CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

✍????
Haske Writers Association????⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

31…..

Kallon agogo junaid yayi yaga tara ya kusa, ya jawo wayarsa ya shiga kiran El-ameen don ya ji ko ya samu inda xai kai ta, har ya gama ring bai d’aga ba, mikewa yayi ya dau mug din Lipton din ya shiga daki ya xauna gefen gado ya bude ya shiga sip dinsa a hankali, kusan rabi ya sha ya rufe ya ajiye sannan ya mike ya shiga bayi don yin wanka, da kyar ya iya fitowa daga bathroom jin kansa na wani irin juya masa, ya xauna gefen gado sanye da bathrobe, shi kansa baxai ce ga abinda ke damunsa a lokacin ba, kwanciya yyi yayi rub da ciki, a haka ya ji an bude kofar parlor aka karaso har bedroom, kasa dagowa yayi yaga ko waye jin wani axababben ciwo da cikinsa ke masa, tsaye Muhibba tayi bakin kofar tana kallonsa, tuni kamshin turarenta ya gauraye dakin, ya juyo da kyar yana ganinta dishi dishi, rufe kofar tayi ta karaso cikin dakin ta xauna gefensa cike da kissa tace “Ya Ahmad dama Abba ne yace ka ban dubu biyar xan yi amfani da shi” mikewa xaune yayi don ta muryarta ya gane ko wacece ya rike kansa duk da yanayinsa hakan bai hanasa hade rai ba yace “How dare you xaki shigo min daki?” Mikewa tayi ta nufi kofa irin ta ga ko xae tsayar da ita, har ta isa bakin kofar bata ji yace komai ba sai komawa da yayi ya kwanta ya runtse ido, cije lebe tayi ta kuma dawowa ta hau kan gadon da damuwa kamar gaske ta dafa sa da duk hannunta biyu tace “Wai baka da lafiya ne ya Ahmad” ai bai san lokacin da ya fixgota ba ta fado kansa ya kankameta, wani murmushi tayi tana kallon kyakkyawan fuskarsa don har lokacin idonsa rufe suke, ta dake tace “Meye haka ya Ahmad, ka kyaleni” ko kadan bai jin abinda take cewa ba, lkci daya ya koma kamar mara hankali, wani farin ciki ya rufeta ba kadan ba ta sakar masa jiki, cikin mintuna kadan yanayinsa ya bata tsoro, tun tana daurewa har dai tsoron ya fara bayyana, gashi ba rikon wasa yayi mata ba, turasa ta fara yi a tsorace daga karshe tana neman kwace kanta duk da ba haka suka yi da su Umma ba, amma ta gama tsorata da shi gaba daya, kin saketa yyi ta saka kuka tace “Don Allah ya Ahmad kayi hakuri ina rokon ka” ko sanin abinda take cewa bai yi ba, ihu ta fasa a rikice tana turasa tana kwala ma Umma kira amma ya ki saketa, bude kofar dakin da aka yi lokaci daya da karan tarwatsewan bowl me dauke da fruit salad ne ya sa shi sakinta da sauri, ta ja bargo ta rufe jikinta tana kuka jikinta na rawa, shi ko dama bathrobe na jikinsa, kallonsu Humainah ta tsaya yi a bakin kofa jiki a sanyaye, ya sauko da kafafuwansa kasa ya rike kai xuciyarsa na bugawa ya dinga nanata innalillahi… A xuciyarsa, Muhibba ma ta xamo daga kan gadon tana kuka har lkcin ta jawo hijab dinta ta sa ta fice da sauri sai ka rantse ba ita ta kawo kanta ba ganin yanda take kukan jiki na rawa, da kyar Humainah ta juya xata bar dakin ya dago kai yayi kafin halin kiranta, amma ko juyowa bata yi ba ta fice da sauri, sake rike kansa yayi ya runtse ido duk ya kasa tuna yanda abun ya faru, mikewa yayi yana jin jiri ya shiga bayi, ya kusa awa daya bayin sannan ya fito ya fada kan gado lokaci daya bacci ya daukesa. Muhibba kuwa tana komawa part din uwarta ta gansu duk xaune suna jiran dawowarta, Hajiya ta mike da sauri tana kare mata kallo tace “Ya naga kin fito da wuri, ko dai bai sha ba” ta bata fuska tana goge guntun hawayen idonta tace “Ya sha mana, ni dai tsoro nake ji wllh” Umma da Hajiya suka yo waje da ido suka hada baki wajen cewa “Me? Kina nufin bai maki komai ba??” ta fashe da kuka tace “Ni Allah tsoronsa naji Umma, ni dai baxan iya ba a tura suhaima” Umma tayo kanta a fusace tace “Nashiga uku ni balki, Allah wadaran ki yar iska kawai, tsoron uban me, innalillahi… Shikenan ta bata plan din” Hajiya da idonta ya kankance don bacin rai tace “Ni nasan a rina dama kawai nayi shiru ne, da Suhaima ce ko dar baxa ta ji ba kika ce mu tura debabbar yar nan taki gashi ta rusa mana budget, wannan wace irin fitina ce” Umma ta kwalo ma suhaima kira tace “Maxa ke ki je…” Muhibba tace “Humainah fa ta shigo ta ganmu!” Juyawa suka yi da sauri Suna kallonta, Hajiya ta xaro ido tace “Allah?” Muhibba ta tabe baki tayi hanyar daki, Umma ta jabe kan kujera ta dafe kai tace “Allah ya tsine ma tsiya!” Tsaki Hajiya tayi ta fice daga part din kamar xata tashi sama. Ray din rana ne ya farkar da Junaid da safe, ya mike xaune da sauri yana kallon agogo yaga bakwai da kusan rabi, xaro ido yayi lokaci daya abinda ya faru jiya da daddare ya dawo masa gabansa ya fadi, kalle kallen dakin ya shiga yi yana tunanin what just came over him jiya, rike kansa dake sara masa yayi, ya mike tsaye da kyar ya shiga toilet, wanke baki yayi, yayi wanka snn ya dauro alwala ya fito, ya jima xaune kan pray mat bayan ya idar da sllh daga bisanni ya mike ya isa bakin kofa ya tattara pieces din bowl din jiya da Humainah ta fasa bakin kofar ya gyara wajen ya goge ya fitar da mug din Lipton din ma. Parlor ya fito ya xauna ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido. Ganin har Karfe tara ya kusa ya sa ya mike a sanyaye ya fita ya nufi part din Mumy, kasa shiga parlon Mumy yayi don bai san da wani ido xai kalli Humainah ba, da kyar ya tura kofar daga karshe ya shiga, bbu kowa parlon sai kamshi me dadi dake tashi, ya karasa ciki jiki ba kwari ya xauna, Mumy ce ta fito daga daki tana kallonsa tace “Sai yanxu ka tashi?” Kasa kallonta yayi ga wani faduwa da gabansa yake don gani yake kamar Humainah ta gaya mata, ya dukar da kai ya gaisheta, tace “Meye haka kake kamar munafuki” dagowa yayi da sauri ya kalleta yace “A’a kaina ke min ciwo Mumy” tace “Toh ga breakfast dinka can a dinning sai ka sha magani idan ka gama” mikewa yayi ya tafi dinning din ta bi sa da kallo, tabe baki tayi ta koma daki, tea kawai ya iya sha sai dube duben inda xai ga Humainah yake, mikewa yayi daga karshe ya tafi dakinsu, kwance ya sameta ita kadai fatima kuma ta tafi boko, mikewa xaune tayi ganinsa ya rufe kofar dakin tana ganin haka ta fashe da kuka tace “Ni wllh ka fita kar in kira maka Mumy” tsayawa yayi yana kallonta, tana share fuskarta tace “Ni dai ka fita” ganin ya nufota tsoro ya kamata ta fasa ihu tana kiran Mumy, still yayi yana kallonta, Mumy ta bude kofar dakin tana kallon ciki da mamaki tace “Meye haka?” Ta fashe da kuka tana kokarin sauka daga kan gadon, Mumy ta kallesa tace “Me ya shigo da kai nan?” Rasa abun cewa yayi ya fara kame kame, can yace “Ni ban san…” Wani tsawa Mumy tayi masa tace “Get out!” Juyawa yayi ya fice daga dakin, Mumy ta kalleta tace “Ihun me kike ma mutane ke kuma” share fuskarta tayi a hankali tace “Ba komai” Mumy ta kusa second ashirin tana kallonta sannan ta juya ta fita daga dakin. Junaid kam part dinsa ya koma ya dau makullin motarsa ya fito ya tafi parking space ya dau motarsa ya fice daga gidan, hotel din jiya ya nufa yana gama parking ya fito ya hango El-ameen ya fito, kallo daya El-ameen yayi masa ya nufi gun motarsa dake ajiye har ya bude xai shiga Junaid ya bi sa da sauri yace “Hey…” Wani kallo El-ameen ya watsa masa yace “A haka xaka auri yarinyar ka kula da ita?” Junaid yayi tsaki ya xaga ya bude seat mai xaman banxa ya xauna, girgixa kai El-ameen yayi ya shiga motar shi ma, junaid yace “Kasan me frnd ina cikin damuwa wllh” El-ameen ya kallesa yace “Me ya faru kuma?” Dafe kansa yayi na kusan second goma sannan ya dago ya shiga gaya masa abinda ya faru bai boye masa komai ba, murmushi kawae El-ameen yake yana kallonsa can kuma ya fashe da dariya har da kyakyatawa, junaid ya tsaya kallonsa da mamaki lokaci daya ransa ya baci, bude motar yayi xai fita El-ameen ya tsagaita dariyarsa ya rikosa yace “Haba it’s very funny mana, daga shan lipton? Seductive aka xuba maka cikin ruwan lipton din, its a plan, ba dai kace kayi trusting wannan khadijar ba kana tare da wahala,” Xaro ido Junaid yayi yace “Seductive kuma?” El-ameen ya kuma fashewa da dariya yace “Of course, ita kuma warce aka turo maka taji maxa ta tsorata… Ohhh my God! Kai ban taba ganin makirci a xahiri irin na yan gidan nan naku ba” Junaid kallonsa kawai yake don kansa ya gama daurewa, El-ameen ya daga kafada yace “Allah ya taimakeka ka nuna mata kai din ba na wasa bane, da kawai sharri xa a maka ace kayi raping dinta you know daga nan ka kuma shiga wani case kila ma daga karshe Abba yace sai ka aureta, tunanin da Humainahn ma ta yi kenan kuma gwara da Allah ya kawo ta a lokacin don da komai xai iya faruwa” junaid ya rike kansa yace “Innalillahi……” El-ameen ya tabe baki yace “Allah ya kyauta! Ni dai am going to clinic Abba ya Kirani yanxu” junaid ya dago kai ya bude motar xai fita jiki a sanyaye, El-ameen ya d’an bude ido yace “But wait! ina xa ka yanxu? Uhn…. kar kuma pills din bai gama sakin ka ba kaje ka afka ma…..” Kasa Karasawa El-ameen yayi ya dinga dariya, junaid ya hade rai yace “Wai mahaukaciyar?” Shi dai El-ameen bai ce komai ba sai dariya yake, Junaid ya dawo ya xauna yace “Look ko da ace na aureta yanxu me kuma xan ma mahaukaciya, infact ko ta samu lafiya sauwake mata xanyi ta tafi ta nemi yan uwanta frnd” El-ameen yayi shiru idonsa a kansa yace “Promise dat!” Shiru Junaid yayi shima yana kallonsa can yace “Promise what?” El-ameen yace “That tana samun lafiya xaka sauwake mata kuma baxa ka taba ‘yar mutane ba” junaid bai ce komai ba can ya tabe baki yace “Do i need to, ba dai ni nayi niyyar yin hakan ba, ohk I promise” A hankali El-ameen yace “Kuma alkawari dai kaya ne” junaid ya masa wani kallo yace “Na fi ka sanin wannan” El-ameen yace “Good, yau Thursday sai ka fara shirye shiryen kai ta gidan ku on Sunday, I promise xan yi iya kan kokarina in ga everything goes smoothly” Junaid yace “But ni ban san wanda xai mata shiri me kyau ba irin na xamani” El-ameen yace “Ba sai kayi hiring a xo har hotel a mata ba” junaid yace “Ohk” bude motar junaid yayi ya fita ya nufi cikin hotel din El-ameen ya bi sa da kallo.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button