BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

.murmushi dady yayi yace inna fahinta budurwa kayi kenan?

Da sauri Musayyet ya d’aga kai Dady ko dariya yayi harda cire hula ya aje kan center yace my son karka damu idan na dawo dg tafiya zan nemo mk duk inda tk kuma zami magana da iyayenta ka kwantar da Hankalin ka kamar ta zama matarka.

Dady yace mene sunanta Nan Musayyet ya danyi murmushi yace nima bansani ba tak’i gayamin.

Wata dariyar Alhaj Sa ed yayi yace kafiye shiririta wace wannan tk garamin d’a haka.
?

Kaga maza tashi kaje gida nima ina hanya yanzu “” nan musayyet ya mik’e cikin murna yana k’ara goge face d’insa.

Alhaj yabishi da kallo yana dariyä.

Zarah kam sosai hankalinta ya tashi akan wannan saurayi me dad’in murya tashi tayi tashiga kai kawo cikin room d’in tana tino kalamansa .

Tabbas ya shigo rayuwarta kuma da alamu zeyi nasara akanta tinda gashi tafara sonsa wannan wane irin abune ya ilahi ta furta tana me dafe kai.

Musayyet cikin farin ciki ya dawo gida su Momy na palour banda fa ‘eza dan tana d’aki.

Duk murnar da yake yana shigowa ya maida kayarsa Momy na ganinsa ta dauke kai “” da gudu khairat ta nufe shi tana oyoyo ina ice cream d’ina ?

Idonsa akan Momy amma ko kallonsa bataiba y dauki khairat yace yanzu zamu fita muje musiyo ko.

Tana hannunsa ya nufi inda Momy take ya durkusa yace momy ina yini.

Juyowa tayi ta tsareshi da ido tace eh ai ka isa kaima kanajin kanka namijine ka kawo k’arfi harda zk fita batare da kazo ka gaidani ba “””‘ ya maka kyau .ta maida kanta kan TV wanda suke cartoon .

Cikin ladabi yace wlh momy ba hk bane inada aikine sosai amma kiyi hkr.

Kallonsa tai tace aiki aiki koda yake dole kace aikine dakai ai wlh Musayyet kaban mamaki abunda kai ya d’aure min kai amma kanka kaiwa bawani ba ”””‘ idan aure kk so ai seka fad’a amma bawai kasamin 6acin rai a zuciya ba tai maganar idonta taf da hawaye yanzu nina sake Alhaj yaji maganr nan ko dan kana gani bashine ya haifekaba inda mahaifinka ne a cikin gidan ai bazaka ai kata abinda kaiba .

Kuka Musayyet ya saka mata yana rik’e k’afarta yace wlh Momy fa ‘eza k’arya takeyi tin dana dawo ban ta6a shiga dakin taba seranar ‘ a ranar ma ita takirani tace nazo nai mata addu ‘ah Ajanunta sun tashi wai takasa bacci amma wlh k’arya takemin momy banyi abinda kk tinaniba.

Fincike k’afarta Momy tayi tai hanyar d’akinta da sauri tn kuka briefcase d’insa ya d’auka yai hanyar d’aki yana share hawaye.

Da gudu khairat ta bishi ta rik’e shi tace ya musayyet kadena kuka ta fad’a idonta ta kawo kwallah kai kawai ya d’aga mata yace taje d’aki.

Yana shiga room ya fad’a kan bed yana kuka shi kam fa eza ta cuceshi. Ta had’a shi da momynsa me sonsa.

Wajen 6:30 Alhaj sa ed ya shigo gidan khairat kawai ya gani a palour tanata wasa tana ganinsa ta tafi ta rungumeshi “” da fara a ya dauketa yana mata wasa yace ina momynki?

Tana d’aki cewar khairat yace oya jeki kirawota .

Da gudu tatafi yana cewa khairat sarkin guje guje.

Tare suka fito da momy face dinta tayi ja saboda kuka dk momy farace sol.

Guru ta samu ta zauna kusa dashi suka gaisa drinks aka kawo masa se snacks dake ma aiatan gidan sunga shigowarsa.

Yace yade naga kamar face dinki ya sauya tace kantane ke ciwo amma tasha magani.

Yace idan be denaba ki kirawo doctor ko k’aruwa muka samu””” duk 6acin ran datake ciki seda tai murmushi tace Alhak kenan mumbarwa amarya de.

Dariya yayi kawai yace wa khairat ta kirawo Musayyet.

Yana kwance dagashi se singlet se wando iya gwiuwa khairat tai knocking tana shigowa tace ya musayyet kazo inji dady.

Hannunta yakama suka fito dede nan ya hango fa ‘eza na tahowa zuwa palour suna hada ido ya doka mata harara “” wani smile tai masa batadamu da kallon stanar dayake mataba.

Guri yasamu ya zauna kansa na k’asa dan bayaso dady yaga face d’insa karya gano wani abu.

Fa ‘eza kam dg cen gefe ta zauna inda momy bata hangota.

Dady ne yai magana yace dama inasone gobe jibi zaka koma gidana da zama sbd kasan ni mutunne me yawan tafiye tafiye so banaso abar yarinyar mutane ita kadai ba wani nawa agidan”””” nan tinda momy ga fa e za nan ina gani ba damuwa.

Da sauri yace to dady dan aganinsa yasamu hanyar tsira dg auran fa eza.

Wani kallo momy ta watsa masa wanda yasa shi yin kasa da kansa .

Ummolo ce taku????
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

  *AURAN* *BABBAN* 

        *MUTUM*

Creating And Written By

 *UMMEE* *MUKHTAR*????



      ????14

Musayyet K’asa yai da kansa yana shafa sumar dk kansa wacce ta kwanta luf “””Momy ta kalli Alhaj tace haba yazakace ya koma ce da zama bayan kasan ko unguwa zani bana yadda kowa ya kaini se shi””” Alhaj ya gyara zama ya fuskance ta yace hkr zakiyi Momyn Khairat ai ba nace inya tafi baze dawo bane a a ze zauna ne zuwa wani time shida ze aure ma dan nagaji da ganinsa hk.

Se anan Momy ta saki ranta tace yauwa dama ko inaso mi maganar dan kuwa ya isa aure gashi nan kullun nai magana yace ba yanzu ba to ko yanzu lokaci yayi ni kaina nagaji da zamansa hk.

Jin hakan Mufeedah yasa ta cillawa Musayyet wani kallo wanda yana kallonta yai saurin d’auke kai yace dady zan shiga ciki .

Alhaj yace shikenan gobe da yamma seka tafi seka zauna acen ciki wajen upstair nan ko?

Musayyet ya kalli Momy yace Dady dana zauna a d’aya part din dk farfajiyar gidan “”””” Dady yace a a gara ciki d’in zefi yakamata ace taji motsin wani nawa makusancina gidan tinda masu aiki wajensu daban suna da nisa daga Dady ya tashi yacewa Momy ze mata transfer kud’in data keso “”””

Sallama sukai Alhaj ya fita Musayyet yai saurin wucewa bangarensa Momy ta dakatar dashi””” bakaji ba nace “”” tsayawa yai be juyowa ba ya runtse ido “””” seda tazo har gunsa sannan ta kalleshi tace naga murnar barin gidan nan kk ko?

To inaja mk kunne duk inda kaje ka tsare mutuncinka koda yk bama zk faraba nan niku ka rainawa wayo da har kukai abunda kukai””””””

Kasani cewa yana dawo wa zami maganar auranku tan fadin hk tabarshi a gun.

Mufeedah ta kallah wacce tai kamar batasan sunayiba tai saurin ķ’asa dakai tana wasa da hannu.

Sedata wuce ya bud’e ido
Wanda yakad’a yai ja ya furzar da iskar dk bakinsa ya kalli fa ‘eza wacce ta mik’e tsaye tn shirin barin gun yace kin kyauta abinda kikai kinji dad’i ko?

Tokisani bakya dg cikin irin matan danakeso kuma kisani wlh bazan aurekiba komai nacinki dg hk yai ciki tai saurin jawo singlet d’insa yai saurin juyowa tace ai kamakara Musayyet wlh aure dole muyishi tinda Momy ta furta kasan kuma bazata karya Alqawari ba'”” gara ma kasaki ranka mene aciki.

Naga ni ‘yar uwarkace kuma me sonka.

Fincike hannunta yayi ya zabga mata marı yn nunata da yatsa yace yakamata ki farka dg gajeren baccin da kike domin inada wacce nakeso,,,, kuma karki manta Abunda nakeso shi Dady keso babu yadda zakiyi banza shedaniya kawai tafiya yai ya barta rik’e da kunci amma ko alamar kuka babu .

Kayi ta banzar ai tinda zami aure kuma sena nuna mk ni shedaniyar ce ta hak’ik’a.

Dakinta ta nufa ta maida kofa ta rufe.

Yana shiga room ya zauna bakin bed ya shiga duniyar tinani”””” kenan Momy ta maidashi wani dan iska har ja masa wani kunne take wai ya tsare mutuncinsa “”””” .

Zamansa acen zefi masa kuma baze sake yarinyar taga fuska dg gareshi ba balle ta raina shi dan yaga kamar bata da kunya””””” tashi yai ya fara had’a kayansa befi 5 set ba .

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button