BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Kallon momy yayi yanason magana amma ta d’aure face a haka ya daure yace wai khairat zata bi tin kafin ya k’arasa tace ba inda zata

Wani uban ihu khairat tasa ta kwanata kan bed ta hau birgima ita lalle setaje “””” sanin halin khairat wajen kuka yasa momy tace tatashi su tafi domin tasan in bata barta ba to yini zatai tn rigima tak’i kumacin abinci.

Cikin Murna ita da Musayyet suka rungume juna momy na kallonsu suna had’a kaya kamar wadda zata bar garin abin yaso bata daria amma ta maze cikin d’aure murya tacewa musayyet had’a kayan me kk yine ? Yinifa kawai zatai ta dawo ama se wani had’a uban kaya kk kamar wadda bazata dawoba .

Musayyet jiki ba k’wari ya juyo yace to momy nadena d’iba hk khairat muje zuwa yamma semu dawoko?

Baki ta cuno masa ita alallai se an had’a mata kayanta itacen zata koma.

Seda momy tai mata wuk’a wuk’a sannan ta yarsa suka tafi hk dama ‘yan kantine ajikinta riga da wando ruwan powder .

Sallama yaiwa momy suka fice tana binsu da kallo “””” su kadai sk rage mata wanda tafi jinsu a ranta se umman mufeedah tabbasa tn nuna masa rashin ko in kulane a zahiri amma a bad’ine tana kewarsa sosai.

Hk suka wuce mufeedah tn zaune tai zunbur tamik’e tasha gabansa tace ina zaka?

Khsirat kallon Musayyet takeyi tana kuma kallon mufeedah , be kulataba ya ratse mata ze wuce ta kuma shan gabansa cikin 6acin rai yasa hannunsa ya hankad’e ta har tana buguwa suka fice sk barta tana kuka.

Momy ce ta fito nan taganta tn kuka tace ke lfyanki kuwa”””” wani sautin kukan tasake rerawa tace momy wai dg na gaisheda yaya ya mareni harda cemin mayya.

Mayya kuma ? Momy ta fad’a tn kallon mufeedah ,,, eh momy harda cewa wai shi dole aka masa ze aureni amma meze dani waini jinin mayyace ta kai k’arshen maganar tana kuka harda shashshek’a.

Sosai ran momy ya 6aci tac nasan a rina ai dama duk namijin daya san mace kafin aurensu wlh baze ga mutun cin taba kuma taita ganin wulak’anci kenan kala kala.

Ke kikaja kanki da har kika bashi kanki Alhaj zedawone ayi auran cen kuje kuci gaba da rigimarku amma baku isa kunsamin hawan jina ba wlh kunyi kad’an .

Tana fad’ar hk tabar gun mufeedah kan dady kamar kamar yakasheta dan murna dan tanason taji maganar auransu dg bakin momy dan tasan kamar anyi angamane sbd Alhaj Sa’ed yn son duk wani datakeso.

❤ love you all
[06/09, 16:21] Ummee Mukhtar: BRILLIANT WRTS ASSOCIATION????

       ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

    _*AURAN*_ _*BABBAN*_ 

          _*MUTUM*_

Creating And Written By

UMMEE MUKHTAR????

Sadaukarwa ga Nabeelah Rabi’u Zango.

          ????23

Tin a hanya khairat keta zuba surutu hk shima ya biye mata har suka zo gida ,,,, da kansa ya fito da ita rik’e a hannunsa har cikin gidan “””””” knocking yayi dede room d’in Zarah da kyar ta taso sbd baccin daya d’auketa tin bayar fitarsa , tn bud’ewa ta ganshi da yarinya rik’e a hannu “” murmushi tai musu dukkan ninsu gamida mik’o hannunta tn son tazo gareta “”” khairat kallon musayyet shiko ya d’aga mata gira alamun taje””” .

Ita ma hannu ta mika mata tn murmushi dukkansu sukayo palor “””” seda sk zauna tace my son ina kasamo baby me kama dakai? Tin kafin yabata amsa khairat tace la kunfi kama da yayana har idanuwanku da farinku “””” dariya sukai musayyet yace dole mi kama a momy nace “”” khairat k’ara kallon Zarah tayi ta kalli musayyet tace amma yana ganta k’arama ba irin momy ba kuma kenan ynz momynka biyu? Ta fad’a tana nuna ya tsunta guda2,,….

Dariya Zarah tayi tace yasu nankine tace sunana Khairat ni suna dayane dani ba kamar anty fa’eza ba ita tafiso wai ace mata mufeedah ko mufy “”””””.

Musayyet yace wannan bakin sea yankeshi sbd surutu .

Zarah dariya tayi ta kalli musayyet tace wacece fa’eza wacece mufeedah?

Seda ya aje kan center sannan yace duk macs dayace ,kawai batason ace mata fa’eza sbd sunan kishiyar ummantane kuma bata raye amma duk da hk tana taya ummanta kishi.

Zarah tace meye abun kishi ga wadda bata raye””””

Yayana zanyi wanka “”” eh aiko nima zanyi my daughter zomuje “”hannunta yaja sk fita harda d’an gudunsu Zarah ta ware ido tn dan d’aga murya tace kuma a waje zakuyi wankan ta fad’a tana dariya “”” tashi tai ta bisu dan taha ikon Allah.

Yawo kawai taha sunayi cikin swimming pool khairat se dariya take suna ‘yar tsare “””””…baki Zarah ta bud’e ganin k’aramar yarinya ta iya wanka a ruwa amma ita ko za a kasheta bazata iyaba.

Cikin mamaki ta zauna dg gefe tn kallonsu Musayyet murmushi kawai yk mata yn yawo a ruwa kamar wani kifi “”””””.

Tace kaga ku fito kada babyn nan tai mura “”” seda yai juyi a ruwa sannan yace mura ai sede kar a kuma amma nasan setayi “”” shiyasa a gida momy take hanata wankan amma kinga yau tn free yakamata koyayane tayi.

Murmushi tayi kawai seda sukai me isar su sannan sk fito khairat se tsalle tk tana dariya shima fitowar yayi kayansa duk ajik’e “”” kallonshi zarah tayi tace aiko bazaka shigarmin palor a hakaba kana jike ta fada cikin wasa”””” smile yayi yace aiko sena shiga zan zauna anan ne kamar wata shanya.

Dariya tayi yayinda ta d’auki khairat tsam sk kama hanyar part d’in su””” kamar ze kuka yace momy ni kumafa ?juyowa tai tn dariya tace seka bushe ka shigo .

Hanni yasa a kansa ya tsuguna yn dariya khairat na masa gwalo tana cewa yeee shi ba a d’aukeshi ba .

Dariya ya kumayi yn nuno khairat da hannunsa.

Suna shiga ciki sukai toilet yayinda ta kwanto ruwa dg hiter dispenser me zafi ta sirkashi taiwa khairat wanka tasamata wata ‘yar riga body hock kasan cewar wancen kayan sun jike.

Abinci Zarah ta zuba musu khairat sezuba hira take zarah ko na biye mata .

Ihun Musayyet kawai suka jiyo dg farfajiyar gidan da sauri sk nufo wajen rungume suka gansu shi da dady , dady meyasa bk fadamin zakata hoba ai danazo ,kafin ya bashi amsa aiko khairat na ganin dadynta itama ta kwasa da gudu tai wajensu “”””

ZARAH kam kamar wacce aka dasa ta kasa gane halin datake ciki ,gaba daya bataso dawo warsa ba hk kurun tana cikin farin cikinta wani zezo yashiga rayuwarta.

Da gudu ta koma ciki Musayyet yaga hakan amma seyai tinanin ko itama murnar take amma seyaga har anyi mintuna bata sake fitowa ba.

Alhaj Sa’ed ya d’auki khairat yn mata wasa ya shafi jikin Misayyet yace yana ganka a jik’e ?

Smile yayi kawai khairat tace wanka mukai shine momynsa tace wai baze shigoba karya 6ata waje .

Dariya Alhaj Sa’ed yayi yace ah da gaskiyarta kasan zakai wankan base ka dakko wasu kayan ka ajeba koda kagama seka saka.

Musayyet ya shafi kansa yace ai dady momyn nan ta fiye rigima d’an duka dady yakai masa gaba daya sukasa dariya.

Gaba daya part d’in dady sukai basu ganta a palor ba Alhaj Sa’ed hankalinsa nakan ta sosamune yafara ganinta kafin ya shiga room dinsa amma hakan besamu ba.

Suna shiga khairat ta haye kan bed yayinda suka k’ara gaisawa da dady yai masa ya hanya yace lfy lau my son ya zaman gidan namu inceko yana mk dad’i ?

D’an murmushi yayi yace eh dady bakinsa yak’i rufuwa dan murna dady yace da magana a bakinka my son tell me “” smile musayyet yayi yace I didn’t say anything “”” dady yace nasani shine nakeso ka fadamin ai .

Ummm dama idan ka huta dady akan maganar nan ne dakace zk nemo mini wacce akeso yana fad’in hk ya yatashi da sauri ya fita cikin jin kunya. dan

Dariya Alhaj Sa’ed yayi yace my son kenan khairat ya momynki ? Ya fad’a yn shafa kanta dariya tayi tace lfyarta lau dady.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button