinga sako shirme, idan zuwa yayi ya shake ni na mutu fa?” ‘ Ta kamo hannunta yadda ta sha yi mata idan tana son’lallashinta, “Kinga hakan ba za ta faru ba, da son cutar yakesonyi ba zai shigo kowa ya’ ganshi ba,‘ da ba zai bari ki iso gare mu ba, ki sanya yarda da‘ aminci cikin ranki ki dinga yi masa‘kyakkyawan zato, wannan shi ne halin mUsulmi na gari”; Hasna ta yi ajiyar zuciya. hankalinta ya dan, fara kwanciya, ta samu nutsuwa, “Na gode sister, shi yasa nake sonki…” “Kin ga maza kije kin barshi a .zaune shi daya babu dadi”; Husnata fada Tace, “Haka’ bari _na’ koma, ina zuwa”.” ‘ “Ba za kiyi kWalliya ba kenan yau ta haduwa da masoyi Husna ta’ kuma tsokanarta. ‘ Ta juya ta dalla mata hararar wasa, sannan fice da sauri husna ta fashe da dariya. Ta ratso ta falo, Hajiyarsu na zaune ta bi ta da kallo kamar za ta yi magana sai kuma ta fasa. tunda ta ga ta nufi hanyar falon baki ta san akwai magana. Hasnar ta kalli Momin nasu tana dariya ta shige da sauri. Husna ta fito tana dariya, Hajiya ta kalle . ta, “Wai me kuke Kullawa ne cikin gidan nan?” Husna ta zauna, “Momy wani abu ne, za~ mu gaya miki amma daga baya ba yanzu ba”. Momy ta taBe baki, “Ku kuka sani, kada ma ku gaya min har abada”. Ta Ci gaba da kallonta. ‘ Husna ta yi murmushi kawai cikin ranta tana jin dadi, amma fargaba da faduWar gaba na neman yi mata yawa. ” A Bangaren Hasna‘ ta dan jima tsaye jikin‘ Kofar da za ta sada ta da Bangaren da ya ke’ tana saKawa da kuncewa, daga karshe dai ta runtse ido bayan doguwar addu’a ta bude kofar Idonsa yana kan kofar don ya dan soma gajiya da jiranta, tana shiga ya yi murmushi. “Ai na yi zaton kin gudu ke nan, idan na gaji da zama na tashi na yi gaba”. Ta zauna tana dan kada kai tana son ta dake, “A kan me zan yi hakan? Kawai dai na Dan tsaya yin wani abu ne”. “Allah dai ya sanya ba gulmata ku ka yi . ke da Husna ba”. Ya fadi yana dariya. Ta kalle shi da mamaki da sauri, ta ya ya ya gano ‘abin da suka yi kamar maye, kallon da ya tsare ta da Shi da idanunsa masu rikitar da ita ne ya sanya ta saurin kau da kanta gefe. Yanayin bugun Kirjinta yana neman sanyawa, da Kyar ta iya cewa. “Gulma kuma, sai kace wasu munafukai “A’a, ba irin wannan gulmar nake nufi ba, wai ta mamakin ganina k0?” Ta kuma shiga rudu, anya ba maye ba ne, Abdul? Ammma dai ta basar ba ta ce komai ba, tana dan wasa da yatsun hannunta. Ya kura wa yatsun nata ido yana murmushi, “Komai naki mai kyau ne Hasna, da hakan ki ka yi nasarar kama zuciyata na sani”. Ta kuma daga kai ta kalle shi da tsoron jin abin da yace daidai lokacin tsohon ciwonta ya taso. Ta lumshe ido tana zaton k0 mafarki ne ta ke yi, idan ba mafarki ba, Abdul din da ya ke wahalar samu ga ‘yammata, bai yin magana da ta wuce ta ‘yan mintuna shine yanxu ya zauna yana zaro mata zance irin Wannan. Ya kula da halin da ta shiga, don haka ya ce”Ki bude idonki Hasna ba mafarki bane, ni ne dai Abduljabbar Falmata‘ a gabanki na zo miki da maganar soyayya. Ni kaina ina jin kamar ba gaske bane, kamar ba niba. Sai dai daga karshe na yarda na sallama ninedin Ba zan manta ‘ ba, ranar‘ da ki ka fara ganina gabanki ya fadi sona ya‘shiga ranki”. Ta kada kai da mamaki,‘tanason ta ce garin yaya ka gane hakan, amma ta kasa. Fadi yayi murmushi yana kada kai ya ci gaba da magana. “Kada kice ta yaya na game haka. bakeba hatta sauran- dalibai na kan‘ gane duk wacce ta kamu da soma. don Sukan yawaita kwalliya da shishshige mini, sai dai tunda nake ban taBa jinkomai ga wata ba sai ke. wallahi kallon da ki ka min na farko shi ne asalin sonki cikin raina, da za ki.ku1a na dan rikice na wani lokaci, k0 da yake kwarjinina da yadda na basar’ ba zai bari ki gane ba. Hasna kamar yadda ki ka jima kina dakon sona a ranki hakan ce ni ma a gare ni,~ sai dai ni na yi Kokarin danne sonki da Boye shi a raina a dalilina na son mantar da kaina kene, sai daga baya na game ashe shi so ba ya Boyuwa duk inda yake sai ya bayyana,‘domin son ya sanya ni shiga damuwa kala-kala”. “Hasna ta yi ajiyar zuciya da jin dadi , tana jin kamar ta durkusa ta yi wa Allah sujjada ne a nan guring amma ta dan dake tana sauraran bayaninsa da take jinsa kamar busar sarewa, ya Ci gaba da magana. “Kada ki tambaye ni dalilin da ya sanya na Ki bayyana miki ina sonki, wannan wani Boyayyen sirri nane, don na yi tsammanin ba zanyi aure ba har abada, wannan shi ne tsarina da burin da na daukar wa kaina, amma sai da ki ka rusaminshi shi. Za ki ce mai ya sanya na dora miki karan-tsana‘? Tabbas sanda ki ka Kara shige mini. kwalliyarki ke kuma Kayata zuciyata, sai shawara ta zomini ta yakice ki, hakan ne kadai zai zaunar da zuciyata lafiya har ki fice daga raina, don haka na yi niyyqr nuna miki Kiyayya Karara. Ranar da na kore ki daga lakcata randa’ ku ka shigo da Husna, ina kallon shigowar‘ Husna don kawai na kona miki rai ya sanya’na miki haka,‘ amma bayan na koma gida sai; da zuciyata ta hora ni bisa abin da na’yi miki, don daren ban yi bacci ba, ina ta tunanin halin da za ki kwana a ciki. Daga wannan lokacin sai‘naga kina Kara shige min, har zuwa sanda na yi miki wannan wulakancin gaban dalibai, har suka yi miki dariya. A ranar kam sai da na zubda hawaye ban kuma ji komai ya ragu na daga sonki ba, sai dai ina fatan ki tsane ni har ki daina sha’awar ganina, watakila idan aka yi hakan zan manta da ke. “ Ban yi sa’a ba, domin daga sannan ki ka fara rashin lafiya, wacce ta daga hankalina, a wanan lokacin na dinga jin kamar na zubda makaman na same ki, sai dai zuciyata ta gaya mini mun fa rabu, da kin dawo za ki tsane ni sai dai akasin hakan ne ya faru da ki ka .dawo sai ki ka dawo da sabuwar soyayyata da.‘ wata siga ta daban”. ; Ya yi dan shiru yana kallonta, ya kula dadi ya cika ta da jin jawabinsa, ya kada-kai. “A wannan lokaci na Kara yanke shawarar abin da zan miki mu rabu rabuwa na har abada, shi ne na kayar da ke bayan na san kin ci, abin da ki ka yi mini wallahi ba Batan rai ya yi ba, illa .fama min tsohon sonki da ke kwance a raina, sai kuma kukanki da hawayenki zake zuba dukan zuciyata ya dingayi har naji ba zan iya jurewa ba na bar miki offis din da zummar na tafi gida na‘huta na yanke shaWarar abin yi, sai dai ban samu damar yin hakan ba; har sai da sonki ya doki zuciyata ‘na fadi warwas. K0 a gadon asibiti da na kwanta rikici muka dinga yi da zuciyata a kan na bi ki da sunan daukar fansa mu rabu k0 kuma na sallama wa zuciyartawa sonki. na karya dukkan alkawarin raina na bayyana gabanki da sunan so? Wannance tambayar da ta dinga damun raina. ban Sami sonki ba ‘sai yanzu da zan ce miki Hasna ina sonki Ta kuma daga kai ta kalle shi, kallon da ya ke mata ya bata kunya, ta kau da kai da sauri da wata uwar kunya, wacce irin rana ce yau mai sa’a a gare ta‘? Ta ma rasa me za ta ce me kuma za ta yi. Ya taso tsam daga inda ya ke, ya iso gabanta ya ‘zauna daidai qafafunta a bisa kan kafet ya Kura mata ido yana murmushi. “Na san kin jima ‘kina ‘ jiran wannan lokacin, don haka kema ki dubi cikin idona kice mini. ’ABDULJABBAR FALMATA INA SONKA!”’ Ta hade kai da gwiwa tana dariya, daidai’ lokacin‘ Husna ta turo kofa da qaton faranti’tana sallama. Bai matsa daga inda yake ba ya amsa yana murmushi. Husna ta; tsaya jim da‘ ‘yar kunya kafin ta fara Kokarin shigowa da mamaki a kan fuskarta. Hasna dai ta kasa k0 daga idonta’don kunyar abin da ke faruwa. ’ Ya juya ga Husna yana murmushi, “Yayarmu, sai ki ka ganni k0?” Ya karasa maganar da tsokana. Husna ta zauna tana murmushi da jin nauyi. tace, “Malam ina wuni?” Na yanzu ba malam za ki ceba, qanina. Zakice domin gaban qanwarki nake da kokon barata, taya ni roko?” yi ajiyar zuciya tana murmushi, tace ai ako ina kai malam ne, amma na yi mamakin :yadda ka sami damar zuwa gidanmu, gano gidan, da faruwar komai ma”. Yayi murmushi yana leKen fuskar Hasna dake mimushi har lokacin ta kasa daga ido ta kallesu “Ni ma haka abin yazo mini, ina jinya a gadon asibiti ina tunanin Kaunarki, ina warkewa na hau bincikar komai nata, abin fargaba da damuwa ban san ina ne ainahin indakuke ba. sai da na yi dogon bincike kaf’in na gano gidanku, ’Allah ya rufa mini asiri gidajen ‘yan gayu ne don haka hatta lambar ma na samu”. Suka yi dariya a tare gabadayansu, Husna—ta’mike tama fadin. “Bari dai na Wuce haka amma har yanzu ina Cikin mamaki da shakku Malam. wai sai ga ka kana ta. surutu kamar ba kai ba. sai anjima dai”. Ta nufi kofar fita da Sauri tana dariya. Hasna – ta dago ta kalle shi tana murmushi, “Wai ba ‘ka jin kunya ne. Baka ga yadda ka ke magana ba don Allah?” “Yauwa‘ haka nake son na ji kin ce Hasna, don Allah ki yi magana ki gaya mini abin da ya ke ranki. na san dai da kina sona, amma ran da‘ki ka tsare nida masifa na shiga shakku shin kina sona’ yanzu, k0 a’a, domin na gano tsana ta a ‘Cikin ranki karara“. Ta Kara kau da kai gefe “Kaga’kaci abinci don Allah”. Ta miqd ta dauko farantin’da Husna ta shigo da shi ta ajiye a gabansa. Yana kallonta yana murmushi, yace, “Wato kina son shashashantar danii kenan k0?” Ba haka bane, ka dai Ci tukunna kada ya huce Ta kuma fadi tana kwantar da kai. “Ba zan Ci komai ba ban san waye ni ‘cikin ranki ba, sai kin sanar dani hakan ne zai ba ni nutsuwar Cin komai”. Ta kau da‘ kai gefe tanajin kunyarsa matuka. tana son sanar da shi abin da. ke‘ ranta, amma tanajin nauyi, Abin yazo mata a bazata, ta yi ajiyar zuciya tana shakar numfashi ta ce, “Na amince Ya fashe da dariya ‘yana kallonta. Ta kalle shi da mamakin dariyar da ya ke yi.’ shin me wannan dariyar tasa ke nufi ya katse mata tunanin nata da . , “Wallahi kin bani dariya, kamar irin tsofafftin nan, wai wai na amince. Wannan ne abin daya sani dariya, cewa za ki yi, ‘ina sonka Abdul dam Falmata”. Ta yi’ murmushi, “To nace ina sonka Abdul”. . Ya kada kai gami da,jan manners din abincin gabansa yana fadin. “Yanzu’ ya dace na Ci abincin ma?” Ta dinga kallonsa tana kada kai sanda ya ke cin abincin,‘ da ma haka ya ke, tun da ya fara cin abincin bai ‘yi magana ba, sai kallonta da ya ‘ ke yi kawai. Ita ma ta dinga satar kallonsa da sakin fuska da barkwanci amma ya ke bata da muguwar dabi’a ga dalibai‘.’ Ya kammala Ci ya gage bakinsa har lokacin tana kallonsa tana mummshi ya dago kansa daidai lokacin data kauda kanta. “Mene ne na kau da kai, ki kalle ni ki more wataqila zaki gano ni mummuna ne yau”. ‘ Sautin kiran sallar magriba ne ya katsd masa zanccn ya ja ajiyar zuciya. . “Ga kiran sallah, ga soyayya ta dauko dadi”. Ta kuma fashewa da dariya, “Malam wai daman haka ka ke, don Allah kada cikina ya yi ciwo”. Ya mike tsaye, “inba, damuwa zan dawo gobé kanmar yanzu, kin aminzcé? Ta daga kai, sai kuma ta ji bata son ya tafi din. Ya miqa mata wata hadaddiyar waya, mai suna SAMSUN GALAXY ACTIVE yace “Ga waya da layi, nawa ne kadai ka da a sanya mini gara one k0 gara two…” Ta Kara fashewa da dariya. Suka fito tare suna tafe yana janta da hira, tana dan dakewa tana ba shi amsa. Abba ya shigo ya sami guri ya yi fakin tunda ya shigo maigadi ya kada kai yana cewa: “Lallai yau za a yi gumurzu ke nan”. Abba ya fito daga cikin motarsa, ya hango Hasna tafe da Dr. Abdul suna hira cikin jin dadi da nishadi mamaki da takaici ya cika shi. Ya tsaya ,turus yana kallonsu, sai yaga kamar ya tunkare su ya cakumi Abdul, amma sai. ya dan tsaya yana shawarta abin da ya dace ya yi, domin ya kula akwai wani abu tsakaninsu. Sam basu bango shi ba har sai da suka zo gab da shi Gaban Hasna ya yanke ya fadi, amma sai ta dan dake “Lah Yaya Abba sannu da zuwa”. Ta kalli Abdul da sauri “Malam ga Yayana Abba”. Abdul ya fuskanci akwai wani abu tare da Abba, amma da ya ke namijin duniya ne sai ya mika masa hannu yana fadin. “Salamu alaikum”. Da Kyar Abba ya iya mika masa hannun suka gaisa, sannan Hasna ta Kara fadin “Ka shiga ciki mana Yaya Abba. kowa na ciki”. Ta dauke kanta da sauri zuwa ga Abduljabbar. “Muje mana: kada ka rasa sahu”, Abduljabbar ya wuce tana gefensa suna hira, Abba ya bi su da kallo da’takaici, yana kada kai har zuwa sanda Abdul ya shiga mota, Hasna tana tsaye har ya fice, :a ranta sai takeji kamar sun shekara guda da Abdul .kamar ba yau suka fara- sanar da juna suna son junaba. Abba da ke tsaye yana huci ‘ya’ nufeta da sauri, “Hasna! Hasna!!” Sam ta manta da Abba a gurin, sai da ta ji ya ambaci sunanta ta waiga da: sauri babu» Wata damuwa a kan fuskarta har ya isa inda take “Waye wannan‘? me kuma ya shigo da shi gidan nan?” Ta yi dan murmushin yake. “Sunanshi Dr. Abduljabbar. malamine a makarantar….. “Karya kike .yi, wannan bai yi kama da malami ba, a hakanne zai iya koyarwa ko mahaukacine yaima wannan mutumin kallon tsab zai gane irin maxajennanne da gata yai musu yawa sannan hirarku tafi dacewa da Wani salo ta daban. to idan ma da’ gaske malaminku ne me ye ya kwawo shi’ gidan nan?” Ta daga ‘masa hannu tana murmushin zolaya,‘ “Me ya kawo dukkan wadannan tambayoyi’n kamar wani ubana k0 mijina? Ka ga don Allah dakata Abba”. ‘ Ta wuce ta nufi cikin’gida, ya bi‘ ta da’ kallo da bakin ciki. Tana shiga kai tsayedakinsu ta wuce ta sako mukulli da alama Husna ba ta nan, ta jingina da jikin bango tana murmushi, wani dadi yana shigarta,“ wai’yau‘ ita ce tare da Abduljabbar a’matsayin masoya, ta nufi bandaki don dauro alwala ta sauke farali. Abba ya shigo falon yana Kare masa kallo a fusace babu kowa da alama duk sun shiga ’sallah ne, ya nufi kujera ya zauna ya dafe kansa. ‘ Me ke shirin faruwa “da shi ne, ba dai wannan ya sanya hasna keyi masa wulakanci cikin wadannan kwanakin ba? ‘ Momy ta shigo da carbi a hannunta, da alama kicin za ta shiga ta ci karo da Abba zaune. Ta kalle shi kafin ta tuno dalilin bacin ransa, tabbas da’ alama saurayin da ya zo gurin Hasna yau tana natuqar sonsa, har kuma Abba ya gansu, Allah ya sani k0 can baya ba wani farin Ciki ta keyi da auran Abba. da Hasna ba, balle da wani abu mummuna ya faru a wannan lokacin na nuna kishi da Kin “abin da ya fito daga fuskar mahaifiyar Abban. Amma ta dake ta isa kusa da shi tana fadin. “Abba ya ya dai?” Abbaa ya dago kanshi da sauri ya kalle ta. ‘ ‘Na’am Mommy?””Ya ya lafiya na ganka a nan-kayi sallah kuwa?” , v ‘ Ya mike da sauri don ya san Mommy ba ta son wasa da sallah, duk da bai cikin nutsuwarsa ba za ta yi masa uzuri ba, don haka ya mike ya nufi masallacin da ya ke jikin gidan. Tsawon daren babu yadda Abba bai yi ba don ganin Hasna, amma abin ya ci tura,‘ ga Husna tana canyau ma tana hira da saurayinta da alama ma sun fita unguwa ne tare da kunya kuma ya sami Hajiya da wannan maganar, haka ya yi ta zagaya gidan kamar wanda ya samu ciwon‘hauka, har zuwa sanda ya gaji ya wuce gidansu kamar kububuwa yana cika yana batsewa. Ita kam Hasna tana idar da sallah, wayarta-ta fara Kara saboda Abdul ya ba ta lambarsa, sunan masoyi ne ya ke yawo a kan ‘madubin wayar ta daga da sauri tana ajiyar zuciya, amma ta yi shiru ta kasa cewa komai, sai shi ne ya yi mata magana cikin zolayarsa.. “Masoyiyata”. Ta fashe da: dariya da jin dadi, daga nan hira ta fara yin dadi Cikin kwanaki qalilan soyayya mai Karfi da shaquwa ta shiga tsakanin masoyan, ba Husna ba hatta Momy ta yi mamakin hakan, har sai da ta matsa da sanin waye. wannan Abdul din? Ganin yadda yar tata har wani qiba da fresh na musamman take lol Abduljabbar yana iyakacin qokarinsa – don ganin ya boye abin da‘ke tsakaninsa da Hasna ga dalibai, ita ma ba ta nuna komai, sai dai yana yawaita kallon dukkan Bangaren da take zaune, idan ya so sha’afa sai ya dauke kansa da sauri. . Hasna kam burinta ya cika, duk da tana cikin fargabar abin da zai ‘ je ya zo idan maganar ta isa ga iyayensu maza. Abba dai ya zama tamkar wani zautacce, ya rasa abin da zai yi, Husna taqi yarda ma su yi wata magana da ta dace a kan Abdul din, hakan ke kara dagula lissafinsa. Yau ma’ya iso gidan da yammah suna hira a lambu ya hangosu, ya tsaya yana saqawa da kwancewa, to wai me ya sanya zai tsaya ta dinga yi masa‘ yawo da hankali ne? Ya kamata ya tunkari Alhajinsu kawai da maganar, ga shi daman yana gari, bai yi wata wata ba ya ‘ juya da sauri‘ya nufi motarsa don zuwa ofis din Alhaji Sammanin. Hasna da Abdul basu ganshi ba sam suna ta soyayyarsu kamar zasu lashe juna. Hasna ta kalle shi da nutsuwa tace “Malam ina da tambayar da na ke son yi maka, amma ban san yadda za ka kalle ta ba, k0 zata yi’ maka ciwo ne’? ba dai nufina ne na Bata maka rai ba”. Ya maida bayansa jikin kujera yana kallonta. “Na sab tambayar da za ki yi min, domin dukkan wanda ya sami damar zama da ni fiye da sati muka saba ita ya ke mini, amma na baki dama kada ki damu, raina bazai baciba, ki tambayi komai Hasna”. Ta gyara zama gami da yin doguwar ajiyar zuciya tace “Tunda na shiga B.U.K, sunanka ne ya fara ba ni mamaki cikin malaman- makarantar, ba ni ba hatta sauran dalibai suna yawaita maimaita fadinsa, ‘abin mamaki‘bai wuce yadda ka ke amfani da sunan mace a madadin sunan mahaifinka ba. Na taba jin wasu masu irin sunanka da suka yi amfani da sunan mace, amma cikin tarihi ne ban gansu da idona ba. sannan daga baya mun ji bayani a kan dalilin yin hakan kamar shugabar Najeriya kishin kasa wato Murtala Ramat, amma» kai naka kowa ya gaza sanin”da1i1in yin’hakan, idan ba damuwa k0 ni zan sani Malam?”. Yanayinsa ya sauya ga tsananin damuwa da bakin ciki, yana kada kai idonSa ya sauya launi zuwa jajir. Ta dan tsorata da ganin yanayinsa da sauyawar da yai lokaci guda, ta yi yaken Karfin hali taci. gaba da magana. “Ka yi hakuri, ba nufina ‘ganin Bacin ranka ba, na yi zaton hakan daman”. Ya dago yana kallon gefe idonsa ya fara zubda hawaye, amma ya dake yace “Ba abin da kika’yi mini ne abin da yaf1 damuna ba, a’a abin da nake tunowa a cikin rayuwata ke,damuna. Kamar yadda kowa ya ke alfahari da sunan mahaifinsa, ni kuma sai na tsinci kaina.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29Next page

Leave a Reply

Back to top button