CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske writers association????
[1/14, 9:15 AM] Elhajj: ⚓ Captain Ahmad Junaid⚓
By Khaleesat Haiydar✍????
44/45
Da asuba Junaid ya dade xaune gefen gado daga bisanni ya mike, kallo daya ya ma Humaina dake bacci ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito har xai fita xuwa masallaci ya dawo ya isa kusa da gadon ya buga kafarta, bude ido tayi a hankali tana kallonsa ya juya ya fita daga dakin, ko da ya dawo daga masallaci samun ta yayi kwance tana bacci har lokacin, bayi ya shiga ya debo ruwa ya fito ya watsa mata, ta mike xaune da sauri tana kallonsa, yace “Sllh!” Daga haka ya fita daga dakin, tsaki tayi ta bi sa da harara ta sauka daga gadon ta shiga bayi. Tana idar da sllh tayi jigum kan darduma, can ta mike ta shiga gyaran bedroom din, tana gamawa ta shiga bayi ta wanke baki tayi wanka ta wanke bayin ta fito daure da towel, gaban mirror ta xauna ta gama shafe shafenta sannan ta shirya cikin Abaya baki da veil dinsa ta d’an gyara fuskarta ta koma gado ta xauna tayi tagumi. Bude kofar dakin aka yi fatima da khadija suka shigo, Humainah ta mike da sauri lokaci daya tayi murmushin jin dadin ganinsu, fatima tace “Uhum Amaryar yayarmu, Antynmu!” Hade rai tayi can ta fashe da kuka tace “Ni ba amaryarsa bace, ai Hajja tace sbda a raba sa da mahaukaciyar nan ne aka aura masa ni, amma da ya rabu da ita sai a sa ya sakeni in ci gaba da karatuna” innocently tayi maganar tana kallonsu, Khadija da fatima suka fashe da dariya barin khadija, juyawa Humainah tayi a sanyaye ta koma gefen gado ta xauna, hade kanta tayi da gwiwa tana kuka, fatima ta karasa kusa da ita da sauri tace “Toh ai ba mu ce ba haka bane ba fa Humainah” Humainah ta girgixa kai tana kuka tace “Ba wani nan nasan wayo aka min baxa a ce ya sakeni ba, yar yarinya da ni xan je ss3 za ayi ma aure bayan ku ba a maku ba…..” Khadija ta xauna gefenta tace “Ni dai ba dariya nake maki ba, ba ruwana, ga abinci Mumy tace a kawo maki” Humainah ta dago kanta tana share hawayen idonta tace “Hajja fa?” Khadija tace “Ta ce anjima xata xo” Junaid ne ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa yana kallonsu yace “A baki aka ce ku bata abincin?” Kallonsa suka yi gaba daya basu ce komai ba, ya nuna masu kofa duk suka mike, Humainah ta hade rai tana kallonsa tace “Ba yanxu xa su tafi ba toh” Ko kallonta bai yi ba, ganin su fatima sun nufi kofa kamar xata fashe da kuka tace “Don Allah kar ku tafi” murmushi fatima tayi ta raba ta gefen yayan nata ta fita khadija ta bi bayanta, kuka sosai Humainah ta shiga yi, ya karaso cikin dakin ya xauna d’an nesa da ita yace “baki san ke ba yarinya bace yanxu tun da har aka aurar da ke” hade rai tayi tana kallonsa tace “Ni dai yarinya ce” murmushi yayi yace “Toh naji! tsoron xama ke kadai kike a dakin da kike son su xauna da ke?” Ta kallesa hade da gyada masa kai, yace “Toh xan samo maki warce xata dinga taya ki xama ai kina so?” Tana kallonsa tace “Amma babba ce?” Ya girgixa mata kai yace “No yar yarinya ce kamar ki sai ta dinga taya ki xama kuna kwana ma tare” sosai ta hade rai tace “A’a bna so, xan iya xama ni kadai” shiru yayi yana kallonta, can yace “Saboda me?” Ta mike tace “Haka nan kawai, xan iya xama ni kadai abuna” daga haka ta nufi kofa ya bi ta da kallo har ta fita, lumshe ido yayi ya bude yana naxarin abinda ta ce, Mikewa yayi shima ya fita daga dakin ya koma nasa. Karfe sha biyu saura aka danna bell downstairs, Junaid dake bedroom dinsa yana danne dannen waya ya mike ya fita, dai dai lokacin da Humainah ma ta fito, kallo daya yayi mata ya sauka ya je ya bude kofar, Hajja ce tsaye bakin kofar da Sadiya, ta washe hakora ganin Junaid tace “A’a ango, to gani na biyo ka don kayi amarya sai ka mance da uwar gida?” Juyawa yayi ya bar bakin kofar ya koma parlor, Hajja ta shigo tare da Sadiya da gudu Humainah ta sauko jin muryar Hajja ta rungumeta, Hajja tace “Lalala kinga yanda kika yi kyau kika yi fresh kuwa? Lallai Amadi ya iya kiwo daga jiya xuwa yau” hade rai Humainah tayi tace “Ni babu abinda ya ban na ci har yanxu” Hajja tace “Ehh amma ai kin kwan masa a gida” turo baki tayi ta tafi ta xauna, Hajja ta kalli Junaid tace “Banxa kai kuma ko ka kira ka mana godiya ka ga xukekkiyar amarya ba mahaukaciya ba” Kallonta kawai yake can ya tabe baki yace “Nii ban gode ba tun da ban ce ina so ba, kawai makala min aka yi” Humainah ta fashe da kuka tace “Hajja kin dai ji ko, ni dai tare xa mu koma don ni ma makala min aka yi ban ce ina so ba” Hajja ta hade rai tace “Kai kaga irin hada ta da Allah annabin da aka dinga yi don ta amince da gantalallen auren ka, banda kaddara me xata yi da kai Ahmad, kai da cikakken saiti baka da, wllh wllh ‘yar nan tafi karfin ka, kawai ka kara gode ma Allah da ya sa aka baka ita” juyawa tayi tana kallon Humainah tace “ke kuma kar ki kuskura ki bari ya kwana dakin ki tunda haka yace, hanyar jirgi daban ta mota daban kin dai ji ni…” Humainah ta gyada mata kai tana goge hawayen idonta, Hajja ta nemi kujera ta xauna tana cewa “Banda walakanci an samu an lallaba yarinya da kyar ta amince ta rufa maka asiri ta aureka xaka dinga gaya mana magana, ko fa kwandalar ka bbu a bikin nan don tsiya…. Amma bari na fi ka iskanci sai ka xo ka durkusa kana rokona in ce mata ta so ka” girgixa kai Junaid yayi ya mike ya haura sama abun sa. Har Karfe uku Hajja na gidan ita dai Sadiya dama turo ta aka yi ta ga kwakwaf ta ga yanda gidan yake da abubuwan da aka xuba, tana gama abinda ya kawota ta kara gaba ta bar Hajja. Har dai bayan la’asar Hajja bata da niyar tafiya Junaid ya rasa me suke kullalawa a dakin gashi El-ameen ya ki xuwa saboda Hajjan, mikewa yayi ganin har biyar ya gota ya shiga dakin, suna ganinsa suka yi shiru, Hajja ta hade rai tace “To ya aka yi kuma?” Ya d’an shafa kansa yace “Kawu Abubakar ne ya kira wai yana ta jiran ki xai koma” mikewa Hajja tayi da sauri tana xuge yar purse dinta tace “Auu bawan Allah to bari in je” Humainah ta marairaice kamar xata yi kuka tace “Yanxu tafiya xa kiyi ki bar ni Hajja” Hajja ta hade rai ta kalli Junaid sai kuma ta duka kusa da ita murya can kasa tace “Kin dai ji abubuwan da na gaya maki dai koh?” Humainah ta gyada mata kai, Hajja ta mike tace “Ehh to ba dole in tafi ba Humainah, amma ina nan dawowa kila ma da kayana xan taho tunda ai jikokina ne ko na xauna bbu komai” daga haka ta nufi kofa tana cewa “Toh kai d’an ubanka xaka kai ni gidan ne ko in je in hau machine tunda Sadiya sun koma da driver” ficewa junaid yayi daga dakin ita ma ta fita tana cewa “Toh Humainah sai Allah ya sake dawo da ni” har gida Junaid ya ajiye Hajja sannan ya kira El-ameen yace “Toh ta tafi, am waiting for you” daga haka ya katse wayar ya kama hanyar gida. Kusan a tare suka iso gidan da El-ameen, El-ameen yayi parking ya fito yana murmushi yace “Daga ina haka ango?” Junaid yace “Nayi dropping dinta mana” bude motar El-ameen yayi ya shiga yana kallonsa yace “Tabdi gaskiya Humainah ta karbe ka, ka ga yanda ka kara kyau yau kuwa” girgixa kai Junaid yayi yace “Kaga ni mu yi maganar arxiki, kasan kuwa yarinyar nan tace ita bata son a kawo mata kowa gida?” El-ameen ya hade girar sama da ta kasa yace “Kamar ya? Kaga matsalar ka ko Ahmad, daga aure har yarinya xata fara raina ka tana fadin abinda xa ayi a gidan da wanda baxa ayi ba, gidan ta ne da har xata gaya maka abinda xa ayi? Kai wani irin Human being ne junaid” Shiru Junaid yayi yana kallonsa, can ya sauke ajiyar xuciya yace “Am afraid kar ta ce xata gaya ma su Mumy ne shi yasa ban ce komai ba” El-ameen yace “Tabdi! Yarinyar nan fa wllh sai kayi gaske da ita Idan ba haka ba second Mumy dinka xata xama, naga alamar fitinanniya ce, shikenan kai kuma ka xama abun tausayi baka da say a duniya sai na Mumy da wife, haba sai kace ba captain ba kawai ka cika ma kanka girman kai da miskilanci maimakon being ur own self, ita wannan har ta ma wuce ka bubbuge ta Idan tace xata kawo maka rainin hankali” girgixa kai junaid yayi hade da yin murmushi yace “Uhum lallai” horn ya danna aka bude gate ya shiga da motar yayi parking ya juya yana kallon El-ameen, El-ameen yace “Toh gobe dai Dr Sumayya xata yi tafiya ban kuma san inda xan kai patient dinka ba” junaid ya bude motar ya fita shima ya fito suka shiga cikin gidan. Parlor El-ameen ya xauna junaid ya haura sama ya sameta xaune ta kunna kayan kallon parlon, yace “Ki fito ku gaisa da abokina” Ta hade rai tace “Baxan fita ba ni indai wannan El-ameen din nan ne” juyawa yayi ya bar dakin ya koma parlo, El-ameen yace “Xuwa kayi kace ta sauko?” Junaid bai ce komai ba ya xauna, El-ameen yace “In dai nine ta rike gaisuwar ta, kaga ni kasan yanda xa ayi kafin gobe, yanxu clinic xan tafi” Junaid yace “Dama baka yi niyar xuwa yau ba kenan koh?” El-ameen yace “Da wata daban ce matar ba wannan fitsararrar ba” dariya junaid yayi ya mike ya rakasa har waje gun motarsa, Junaid yace “But ka gaya min yanda ya kamata inyi approaching dinta har ta amince” El-ameen yayi murmushi yace “Babu abinda ka iya a rayuwa sai sa uniform da yi ma Mumy biyayya kamar yaya, all the same xan kira ka later dai” daga haka ya shiga motarsa ya tada ya bar layin. Da daddare shinkafa da miyar da Mumy ta aiko masu ya diba ya ci, ya jima xaune parlor yana tunanin yanda xai shawo kan Humainah ta amince da xuwan jasmine gidan ganin har lokacin El-ameen bai kirasa ba, Karfe goma kiran El-Ameen ya shigo wayarsa ya daga, sun dade suna waya har kusan karfe sha daya daga karshe suka yi sallama Junaid ya ajiye wayar, murmushi kawai yake ba wai don yasan dalilin murmushin shi kansa ba, mikewa yyi ya haura sama ya shiga dakin sa, wanka yayi ya fito ya saka pyjamas dinsa ya xauna gefen gado har sha biyu yayi sannan ya mike ya fita daga dakin ya nufi nata, a hankali ya tura kofar ya shiga ya rufe, kwance ya sameta waje daya tana bacci tv a kunne ga remote kusa da ita alamar kallo take bacci ya dauketa, kashe wutan dakin yayi ya karaso ya xauna gefenta yana kallonta doguwar rigar bacci ne jikinta sai net da ta xura gashinta ciki, haka kawai ya ji gabansa na faduwa, a hankali ya kira sunanta, da sauri ta bude ido don ba wani nisa baccin nata yayi ba, ta mike xaune tana kallonsa, pillow ta jawo ta daura jikinta tace “Me ya faru?” Ya d’an bude ido yace “Magana xa muyi” kalle kallen inda hijab dinta yake ta shiga yi, can ta turo baki tace “Ina jin ka” mikewa yayi xai dawo kusa da ita, da sauri tace “A’ah a’ah ka tsaya a nan mana ai ina jinka” sunkuyar da kai yayi yana murmushi ya xauna, murya can kasa yace “Saboda me kika ce baki son warce xata taya ki xama?” Hade rai tayi tace “haka nan” a hankali yace “kinga Idan na fita aiki tun sassafe fa sai yamma nake dawowa, baxa ki iya xama ke kadai a babban gidan nan ba sbda in some cases sai ki ga akwai aljanai a babban gida haka” xaro ido tayi ta matso kusa da shi a hankali tace “Aljanai kuma Ya A.jay?” Yace “Of course tunda sabon gida ne ba a taba rayuwa ciki ba” kamar xata yi kuka tace “Toh ai Abbana yace min xa ka sa ni school soon, kaga sai ka sama min from 7 to 6 kaga kenan tare xamu dinga dawowa gidan” ya d’an hade rai yace “Nan da sati biyu fa xan je Lagos inyi aiki a can to ke kadai xa ki xauna?” Tace “A’ah to ba sai in je gun su Mumy kafin ka dawo ba” dauke kai yayi can ya juyo yace “Toh Idan tare xamu lagos din fa, kenan Idan na tafi aiki ke kadai xaki yi ta xama can din ma” kamar xata yi kuka tace “Toh mai aiki xaka sama min kenan?” Ya girgixa mata kai yace “A’a ba mai aiki bace amma xata dinga taya ki aikin” hade rai tayi tace “Wai wacece ita ya Ahmad?” Kamo hannunta yayi a hankali yace “Idan ta xo xa ki ganta, nd you will like her, bata da matsala” fixge hannunta tayi tana komawa baya tace “Aljanan su cinye ni wllh kuma ni kar ka sake cewa wata xata taya ni xama xan gaya ka da su Mumy da…..” jawota yayi jikinsa ba shiri tayi tsit ta fara turasa tace “Meye haka ya A.jay” a hankali ya daura bakinsa kan wuyarta, lokaci daya ranan da ta gansa da Muhibba a daki ya fado mata, ta fasa ihu a tsorace tana kokarin kwace kanta tace “Don Allah ya Ahmad ka yi hakuri ka kyaleni bana so” murya can kasa yace “Meye ba kya so?” Da kyar muryarta na rawa tace “Toh to naji wacece xata taya ni xaman?” Dago kanta yayi yana kallonta, tsoro fal ya ga cikin idonta, yayi murmushi yace “Kin dai amince ta xo sai ki ganta” kai ta shiga gyada masa da sauri, a hankali ya saketa yace “Gobe da safe xa a kawo maki ita” komawa baya take tana gyada masa kai, yayi murmushi ya mike ya kashe kayan kallon dakin, kamar xata yi kuka ta isa gun bedside lamp da sauri ta kunna tace “Wayyo me yasa ka kashe” xagawa yayi daya side din ta bi sa da kallo yayi kwanciyarsa tare da juya mata baya, ajiyar xuciya ta sauke a hankali ita ma ta kwanta, juyowa yayi ta mike xaune da sauri kamar xata yi kuka, yace “Ki kashe wutan nan da kika kunna” girgixa masa kai tayi tace “Plss ya Ahmad bana son duhu” mikewa xaune yayi tana ganin haka ta kashe wutan da sauri tace “Oya yi hakuri kwanta na kashe” dariya ta basa ya koma yayi kwanciyarsa, bayan kusan minti ashirin yaji ta birgino a hankali gefensa ta kwanta. Da asuba ya tasheta yin sllh ya fita daga dakin xuwa nasa, yau ma kamar jiya daga gida aka kawo masu breakfast, tea kawai junaid ya sha yayi kwanciyarsa a parlor yana jiran xuwan El-ameen don ya kirasa yace suna hanya, Karfe goma saura El-ameen ya shigo compound din da motarsa, mikewa junaid yayi ya nufi kofa ya bude, El-ameen ne ya fara fitowa ya xaga ya bude mata side din da take ta fito, sanye take da atamfa da hijab dinta fari har kasa, kallonta junaid yake ko kiftawa bai yi, El-ameen ya rufe motar ya bude baya ya fiddo jakar kayanta yana kallonta yace “Mu je baby” kallon gidan take ba tare da ta yi motsi daga inda take ba, yayi murmushi ya shiga gaba ya fara tafiya, bin bayansa tayi kamar me tausayin kasa, ya juya yaga tana biye da shi ya ci gaba da tafiyarsa, kallonsu junaid yake har suka iso balcony ya lumshe ido ya bude ya basu hanya, El-ameen ya juya yana kallon Jasmine ya ga ta ki karasowa, yace “Come on mana” a hankali ta shiga tahowa Junaid ya bi ta da kallo har suka shiga parlon, juyawa yayi ya bi bayansu, El-ameen ya nuna mata kujera ta xauna bayan ya ajiye kayanta da ke hannunsa shi ma ya xauna yace “Baby ba ki gaishesa ba” ya fadi hakan yana nuna mata Junaid, kallon junaid tayi da fararen idonta a hankali tace “Ina kwana” kasa amsawa yayi ya d’an mata murmushi kawai, sosai haskenta ya kara fitowa da gani kasan ba karamin kulawa take samu gun Dr Sumayya ba, Humainah ce ta sauko parlon jin shigowar mota, kallonsu ta shiga yi da d’ad’d’aya da d’ad’d’aya daga inda take tsaye duk da ba ganin fuskokinsu take ba, El-Ameen ya hade rai, ta karaso cikin parlon idonta ya sauka kan jasmine still tayi gabanta yayi mugun faduwa tana kallonta, Junaid yace “Amm…. Kin ganta she will keep you accompany ana kiranta da Baby….” Wani kallo Humainah ke mata, can tayi dariyar rainin hankali tace “Ko kuma placenta ba!” Lokaci daya ta hade rai tace “Ita mahaukaciyar ce xata yi keep dina company??” Strictly El-ameen yace “Kar ki kuma kiranta da mahaukaciya” hararansa tayi tace “Toh ni dai baxa ta xauna gidan nan ba, kai ka yi auren ka kai ta gidan ka mana” sai kuma ta fashe da kuka ta haura sama da sauri, Junaid ya kalli El-ameen, El-ameen yayi tsaki yace “Wllh da ma bare kawai aka sama maka da wannan yar tashar! An hada ka da balaa’i kawai” junaid ya sauke ajiyar xuciya ya mike jiki ba kwari ya bi bayanta, a hankali Jasmine ta mike ta dawo kusa da El-ameen ta durkusa kusa da shi cikin sanyin murya tace “Uncle ni ka kai ni gida gun Mami” sunan da suke kiran Dr Sumayya da shi kenan, shiru El-ameen yayi yana kallonta, ta d’an taba hannunsa tace “Uncle!” Kifta ido yayi da sauri ya shafa kansa a hankali yace “Toh xan kai ki” xaunawa tayi nan kasa kusa da shi tana kallonsa murya can kasa tace “Uncle Meye meaning din mahaukaciya?” Shiru yayi nan ma yana kallonta, ta bude manyan idonta tace “Idan mun je gida in tambayi farida?” Murmushi ya mata hade da gyada mata kai.