BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Jin shirune yasa ta bud’e face cikin tsoro sede ba wanda ta gani “””””” staye ta mik’e tana waige waige da gudu ta kwasa room d’inta har tana cire dan k’aramin hijabinta .

Tana zuwa tai cikin qarshen d’akin ta haye kan bed ta lilli6a tn Addu ‘a .

Musayyet na shiga room ya kwanta kan bed yana dariya yace wannan yarinyar a kwai ‘yar cartoon aiko naita tsorataki kenan bade bakida kunya ba ya qarashe maganar yn dariya.

Zarah ko abincin dare bataci ba hk ta kwanta

Musayyet naga ya tashi yn dariya a hankali ya sakko qasa cikin sand’a har gun dinig plate ya d’auka ya zuba abinci kad’an yaci ya zuba juice a cup yasha rabi cikin taku kamar na 6arawo ya koma sama yn dariya.

Asubar fari Ya nufi masallaci koda ya dawo bangaren zarah ya kalla yn dariya kad’an kad’an “””””.

Itama ta tashi tai sallah tana ta Addu’a r neman tsari da Aljanu???? .

A round 8am Musayyet ya fito cikin shirin tafiya office dan yanzu ya koyi zuwa gun aiki da wuri .

Dining ya kalla yaga kayan breakfast “””zama yai yaci kad’an sannan ya barbaza potatoes da wainar k’wai akan table ya fita cikin sauri dan bayaso matar gidan ta fito ta gane plan d’insa ””’ haka ya fita yn murmushi.

9 zarah ta fito cikin doguwar riga ta atamfa dinkin ya d’ameta tana fitowa taqarajin irin k’amshin dataji jiya da daddare .

A hankali ta lumshe ido ta soma taku har gun dining mezata gani gani tai anci a binci ga shi an barbaza wasu ‘ a iya saninta daren jiya bataci komaiba ta kwanta bare har gun ya 6aci ita hasalima kotaci abinci bata 6ata waje.

Tinowa tai da film d’in jiya na horrow aiko hannu tasa aka ta zuba ihu tace wlh bazan zauna a gidan nan ba jiya wato dabasu cinyeni ba shine sukaci abincina “‘ai da gudu ta koma d’aki har tana yarda siririn mayafinta.

Ai hkr dan Allah kunsan haryanzu da sauran fever ajikina????????????
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: . ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

  *AURAN* *BABBAN* 

          *MUTUM*

Creating And Written By

 _*UMMEE*_ _*MUKTAR????*_

INAYIWA KOWA BARKA DA SALLAH UBANGIJI ALLAH YA MAIMAITA MANA ???????? Aci Nama kad’an kad’an kada kuyi cin irin Ummy ontop????????.

Dedicated to Baby Suhyla ALLAH yaray manake musha biki????

        ????17

Zarah na shiga d’aki ta banke k’ofa harda sa key “”” D’aya d’akin ta k’ara shiga namma tasa key ta zauna cen k’arshen bed tana damk’e hannu gamida lek’e lek’e.

Wannan ne karo na farko da Zarah ta nemi layin Alhaj Sa”ed sede tana kira taji wayar a kashe .

Kuka tasa tana magana k’asa k’asa dama nasan dole gidan nan yai Aljanu wlh bazan sake fita ba “”””””””‘” A tsorace tk sosai k’irjinta n bugawa da k’arfi “”””

Wayar ta ce tai ringing aiko a firgice ta tashi tana shirin gudu domin kiran wayar ya shammaceta “””” ..daga baya ta dawo gamida lek’a phone d’in “”” se taga me wannan Number ne de wanda bata san shiba yanzu ma shiyake kira ,

Ajiyar zuciya tayi tace bazan d”auka ba Inasonsa koda bangashi ba amma Abinda nai bedace ba najin muryar wanda ba mijina ba duk da banason wanda nk aure amma hakan yazama cin amana””” kallon phone d’in tak’arayi yayinda zciyarta da shed’an ke k’ara k’awata mata muryar Musayyet gamida son jin voice d’insa .

Hannu tasa ta d’auki phone d’in gamida kashewa.

Zaune yake a office yayinda dg waje mutane masu neman aiki da wanda sukazo gunsa dan k’ulla business keta jiransa .

Shikam yama manta da cewa a kwai wasu mutane a waje sonjin muryar funny gal d’insa ne kad’ain a ransa.

Waya aka yomasa kn cewa mutane sun taru tin d’azu suna son ganinsa.

Nan yai tsaki seda yai 2minutes sannan yai magana yace mutun 5 zegani sauran sa dawo gobe .

Yes sir cewar d’aya dg cikin ma ‘aikatan.

Merry da sauran ma ‘aikatan gidan sun gyara komai sun kuma k’amsasa ko ina daga kan room freshner har turaran wuta amma har yanzu Zarah bata shigoba dan suna son shiga room d’in su gyara su kuma sauya bedshit.

D’aya wacce ake kira da oduwala merry tace taje taga madan ko lfy.

Oduwala a hankali tai knocking wanda zarah tai firgigit dg dan guntun baccin daya d’auketa .

Cikin muryar tsoro tace waye ?

Bataji amsaba kasancewar gun da dan nisa “”””Ahankali ta taso zuwa daya room d’in tace waye “”‘ cikin muryar gwaranci aduwala tace nice madammu “””‘ Ajiyar zuciya Zarah tayi cikin ranta tace keda Aljanar ai ba van baci ,duk gida anbi ancikashi da arna “staki tayi sannan ta bud’e k’ofar “”” wani suman tsaye tayi ganin oduwala domin irin black gal din nance gata taci doya ta k’oshi.

Tace lfy ? Dama munji sirune siyaca mukaci bare muzo a duba ki tafad’a cikin murya irinta masu koyon hausa.

Zarah tace am fine you can go ta tsareta. Da ido dan itama kallon Aljana take mata????””” Oduwala zatai magana tace gyaran room sukeson yi amma Zarah ta d’aga mata gira alamun tatafi kawai.

Banke k’ofa tayi ta koma ciki abinta tn cewa yanzu wannan meye amfanin ajesu agida kosu basa kawo aljanu ba mutanenda basa sallah basa addu a basa saka kayan arqik’i ji d’an siket d’inta tsaki tayi sannan ta shiga bathroom.

A round 3pm Musayyet ya dawo gida zuciyarsa nasan taje ya gaida Momy amma yana tsoro “””‘

Zarah na d’akinta taji alamun mota dan hk da sauri ta lek’o ta window dk wajen aje motar na kallo window d’inta.

Wani matashi ta gani tsaye sanye yake cikin suit black wanda suka amshi jikinsa da alamu waya yk yayinda d’aya hannun nasa ke cikin Aljihun wandonsa ya juya baya “””” bata iya jiyo muryarsa amma tana iya ganin bayansa.

Seda ya gama yana shirin juyo baya tai saurin sakin labulen window wanda yasha ado mekyan gani.

Laptop kad’ai ya d”auka ya nufi k’ofar dazata sada shi da babban palon.

Yana shigowa yaga komai tsaf ba kowa kuma an kwashe komai na dining an jera wasu flask d’in.

Da murmushi ya nufi dining d’in flask ya bud’e seyaga jollop rice ce wacce tasha bushashshen kifi se farfesun kan rago zama yayi ya zuba kad’an yaci sannan ya nufi bangarensa “”‘ daf da ze wuce bangaren Zarah seya tsaya yana kallon wajen da ido .

Upstair ya hau yaje yai wanka yasaka red shirt da bak’in wando iya gwiwa ya kaunna kallo.

Zarah kam yunwa ta isheta firij ta bud’e setaga cake saura guda 5 da sauri ta d’auka ta hada da juice ta kamaci.

Ammi ce zaune gaban wani bak’in inyamurin boka wanda haka yake kamar tsinke se k’aton kai ganye ne kad’ain ajikinsa zaune yk cikin wata bukkar zana “””” Ammi tace sonake yaci gaba da sonta kamar hauka duk da dama yana sonta sosamune duk inda zashi tana tare dashi.

Dariya Boka Emeka yayi yace zanbaki Abinda zècigaba da sonta kuma koda yaushe ze kasance yana sha’awarta ta harkar Aura tayya ze kasa sarrafa kansa aduk sanda yake gunta “”haka kuma koya fita zeta zauna a k’wak’walwarsanė kamar yadda rubutu ke zama akan k’aramin yaro me basirah koma fiye da haka.

Amma SHARAD’IN anan shine kartai amfani dashi inzata fita idan baso kike ‘yarki ta dawo gida da gudu ba dan mazane zasu ta binta kamar hauka “””” ina had’a wannan abunne gamata masu kud’i ko manyan karuwai””” idan hartai amfani dashi to mijintane kadai zezauce akanta …. Seya mik’awa ammi wata kwalba wanda wani tirarene a ciki bak’i dashi kuma dan kad’an bame yawa bane.

Hannu na rawa ta amsa tasa a jaka ta d’ebo damin kud’i masu yawa ta bashi amma yace ta aje cikin wata k’warya “”””

Daf da zata tashi ya k’ara maimaita mata dacewa ita wacce za a kaiwa ta tabbata mijinta kad’ai zatai amfani dashi kuma ajiki kawai zata shafa kar a sake wani namijin yaji wannan k’amshin.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button