AURAN BABBA HAUSA NOVEL

Baki ta bude tace sannunku wannan fa ? Ah dama yalla6ai ne yace akawo muku sbd nan zaku kwana idan yaso gobe se amai daku gida ga wannan abincine idan be I saba sekuyi magana “”” dg hk suka juya sukace mata se anjima.
Baki ta bud’e tace yau naga ikon Allah yoni daza abarni agidan nn wlh zama zanyi.
Nan ta kira sauran aka shiga diba ana shiga dasu gidan .
Kowa ce kula idan aka bud’e abinda ke cikinta daban ne
Kaji soyaiyu da farfesu se nama soyaiye da farfesunsa .
Soye soye ga sunan kala kala cake meat pei sncks kala kala fride rice har wani abun ma basu san shiba.
Kitchen sukaje wanda gashinan gari guda ne me girman gase spoon suka diba da plate suka dawo palour
…ciki aka ware aka shiga aika masa da sak’o
Baba maryam naga ta dauki wani plate ta nufi d’akin da zarah tk wanda tin dazun da suka barta suka kama yawo cikin gidan.
Kwance ta ganta dafe kai idonta yai ja tace suba hannallahi zarah lfy?
Umma kaina ke ciwo uhmmm zaki ware ne gajiyar hanya ce .
Ai hkr wlh d’azu nayi typing me yawa ya goge amma gobe insha Allah zakuga me yawan gaske????????????????????????????????????????
[31/08, 16:19] +234 905 934 3174: ????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀????????♀
*AURAN* *BABBAN*
*MUTUM*
Creating and Written
By
UMMEE MUKHTAR????
This page is ur MOM MANAL .Sarkin rigima????. Allah yabaki lfy ya qaro sauki ..
????8
Nasan gajiyar hanyace tashi ki daure kici “”” zarah bataso tai mt gaddama dan hk ta mik’ea hankali ta tura mt plate d’in tafaraci kadan kadan.
Minti 2 tace ta k’oshi.
K’yaleta tayi don itama bataso ta takura mata a wannan lokacin.
Bayan sungama ne sukaji shigowar motoci gidan da sauri ‘yam matan suka lek’a don ganin su waye “””maza suka gani ko wanne sanye cikin kwat da glass komai bak’i ne ajikinsu har shoes dinsu “””” wani ne ya fara shigowa yaiwa sauran matan magana cewa anzo d’aukan sune za a wajen dinner .
Manyan matan sukace ah to kuramu gamunan zuwa .
D’akin da zarah tk suka shiga suka shedawa baba maryam cewa anzo daukan sune.
Baki tq washe tace lalle kaji inda ake abu aiko yanzu wlh zamu tashi Aysah ce ta kallesu da mamaki donko ko sallah ba suyiba amma suke shirin tafiya. Aysha ce ta ciro wayar zarah ta kunnata ta mik’a mata tace gashi da badan na tuna na dakkoba da shikenan sede ase wata “”” jiki a sanyaye zarah ta amsa fuskarta taija sosai harta d’an kumbura sbd kuka.
Baba maryam tace yauwa aysha ku zauna tare da ita muzamuje mudawo dan ba abarta ota kadaiba .. to kawai aysha tace dan itama batason zuwa.
Nan da nan aka shirya se murna suke suka motocin suka bar gidan .
Ya rage daga aysha se zarah.
Kuka zarah ta 6arke dashi tai cilli da mayafin kanta ta had’a kai da drower .
Aysha ta dafata tana lallashinta haba zarah meze dameki kin bude ido kina gidan ki kuwa?
Dazu dana zaga baya har wani swimming pool nagani me adon heart komai yayi ki kwantar da hankalinki ga gidanki kamar mutun ishirin ne zasu zauna kuma duk ke d’aya .
Dago kai tayi tace ni duk wannan be dameni ba wlh kawai ninasan menakeji.
To wani waje na musamman aka kaisu su hajara dasu baba maryam se washe baki ake nan suka tadda mutane mata da maza zazzaune ba wasu masu yawa bane nan suma aka basu wajen zama da aka tanada dominsu.
Daga gefe Alhaj sa’id ne da uwargidansa sun sha kyau sosai se d’aya bangaren yan uwane da abokai se baby shukrah dake kusa da fa’eza “”” fa ‘eza kam se raba ido tak ko zata musayyit amma ko k’eyarsa bt ganiba abunda ya harzukata kenan.
Alhaj sa’ed yaga ‘yan uwan zarah amma se raba ido yk yaga koze ganta amma bata agun.
Waya yaiwa d’aya dg ciknin yaransa cewa ina amaryar?
Cewa yai wlh besani ba amma bari ya tambayi daya dg cikin iyayenta mata.
Nan yaiwa inna hajara maganar cewar ina amarya baba maryam najin hk tai salati tace mun barta gida ai mun dauka ita ba inda zata ne oh ni ‘yan nan .
Alhaj sa id ya gayawa yanda akai cewa tn gida an barta.
Ransa ne ya 6aci sosai har momy ta kula dashi wacce tasha wani arnen less na manyan mata.
Musayyit na kwance a tafkeken gadonsa yaji wayar Dadynsa da sauri ya d’auka yace dady barka da dare.
Yauwa kawai yace kana ina ne ?
Um um dama nima ina kan hanyata ta zuwa gun dinner “”” hmmm dady yace dan yasan k’arya yake donshi bayason shiga mutane sosai.
Yace ok kaje cen gidan dana ta6a watan nin baya wanda aka ginashi d’in nan kaje zaka d’akko amaryata yanzu muna jiranka dg hk ya kashe wayar.
Musayyit na cire wayar dg kunnensa yace oh no banson fita wlh amma ba yanda zanyi.
Hk ya shirya cikin wani yadi me walwali light coffee ne shoes ma hk se hula da agogo duk iri daya.
Wanka yai da turare yasa chewgum abikinsa me kamshi ya nufi gidan zarah.
A gun dinner tini an fara raba kaye kaye na gani ma fada dama na ciyr ciye.
Alhaj sa id idonsa na kan hanya ganin zarah.
Masu gadi suna ganin motar Musayyit da gudu suka bude suna daga masa hannu.
Koda yai parking ya fito gidan ya qarewa kallo lokaci daya kuma yasaki wani murmushi me tsada ya fara taku.
Aysha ce ke rik’e zarah wacce tk k’ok’arin fita ita alallai seta gudu dg gidan mayafine kawai a hannunta da gudu ta fito aysha na binta abaya tana shan kwana Musayyit ya kawo kai sukai karo ta fad’o jikinsa “””” da sauri ya rik’eta kanta lille6e da mayafi dan hk be samu ganin fuskar kowaceba “””” jikinsa rawa kawai yk dan be ta6a had’a jiki da wata mace ba”” da sauri ta juya masa baya itama se kyarma take yayinda takejin gabanta na fad’uwa “””” Tak’i gab tak’i baya hk shima hk sekace wanda aka kafe agun kallon baynta kawai yk numfa shinsa na fita da sauri
Bata juyo bayanta ba tafara magana cikin kuka kūka tace dalla malam bk gani zk bige mutane ?
Sosai yaji haushi dan ba a ta6a yimasa hk ba dakewa yai yace ni kk cewa dalla?
Eh na fad’a d’in zarah tace tana k’ara rufe fuskarta.
Da gudu aysha ta k’araso wacce tk haki ta fisgi zarah wacce jikinta ke rawa ita azatont ta dauka Alhaj sa id ne a shigo.
Aysha tace muje ba inda zaki ya daga zuwanki gidan miji kice ke gida zaki .
Musayyit ya sauke ajiyar zuciya wanda se a lokacin aysha taga mutun agun.
Sosai kyansa ya birgeta gaskiya guy yayi ba k’arya .””””” Sannunko abinda yacewa aysha kenan cikin rawar murya tace yauwa “””” hannunsa ya zuba a aljihu yace wannan itace Amaryar?
Zarah jitai kamar ta ta6ajin muryar kamar ta juyo se kuma ta fasa.
Yace ok amma meyasa takeson zuwa gida ?
Ya salam zarah ta fad’a cikin zuciyarta wannan muryar da alamu mutun d’aya keda ita a duk duniya sosai voice dinsa yk shiga kanta harta na rufe ido.
Aysha tace ah ah dama kawai de ummanta takeson gani.
Wani murmushi yayi yn k’arewa zarag kallo ta baya wanda bayanta kawai yk gani “”” cikin murya sassanya yace duk wata mace tana murna da wannan ranar inde har tanason mijin data aura amma yanzu na gane wani abu d’aya dan hk kuje ku kwanta kawai seda safe dg ya juya yai waje kamshin turarensa yadaki hancin zarah.
Da sauri ta juyo bayansa kawai tagani idonta taf kwallah a ranta tace duk da ban ganshi ba Allah yayi halitta anan tace aysha dubi bayansa tsayaiyen namiji matashi dashi kisan cewa an cuceni.
Kul karki k’ara babu kyau matar aure ta dinga yabon wani namijin daba nataba.
Muje kawai .
Musayyit da sauri ya koma mota ya zauna ya kasa tada ita ya d’aga kansa sama yana tina karon da sukai da waccen yarinyar d’azu.