ABIN DUHU COMPLETE NOVEL

Godia ta musamman ga marubuciyar wannan book din FAUZIYYA D SULAIMAN (MATAR BELLO Q. FOR. Q)
Daga group na:-
???? HAUSA NOVELS????
☎ 08034691340
???? ABIN DUHU????
????????????
Na
FAUZIYYA D SULAIMAN
PAGE
0⃣9⃣
Kamar yadda ki ka ji sunan‘ mahaifiyata Falmata, ‘yar: salin Kauyen Kaburma, mahaifiyata ta tashi marainiyace, wacce bata da mahaifiya sai mahaifi da matan uba, kasancewar tun gurin haihuwarta Allah ya amshi ran mahaifiyarta. kakarta ce ta riqe ta wacce ita ma daga baya Allah ya amshe ta «bayan ta yi wayo.riqonta ya ‘koma hannun matar babanta Larai, Larai mace ce muguwa ‘da ta. ,azabtar da ,mahaifiyata, Allah dai ya kaddara sai ta rayu. Tunda mahaifiyata ta. tashi da farin jini ta tashi, wannan abin ya dinga yi wa Larai ciwo, ‘domin tana da manyan ‘yammata da suka girmi mahaifiyata, ammaa basu sami mazaje ba, sai dai ita mahaifiyata ta fi Kaunar Abduljabbar duk cikin maneman nata, saurayi ne matashi, dan sarkin noman garin, mahaifintai ya so kwarai bayar da auranta ga Abduljabbar amma Larai ta shiga ta fita ta soke wannan aure. daga Karshe ta hada auren mahaitiyata da Alhaji Mudi, wani mai arziqin garin. Alhaji Mudi babban mutum ne mai arziqin gonaki da gidaje, amma kuma Allah bai taba ba Shi haihuwa ba, yayi matukar farin ciki da wannan aure, duk’ da ya san mahaifiyata ba ta kaunarsa. A haka aka yi wannan aure, bayan Karin kudi da ya yi wa Larai, aka fita da mahaifiyata daga gidan tana kuka kamar za ta mutu. Tunda ‘yan kai amarya suka watse mahaifiyata .ta dinga guje—guje ta Ki zama cikin dakin, daren nan haka ango ya kwana cikin takaici, ‘domin ya yi neman duniya bai ganta ba, da kunya kuma ya tambayi matansa k0 masu hidimar gidan. Tun daga wannan rana ta Ci gaba da guduwa har cikin garken shanu ta kwana, ta kuma kwana cikin gonaki saboda Kin Alhaji Mudi, idan an ‘ganta da safe sai a dawo da ita gidansa. Hankalin Alhaji Mudi ya tashi, ya dinga sintiri gidan Larai yana’ba ta kudi da kyauta‘. Daga karshedai sai da Larai ta sanya mahaifin babata ya yi mata duka. gami da Barazanar ‘ tsinuwa. duk da tana da karancin‘ shekaru a lokacin ta san illar tsinuWa, don‘ haka ta haqura ta zauna. ‘_ Daren da Alhaji Mudi .ya fara shiga‘ dakinta ne ya sanya ta Kara tsanarsa ta kuma qi yarda da zaman gidan, domin bai tuna da ita yarinya ba ce, sai da uwargidansa ta taimaka mata da safe gurin gyaran jikinta. Tun daga wannan rana tace: bata ga ta’ zama a gidan ba, duk irin azabar da ta ke sha ‘ kuwa daga karshe dai Larai tace da Alhaji’ Mudi ya sake ta ta aura masa’diyarta, yace to shikenan yako saketa Wannan labari ‘ ne mai :dadi gurin ‘ mahaifiyata, duk da bata- san inda Abduljabbar ya ke ba a yanxu Don‘tunda ya ; rasa ta ya tattara kayansa ya bar garinya tafi. neman kudi, mahaifansa sun goyi bayan‘ hakan don sun ga irin damuwar da ya shiga-a kan rasa masoyiyarsa da ya yi. Bayan tsawon wata uku tana zaman idda ba a fuskanci tana da komai ba saboda yarinta da rashin girman jiki, har mahaifinta na matsa mata a kan Kara yin wani auren, kwatsam sai ga ciki ya bayyana a jikinta, hankalin mahaifinta ya tashi yace lallai cikin Alhaji Mudi ne, amma Larai tace tana da shakku don koda aka tunkari Alhaji Mudi da maganar sai‘ cewa yayi. Allah ya kashe shiba cikinsa’bane ai kowa ya san ta kammala idda, kumashi ba haihuwa ya ke ba. Mahaifinta ya so shigar da kara, amma ba shi da halin yin hakan, ita kam duk inda aka matsa sai tace wallahi bata san kowa ba sai Alhaji Mudi, a haka cikin nan ya dinga girma, bakin ciki yana’ qaruwa a zuciyar mahaifinta. Haka ta yi rainon cikin a cikin bakin ciki da tsangwama da takurawa. Ranar da aka haife ni cikin tsakiyar rana ne, mahaifin babata yana tsaka da shigo da kayan amfanin gona, ita daya a, cikin tsahon dakin da ya kasance nata ta haife ni cikin tsananin azaba da wahala. Mahaifinta yana jin kukan yaro ya yi tsaye cak kamar an dasa shi, ita kam Larai dakin ta {ado da gudu tana sallallami da : fadin. “Shi kenan an haifi shege yau a gidanmu”. Tana kallona cikin jini ina kuka ba ta taimaka mini ba, mahaifiyata kuma tana gefe durkushe tana kuka, sai da makota suka jiyo ihun jariri suka kawo agaji, aka yanke mini cibiya, mahaifinta kam tun daga wanna: tsayuwa bai sake motsi ba sai da aka je aka taBa shi, ashe ya rasu a wannan tsayuwar ya yanke jiki ya fadi…” Abduljabbar ya yi shiru yana mai da . numfashi yana jin kamar a gabansa abin ya faru kuma yanzu. Idon Hasna ya dinga zuba kwalla, ‘ wanne irin labari ne wannan mai tafasa zuciya kamar cikin littattafan dare dubu da daya? Abduljabbar ya goge hawayen dake ‘ gangaro masa yana kada kai. “Ba wannan ne abin kuka ba, sai kin ji halin da mahaifiyata ta shiga a kaina. Dukkan dangi suka dinga yi mata tofin Allah ya tsine, gami da la’antarta. don sun ce ita ce ta kashe musu dan uwa da baqin cikintar,» babu wanda ya yi tunani a kai”. Ranar da mahaifinta ya cika kwana bakwai da rasuwa, Larai ta ce, lallai sai ‘ta bar gidan don ganinta yana Kara haddasa mata baqin ciki. Tana kuka tana rokon Larai a kan ta barta ta zauna, amma Larai tace ba za ta zauna ba, sai dai idan ta zaBi yada ni cikin bola, ko kuma‘ ta kai ni gidan marayu, don ba za su rayu da shege masifu na sauko musu a gida ba, ga babbar masifa nan ta rasa mijinta ta fara gani. Mahaifiyata ta zaBi tafiya ta bar gidan da dai ta rabu da ni, daman ba ta sami wani gata da ya kasance na maijego ba, babu wankan jego, balle naman gashi ko kunu. Kai tsaye dangin mahaiflyarta ta tunkara su ma suka ce ba su san zancen ba, ta san inda dare ya yi mata. Haka ta fita tana rungume da ni tana kuka. Kwatsam sai suka yi kiciBus da Abduljabbar, mamaki da tsoro ya kama shi ya fara tambayarta abin da ya faru. Ba ta Bata lokaci gurin sanar da- shi komai ba, hankalinsa ya tashi kwarai da gaske, ya sanarda ita tUnda ya tafi birni bai dawo garin’ ba bayan» ya tabbatar da ya rasata, ‘sai ya kama neman‘ kudi, yanzu haka’” ya dan zo ganin gida‘ne, amma zai taimaka mata. ‘ Haka nan suka juya suka nufi ’tasha, amma bai yarda sun shiga mota lokaci daya ba, don kada mutan garin‘ su ji labari sai suka hau daban-daban. A inda yake wata unguwa mara wadatar gidaje ne masu kyau, da alama sabuWar unguwa ce ta talakawa, haka ya kai ta dakinsa da ya ke kwana ya ce ta zauna a nan sai da ya tanadar mata komaina bukatar yaro da ita kanta ya koma kauyen’ donvyaga iyayensa kuma da ya’dawo zai aure‘ ta k0 ‘da bada sanin kowa. Ba ya bar mata abin da za’ta ci kafin ya dawo,:da yake gida ‘ne iriri na’hadaka maza da mata gidan haya hakan yasa bata damuba ~Ashe wannan shi ne ganinta na‘ karshe da Abduljabbar, domin a ‘hanyarsa ta’ tafiya kauyen nasu yayi hadari ya rasu, ‘sai labari aka kawo mata. Ta yi kuka, ta damu iyakar damuwa. Tun daga wannan lokaci ta sanya a zuciyarta ba ta da’ kowa sai ni, ta dinga ambatona da sunan tsohon masoyinta Abduljabbar, duk da babu ragon suna balle wani abu na radin suna. Gidan da ta ke gida ne na neman kudi, don babban gida ne, na haya cakude da yaruka kala-kala, yarabawa da hausawa da sauran yaruka a cakude kusan daki talatin ne a cikin gidan, haka ta dinga bin matan gidan tana musu wankau da Sauran nau’inkan bauta tana samun abinDa zataCi, har zuwa sanda na fara wayo. Mahaifiyata ta fuskanci ilmi shi ne gishirin zaman rayuwa haka ta dage da lallai sai na yi shi, ni kam ban taba tallaba, amma ita babu irin nau’in neman .kudin‘da‘ba ta yi ba a kaina. Wallahi mahaufiyata tayi yawo babu takalmi a Kafarta, saboda’babu Ta zauna a gidajen haya da dama, wasu’ sun ce karuwa ce, daman ni tunda na taso’ da sunan shege na taso, amma ban damu ba don tun ina karami-mahaifiyata ke ’bani tarihina, har sai da‘na haddaCe shi. ‘ Sanda na yi wayo wajen shekara goma, cikin ikon Allah manema sUka dinga zuwar ‘ mata, amma ta Ki yarda tana sanar da‘su ni ne kadai rayuwarta da burinta, sai kuma Allah ya sanya ni ma na kasance haziki, dukkan ajin da na zauna na kan zamo na daya, har sanda na kammala karatuna na sakandire cikin wahala da Kunci da kyar…” Ya yi shiru hawaye na ci gaba da zubo masa. Hasna da ke kuka wiwi ta Share hawayenta ta ce. “Me ya faru kuma bayan sannan?” Ya yi ajiyar zuciya. “Ba. labari ne mai dadi’ ba, wani ginshikin sirri ne cikin rayuwata, amma dai na sami ilimin da .nake bukatar samu ta hanyar wani babban maikudi Alhaji Shazali Mafia, shi ya fitar dani kasar, waje nayi“ digiri na yi masters, ‘abin da mahaifiyata. Ke muradi, wannan shi ne abin da ya ke wanke. mata zuciya tunda na tashi na ji tana kirana da Abduljabbar Falmata, wannan ke nuna mini itace uwata, kuma ubana. Na dawo daga kasar waje da sakamako mai kyau; na zama irin mutumin da mahaifiyata ta ke fata, domin ban jima da dawo wa ba na sami aikin koyarwa a jami’a, cikin matukar sa’a. Daga nan na fara kyautata mata, na gina mata gida, na kai ta saudiyya, sai dai abu daya ke damun rayuwarta, shi ne rashin aurena. Amma a yanzu ma wannan damuwar ta kauce, tunda na hadu da Hasna ta wargaza mini tunanina zan mata wannan ma”. Hasna ta yi ajiyar zuciya, labarin na Ci gaba da tsumata, ta ce “Bayan wannan: tsawon lokacin babu wani naku da ya taBa nemanku har yanzu‘?” “Akwai mana, mahaifina da kanshi ya ‘ dinga nemana, addu’a babu irin wacce bai yiba a kan Allah ya dawo masa da mahaifiyata dani ba. don bayan tafiyarta ya dinga magana , mun sami wannan labarin ne ta wani tsohon abokin Abduljabbar da suka .taho ci-rani tare, sai dai mahaifiyata tace babu inda za ta je. ba ta buqatar kowa ‘ya zama dangina a yanzu. ita ce komai nawa. Amma mutumin nan ya dage sai da ya kawo Alhaji Mudi inda muke, lokacindana kammala karatun digirina na dawo najeria, da Kyar Alhaji Mudi ya ke iya takawa, ya tsufa ya fita daga kamanninsa, yana isowa ya zube gaban mahaifiyata yana kuka da fadin “Ki yafe mini Falmata, tabbas na zalunce ki ba a kan hakkinki ba, amma Allah ya sani a wancan lokacin ba ni da ilimi a kan saduwa daya zai iya samar da ciki, sai da na sami sani akan hakan Bayan barinki garin nan baifi da wata biyu ba,‘ Allah ya qaddara matana suka sami ciki su duka ukun kusan lokaci guda, wannan abin ya ba ni mamaki da tsoro dan da na yarda ba zan haihu ba har abada, sai dai Ubangiji ya jarrabe ni da rashin samun rayayyen da daga cikin cikin nan guda uku, biyu sun yi Bari ba‘yan cikin ya yi watanni‘ biyar zuwa shidda. dayar da ya kai lokacin haihuwa wacce na sanya rai na dinga lattalinshi ta haife Shi babu rai. Sai dai duk wanda ya kalli gawar yaron ya kan tuno da danki don babu bambancin kama k0 sura, tun daga wannan lokacin na fara tuno ki da dana. Tun kuma daga lokacin kusan kowacc shekara sai an sami ciki a gidana, amma ba ya kai wa lokacin haihuwa a ke rasa shi, wannan abin me ya haifar mini da mugun ciwon zuciya da damuwa, kwatsam rannan ina jin wa’azin wani malami sai na ji yana fadin k0 sau daya namiji ya kusanci mace ciki zai iya shiga, har ya Ce ai sau daya ciki ya ke shiga ba sau biyu ba, don haka idan namiji ya sadu da mace sau daya tal za ta iya ,samun ciki, kuma idan namiji ya rabu da mace sai ta yi wasu tsawon watanni uku tana yin al’ada wata kuma ta kan yishekara ma, ya dangama ga yadda mace keyin al’ada, don wata na yin wata dai-daya, wata kuma wata bibiyu ‘har da mai wata uku da fiye da haka daga’sannan na kuma shiga tashi ’hankali, na kasa samun nutsuwa sai da na tadda Larai wacce ita ce ita tace mini bayan na sakeki yaron nan Abduljabbar yana zuwa gurinki, kuma na sami labari a lokacin ya rasu ma bai dawo ba tun bayan aurenki, domin ta Kara tabbatar mini da gaskiyar abinda ta sani.‘ Ta dinga kuka tana fadin, na yafe mata Wallahi cikina ne tunda ki ka dawo gidan nan ‘‘ ba ki taBa ma k0 fiba, tun bayan data kore ki ba ta qara ‘ganin farin ciki ba, yaranta sai haduwa suke yi da masifu kala-kala, ga gobara da suke yi duk shekara, ban. da mugayen mafarkai da gane-gane data keyi na _ sammun da ta dinga yi wa mahaifinki, ga kuma uwa—uba talauci rabin gida ya zube, ba su da komai, dangi kowa ya guje ta don Allah na nemo ki ta ba ki haquri Na yi kuka, na yi baKin ciki? na yi mata Allah ya isa da ta sanya na wulakanta dana na _cikina, na tozartaki, tun daga wannan lokaci kusan shekara ashirin‘da wani abu ke nan ina nemanki Falmata, ki yafe mini don Allah”. Lokacin ina cikin daki ina jiyo mahaifina yana kuka, amma mahaifiyata ta kasa cewa komai, sai da na fara rokonta, sai ta fashe da kuka tana fadin. “Da na rantse har abada ba zan yafe wa Alhaji Mudi da Larai ba, domin har yanzu kalmar shege ba ta sauka daga kanka ba, amma ya ci darajar haihuwarka na yafe masa, sai dai bai isa na ba ka shi ba. domin kai dana ne har abada”. Alhaji Mudi ya kalle ni jikinsa yana rawa domin tsufa da ciwuka sun kassara shi. ’kawo shi aka yi har Cikin gidan Cikin kekensa na guragun da aka dauko Cikin mota. yace “Wannan ne dana? Shi ne dana‘.’ Ya ka nan don Allah! ” Yana kuka yake mini magana, na karasa na durkusa, ya rungume ni yana kuka yana cewa, na yafe masa na gafarta masa. Cikin kuka na ce na yafe masa. Sai a lokacin ya ji sunana Abduljabbjar, daga karshe ya roki mahaif’iyata ta amince yaje dani garin. ta ce har abada ba zan je ba, mutanen da’suke tare da baban nawa suka dinga rogonta amma ta Ki yarda, daga qarshe ma ta Shige daki ta bar su a nan. Na lallaBa shi nace yayi hakuri zan lallaBata idan ta amince zan je garin da kaina, da wannan muka samu ya tafi Hasna ta goge hawayen dake mata mala. ‘ “Wannan labari naka yana cike da ban ’tausayi da tsayawa a zuciya, yanzu kuma na ji tausayin mahaifinka ya kama ni, Allah dai ya sanya ka je din kamar yadda ka yi masa alqawari”. “Abin da ya ke damun zuciyata ke nan har zuwa yanzu, domin ban cika masa wannan alkawarin ba, duk da bai mini komai ba, bai san wahalar da na sha a rayuwa kafin zamayadda ya ganni ba. Yana da hakkin samar da cikina, yana da hakkin kasancewarsa uba, sai dai banKi Zuwa don kaina ba, sai don bin umarnin mahaifiyata, domin bayan tafiyarshi ta sanya ni a daki tana kuka da Kara sanar dani komai game da labarina tana kuka. Ta Karashe zancen da fadin. “Abdul, kada ka manta har yau kai da ne da ba a yi wa ragon suna k0 radin suna ba, ba a yi maka haKika. ba, babu wani da ya taBa yarda kai nashi ne bayan ni, sai yanzu da ka zama mutum za a raba ni da kai? Na yi yawo da zani yagagge a kanka, na yi dukkan tallan da ka sani da wannan kan nawa saboda kai. Na Ki yin aure tunda kuruciyata har zuwa yanzu da tsufa ya kama ni saboda kai, amma ban hana ka zuwa gurinsa ba, sai dai idan ka aikata haka ka yarda babu ni babu kai, ka yi zamanka a can har abada”. Yadda na ga hankalinta- ya tashi ya sanya na tahbatar mata da babu inda zan je in dai ba da yardarta ba. Shi kuWa mahaifina tunda ya koma garinsu ya hada manyan gari har da sarkin garin ya ce su zama shaida,,Abdu1jabbar dan Falmata dansa ne, shi ne ubansa. Abin da ya yi a baya sharrin shaidan ne, ya dinga rantsuwa da fadin shi ne mutum na farko da ya fara kusantarta, uwargidanshi shaida ce, domin ita ce ta taimaka mata da gari ya waye. Kafin kace mene, ne wannan labari ya baza gari, masu tausayin Falmata na yi, masu tausayin mahaifinta da ya rasu bai ji wannan abin ba na yi, Sai dai wasu da yawa zaginsa suka dinga yi, domin a ganinsu shi ya haddasa komai. Larai da kecan kwance da cutar rabin jiki babu mai kulawa ,da ita ga girma ta dinga kuka tana rokon a kai ta’ inda Falmata ta ke k0 ta yafe mata ta sami sassaucin azaba, tunda shi maigidanta kasa ta rufe idonsa ba ta nemi; gafara ba, amma babu wanda ya kula da ita. Shekarun mahaifina goma sha biyu ‘ kenan da rasuwa yanzu Hasna, ina jin kewarsa duk da sau daya na taBa ganinsa”. Hasna ta dan waro ido da damuwa. “Har ya komaga Allah ba ka je din ba, mai ya sanya mahaifIyarka ta kasa yafe ‘ masa?” “Ta yafe masa mana, sai dai ta kasa yarda na je ga inda ya ke, duk da yana ta aike a kan na je din. Ranar da dan aike na qarshe: yaxo yace mata, wallahi Alhaji yana cikin tsananin ciwo, sanan dansa da gafararta kawai yake ambata, a ‘sannan ne zuciyarta ta sassauto, ta amince na je, amma’; ta ce bayan gidan mahaifina ba ta yarda na je’ gurin kowa ba. Naji dadin hakan ma kwarai da gaske, na shirya na nufi asalin mahaifar iyayena, sai; dai kafin mu isa Allah ya amshi ran; mahaifina, Allah ya sanya da isha’i ya rasu don haka dole sai ya yi kwanan keso, na tadda? gawarshi na kwana tare da shi, ban bar shi yayi kadaici ya kwana shi daya ba, don an rasa wanda zai iya kwana da shi, sai da na je ni ne na yi masa’wanka da safe, na shirya shi da taimakon dan uwansa, duk da ina bakin cikin sau daya na taba ganin mahaifina, amma ina farin cikin nine na sanya shi a makwancinsa, ina yi masa addu’a da kyakkyawan fatan samun rahama”. Ta yi ajiyar zuciya da jin dadi. “Amma ya ya Larai ta Kare kuma?” Hasna ta kuma tambaya a Kagauce. Ya kalle ta ganin duk ta shiga damuwa, ya ce “Bayan labari ya tadda ta na zuwana gani cikin motar kaina da kuma yadda na kasance sai ta fashe da kuka, ta dinga aike nazo ta ganni don Allah ta nemi gafarar mahaifiyata a gurina, sai dai na ce a gaya mata Innata ta ce kada na shiga gidan kowa bayan na mahaifina. Ta yi ta kuka har zuwa cikin daren da ta rasu ita ma washegari-da ni aka yi sallar gawarta aka kai ta makwancinta. Ina ganin gidan kakana na kasa shiga. ya lalace kamar ba mutane ne ke rayuwa a ciki ba Bayan sadakar bakwai na koma gurin Hajiya ta na sanar da ita dukkan abin da ya .. faru, ba ta wani damu ba sai kalma‘ daya da naji ta fada. * “Tunda na rasa mahaifina cikin halin ‘ fushi da ni, ban’ damu da kowa ya‘mutu ba ma”. Wannan ce kalmar da na kasa mantawa i’ da ita, Babana ya rasu ya bar dumbin dukiya da gonaki. Bayan wani lokaci na koma domin ‘ duba gadona, wanda ya kasance ni daya ne mamallakinsa, Hajiya ba ta hanani amsa ba, domin ta ce hakkina ne da Allah ya halatta mini na ci, sai dai ba ta so na da zuwa garin, dukkan abin da zai dinga tuna mata garin mai ba ta sonshi. ‘ Bayan na yi shawara da abokina Murata, gidan mahaifina na maida shi makarantar islamiyya, gonakinshi kuma na hade su na saida na yo gaba da garin na bude babban gidan gona, wanda ke kawo mini maqudan kudi a cikin garin kano . A yanzu babu abin da ba a; kiwatawa kama daga kifl zuwa kaji da shanu da akuyoyi…tsuntsaye” “Wannan dalilin ne ya sanya ka tsani mutane, ba ka son yin mu’amala da kowa ba ka yin dariya?” Hasnar ta jefa masa tambayar ba tare da ya shirya amsarta ba. Ya kalle ta a dan razane kamar ta san wani abu kadan da ke Boyo cikin zuciyarshi da ba kowa ya saniba, bayan shi da Ubangijinshi, amma sai ya dake ya dan “Wannan sirrin raina ne, amma kada ki damu ba wani abu ba ne mai yawa ba fa”. Ya karasa maganar’da zummar zolaya. ganin yadda ya daure fuska gabadaya. Ta yi dariya, “Shi kenan. ka riqe sirrinka, amma ni ma ina da nawa sirrin fa”. Ya dan waro. ido, “Allah dai ya sanya ba irin nawa ba ne”. Ta fashe da dariya. “Oho, kai kuma ka jiyo, amma ga kiran sallah can”. “Bar murna yarinya, idan na idar ma nan zan dawo, don ki ji ma”. “Naf1 son ka dawo din ma. ko babu komai na kalle ka na more”. Ya fice yana kada kai yana dariya, -idan ya biye wa Hasna ba zai yi sallar ba ma; *** *** *** Wajen qarfe.tara ya iso gidan cikin motarshi, yana ta hon maigadi ya bude da sauri. Ya nufi gurin ajiye mota ya ajiye‘ya nufi sashinsa kai‘ tsaye Hajiya tana zaune a babban falonta tana ta gyangyadi amma ta kasa kwanciya don tana son ya shigo. a ranta tana damuwa da wannan daren da yake yi Cikin kwanakin nan. sau biyu masu aikinta na yi mata magana a kan taje ta kwanta sai ta Ce to. Amman taci gaba da gyangyadinta. Sai da ya yi wanka ya sanya jallabiya sannan ya nufl sashin Hajiyar tashi da sallama. Yana yin sallama ta wartsake.ta kalle shi da harara. “Ban san inda ka ke yin dare yanxuba yaron nan”……………….