CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????
Captain_Ahmad Junaid

  _By Khaleesat Haiydar_✍????

9…..

Gida Junaid ya nufa, yana gama parkin ya fito ya shiga bangaren Mumy ya gaida ta sannan ya tafi nasa part din, kwanciya yayi Palo ya lumshe ido, ko minti goma bae yi da kwanciya ba wayarsa ya soma ringing, daukar wayar yayi yana kallon mai kiran nasa ya ga abokinsa ne Faisal, d’agawa yayi yace “Yane Faisal!” Faisal yace “Are yhu at home capt?” Junaid yace “Yea ina gida” Faisal yace “Ohk gani nan shigowa” daga haka ya katse wayar, bayan minti takwas Faisal ya shigo palon, Junaid ya mike xaune yana kallonsa yace “Daga ina haka” Faisal ya xauna yace “Gida mana tun da kai baka neman mutane sae El-Ameen” Junaid yayi dariya yace “Kai haba ko ranan da daddare ban kira ka ba” Faisal dake kokarin kira a wayarsa yace “Really!” kallonsa kawae junaid yayi yana murmushi, faisal yace “Hello Muhibba gani gidan ku part din Captain” daga haka ya katse wayar, Junaid ya hade rae yace “idan gun ta ka xo ba sae ka je can bangarensu ba xaka wani kira min ita nan” faisal yace “Chill guy sako xan bata” ko rufe baki faisal bae yi ba sae ga ta ta shigo, murmushi dauke fuskarta tace “ashe da gaske kake” hade rae sosai Junaid yayi ya jawo waya yana dannawa, faisal ya ciro waya aljihunsa ya mika mata yace “Gashi nan na bada an gyara maki” ta wara ido ta karbi wayar tace “Waow am so happy ya faisal, kuma nawa?” yace “No don’t bother” tace “Toh na gode kwarai, ya salima fa?” Yace “Tana gida,” kallon Junaid tayi tace “Sannu ya Ahmad” ba tare da ya kalleta ba yace “Yauwa!” Tayi niyyan xama palon amma sanin junaid sae ya iya gwaleta yasa ta juya kawae ta fita tana tunanin yaushe ne wannan ranan da junaid xae fara sonta kamar yanda Hajiya ke yawan assure dinta. Faisal yace “Fatee fah?” Junaid yace “Oho!” Sae bayan Magrib faisal ya bar gidan bayan sun shiga ya yi ma Mumy sallama ya kuma shiga part din Hajja ya gaidata, a tare suka fita bayan Junaid ya ce ma Mumy bari ya rakasa, sai dai rakiyar iya bakin gate yyi sa, yana ganin tafiyar Faisal ya nufi titi don yasan in har yace ma Mumy fita xae yi sai ya amsa query, kalle kallen abun hawa ya shiga yi ya rasa yanda xae ce su tsaya, can dae wani mai adai daita ya tsaya yana tambayarsa ina xa shi, shiga kawae Junaid yayi yana kallon mai adai daitan yace “Mu je” sae da suka dan yi nisa kafin ya gaya masa inda xa shi, suna isa junaid ya sauko ya fara dube duben kudi a aljihu, dubu daya kawae ya gani aljihun nasa, mika masa yayi a hankali yana kallon mai adai daitan yace “Kayi hakuri malam ban san ban fito da kudi ba, dubu daya ce a hannu na nagani” dariya mai adai daitan yayi ya karbi kudin, ko ba a gaya masa ba yasan junaid sabon shiga ne a tricycle, canjin dari shidda ya mika masa yace “Ga canjin ka bawan Allah” dan xaro ido Junaid yayi ya karbi kudin yace “Har canji gare ni? Toh na gode” mai adai daitan yayi murmushi ya ja machine dinsa ya wuce, Junaid yayi mamakin ganin motar El-Ameen a parke waje, shi da yace baxae xo ba kuma, tabe baki yayi ya shiga gidan, mama ce xaune Palo ita kadae Junaid ya gaisheta da ladabi, ta amsa tana murmushi ta tambayesa ya aiki, Junaid yace “Lfya mama, ya kamata a siyo maki tv ya dinga debe maki kewa koh” dariya tayi tace “lallai kam” Junaid yace “El-Ameen ya xo ne” mama tace “Eh yana sama” mikewa junaid yayi sae dae duk bae da kuxari ya nufi saman, a hankali ya tura kofar dakin yana kallon ciki, xaune ya ga El-Ameen gabanta ya tankwashe kafa plate din abinci a tsakiyarsu hannunsa rike da spoon ga wayar rechargeable dake gefensa, ita ma xaunen take ya daure mata hannu sae shisshigewa jikin bango take hawaye kwance fuskarta, duk gashin kanta a birkice yake, Junaid ya rungume hannayensa yana kallon El-Ameen, El-Ameen yace “Uhnn! yau baka kwanta da wuri ba kenan mumy’s boy” junaid dae bae tanka sa ba ya maida kallonsa kanta ganin yanda take kokuwa da bango kamar xata shige ciki, yunkura tayi xata mike El-Ameen ya daka mata tsawa ya dauki wayar rechargeable din gefensa ta koma da sauri ta xauna, shinkafar ya diba ya kai mata baki, ta dinga kauda kai tana boye fuska, tsawa ya kuma yi mata ya juyo da kanta ya matse bakinta har sai da ta bude ya xuba mata abincin da sauri, murmushi Junaid yayi ganin yanda jikinta ke rawa tana hadiye abincin ba tare da ta tauna ba, da ganinta kasan ba karamar matsoraciya bace, Haka El-Ameen ya dinga mata har sae da ta ci kusan rabin abincin sannan ya mike yana kallon Junaid yace “Bata cin abinci shi yasa na mata haka,” Junaid ya buda manyan idonsa yace “So yhu do really care ashe haka?” El-Ameen yayi dariya yace “Darajar ka take ci ae” Junaid bae kuma cewa komae ba sae kallonta yake duk da ba ganin fuskarta yake ba don dogon gashin kanta ya rufe fuskar, wasu allurai biyu El-Ameen ya fiddo ya shiga hadawa, ae tana hango alluran ta mike tayi kofa da gudu, fixgota El-Ameen yayi don shi Junaid hanya ma ya bata da sauri, El-ameen ya jefa ta kan gado, yana hararan Junaid yace “kaji d’an iskan hanya ma ya bata” Junaid yayi dariya yana shafa kai, ta fasa wani uban ihu da ya tsorata Junaid xata mike El-ameen ya hau gadon ya rike ta yana mata wani mugun kallo yace “Keehh”, Ribbon dinta da ke kan gadon ya dauka ya shiga daure mata gashin kanta, yana kallon fuskarta yace “Kika kuskura kika sake cire ribbon dinnan sae na gaggaura maki mari” banda rawa babu abinda jikinta yake tana kallonsa, murmushi yayi ya kwantar da ita a hankali ya kwance daurin hannunta sannan ya juya yana kallon Junaid yace “Miko min alluran ko shi ma tsoron sa kake” Junaid bae ce komae ba ya dauki alluran ya mika masa, juyar da ita El-Ameen yayi xae mata alluran Junaid ya juya ya fita dakin, El-Ameen ya bi sa da kallo sannan ya tabe baki yayi mata alluran, tsam ya riketa a jikinsa ganin yanda take shure shure da ihu, sun kusa minti goma a haka har ya ji duk jikinta ya saki, ya dago fuskarta yana kallonta ya ga bacci tayi, kwantar da ita yayi ya lulluba mata bargo, sannan ya dauki abincin da ta rage da ruwa ya fita ya kullo dakin, xaune ya samu Junaid a Palo, ya ajiye abincin nan tsakar palon yace “Mama a xubar da wannan ta d’an ci kad’an,” Mama ta jawo abincin tace “A’a baxa a xubar ba xan ci” El-Ameen bae kuma cewa komae ba, Junaid ya mike yayi ma Mama sae da safe ba tare da ya kalli El-Ameen ba ya fice daga falon, bin sa da kallo El-Ameen yayi sae kuma ya tabe baki shi ma yayi ma mama sae da safe ya fita.

Washegari Junaid ya fito bayan ya shirya cikin khakin sa ya shiga part din mumyn sa, tana jera masa breakfast as usual ya shigo, bata amsa gaisuwar da yake mata ba tace “ka shiga gaida Hajja kuwa?” Girgixa Kai yayi yace “Na ma manta tana nan” Mumy tace “Toh tafi ka gaida ta ka dawo tukun.” Ba musu ya fita yayi bangaren kakar tasa, xaune ya sameta Palo tana shan kunu ga kosai cike kula, dariya yayi yace “Dama abinda ke kawo ki gidan nan kenan ae Hajja” kallo daya yayi ma Humainah dake goge goge palon ya dauke kai, ita kam dama ko kallonsa bata yi ba, Hajja ta hade rae tace “Wae baka ga Humainah bane Junaid?” Ya hade rai shi ma yace “Toh ni xan gaisheta?” Hajja tace “Toh ba kai ka xo ka sameta ba” bude baki yayi yana kallon Hajja, ita ko Humainah ta mike ta dauki bucket fuu xata wuce, fixgota yayi ta kusa faduwa ya turata ta xauna nan kasa, bata fuska tayi xata yi kuka, ya hade rai yace “ke yaushe kika girma har kika iya fitsara haka?” Kuka ta fashe da tana kallon Hajja, Hajja ta mike tsaye ta tsuke fuska tace “Kai Amadidi ka fita idona wllh, walakancin da cin fuska har a gabana, a haka xan baka ‘yar kaje kana cutar min da ita in shiga uku?” Dariya Junaid yayi yace “Tabdi! Allah ya tsare ni, ke in kin ga matar da xan aura ma wllh kunyar fito min da wannan fitsararriyar xa ki yi” Humainah ta tabe baki tana hararansa tace “Ni ma in kaga saurayina wllh kunyar tsayawa gabana xa kayi” Hajja ta fashe da dariya kyal kyal kyal har da kwanciya, shi ko bude baki yayi yana kallan Humainah da ta wani tabe baki, murmushi yayi ya saketa ya mike ya fice daga palon, Hajja na dariya tace “A’a da ka tsaya mana fitsararre” Humainah tayi dariya tace “Ya fa ji tsoro ne Hajja, shi in banda haske da dogon hanci me garesa xai wani sa uniform da hula ya xo yana d’addaga mana hanci” Hajja tace “Atoh! Gane min hanya ‘yar nan, ko ubansa xai burge Oho!” Humainah ta fashe da dariya har da rike ciki.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button