BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Aysha fara’a tai tace Zara kimmin komai bansan dame zan saka mikiba .

Juyowa Zarah tai tace kinsan dame zaki sakamin?

Girgiza kai Aysha tayi zarah ta tashi zaune tace to sonake kidena cewa nai abunda zesa kowa yasan inason auran nan kawai kija bakinki kiyi shir,,,,,,,,,,,,,,
Ai kafin tak’arasa Aysha ta kwashe da dariya tace ok tona dena

Mintsininta Zarah tayi cikin wasa Aysha tace Allah zesakamin Zarah tace yasakama na tare.

Dariya sukai me isarsu””sunata hira har wajen k’arfe 11 sannan sukai addu’ar kwaciyar bacci kowanensu yaiwa d’an uwansa seda safe.

Kyakyawan matashine wanda kallo d’aya zakai masa katabbatar da cewa shid’in daga gidan hutu ya fito duba ga fatar jikinsa zuwa kayan dake jikinsa .

Kallo d’aya zakai masa kasan shid’in sun had’ajini da shuwa Arab”” ya had’u sosai dogone amma ba cenba farine sosai kamar balarabe haka sumar dake kansa bak’ace wuluk wacce ta kwanta luf akansa”””” kana kallon idonsa zakaga har wani walwali yake kamar gwal”

Yanada hanci dogo se matsakai cin baki.

K’irjinsa kwance yake da gashi kamar na india wa wanda yake tafiyar da hankalin ‘yam mata .

‘Yam mata basu da meshi ba ko kad’an sede su suke kawo kansu gareshi da k’ok’on barar soyaiya koma ya aure su.

Hakan baya gabansa domin shi har yanzu bega macen datai masaba.

Mata da yawa kan nemi shi koda kwanciya ce yayi dasu koda be aure suba Amma shid’in mugun miskiline ba kuma ya fasik’anci ko Alfasha.

Sanye yake da jar T shirt se bak’in 3quter wanda ya baiyanar da sumar dake kwance a k’afarsa ta kwanta a dukkan jikinsa.

Wasu turawa ne biye dashi a bayansa rik’e da wata box wanda suke d’auke da muhiman papers aciki wanda ake gudanarda harkar cinikayya tsakaninsu da wasu daga cikin companin dake k’asar ta Switzerland.

Wani bene suka hau yayinda suka danna lifter tai sama dasu seda sukaje har wani guri megirman gaske sannan suka bashi box d’in ya shiga ciki ya d’akko musu wata box d’in sannan sukai sallama suka juya.

Yana shiga kai tsaye toilet ya shiga yai wanka wanda fad’ar had’uwar toilet d’in 6ata lokacine.

Komai na d’akin a don golden ne nan ya fito sanye da tawul yana goge jikinsa lokaci lokaci yana d’an tsaki .

Seda ya 6ata time a gurin shafa mayukan dake zube akan mirror kamar wata mace sannan daga k’arshe yasa singlet da wani 3quter amma dukansu white ne sannan ya haye bisa makeken gadon.

Phone d’insa yad’akko yana k’ok’arin had’a wasu numbers alamun yayi missing number dayake son kira.

Zarah misalin 12 na dare bacci take sosai taji phone d’inta ya d’auki ruri .

Cikin lalube takai hannu ta d’akko idanuwanta duk a rufe tai picking call cikin muryar bacci tace hello “”””” daga d’aya bangaren yace ina magana da wace?

Turo baki tayi duk da hk idonta a rufe tace oho kai daka kira bakasan waka kiraba ?

Cire phone d’in yayi daga kunnensa ya k’ara kallon phone d’in ” yace am sorry dan Allah ba momy bace?

Cikin tsiwa Zarah tace ah kakace ” dariya taso kamashi amma ya daure beba yana dad’a saura ranta. zaune ta tashi itama tana kallon number da alamu ta k’asar waje ce towa suke dashi a k’asar waje?

Taiwa kanta wannan tambayar.

Tace ko bakajiba ok kaima kasan BABBAN MUTUN zan aura shine kakirani kaci min mutinci?

Katseta yai yace kiyi hakuri wallahi momy na nakeson kira inaga ba dede nasa number bane but am so sorry.

Tsaki tayi tace to wannan baby ka kira ba momy ba d’if ta kashe wayar gaba d’ayanta tai cilli da ita gamida komawa bacci.

sosai yarinyar ta bashi dariya kalamanta duk na k’uruciya ne zeso yaga yarinyar nan azahiri””” Haka nan ya tsinci kansa cikin farin ciki dajin muryar wannan yarinyar dabema san sunan taba.

Seda ya had’a number wajen so 3 yana kira amma ba wacce yake nema bane.

Harya hkr ya k’ara gwadawa cikin ikon Allah number momy ta shiga.

Zaune take kan dadduma da casbaha a hannunta tanaja taga kiran sa.

Da sauri ta d’aga dan ko ba a fad’a ba tasan k’anin natane .

tana d’agawa tace kaiko MUSAYYIT anya lfy kuwa yau sati 2 data fiyarka ba kira ba d’aga hannu?

Dariya yai yace am sorry momy wlh na yarda duka sim dina ne kuma kinsan bana haddace number waya shine dalili wannan ma dakyar na had’a ma kira bayan nase wani layin amma amin afuwa.

Murmushi tayi tace Musayyit sarkin shirirta to da ftn ka gama komai kasan Auran Abbanka ya kusa “””” seda yai jim sannan yace to momy insha Allah jibi ina hanyar dawo wa kitana di kayan dad’i dariya tayi tace bazan ba inkayi zuciya kai aure.

Murmushi yayi yace inna dawo akwai labari .

tace da gaske ?

Yace Allah momy daga haka seda suka dauki tsawon awa daya suna hira daga k’arshe sukai sallama.

Kwanciya yayi yana murmushi yana tina hirar da sukai da yarinyar dabe santaba gashi tana nema tazauna a zuciyarsa.

kalma d’ata tak ya tuno da take cewa kaima kasan BABBAN MUTUN zaura shine ka bugo kamin rashin mutunci.

Tsam ya mik’e tsaye yana zagaye tafkeken d’akin zuciyarsa na masa wani iri wandabe san komeye ba.

kubiyoni dan jin yazatakasance tsakanin MUSAYYIT DA ZARAH

Shin musayyit kode d’an Alhaj sa’id ne?

ummulo ce taku har kullun????????????
[31/08, 16:19] ‪+234 905 934 3174‬: ????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀????????‍♀

*AURAN* *BABBAN* 
         *MUTUM*       

Creating And Written by

 *Ummee* *Mukhtar*

HIKIMA WRTS ASOO????

          ???? 4

A subar fari mutan gidan suka tashi dan gabatar da sallar Asbah bayan sunyi ne wasu daga ciki suka koma bacci ” yayin da wasu suka zauna zaman hira .

Zarah da Aysha tin 4:30 suka tashi suka zauna suna hira bayan sunyi sallar Asbah ne suka koma bacci.

Misalin 7:00 kiran a wayar Zarah ya fara ruri yayinda suketa bacci abunsu.

Aysha ce ta farka ta d’aka mata duka tace tashi inaga Angon ne ke kirah “”” Mik’a Zarah tayi ha’d’i da salati tana mutsitstsika ido tace yanzu akan wannan kike tashi na ?

Wama ya fad’a miki yanada lokaci na mutum kullun a tafiye tafiye daga wannan k’asa zuwa wannan k’asa ” kai ta mayar ta kwata gamida yara pillow tana cuno baki.

Haka wayar ta gama ruri ” Aysha na shirin kwanciya ta kuma jin wani kiran ya shigo tashi aysha tayi ta jawo phone d’in setaga number amma ba suna d’agawa tai gamida sallama .

Kwance yake a d’aya daga cikin sofa d’in dake palourn hannunsa rik’e da cup na green tea yana sha kad’an kad’an aje cup d’in yayi yace mrng funny gal how are u anda how was ur lst 9t? Aysha k’unshe bak’i tayi tanaso tai dariya cire phone d’in tayi tana k’ara duban wayar “”” am sorry barina tashe ta bacci take me wayar .

Tsaye ya mik’e yace no karki tashe ta batta tai baccinta amma pls idan ta tashi ko plashing ne kimin kinji dan Allah.

Da sauri tace to to .

Kashe phone din yayi ya kama had’a mahimman kayaiya kinsa domin yau yakeson tafiyama tinda yariga daya kammala komai daya kawo shi.

Mamaki aysha take waye to wannan kode kabeer ne wanda ya tafi da har yanzu bedawo ba?

Tace kai bashi bane wannan muryar sa kamar ma ta larabawa ba haka voice d’in kaber takeba.

Kwanciya tayi abunta gamida aje wayar akan table.

Ta kwas dede suka farka a time d’inne suka fito dan kar6ar breakfast.

Kitchen suka nufa da kansu suka hada komai suka koma d’aki.

Bayan sun karya wanka sukai suka fice yayin da Zarah ta d’auki jakarta wacce take d’auke da kud’i.

Aysha tace muje mugaisa dasu mana kafin mu fita “Zarah cewa tai ita ba inda zata kawai tataho su tafi.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button