BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Ga mata nan masu aiki kowacce da uniform white shirt and red jeans.

Fulawo yi ko ba a magana gasunan se rangaji suke suna fitarda kamshi.

Wasu manyan maza nagani kaida ganinsu kasan sunci suntada kai duba ga yanayinsu da kuma kayan Alfarmar dake jikinsu.

Wani mutun na hango fari ne sosai sanye yk da farar shadda wacce kudinta idan aka fada zakai matukar mamaki agogon dk hannunsa ma kaida gani kasan yaja kudi.

Yanada kyau sosai kamar kata6ashi jini a fito sede kana kallonsa zaka gano shekarunsa duba da yanda furfura ta fara futo masa kadan kadan.

Hira suke cikn harshen turanci wanda a time din suke shirin tafiya daurin aure”””

Wata mata nagani dauke da turare a a hannunta se fara ‘a take da alama itace matar gidan ” tana zuwa ta fesawa Alhaj sa’id ,”” Abokan nasa kuwa dariya sukai ciki tsokana suke cewa ah lalle kin cancaci kyauta madallah da matar Arziki irinki ‘ dan murmushi tayi ta gaidasu yayinda Alhaj sa id wata kunya takamashi domin yana matukar ganin darajarta domin tayi masa halacci arayuwa.

Kudi suka hau aje mata dami dami tin tana godiya har tai shiru se murmushi kawai tk.

Fita sukai dukkaninsu Alhaj Sa’id ya sumbaceta gamida shafar fiskarta yace semun dawo ko.

Kai kawai ta d’aga masa harya fice yayinda hawaye kebin fuskarta.

Da sauri ta share fuskarta ta koma inda ‘yan uwanta suke wanda sukazo jiya domin biki.

Suna fita motacine masu yawan gaske ko wacce da driver nan suka shiga se filin jirgi.

Zarah zarah wai dan ubanki har yanzu me kikeyine a d’aki daurin auran nan kinsan fa shad’aya da rabine shine bazaki fito ki gyara jikinki kiyi kwalliya ba?. Cewar Larai.

Ah k’ila gyarawa suke kinsan kwalliyar yaran nan ta zamani bare su zainab da hafsat ga sunan duk sunzo d’azun zasu gyarane “””” baba maryam ce ke maganar.

Am wai yanaga ba a d’ora komai ba ne ko tukwane banga an d’oraba ?

Larai tai murmushi tace ai order na bada kinsan yanzu in kanadashi base kasha wahalar komai ba ai tun bikin saura sati d’aya na bada kud’i ayo sede kawai kiga an kawo nan da anjima zakigan su ‘ kawo da ranama zasu kawo wani.

Eh lalle shiyasa naga wlh banga tukunya ba to kinga ai muma hutummune ” Ah to cewar wata dake shirin shiga toilet wanka.

Zarah na kwance a d’aki se kuka take jikinta ya d’auki zafi aysha se lallashinta takeyi akan tai shiru amma tak’i

Sauran ‘yam matanne wanda zasu kai su biyar wanda duk ‘ya’yan ‘yan uwane domin zarah ba wanda ta gayyata suma hakurin suke bata amma kamar tirata suke.

Shigowar Larai kawai suka gani hannunta d’auke da wayar caja se huci take “”” Zarah na ganin ta ta mik’e tana jan k’afarta zuwa jikin bango.

Larai tace wuce muje muje nace ko”””” zarah kuka take sosai tana cewa ammi dan Allah kiyi hkr “””” mari Larai ta d’aukr zarah dashi wanda seda aysha taji kamar ita aka mara ta rintse idonu .

Jan hannuta tayi ta cillata toilet d’in dake d’akin tace ai ba wanka kika wuce nai miki ba so kike kitsinkan mutunci kuma wallahi baki isaba .

Aysha cikin tsoro tace Ammi kiyi hakuri zatayi “”” kallon banza Larai tayiwa aysha tace ke rufemun baki ‘yar karere nayi magana dake ? Waya samma koke kike hure mata kunne saboda kinga zatashiga daula “irinku nada yawa adoran k’asa na sani kawai fitowane da bazaki ki nuna ba se zagon k’asa zaki fara wankan ke kuma kose na danno k’ofar nan .

Zarah tafi jin bak’in cikin kalaman da Larai ta fad’awa aminiyarta me lallashinta kuma mebkaunarta Akan wankan da akasata setayi.

Aysha kanta na k’asa tana wasa ta farcenta yayinda ta hadiyi yawu na takaici.

Larai kanta tsaye ta shiga tafara wanke zarah sosai itako se kuka take abinta .

Sauran yan matan suma basujj dadiba duk fita sukai farfajiyar gidan suka zauna.

Wanka suma suka yi yayinda suka shiga fesa kwalliya.

K’ofar gidansu zarah cike yake da ‘yan d’aurin aure kowa ka gani cikin farin ciki domin kowa ma murnar zeyi tozali da matemakin shugaban k’asa.

Malam Hadi anci shadda gezna fara kana kallonsa kasan a farin ciki yake,

Jiniya suka faraji yayinda kallo ya koma kan hanyar wacce da sassafe mlm hadi yasa aka share layin kaf dinsa aka kafa runfuna.

Nan Manyan k’usoshin gobnati suka fara fitowa kama daka kan ministoci ‘yan majilasu govnoni da kuma manyan ma’aikata.

Malam hadi da sauri ya nufesu se washe baki yake yana cewa sannunku da zuwa mutane nan aka shiga hotuna unguwar gaba d’aya tacika da jiniya sojoji rik’e da bindugu kamar za a fita yak’i.

Alhaj Sa’id da murmushi yabawa ml hadj hannu sukai mufabaha hannun mlm hadi se rawa yake dan murna da zumud’i.

Nan suka zazzauna a inda aka tanada don d’aura auran .wayarsa ya ciro wacce se walwali take yaiwa zarah tex kamar hk.

My baby ina ftn kina lfy yau Allah ze cika mana burimmu
I love you .

Nan ya kashe phone din gaba daya aka shiga daurin aure mutane se hotuna suke.

Zarah na zaune fuskarta tai ja daure da tawul ajikinta iya cinya se kuka take k’asa k’asa Larai ce dasauran ‘yn uwanta se lallashinta suke akan ta daure tai kwalliya me kyau aysha na gefenta tace wa Larai Ammi zami mata yanzu .

Larai kallan aysha tayi tadanyi fara’ah dake tasan zata gyara mata ‘yarta tace to ku daure ayimata da wuri gasucen sunzo.

Fita sukai sy larai aysha ta rufo kofa tazo suka fara gyara zarah Abun mamaki gani sukai kawai ta tsaya ta dena kukan se ajiyar zuciya datake yi.

Daga waje sukaji ance an daura auran Auran Alhaj Sa’id wati vise president da Zarah Habib Akan sadaki naira million 10 .nan aka d’auki tafi yayinda wasu ke mamakin adadin sadakinta .

Malam hadi kamar ya suma dan dadi jiyake kamar yafi kowa sa’ar haihuwa.

Zarah najin haka ta rik’e kanta wanda ke juyawa ta runtse idonta se kuka kwanciya tayi tana burgimase shure shurw take su Aysha da hafsat na rik’eta.

Larai kuwa wata uwar gud’a ta rangad’a ita da matan gidan se barka suke wa juna sunfita zakkah a dangi.

12 dede MUSAYYIT ya sauka a Airport fuskarsa dauke da fara’a nan naga mutane sun baibayeshi suna masa barka da zuwa yana amsawa cike da kulawa yana raba musu kudi””” hak yake aduk sanda yai tafiya ya dawo dake sun saba da ma aikatan haka zeta basu kudi kamar banza.

Wani ne yace yalla6ai zamu kaika ne ko kuwa kayi waya gidane ? Musayyit ya cire farin glass din dk face dinsa yace no kaini kawai zakuyi inaso naiwa momy na surprise ne.

Murmushi sukai dukkan ninsu sukace girman kane yalla6ai.

Phone dinsa ya ciro kai tsaye layin Zarah ya fara kira wacce yai mata saving da funny gal Amma a kashe so 5 yana bugawa amma shiru.

Suit d’insa ta saman naga ya cire yana furzar da iska alamar beji dad’in hakan ba. Yaso ya fara jin muryarta domin itace a zuciyarsa amma hakan be yuwuba.

Wayar Dad ya buga itama akashe kallonsa yai yace we can go “”” nan wata mota ta parka me d’an banzan kyau suka d’auki hanyar gida.

Ummulo ce taku inasonku masoya wannan novel????????????????????
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

*AURAN* *BABBAN*                              
          *MUTUN*


Creating and written
         By

  UMMEE MUKHTAR????

SADAUKARWA ga Mom manal
Nafisa
Fulanin tashi ????
Ummu taufeeq
Amrath Amrath
First lady ko nace last lady????
Ummu nawaz

Allah yabar k’auna mutane na????????????.

        ????6

Bayan an gama d’aurin Auranne aka shiga gaggaisawa da mutane yayinda ake raba manyan bags wanda ke d’auke da manyan goro biskit sweet leman kwali da kuma shaddodi acikin kowa jaka.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button