BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

D’ayan yai dariya yace eh mana Ai kasan ance kud’i hana magana idan kanadashi balarabiya zaka iya aura . D’ayan yace kai wallahi kwadayi ma beba suka kwashe da dariya.

Da gudu ta wuce su tana kuka ta fad’a gidansu Aysha .

Aysha na tsakar gida umanta bata nan da sauri ta tasa kanta kan
K’afar aysha tana kuka.

Aysha ta d’agota ce menene Zarah dan Allah kidena sa kanki a damuwa kada wani ciwon ya kamaki.

Zarah cikin kuka tace kowama yasan Auran kwadayi za ‘ min Aysha ya bazanyi kukaba ?

Nan taita bata hkr akan komai mewuce wane .

Kud’in da ummanta taba ta tafi to dasu ” Aysha ta dubi kudin tace wannan fa ?

Hawaye Zarah ta goge tace wai gyaran jiki zani kome zan gyara oho.

‘Yar dariya aysha tayi tace ah bari mu tashi muje afara yau zuwa gobe shaken an kada lokaci ya k’ure duk da yariga yak’ure.

Harara Zarah ta watsa mata tace malama ba inda zani wallahi kawai na fitone de dan kar ace banje ba.

Kallon ta Aysha tayi tace aike ko ba gyara wallahi da kyanki ko baki kwalliya kullun k’ara kyau kike musamman yanzu da kika samu Alhajin nan irin cimar dayake kawo muku gaba d’aya kin koma kamar wata shuwa Arab.

Ga rayuwa data sauya muku kun koma kamar damacen kud’in masu kudine ki godewa Allah.

Zarah batace komai ba se daga cen tace kawai ni kurkur zan ganbad’a ajiki da fuska shine zesa taga kamar naje .

Dariya sukai Aysha tace kin kawo shawara.

Nan suka had’a madara da kur kur se lemon tsamj kad’an wanda suka matsa ciki gaba daya suka shafa jiki da fuska .

Seda yai kamar 20mnts sannan suka wanke .

Wani suka had’a daban kurkurne da manja shima suka shafa daga baya suka wanke.

Sosai zarah ta k’ara haske damacen farace sol gata da gashi hanci kuma ga ido fari tas kamar madara.

Ba doguwa bace baza kuma a sata a sahun gaeru ba tanada jiki me kyan k’ira Allah ya hore mata mazaunai da dukiyar fulani dede misali wanda yake jan hankakin ‘yan maza , .se d’an k’armin bakinta wanda aduk sanda take magana seya burge me kallo.

Aysha chocolate ce tanada kyau dede azanci.

Aysha kallon Zarah tai tace saura abu daya .

Tace me kenan? Aysha tace baki lalle ajiki ba duk da nasan jikinki damacen me laushine ga shinan ko a ido aka kalla.

Tsaki tayi tace bazan ba .

Dariya Aysha tai tace wallahi sekinyi so kike ta ramfoki baki jeba?

Zarah Tace kuma hakane fa.

Lallan suka sa a tasa nan ma sukazuba kurkur kadan suka juya suka dora a wuta minti biyu ya tafasa suka sauke suka zuba man zaitun sannan suka.shafa ajiki.

Ruwa me dumi Aysha ta dora Zarah ta fara shiga tai wanka “”” bayan ta fito aysha ta shiga.

Umman Aysha ce ta dawo suka gaisa da Zarah tana tsokanarta Amarya kinsaha kamshi.

Nan zarah tace zash tafi da aysha a gidansj zata kwana .

Tace ai bakomai kuje Allah yai muku albarka.

Ahanya Aysha tace kinga yanda kika kara haske kamar gyaran jikin gaske kikaje?

‘Yar dariya sukai nan Zarahta d’akko 30k daga cikin kudin ta bawa aysha .

Aysha tace mezanyi da wannan ? Zarah tace baki nai ” ni kuma? Cewar aysha ai ban ta6a rik’e irin wannan kudin ba ko ummata bata da wannan kud’in.

Zarah tace shiyasa na baki kuma umman ma zan bata nata kinga ko jari kwaja
tinda mahaifinki ya rasu Aysha.

Rungume juna sukai Aysha na kuka tanai mata godiya.

Suna shiga gidan kai tsaye d’akin Zarah suka wuce dan ita bataso ma kowa ya ganta.

Ummulo????????????????
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

    *AURAN* *BABBA*

Creating and Writting by

Ummee Mukhtar

HIKIMA WRTS ASSO????

SADAUKARWA GA DUKKAN MASOYA WANNAN NOVEL ALLAH YABAR ZUMUNCI????????

         ????3

Suna shiga d’aki zama sukai a kujerun dake d’akin suna kallon juna gamida murmushi Aysha tace Allah yasa de kada umma ta gane bamu jeba “”””” Zarah ta cire hijab gamida warware dogon gashinta wanda ya zuba har baya ta zauna kusa da Aysha tace karki damu bazata ganeba .

Wata jaka ta dakko dake cikin drower ta zuge kud’ine a ciki fal wanda zasukai kimanin dibu d’ari uku da hamsin Aysha tai saurin zare ido “””” tace ke wannan kud’in fa ?

Wani dan guntun smile Zarah tayi gamida yin tagumi tace zaki d’auki dukansu ki kaiwa ummanki “”” Aysha tace wa? Rufamin asiri ai in aka ganni da wannan kud’in cewa za ai mutun na siyar nasame Su.

Dariya Zarah tayi wacce rabon datayi irinta harta manta domin yanzu bak’in ciki ne lullu6e a zuciyarta gameda Auran nan .

Tace ok ni zan kai mata da kaina amma ko kin manta mutumin nan d’an siyasane yana daya daga cikin masu baiwa shugaban k’asa shawara kin tina?

Aysha ta gyad’a kai tace hakane.

Zarah tace to su kud’i ba wani abu bane a gunsu dan haka kema kici naki rabon domin kuwa kud’immune .

Dariya sukai Aysha tace gaskiya zakiji dad’i ‘yan nan wannan idan kikai wata daya nazo gidanki wallahi zan iya kuwa ganeki?

Duka Zarah takai mata tace eh saboda kinsan zan koma kamar dodo ko?

Nan Aysha tace no ba haka nake nufiba zade ki k’ara kyaune hajiyata.

Suna cikin magana Larai ta shigo kafin tai magana se taga Zarah k’ara wani haske da kyau””” fuska a sake tace kai masha Allah kin ganki kuwa nagode miki ‘yata ai shima ya dad’a ganinki da kyau.

Motsi Zarah takamayi da bakinta Alamar tana k’unk’uni domin ta tsani taji an had’ata da Alhaj Sa’id.

Nan ta juya kan Aysha tai mata wani kallo na raini tace au kema gyaran jkin kikayi ?

Cikin sanyin murya Aysha tace eh umma.

Baki Larai ta ta6e ta kalli Zarah fuska a tamke tace kinajina gara ki k’ara gogewa da wayewa domin nan gaba kad’an zakifara mu amala da matan masu kudi gogaggun matan ‘yan siyasa to karki da wasa nide nagayamiki .

Zata fita kenan ta k’ara juyowa ta harari Aysha kad’an tace ni yaye yayene banaso kowa ya tsaya iya matsayinsa daga hk tai waje taja musu k’ofa.

Zarah kallon aysha tayi tace pls kiyi hkr dan Allah nasan dake take ” ta manta cewa muma da haka muke ba shine da muba .

Murmushi aysha ta k’ak’aro tace ke kinji ki waya gayamiki dani take kawai fa tana miki baya nine idan kinyi aure kema zaki shiga a dama dake.

Uhmm Zarah tace da Aysha tace kede kawai kin waskene amma dan Allah kiyi hkr .

Dan Allah meye hk banaso na fad’a miki ba dani takeba.

Yauwa wai wane kayan zakisane ran d’aurin aure anya ma kinyi gayya naga ba wata k’awa da muka gayyata?

Baki ta ta6e tace aysha dan Allah dan Annabi idan kinason farin cikina kidena min maganar komai akan auran nan dan Allah.

Tsaye aysha ta mike tana me shirin shiga toilet d’in dake d’akin danyin wanka ” tace yanzj hk za ai auran kamar wani auran bazawara ?

Naga zaurawamma na yanzu idan kikaje bikinsu wallahi seki rantse bikin budurwa kikaje.

Amma tinda kince a barshi ba komai.

Daga hk ta shiga toilet.

Cuno baki Zarah tayi tace lalle ma Aysha dama saurayi zan aura shine zanyi wannan gwad’aren amma ba wannan ba daga tai kwanciyarta a kan gado.

Ba yan ta fito daga wanka Zarah itama ta shiga tai nata wankan gamida d’orawa da Alwala.

Seda akai ish’sha sannan sukai shirin kwanciya bayan an kawo musu abinci me rai da lafiya.

Zarah gwanace wajen yin chart da hakane tai abokai da yawa maza da mata “” Amma komai mutuncinka da ita da zarar kace kana sonta zatai blocking d’inka .

Yanzu ma wayarce rik’e a hannunta se faman latse latse take.

Aysha tace nima gobe idan mun fita waya zan siya nima na shigo gari “”” ‘yar dariya Zarah tayi tace karki damu goben idan Allah ya kaimu semuje cen berud road musiyo ko?

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button