BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Se 7:50 ya isa gidan Zarah fitowara dg wanka kenan body cream kawai ta shafa ta saka rigar bacci doguwa pink se karamin hijab .

Palor ta dawo ta kunna kallo wayarta ta dauka ta shiga chart “‘ Adede time d’inne Musayyet yana kwance a sofa yanashan ice cream yai mt sallama a whasap.

Bakuwar number tagani dan hk tai zaton ko a qawayen tane na grp dasuke gaisawa.

Nan ta amsa masa batare da tasan kowaye ba.

Murmushi yayi dan hk yatashi zaune “”” ..yace ya kk

Reply tai masa da ina lfy amma wacece ?

Smile yayi yace dan yankan kaine.

Itama dariya tayi ta tashi zaune tana gyara hijab tace baseka yanka mugani ba.

Shima dariya yayi yace ai tini na yanka kuma har an bani kudina.

Murmushi tayi ta qara cewa dan Allah wace.?

Seda yai jim sannan yace mata meson kine nine wanda nk kiranki a waya .

Gaban tane ya fad’i reply rai masa da cewa bacci takeji.

A gogon hannunsa ya kalla yace amma dare beba ai .

Zatai reply kenan taga Alhaj Sa’ed na fitowa dg bangarensa dg shi se jallabiya fara fuskarsa dauke da Murmushi “””” hannunta na rawa ta aje wayar gefe d’aya tana cewa a ranta na shiga 3yauhe ya dawo bansani ba?

Jikinta na rawa ta tashi zata bar gun yai saurin rik’o ta yana murmushi yace hk zami dake ko wasan 6uya? Kamar zatai kuka idonta na kallon gefe ya jawota ya zaunar da ita kan cinyarsa kanta na gefe yasa hannu ya juyo face d’inta yn leqawa yn smile yace muga idon dk jin kunyata”””””””.

K’afarta na rawa tace dama dama toilet zani “”‘hannunta ya rike yace muje room d’ina seki abinda zaki ko.

Hannunta ya kama jikinta na kyarma har sukaje bangarensa ya maida key yasa .

A bakin bed ya zaunar da ita shima ya zauna se mutsu mutsu tk da k’afa zufa duk ta keto mata ””kamshin d’akin sosai yai mata dad’i amma batashi takeba.

Kallonta yayi ya tsuguna kan k’afarta yana rik’e da hannunta yasa dayan ya juyo face dinta suna kallon juna “””” ganinsa tai kamar yaro gaskiya yanada kyau amma bazaga iya zama dashiba “” tafin k’afarta ya ta6a yaji alamun gumi takeyi kallonta yai yai smile yagano tsabar tsorone aranta kawai”””kallonta yai yace ok zaki toilet ko?

Da sauri ta d’aga kai dan dama so take ta tsere to ta inama ? Tinda a room dinsa suke.

Tashin ta yai har bakin toilet ya rakata yai mata kiss akuncinta tai saurin kallonsa tana dafe gun gamida zaro ido.

Idon ya hurawa iskar bakinsa sannan ya lakuce mata hanci yai smile yace a fito lfy princess.

Ai da sauri tashiga ta maida k’ofa ta kulle ta ciki harda sa key ta zauna a bakin bahon wanka tana maida numfashi kumatinta take shafawa da duka hannunta cikin rawar jiki ta soma kuka Ahankali tace wlh bazan fitoba anan zan kwana tai maganar cikin rad’a tana k’unshe baki.

Musayyet jin shiru ba reply yasa ya shiga kiran wayarta amma tana ringing ba a daukaba .

Alhaj Sa’ed paloru ya fita dan kashe fitulin dk Palon ””’ wayar Zarah yagani tana ta ringing number ce amma ba suna “””Hannu yasa yad’uka yana murmushi .

Ko wace yanzu take kira oho yafada yana daukan wayar?
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

*AURAN* *BABBAN* 

      *MUTUM*

Creating And Written By

UMMEE MUKHTAR????

        ????15

Wayar na hannusa yn tinanin d’agawa to inya d’aga yace me a matsayinsa na wanda bashi aka kiraba “”” dede nan wayar ta katse yabita da kallo “””” kan chair ya aje phone d’in ya nufi firij’ juice ya d’akko da madara me sanyi sannan ya nufi kitchen ya d’akko plate babba,,,, oven ya bud’a nan yaga kaji a gashe dan hk ya zuba su a wani plate d’in se cup ya jera sannan ya nufi palor .

Seda ya kashe fitilun sannan ya dauki phone d’in ya nufi hanyar bangarensa .

Musayyet zaune ya tashi ya shafa face d’insa yace meyasa yarinyar nan bata d’auki wayana ba? Zama yayi akan sofa ya tura mata tex ta layinta kamar haka.

Hy baby meyasa baki dauki wayana ba bayan kinfara samin farin ciki a wannan daren ? Ina rok’onk’i kidauki wayana pls I beg you.

Alhaj Sa’ed center table ya aje plate d’in nan yaji k’arar shigowar tex yai duba zuwa ga phone d’in sannan ya kalli toilet “”””” yarinyar nan har yanzu metake ne murmushi yayi dan yagano wayo kawai tai masa ba wani fitsari dazatai dan hk ya tashi har k’ofar toilet d’in yaje ya tsaya yace my princess kona zone na tayaki ?

Zarah tsam ta tashi tsaye tana qaraja baya gamida yarfe hannu.

Musayyet kam a wannn daren ba abinda yakeso yaji se voice din’ta dan hk be hkr ba yasake kira.

Zarah k’arar waya taji gabantane ya fad’i dan tasan watakil wannan me muryar larabawan nan ne ya kira dan hk da sauri ta murza key ta fito kanta a k’asa””” nan ko sukai karo da Alhaj Sa’ed hannunta ya kama yn murmushi yace dama nasan ba abinda kikeyi ga phone d’inki nan anata kira.

Da sauri ta dauka wanda a time d’in Musayyet se zarya yake a d’akinsa yn kai kawo.

Jin an d’agane yasa shi ajiyar zuciya yace why did you play with my heart”””” ? Dan Allah ki fad’amin inda kike zanzo komai nisan sa pls “” now I can’t sleep har se kin fad’amin ina kike “”””” Alhaj sa “ed kuwa tinda Zarah ta fito ya shiga wanka dan hk besan abunda akeba .

Ita kam se gumi tk takasa magana in banda kallon toilet d’in datake “”” da sauri ta katse wayar tai hanyar fita amma se taji kofar a kulle domin yasa key “”” dafe kai tayi tace ya ilahi.

Musayyet jin an katse kiran yasa shi cikin damuwa yace meke damun yarinyar nan ? Inasonta k’irjinsa ya kalla dede saitin zuciyarsa yasa hannu ya dafe domin ji yake tana har bawa da sauri da sauri .. Addu’ar kwantar da zuciya ya shigayi wato La I laha illa huwal azimul halim ‘ la ilaha illahuwa rabbul arshil azeem’la ilaha illahuwa rabbus samawati wa rabbul ardhi wa rabbul arshil kareem. So 3 yayi sannan yaji yayi normal kwanciya yayi amma idonsa babu alamu vacci ko d’aya.

Zarah jin k’ofa a kullë yasata dawo ta zauna a time d’in ya fito dg wanka dg shi se tawol dauke kanta tayi gefe seda ya gama gyara kansa sannan yazo ya zauna kusa da ita ya zuba mata madara a cup .

Cewa tai ta qoshi da kansa ya taso ya fara bata tana dan dauke kai gefe “””” k’aramin hijab d’in ya cire mata gashinta ya zuba har baya gabanta ne yafad’i sosai “”””

Murmushi yayi ya shafi face dinta domin ta masa kyau ai nun.

Zarah wani dan ihu tasanya ta rik’e mara tana runtse ido .

Da sauri ya kamata yn tambayarta mk damunta ? Qara rufe ido tayi cikin voice k’asa k’asa tace nima bansani ba inaga lokacin period ne yayi.

Murmushi yayi ya gano plan ne amma ze bita ahaka “””

Cewa yai sorry bari na kira doctor ko?ya fad’a yn daukan waya ‘””‘” a a barshi zata dena zuwa cikim dare tai maganar tn kallon yanayinsa ta gefen ido.

Yace ok sannu amma kidanci wani abu kafin ki kwanta .
A a na koshi.

Ba yanda beba amma taqi cin komai .

Kamota yai ya kwantar da ita dg gefensa ya rufeta da lallausan bargo shima ya kwanta dg cen bangaren yana mata sannu.

Bacci 6arawo tini ya d’auke zarah shiko idonsa viyu se dayaga tai bacci sannan ya matso jikinta ya rungumeta yn jin wani farin ciki ransa yayinda yk shafa gashin kanta me laushi da k’amshi a haka bacci ya dauke shi.

Musayyet haka kawai ya tsinci kansa da kasa bacci se tinane tinane yk .

Da wuri ya farka Alhaj Sa’ed yai sallah be koma bacci ba yana kallon Zarah nata bacci abinta “””” bargon ya bud’e seyaga babu alamun wani period ajikinta “”””” ‘yaŕ dariya yayi aransa yace Zarah kenan zanbiki aduk yanda kikaso banason danuwarki zan danne tawa damuwar koda zata cutar dani.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button