AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Jin kiran sallah ne ya dakayar dashi dg tinanin daya tafi “””””ya fito yasa coffe d’in jallabiyarsa ya sakko k’asa dn zuwa masallaci
Dede room d’in Zahra ya tsaya yn kallon k’ofar cikin ransa yace wannan kota tashi koya jikin nata “”””””” yafi minti 3 agun sannan ya fita bayan an idar ne koda yadawo a palon da sukai kallo jiya nan ya zauna ya kunna tashar sunnah Tv yana jan casbaha lokaci lokaci yn kallo hanyar room din Zarah .
Har wajen 8:00 bata fitoba kasan cewar yau sunday ba aiki hakan ys Musayyet ya d’an kwanta agun k’asan carpet aiko vacci ya d’aukeshi.
Se wajen 10 ta fito sanye da wando skin tei bak’i se jar riga mini wanda ta tsaya mata a iya k’ugunta se farin hijab datasa har gwiwarta “””” makeup tayi sosai wanda tajima batai irinsaba tasa turaranta me k’amshi tai parking da gashin kanta tasa ribon guda d’aya amma sekai zaton da yawa tasa sbd tozon da gashinta yayi sbd Allah yahore mata gashi.
Koda ta fito sauran palon ba kowa ,,,, kallon d’ayan palon tayi nan ta hango shi kwance dan hk tai smile ta nufi wajen tana cikin sand’a dan bataso yajita .
Tana zuwa tsaye tayi kansa tn kallon yanda yk bacci face dinsa kamar me smile yana yin mouth d’insa kawai zk kalla kasan cewa musayyet time d’in dayake yaro ya zuba shagwa6a dan mouth d’in nasa kamar na yaro tayinda yaso shagwa6a
Dariya ce takamata ganin yanda yk bacci da sauri ta rufe bakinta ta 6uya bayan chair cikin muryar ban tsoro tace miyauuuuuuuuu kamar dg sama Musayyet ya farka yn dube dube amma ba abin daya gani giŕgiza kansa yayi yn shafa face d’insa ya koma ya kwanta harda gyara pillow.
Tana kallonsa tn murmushi dan hk ta kuma matsowa dede inda zejita ta kuma cewa kaiiiiiiiii mee bacci miyauuuuuuuu ai da sauri Musayyet ya tashi yn karanto Ayatul kursiyu yn dube dube lek’e lek’e yakamayi ciki kuwa harda bayan kujeru wanda Zarah kanta a k’asa yk tana dariya batasan yn dube dube ba
K’amshin turaranta kawai yaji yasan cewa Zarah ce.
Tsaye yk akanta ya hard’e hannunsa a duka k’irjinsa yn kallonta face d’insa d’auke da smile wanda duk batasan abunda yakeba .
Har ya tsuguna yn kallonta duk batasani ba jitai kawai yace sannu Momy sannu da tsorata d’an naki ya fad’a yn murmushi don yagano jiyama itace ta tsoratashi.
Da sauri ta d’ago kai suka had’a ido ya.d’aga mata gira yana dariya ahankali yace Momy kinyi k’ok’ari fa “””” dariya tayi tana shirin tashi ya tsai da ita “”” juyowa tayi tn kallonsa shiko kallom dukkan jikinta yk ganin skin tie d’in datasa ya matseta k’afa amma baka iya gano komai na jikinta kallon kyawawan fararan legs d’in ta kawai yana ji aransa inama yasamu mace kamarta””” yarinya me barkwanci da iya kwalliya .
Jiyai tace my son ka tsai dani yunwa nakeji kuma .
Dariya yayi yazo har gabanta ya kafe ta ido suna jin K’amshin juna yafara magana kamar bayason yi yace wato so kk d’an naki ya kamu da ciwon tsoroko?
Kanta na k’asa tn wasa da gefen hijab dinta tace ai kaika fara my son.
Dana fara ai na bada hkr ashe bk hkr ba yafad’a yn kallon yanayinta “””””” Zarah tace ai bazan sakeba kawai dama inaso naga jarumtarkane.
Dariya yayi yace zakiga jarum tatane se randa na kawo mk zuk’ek’iyar Amaryata anan zk tabbatarda ni d’in jarumine”””””””” ..dariya tk sosai harda nunoshi da yatsanta tn dariya shiko kallonta kawai yk cikim ransa yn mamakin yanda komai idan tayi kyau yk mata “””””
Seda tai me isarta sannan ta kallo shi tace kai kuma jarumtar taka akan za6o kyakykyawar mace zakai ?
Yace eh man Momy ranar zakisha mamaki nide yanzu nima yunwa nakeji sonake naje gidan d’aya momyn tawa “”””.
Zarah tace nima dana bika”””” Musayyet smile yayi yace sede kuje da dady na .
Lokaci d’aya .face d’im Zarah ya canja dan bataso ace wani abu wanda zasu ke6e da dady ya hadasu.
Musayyet na kallon yanayinta domin batin yanzu yagano kamar batason dadyn saba amma be magana ba kasancewar ba hurumin sabane.
Nan ya canja salon hirar yace shikenan zamuje tare amma sede idan dady yn gari kin yadda?
Girgiza ms kai tayi tace ita ta fasa zuwan ma gamida juya masa baya.
Sosai ta bashi dariya ganin yadda tk masa shagwa6a yace nina ta6a ganin uwa tafi d’anta shagwa6ama ? Bari dady yadawo gidan zan barmiki sede in kiyiwa dady na “””.
Da sauri ta jiyo tn cuno baki cikin jin haushi tai hanyar dining Musayyet ko bita yayi yana dariya yana bata hkr.
Se 12 yabar gidan yai mata sallama kan cewa zashi gidan momy “””””kallon shi tayi kawai taci gaba da danna phone shiko yn tsaye yn smile yace momy sarkin rigima nide gaskiya k’anin da zaki samar min nan gaba banaso kisamo mana me rigima garama tin yanzu na fad’a miki kiji “”” ai batasan sanda tai dariya ba ta d’akko pillow ta jefa masa ya fita yn dariya da jin nishad’i a ransa .
Har yabar gidan Zarah dariya tk domin yasata dariyar daba tai niyya ba”””” can kuma hawaye sk shiga biyo mata cikin k’aramar voice tace bazan haihu da Abban kaba har abada domin bana sansa tsautsayi nima da karan banina ys har yasan gidammu kuma ya aureni .
Gate aka bud’e masa ya shigo har ynz da fara’a zaune kan face d’insa masu gadi suna kallosa d’ayan yace sir Musayyet sarkin fara a .
Muffedah ce da Khairat zaune sunyi ruf da ciki tana nunawa yanda khairat zatai Art d’in bird
Da sallama ya shiga khairat naganinsa ta taso d gudu tm cewa oyoyo my yayana , da fara ah ya dauketa yn kissing d’in gashinta wanda yasha gyara yace dake zan tafi my daughter”””” yeeeeeeee khairat ta fad’a tn daga hannu sama .
Harara ya dokawa mufeedah wacce ta tsareshi da ido tin shigowaraa tn mamakin wani kyau daya k’ara kamar wani ango dan bana bakwai.
Musayyet yace idan mutum mayene sede yaci kansa, da sauri khairat tace yayana meye maye?
Tana kafad’arsa ya juyo da face d’in ta yace my daughter ana nufin duk wanda yafiye kallon mutum shine maye kuma har cin mutane ma sunayi.
Khairat cikin tsoro ta k’ank’ame musayyet tace wayyo Allah ys bazasu cinyenba .
Mufedah tazo iya wuya dan ta fahinci da ita yk rainin wayone kawai yk nuna mata.
Musayyet yace inde kina addu a bazasu cinyeki ba
Muje ciki gun momy.
Zasu wucd kenan mufeedah ta tashi tsaye cikin hasala tace kuma mutum komai taurin kansa da gaddamarsa dole seya kasance mijina uban yarana ba yadda zeyi .
Ko kallonta beba yai ciki shida khairat tn ta bala I dg k’arshe tasa kuka wai itace mayya idan har ita mayyace to shima mayene dan kuwa jinisu d’aya ne.
Da sallama ya shiga d’akin momy tana zaune tn irga wasu kud’i tana ganinsa ta juyar dakai gefe taci gaba da abinda takeyi “”””””” cikin ransa yace yace wato momy na da d’aya momyn kenan bas yafiya? Duk abunda aka musu se sun rama? Dan murmushi yayi ya aje khairat dg gefe yaje har gunta ya tsuguna gamida rik’e k’afarta ta rufe ido yace momy ina kwana yai maganar cikin murya mevan tausayi ,,,.
Seda tai tsai sannan tace lfy lau ya zaman bak’unta ? Sosai yaji dad’i harda fara’arsa yace lfy lau momy tace ma na gaisheki.
Kallonshi tayi da mamaki tace au yaushe kazama me baki bn sani ba ? Kace har hira kukesha da itako?
Da sauri yace a a momy iya kacimmu gaisawa kawai karo na farko kenan daya gillawa momymsa k’arya arayuwa.
Cigaba tai da had’a kudin bata saurareshi ba khairat tace nima zan bika yayana.