CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers association????

Ayi ta hakuri da ni a haka har mu kare pls.
[3/19, 9:36 PM] El-hajj????: ⚓ Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

85…..

Kallon Hajja kawai junaid yake don ya kasa fahimtar inda xancenta ya dosa duk ta cikasa da hayaniyar dake baraxanar haddasa masa ciwon kai, Muryar kawunsa yaji na kiransa ya juya yana kallonsa yayi masa alama da ya xo, part din Abbansa ya nufa ta bi sa tana ci gaba da xaxxaga masa bala’i shi dai bai tanka ba, bai same su parlor ba ya karasa har bedroom, hajja tayi tsaye nn parlon tana ta ci gaba da bala’i ta inda take shiga ba ta nn take fita, xaune ya samu Abbansa da frnds dinsa biyu sai kawunsa, Kawunsa wato Abban Humainah ne yace “Ahmad!” Ya dago a hankali yana dubansa amma ya kasa cewa komai. Kawun yace “Na’am mahaifin yarinyar nan ya bukaci da ka aureta, don me da ku ka dawo baka sanar ma iyayenka komai ba sai abokin ka ne ke fadi ma Abbanka few dayz back…..” Kasa cewa komai Junaid yayi sai dai kansa yayi mugun daurewa, Abbansa dai sai kallonsa yake, Alhaji umar yace “Kayi shiru Ahmad, gaskiya ne Kai mijin mace hudu ne bbu wanda xai hanaka kara aure tunda kana da halin yin hakan sai dai kawai Kayi kokarin xamo me adalci tsakaninsu, amma meye na boye ma iyayenka, da nufin ka yau sai ka taho kace a tashi aje maka daurin aure, Babanka yayi ta xuba maka ido amma shiru baka ce masa komai ba….” Alhaji Habib yayi dariya yace “Kar fa ku ga laifinsa, that’s what it takes to be a 1st child, wauta ne kawai irin tasa” Kawunsa yayi murmushi yace “Gaskiya ne, to Allah ya sanya alkhairi Ahmad, ae kai din mijin mata hudu ne, Allah ya baka ikon adalci” ae sai kawai Junaid ya sunkuyar da kai ya ma rasa gane wani yanayin yake ciki, yanxu ana nufin shi xa’a aura ma Zahrah, amma ai basu yi haka da kowa ba, how is this? No ya ma san kawai basu fahimce xancen bane amma da abokin sa xa ayi auren, Muryar Abokin Abbansa yaji yana ce masa ya tashi ya je, dagowa yayi da sauri cikin sanyayyen murya yace “Kuyi hakuri Abba, ni…..” Kasa ci gaba yyi don bai ma san abinda xai ce ba, cewa xai yi shi bai sani ba ko kuwa ce musu xai yi ba fa da shi xa a daura auren ba, Abban Humainah yace “Tashi kaje, Allah yayi maka albarka… Ya baka ikon adalci tsakaninsu” mikewa yayi da kyar ya fita daga dakin cike da confusion to yaga ae ba fa da shi xa ayi auren ba, how is all this???? Ko kallon Hajja da ta cika parlor da muryarta bai yi ba ya fice daga parlon, ya tafi part dinsa ya dau makullin mota ya fito ya dau motarsa sai gidan El-ameen, Hafsat dake ta mopping din Balcony ta gaishesa da fara’a tace masa yana sama a study room, yana haurawa sama ya bude kofar dakin, Xaune ya samesa idonsa lumshe ya karasa gabansa yana kallonsa, bude ido El-ameen yayi ya gyara xama ganinsa yace “Yahh, xaka iya xuwa kuwa?” Junaid yace “Ahmad I don’t get what my parent are telling!” El-ameen ya shafa kansa yana murmushi yace “Wai na auren ku da Zahrah?” Buda ido junaid yayi yace “Aurena da Zahrah kuma?” El-ameen yace “Yeah” xaunawa junaid yayi jin ya kasa ci gaba da tsayuwar yace “You are getting me confuse, wace Zahran….” Murmushi El-ameen ya kuma yi yace “To ya na iya maka frnd? Ban son wani abu ya sameka mu rasa ka a kan Zahrah, ni na nema maka aurenta, isn’t it nyc….. Nasan yea you are in love with her….. Son da kake mata ya take nawa so I have no option then to let go, ita ma na ga tana son ka sosai shi yasa nayi haka from the beginning, nasan dai yanxu no more love sickness nd the rest, just that kar ku cuci Humainah…..” Tuni idon Junaid ya kada ya kasa ce masa komai yana kallonsa, El-ameen ya dunkule hannunsa ya kamo na Junaid ya kai masa knuckle yana murmushi yace “Chop knuckle frnd” Ana saukowa juma’a aka daure auren Capt Ahmad Junaid da Princess Zahrah El-ameen Moddibo a kan sadaki 1m wanda mahaifinta ne ya bayar, daurin auren nan ya samu halartan dubban mutane da ‘yan gidan masarautu da dama daga ko ina na states din Kasar duk ta dalilin Sarki El-ameen Moddibo, masarautan bauchi ya xamo bbu masaka tsinke tsabar jama’a, kusan duk manyan da suka xo daurin auren mamakin mijin Zahrah suka dinga yi ganin shi ba basarake ba, shi ba yarima ba, shi ba jinin sarauta ba, shi ba kowa ba just a mere military personnel with CLASS, ba karamin alfahari sarki El-ameen yake da junaid ba da ya xamo sirkinsa, Junaid ya gaisa da mutane da dama sunfi dari kowa son ganinsa yake ta dalilin yanda sirkinsa wato sarki ke koda sa gaban abokansa sarakai da manyan kasa, baka taba fadin yanayin da Junaid yake ciki a lkcn sai dai kawai kaga yayi murmushi wani lokacin wanda iyakarsa lips, gam yake rike da hannun El-ameen dake gefensa don bai son su rabu, Su Abba basu suka bar bauchi ba sai kusan magrib don ba karamin walima aka shirya ba, xuwa bayan isha masarautan bauchi yayi tsit baka taba cewa anyi komai ciki don tuni aka tsaftace ko ina, Junaid dake xaune daki na musamman da aka basu shi da El-ameen, Aliyu, faisal da wasu frnds dinsa biyu, ya rike kansa har lokacin don ya kasa gaskata da shi fa aka daura auren nan yau, El-ameen ya dawo gefensa yace “Toh programs kusan goma ne fa gabanmu Mr man!” Dagowa yayi da sauri yana kallonsa, El-ameen yayi dariya yace “Atoh, gwara ka bar rike kai this is just the beginning, Abdul yace ka shirya xaka gun Zahrah, wato xaka je ganin amaryar ka…..” Da ‘yar dariya El-ameen ya kare xancen daga haka ya shiga bathroom don watsa ruwa, Aliyu dake ta danna waya yace “Duk karya ce!” Faisal ya kallesa ya danne dariyarsa yace “Meye karyar?” Aliyu yace “Wannan ji da kan da miskilancin wani mana” dariya sosai Faisal da sauran frnds din Captain suka dinga yi, shi dai Junaid bai tanka kowa ba, El-ameen na fitowa ya shiga toilet din shima, wani kaya irin ta sarauta lafiyayye El-ameen ya ajiye masa gefen gado bayan ya fito yace “Wai kayan da xaka sa kenan suka ce” Junaid da har lokacin bai iya hada ido da abokin nasa ya shiga jujjuya kayan, can ya mike ya tabe baki yace “No, bai yi min ba” dariya sosai El-ameen yayi su Aliyu na tayasa wanda hakan yayi mugun kona ran Junaid, Aliyu yace “Ae ko ka ki malam dole haka xaka sa, coz that’s the rule tunda gidan sarauta kayi auren” sai a snn Junaid ya kalli El-ameen ya hade rai sosai yace “Nooo, bbu wanda xae dinga kafa min rule, snn bbu wanda ya isa yyi forcing dina….” Aliyu ya fashe da dariya yace “Duk karya ce wnn” El-ameen da ya kasa daina dariya yace “See you. Ka dinga bin rules kenan har sai an kai maka matar ka can gidan ka” Junaid bai tanka sa ba xai dau kayansa ya sa El-ameen ya kwace kayan yace “Kasan Allah kar fa ka dinga mana taurin kai nan” faisal yace “Look Capt you just have to obey before complaining as a good militant, idan ka bar nan naga bbu wanda xai bi ka yace ga yanda xaka yi koh?” Daukan kayan Junaid yayi ya fita parlor don sa wa, Aliyu ya fashe da dariya yace “Wato abun sai da lallaba,” ko da Junaid ya dawo dakin duk kallonsa suka tsaya yi don sak yarima ya dawo, yayi kyau ba kadan ba, Aliyu yace “Uhm yarima junaid, ka hadu” junaid bai tanka sa ba, misalin karfe tara da wani abu aka doka sallama can parlor El-ameen ya fita, wata yar dattijuwa ce tsaye ta duka har kasa ta gaishesa tace “Ance in yi ma ango iso har gun Gimbiya Zahrah” El-ameen ya juya ya koma daki yace “Toh an xo daukar ka Capt, if you like go nd misbehave mu dai muna nan” sae da junaid ya ga dama sannan ya mike ya fita, dattijuwar na gaba yana biye da ita a baya, haka kawai yaji gabansa ke faduwa, tafiya me nisa suka yi har suka iso wani babban kofa ta bude kofar suka shiga wani parlor me girman gaske xama yayi parlon ita kuma ta karasa ta bude wani kofa ta shiga ciki, ba a dau lokaci ba ta fito ta risina tace “xaka iya shiga ranka shi dade” mikewa yayi ya nufi dakin har lokacin gabansa bai bar faduwa ba, yana shiga dakin wani sanyayyen kamshi ya doki hancinsa bai san lokacin da ya rufe kofar ba ya juyo ya sauke idonsa kanta.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button