BABU SO HAUSA NOVEL

AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Kowa murna yake da hakane suka nemi cewa zasu shiga gidan domin a gaisa da iyayen Amarya “”” ai Mlm hadi da gudu sauri sauri yana washe baki yace ah bismillah bisimillah ai gidan kune nan ranka ya dad’e baya ya dawo ya tsaya yayinda yakewa Alhj Sa’id da mutanen sa nuni dasu wuce kan gaba.

Mutane da yawa sungano tsagoron son k’ud’insa da kwad’ayi ne yasa shima bada yarinyar ga babban mutun irin Alhaj Sa’id.

Murmushi Alhaj Sa’id yayi yafar wucewa yayinda sauran ke take masa baya.

Cikin gidan kuwa se gud’a ake ana Zarah tayi goshin da ba kowace mace ce keyiba seme sa’a a rayuwa.

K’amshin turare ne me kamshin gaske yaja hankalinsu wanda sukai duba ga hnayr da k’amshin ke fitowa se sukaga Ashe Angone da mutanensa.

Nan naga ikon Allah ai gaba d’ayan matan dake gun k’asa naga sun durk’usa kamar masu neman gafara suna gaida vise president.

Laraice kan gaba wajen iya durk’usa se godiya takewa masa yayin da shi kuma ya durk’usa cikin girma yana gaidata da sauran Abokan nasa.

Cikin rawar murya Larai take amsawa mlm hadi kuwa baki yak’i rufo.

Alhaj Sa’id duba yake ga kowane kusurwar gidan soyake yaga Zarah amma yanajin kunyar tambaya.

Baba maryan ce ta lura da hakan tai saurin cewa bari akira amaryar da kawayenta.

Cikin sauri suka mik’e da Larai suka nufi d’akin dasu Zarah ke ciki.

Kanta a dafe suka sameta amma make up da Aysha sukai mata yana nan sede idonta da yai ja Alamun harta gaji da kukan datakeyi.

Larai ce tafara shiga nan ta iske su sunata kwalliya da fesa turaruka Larai da baba maryam suka wash baki Larai tace yauwa ku d’ad’a gyagygyarawa ga k’usosgin gobnati cen A farfajiya ko kuma Allah yaci daku kuyi mana kamun babban kifi.

Gaba d’aya ‘yan matan sukasa dariya Aysha ko fara ah babu a fuskarta bare zarah dako d’ago kai batai ba .

Larai tace maza ku tashi muje kema harda ke ga angon cen nason ganinki.

Zarah mutsi mutsu kawai take da bakinta ita haka take aduk sanda abu be mata dadi ba setai ta mismis da baki wanda ita kanta batasan dalili ba .

Larai ce ta k’ara fesheta da tirare gamida kara mata wata powder a face dinta nan ko tai wani kyau dam cen din ita me kyance.

Hannu ta kamata suka fito da sauran yan matan harda aysha.

Tin daga nesa ya kafe da ido ko k’iftawa ba yayi Yayinda fiskarsa d’auke da Murmushi “””” Ministern K’udi’i na lura dashi dan hk da sauri ya d’an zungureshi nan ya dawo dg duniyar tinanin daya shiga .

Itako ko d’aga kai bataiba don batason kallonsa bare jin muryarsa.Abokan sa kam sosai suka yaba kyan zarah gata yarinya me jini ajika lalle abokinsu yayi sa’a.

Nan ‘yam matan suka shiga gaidasu cikin kwarwasa suna amsawa aysha ma hk “””” Alhaj Sa’id magana yaiwa da d’aya dg cikin escort dinsa nan aka shiga bawa matan dk gun kud’i ko wacce 30k a cikin ambulan.

Murna kam ba amagana nan suka tashi suka fita matan se godiya suke “””” Alhaj sa id mutunne me kunya sosai shiyasa ma yakasaiw zarah magana kwata kwata.

Zarah kam tazo iya wuya jin kirarin da matan ke masa shida mutanen sa wanda dagaji kasan idon su yarufe akan kud’i suke yin hakan.

Da sauri ta koma d’aki alokacin wani lesa ne a jikinta ruwan zuma anwa d’inkin karamar riga me dan banzar tsadar gaske.

Kuka kawai take.
Larai kuwa tura ‘yam matan take akan suje suyi musu rakiya har wajen shiga mota k Allah yasa wani daga cikinsu yace yanaso.

Aiko da sauri suka fita suna yauk’i baran hafsat dake dama akwaita da felek’e

Wayar aysha na hannun hafsat yayinda aysha tini dama tabi zarah d’aki sukad’ai suke damuwarsu dake dama abokin kuka ba ‘a 6oye masa mutuwa.

Aysha tace hakuri zaki zarah an riga da ‘an daura sede miyi hakuri ” d’an kwalin kanta zarah tacire ta had’a hannayent biyu akan fuskarta tana kuka.

Aysha tace zakisani kuka nima dan Allah kiyi shiru nan aysha ta fara kuka haka suka had’u sunayi tare zarah najin kukan aysha da sauri tace na dena amiyat daga yu na dena kuka shine zeyi kukada harya sake ya aureni.

Aysha ta d’ago kanta tace a a karki masa haka wallahi daganin mutumin nan kamili ne kuma yanason ki sona gaskiya bangano alamar wasa a fuskarsa ba.

Uhmm zarah tace kawai nikon ina wayarki ne inji zarah ? Aysha tace af tanagun hafsat d’an tsaki zarah tayi tace wlh ki kar6o abarki tin wuri bakisan halinta bane tana iya cewa bata gantaba kuma kinga dole ki hkr in kinajin hankama meda d’an wani naka to hafsat ce.

Dariya aysha tayi tace ki kyaleta zata dawone ai sunfita raka bak’i ne.

Mtsss tsaki zarah tayi tace nide wallahi kije ki anso abarki.

To aysha tace tana murmushi ta share fuskarta ta dad’a gyarata dan kar aga alamun tayi kuka.

Zarah tace kinyi kyau sosai “” aysha tai murmushi tace du kyauna ai kinfini had’uwa.

Uhmm kawai zarah tace”” aysha ta fita waje .

A waje ta iske su hafsat da wasu samari da aka zô dasu wajen daurin auran .

Cikin sanyin jiki ta k’arasa wajen kafa funta har rawa suke dan bata saba keta maza ta wuce ba.

NASEER wanda tinda aysha ta fito idonsa ke kanta ko kiftawa ba yayi sosai tatafi da imaninsa kallonta kawai yake duba ga yanda take d’arare jikinta hakan ya nuna masa tarbiyarta .

Sanya yake da wata arniyar shadda shima fara komai nasa farine Naseer chocolate ne yana da kyau sosai d’ane ga ministern ilimi wanda yake karatu a paris saura rabin shekara kada’ai yagama yarone sosai wanda baze wuce 24 yrs ba.

Le6ensa ya d’an shafa ya tunkari inda aysha keyi.

Tana zuwa tace hafsat dan Allah aramin wayar zanyi kirane .

Hafsat taji dadin maganar datayi saboda batace tabata wayarta ba dan kar agane ba tata bace.

Mik’a mata tai kawai aysha ta shige ciki jitai kawai ansha gabanta yayinda wani kamshi ya ziyarci ruhinta “” tana d’agowa sukai ido 4 seda gabanta ya fad’i saboda bata ta6a ganin saurayi me kyu kamar saba.

Yace ki hkr fa nabaki tsoro ko ? Batace komai ba kuma har yanzu bata bar kallonsa ba .

Yace abu daya zakimin dan Allah number ki kawai nakeso ita kad’ai ma ta isheni ko zan samu?

Kai ta sunkuyar k’asa tarasa mezatayi ma jitai yana lura da ita sosai yaji dadin hakan dama mace me kunya da tarbiyya yk nema” kawai jitai ya d’ago face dinta suna hada ido ya kad’a mata ido gamida d’aga mata gira yace zan samuko?

Wani iri taji ajikinta da sauri ta hau karanto masa number yana kallonta yn smile yace wayarsa yaciro me tsadar gaske yace ok kara maimaitawa banjiba .

Yana sane yai mata hakan ita ko cikin tsoro ta karanti masa tai ciki da gudu ‘””” dariya yayi ya shafi sajensa yafita waje.

Da gudu ta shigo d’akin da zarah take wacce bacci ya d’auketa .

Mai da numfashi kawai take aranta tana cewa dama ‘ya’yan masu kud’i basuda kunya .

Tini suka d’auki hanyar komawa gida zuwa airport dan hawa jirgi Naseer na manne jikin dad d’insa se fara a yake dan shi yau yaga matar aure.

Minister yace yade son naga kana cikin farin ciki”” eh dad idan munje gida zangaya maka “” dad yai murmushi irin nasu na manya ya shafi kansa yace ok.

Kulloli aka shiga shigowa dasu masu yawan gaske wanda Larai ta bada order nan aka hau raba abinci hrdasu kaji soyaiyu.

Musayyit na zaune bayan mota yasa earpiece idonsa rufe yanajin k’ira’ ar Al k’ur’ani me girma zuciyarsa na masa dad’i””” jiyai kawai ana ta6ashi ance yalla6ai ai mun iso .

idonsa ya bud’e yana k’arewa gu kallo da sauri security’s suka bud’e k’ofa suna sara masa yana d’aga masa hannu.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button