BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Da k’arfi ya finciketa yace oh yanzu nagane Ashe Aljanun naki naki na iskancine “”‘toki kiyayi had’uwarmu nan gaba bazakiji da dad’iba daga yai waje tabishi da kallo zuciyarta na mata suya .

Wannan wane irin mutunne me taurin rai da bak’ar zuciya haka.

Amma wallahi bazata k’yaleshi ba su zuba su gani.

D’akinsa ya nufa babu kowa agun momy kuwa a time d’in ta fito wucewarsa kawai tagani gashi ko riga babu jikinsa “””

Da sauri ta nufi d’akin fa’eza amma bata bud’e k’ofa ba jitai fa”eza na kuka tana cewa nizakaiwa hk wallahi sena aureka komai abunka.

Da sauri momy tai d’akin taga fa ‘eza zaune jikin gado tana kuka ,,,dafata tayi tace lafyanki kuwa ?
Da sauri ta rungume momy tana kuka tace momy shine ya Musayyet ne ..

Cikin damuwa momy tace subahanallahi meyai miki.?

Kuka taka’rayi tace momy ya Musayyet ne tinda yadawo kullun seyazo dakina nace masa miyi aure yak’i wai akwai wacce yakeso ta k’arashe maganr cikin kuka.

Momy jawota tai dg rungumar datai mata suna fuskantar juna tace da gaske kikeyi?

Cikin kuka tace eh momy ki tambayeshi nasan baze fad’i gaskiyaba .

Momy kallon gadon tayi wanda yk a ya mutse kuma ta tino da wucewar musayyet data gani dazun ko riga babu jikinsa .

Kai ta dafe tace innalillahi wa inna ilaihi raju’un” wannan wane irin abun kunya kukesi kujawi mana ?

Kanta momy ta dafe wanda ke mata ciwo yanzun gamida runtse ido.

Tayama za ai haa ta faru gashi taga hujjoji da idonta babu damar t k’aryata.
Inda wani ne ya fad’a mata haka zata k’arya ta domin tasan ba halinsa bane shida ko mata basu dame shiba .””” Amma ba a shedar mutun dari bisa d’ari tunda harsuka kad’aice shida ita to shed’anne na ukunnsu.
Ta k’ara dafe kai tace ya ilahi.

Musayyet nashiga d’akinsa yace zanyi maģanin yarinyar nan wato ni zataiwa iskanciko?

Kai ya dafe take gabansa ya fad’i jin irin bugun da momy take kuma tana k’wala masa kira cikin d’aga murya a wannan daren.

Love you All my fans????????
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

  *AURAN* *BABBAN* 

        *MUTUM*

Creating And Written by

UMMEE MUKHTAR????

This page is urs

Nafeesa
Mom fauzah
Maman umar
Maryam usman.

Nagode sosai Allah yabar k’aunah❤.

          ????11

K’ofar yabi da kallo wacce momy ke bugata kamar zata 6alla”” cikin rawar jiki ya nufi k’ofar yasa hanu ya bud’eta””” yana bud’ewa momy ta hankad’o masa fa’ezah har tana cin karo da kafad’arsa kamar zata fad’i yana kallonta ko k’ok’arin rik’eta beba dan mugun haushinta yakeji yanzu.

Momy idonta taf da hawaye take kallon jikinsa daga k’asa har sama “”” shima jikin nasa yabi da kallo yanaso ya gano abunda Momy ķe nufi,cikin muryar kuka ta soma magana cikin kuka tace yanzu Musayyet irin tarbiyar danai mk kenan?

Wannan shine sakamakon kulawar dana baka tin kana yaronka harkawo girmanka? Kafad’amin menai maka da zaka sakamin da irin wannan bak’in fetin ? Dama na sani nasan cewa turaka k’asar waje da Alhaj yake dole idonka ya 6ud’e ,nan ta d’urk’usa tazube kan carpet d’in dake d’akin ta soma kuka me cin rai”””” Musayyet kam sam besan abunda tk nufiba dan haka da sauri ya durk’usa yana rik’e hannunta da zimmar ze d’agata tai saurin tankwa6e hannun ta d’ago kai cikin muryar kuka tana cewa karka ta6ani ,,,karka soma ta6ani tinda ka riga ka canja Ashe a hakane kk nuna baruwanka da mata amma cikin zuciyarka ba hk bane?

Kallon fa’eza yai wacce ta k’ame a jikin mirrow jikinta se rawa yk dan batai zaton haka abin ze kasanceba.

Musayyet kuka yafara yana cewa Momy menayi dan Allah wallahi bansan kome kk nufiba. ?
Tsaye ta mik’e goge fuskarta ta kalle shi sannan ta kalli fa’eza da sauri fa ‘eza tai k’asa dakai tana matse hannunta .

Momy tai wani murmushi me ciwo tace kana nuna kamar bakasan komai ba ko? To muje a haka amma kasani cewa seka auri fa’eza tinda kaine wanda kafara saninta a matsayin ‘ya mace “”””” inaso ka shirya cikin lokaci k’ank’ani fa’eza zata zamo matarka.

Tana fad’in haka tai waje da sauri har tana tuntu6e sotake kawai tajita a d’akinta.

Musayyet kallon fa’eza yai ya doka mata harara memakon yaga fuskarta cikin tashin hankali amma se yaga tana murmushi””””

Kallon ta yai cikin tsoro dan yanzu kam ya gano gadar zaran data shirya masa”””.. wani yawu ya had’iya me d’aci tana lura dashi dan hk tai dariya tace baka had’iyi yawuba Musayyet se randa kaji waliyammu suna cewa kazama mallakina ta har abada “”‘ kasani cewa duk abinda nakeso sena sameshi kota tsiya kota arzik’i daga ta fice tana kad’a jiki.

Tana shiga ta fad’a kan gado ta saki wani kuka tana shafa kan khairat wacce keta bacci abinta .

Wannan wane irin abune ? Yau mijinta ya ni santa da ita ranar bak’in cikine agareta dan dama idonta 2 ba bacci takeba.

Gashi a ranara ne Musayyet da Fa’eza sukai mata abinda bazata ta6a mantawa ba.

Ita kam data san hk zata faru da fa’eza bata zauna a gidan ba .

Kuka ta k’ara saki dg k’arshe tai Alwala ta fara sallah ko zuciyarta taimata sanyi.

Fa ‘eza na fita Musayyet yasa kuka ya kwantar da kansa ajikin pillow yana dad’a k’ank’ame pillow d’in cikin kuka mara sauti “”” seyanzu ya fahinci abunda fa’eza tai masa sosai yaji ciwon abun a ransa “”” Abunda be ta6a yiba yau shiza ai wa sharri akan sa? Lalle kaidin mata babbane.

Abinda yafi jin ciwo shine Momy tace seya aureta A kowane time za a iyayin maganar auran, shikam meze da ita yarinyar da batada kunya bare mutunci.

Dama nasan turaka k’asar waje da Alhaj yake dole idonka ya bude,, kalmar data sake dawo masa kenan dan hk ya dafe kai yace ya ilahi.

Kuka yaci gaba dayi daren ranar ko runtsawa beba hk ya kwana cikin kuka da 6acin rai.

Fa ‘eza kam daren ranar kamar sallah haka taita juyi akan gado takasa bacci dan farin ciki.

A subar fari Alhaj sa’ed ya farka wanka yayi yasa coffee d’in jallabiya yq nufi masallacin dake gidan …. koda ya dawo kai tsaye bangaren zarah yayi ya sake knocking wajen so 3 amma shiru ‘ murmushi yayi ya nufi bangarensa .

Zarah bata farka ba se wajen shida na safe tana tashi ta nufi toilet brush a farayi sannan tai wanka ta d’ora da Alwala duk da cewa ba sallar zataiba amma yanada kyau ka zauna da Alwala.

Tana fitowa wani d’akin tayi wanda shima a cikin d’akin yk kaya ta sauya wani material ne coffee me ratsin adon zuma a jiki sosai tai kyau abinta duk da simple make up tayi……. kan gado ta koma ta kwanta tai lamo tana kallon adon dake jikin zanin gadon me uban tsada da kyau.

Idonta ne yagano mata phone d’inta wacce tai wurgi da ita “”” tashi tai zaune ta dauki wayar se kuma ta kama juyata a hannunta tanaso ta bud’e amma tana tsoron kada wancen ya kuma kiranta.

Amma ai koba dan shiba zatai amfani da wayarta ko dan mahaifanta da kuma aysha.

Nan tasa hannu ta kunna ta gabanta n fad’uwa seda wayai tai minti goma a hannunta bataga alamar kiraba sannan ta saki jikinta gamida sauke ajiyar zuciya.

Da wurwuri Musayyet yabar gidan bayan ya shiraya kansa cikin k’ananun kaya sosai yai kyau amma kallo d’aya zakamai kagano idonsa ya d’an fad’a kad’an.

Kota kan drivern sa bebi ba wanda tin daya fito yake gaidashi amma ko kallonsa beba “”‘ hk ya figi mota yabar gidan.

Da mamaki drivern yabi motar da kallo sbd wulak’anta mutun ba halayyar Musayyet bane.

Babban Company ne wanda a time d’in karfe 7am ma ‘aikata masu goge goge ne kawai sukazo kasancewar se 8am kowa ne ma’aikaci ke zuwa .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button