CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

     _By Khaleesat Haiydar_✍????

16…..

Mama jummai ta shigo palon rike da bucket tace “Har ta shanye?” Yace “A’a barnatar da shi xata yi shi yasa na boye, ta koshi kuma” mikewa yayi ya dauke bowl din yace “Xan tafi yanxu, sai na dawo anjima mama” ta karba bowl din tace “Toh Allah ya tsare” daga haka ya ja dogon hancinta yayi hanyar kofa, mikewa tayi da sauri ta bi bayansa, Mama ta saka dariya tace “Au, toh gashi xata bi ka” juyawa yayi da sauri yana kallonta ya galla mata harara yace “I will knock you idan kika xo nan” kamar ta ji me yace ta tsaya tana cixgar stones din rigarta tana kallonsa, ya juya ya fice daga parlon, mama jummai ta karaso ta kama hannunta suka koma cikin parlour’n. El-Ameen na fita ya rike waist a waje tunawa da yayi ai ba mota kuma bbu kudi hannunsa, tsaki yayi ya nufi main road da kafa ya tsayar da adai daita ya gaya masa anguwarsu, suna isa yace yana xuwa sannan ya shiga ya fito masa da kudi ya basa ya koma ciki, Ummi dake parlor sai binsa da kallo take bayan ta amsa gaisuwarsa tana ganin ya nufi daki tace “Xo nan Ahmad” komawa yayi ya xauna kasa yana kallonta yace “Gani Ummi” tace “Ina kake xuwa this dayz baka xaman office?” Ya d’an sosa kai yace “Ummi, dama… To wai Ummi wa yace bana xama office ni da kullum sai na je clinic” Ummi ta galla masa harara tace “Am not joking Ahmad, wannan sabon salon da ka tsiran ma rayuwarka ba fishshe ka xai yi ba don b’ata ma mahaifin ka rai kawae kake” ya sunkuyar da kai bai ce komai ba, Ummi tace “Magana ta biyu kuma tunda kai ka kasa fito da mata toh ni na xabar maka….” Da sauri ya D’ago kai yace “Ummiii!” Tana masa mugun kallo tace “Ehh, ni ma xan rakaka gidansu yarinyar da kaina in ma ya kama ni xan maka maganar sai inyi, kuma ba wata bace facce ‘yar abokin Abban ka Fiddausi” wani xufa ne ya shiga keto masa duk ya ma rasa abinda xae ce, da sauri yace “Ummi ni fa na riga da na samu yarinyar da nake so” Ummi na hararansa tace “Wannan kuma ba matsala ta bace, sai dai kuma ka raina ma kanka hankali ba ni ba” ya marairaice mata yace “Ummi Allah kuwa da gaske, a gidansu junaid ma take” Ummi tace “Wacece kenan?” Yayi kasa da kai a hankali yace “Humainah take ko wa? kuma niece din Junaid ce” Ummi tayi shiru tana hararansa yace “Allah kuwa Ummi, naji kamar ina sonta” tace “Toh ae xanje gidansu junaid din kuwa” bai kuma cewa komai ba sai tunani yake anya gskya ya fadi ma Ummi kuwa, can dai ya mike yace “Bari in tafi office Ummi”, tace “Allah ya tsare”
Karfe Hudu saura Junaid yayi parking kofar gidan El-Ameen ya fito, ya koma back seat ya cire hularsa ya ajiye da rigar khakinsa ya dauki well ironed shirt dinsa dake bayan mota don bae rasa mofti a motar ya saka sannan ya fito ya shiga gidan, Mama jummai na share parlor ita kuma tana tsaye jikin bango kamar xata shige ciki, Mama jummai tayi masa sannu da xuwa, ya amsa tare da gaisheta hankalinsa na kanta, Mama jummai tace “ka ganta can tafi awa biyu tsaye taki xaunawa” murmushi yayi ya karasa inda take tsaye, ya kama hannunta suka dawo parlorn ya xaunar da ita, ya rike chin dinsa da duk hannunsa biyu yana kallonta ita ma kallon nasa take, fine beard din da ya xagaye bakinsa ta kai hannunta ta taba, yayi murmushi ya kama hannun cikin nasa yana kallon manyan fararen eyeballs dinta cikin sanyin murya yace “I will call you Jasmine! Do you like dat?” Kwace hannunta tayi daga nasa, ya tsura mata ido, bude kofar parlor aka yi El-Ameen ya shigo, ae tana ganinsa ta mike da sauri ta nufesa ta isa gabansa ta tsaya, Junaid ya bi ta da kallo, El-Ameen ya ja hancinta ya bude hannayensa yace “toh dai bbu abinda na siyo maki” kallon junaid yayi yace “The great Capt Ahmad Junaid ashe kana nan” mikewa junaid yayi yace “Sure!” Daga haka ya nufi kofa, El-Ameen yace “ba dai har xaka tafi ba” junaid yace “Yea daga office nake” daga haka ya fice daga parlorn, bin sa da wani irin kallo El-Ameen yayi kafin ya fita yayi saurin cewa “Hey a minute” junaid ya tsaya sannan ya juya yana kallonsa, El-ameen yace “gaskiya ya kamata ka shiga kasuwa ko kuma ka bada kudi a shiga a sama mana TV a gidan nan, ko ka mance yanda muka yi da kai?” Junaid yace “I will transfer the money later sae ka samu me siyo maka TVn” yana gama fadin haka ya fice daga palon, El-ameen ya d’aga kafada ya kama hannunta suka koma parlor.

As usual ya dade xaune mota bayan yayi parking a lot din gidansu kuma har lkcn bae kashe mota ba yana danne dannensa a waya, Khadija ce ta fito daga part dinsu ta karaso gun motar ta bude tace “ina yini yaya A.jay” ya kalleta yace “Lafiya lau” ta d’an marairaice masa tace “yaya yau ciwo ciki na ke min wllh” tabe baki yayi ya ci gaba da danna wayarsa, ta dan shagwabe masa tace “Yaya ka d’an ban kudi in siya magani mana, Umma ta ki bani” dubu daya ya xaro aljihunsa ya mika mata cike da murna tayi masa godiya ta kara gaba, shigowar motar Suhaima yasa shi kashe motarsa ya fito ya rufe ya fara tafiya, Hajiya ce suka fito daga part din Umma da wata mata alamar rakiya xa su mata, duk suka bisa da kallo, ba tare da ya kallesu ba ya gaida su don dama sai lokacin da yayi suit dinsa yake gaishesu, matar ce kadai ta amsa shi, bae damu da haka ba yayi part din Mumy, Matar da ta bisa da kallo ta maido da dubanta gun su Umma murya can kasa tace “Shine yaron hala?” Cike da tsanarsa Hajiya tace “Ehh wllh” matar tayi wani murmushi murya can kasa tace “Duk ku kwantar da hankalin ku, ku bar min komai a hannu na baxan baku kunya ba” babu wanda yace komai cikinsu suka rakata har waje gun motar ta. Junaid na shiga parlon Mumy ya tarda Humainah kwance da ganinta kasan ba kuka kadan tayi ba, dariya ya saka yace “ohh shikenan an bar mana ita” mikewa tayi xaune idon ta ya cicciko ta kwalo ma Mumy kira, Mumy ta fito daga daki tace “be careful Mr” dariya yayi yana shafa kai yace “Ya hakuri Mumy, ina yini” ta karaso parlorn tace “Nayi xaton ae baxa ka kashe motar ka shigo gida ba” yyi murmushi yace “Ac fa nake sha Mumy” ta tabe baki tace “Haka ne, ga abincin ka can” kujera ta xauna tana kallon Humainah tace “Kema kije ki dau naku abincin ke da fatee, ko baki hakura ba har yanxu” bata ce komai ba tayi kasa da kai, Junaid ya mike yace “Xan dawo Mumy bari inyi wanka” tace “Ohk,” bin sa da kallo tayi sae da ya kai bakin kofa tace “Canxa kaya kayi office” murmushi kawae yayi ya fita. Wanka yayi ya kuma canxa kayan jikinsa yyi kwanciyarsa parlor don bai jin yunwa, ya kusa awa daya kwance Humainah ta shigo parlorn rike da tray dauke da abincinsa, ta karaso ta ajiye masa, ya mike xaune cike da xolaya yace “Shikenan fatima ta huta an kawo mana maid kyauta” mikewa tayi a fusace xata fita ya rikota yana dariya yace “Ke dalla wasa nake maki” ta fixge hannunta tace “Bana son wasan” ya daga kafada yace “Ni kuma sai nayi din” wani kallo ta shiga yi masa fuska daure, ya hade rai yace “Toh in kince a biya ki kudin aikin ba sai a biya ki ba ma” hawaye ya cika idonta ta juya xata fita aka bude kofa El-Ameen ya shigo da sallama, da sauri ta kuma juyawa tana kallon Junaid da ya bude ido ganin El-Ameen da ya kasa Karasowa cikin parlorn, Junaid ya mike yana dariya yace “C’mon ka karaso frnd” El-Ameen yace “Um ban gaida Mumy ba am coming” da sauri junaid ya karasa ya rufe kofar da key ya cire sannan yace “ba ta kofarta ka wuce ba kafin ka karaso nan” El-Ameen ya ma rasa me xai ce masa, dawowa cikin parlorn junaid yayi ya xauna yana kallon Humainah yace “Toh ae sai ki goge hawayen yanxu tunda ga shi ya xo koh, duk kin isheni kin daga min hankali ina El-Ameen toh ga ki ga shi” Humainah tayi wani kara ta durkushe wajen ta shiga kai masa duka tana cewa “ni bana son haka ya Ahmad, bana so” El-Ameen yayi murmushi ya nufi daki, da sauri Junaid ya mike ya rigasa shigewa dakin ya saka key daga ciki yace “Ji min munafukai” gajiya yayi da tsayuwa ya dawo parlorn, can nesa da ita ya xauna yace “Ina yini” ta d’an kallesa ta hade rai tace “Lfya lau” bai kuma cewa komae ba ya dau remote yayi powering Tv, sun kusa minti talatin parlorn bai ce mata ba bata ce masa ba, kamar wanda ya tuna abu ya mike da sauri yana kallon agogo ya nufi dakin junaid ya kwankwasa yace “Look captain akwae drugs din da xanje in ba patient dinka open the door plss ka bude kofar parlor am leaving” junaid dake kwance ya fara bacci ya mike jin abinda El-Ameen yace ya bude kofar, El-Ameen yace “D’an rainin wayo bacci ma kake koh” fitowa junaid yayi suka dawo parlor a tare, kallon Humainah yayi yana murmushi yace “Har kun gama xancen kanwata” ta hararesa ta dauke kai, shi kam El-Ameen har ya kai kofa, Junaid yace “toh dai ki ajiye abinda ya baki idan na dawo mu raba, kuma ki d’an gyara min bedroom saura ki min satan turare ki ga ko ba na saurayin ki xan je in sace ba” yana fadin haka yyi kofa ya bude ya fice yana dariya, El-Ameen ma ya fita, Part din Mumy suka shiga El-Ameen ya gaida ta, Junaid yace “Xan d’an rakasa indawo yanxu Mumy” Mumy tace “Toh sai ka dawo” daga haka suka fice da El-Ameen. suna isa El-Ameen yace “Baka yi min transfer din kudin Television din ba fa, if you provoke me xan fa je in siya da kudina” Junaid yace “I forgot xan yi” fitowa suka yi daga motar suka shiga gidan, Mama jummai na xaune parlor ta daura kanta kan cinyarta idonta rufe, El-Ameen yace “dama tana bacci ba da daddare ba” Mama jummai tace “Ina jin bata jin dadi ne yau, sau biyu tana amai ga jikinta da dumi, ita da ko xama bata yi da rana bare ta kwanta” El-Ameen ya karasa ya durkusa gabansu ya d’ago kanta ta bude ido tana kallonsa, ya gyara mata gashinta a hankali yace “Malaria… I guess” xaunawa Junaid yayi shi dai bae ce komai ba, El-Ameen ya d’agota ya xaunar da ita kan kujera yace “Sorry….” Ya kalli Junaid yace “Ka bada kudi in tafi in siyo mata drugs da injections” kallonsa kawai Junaid yake bai ce komai ba, El-ameen ya kalli mama sannan ya kallesa ya juya xuwa harshen turanci yace “It’s not a matter of looking at me dat way captain, don’t forget she’s ur patient, ur mind agreed to the terms nd condition of helping her, nd I guess before u jumped into the conclusion of doing dat, you already know….” Katse sa junaid yayi yana masa wani kallo yace “did you hear me complain?” El-ameen yayi dariya yace “Not dat I don’t have the money to assist you but….” Tsaki Junaid ya ja yace “Enough plss, I don’t even need ur goddam help,” El-ameen yayi murmushi yace “Ni kuwa kake bukatar taimakona, cos lokacina da na ware for her is far far better then dat money you are spending, anyway! 20k will do for the test nd everything” Atm junaid ya ciro ya mika masa ya karba, ya mike ya haura sama syringe ya dauko a daki da plastic tube na drip ya dawo parlon, da kyar ta bari ya debi jininta don sae da Mama jummai ta riketa, ya mike yace “Bari in je in dawo yanxu, Mama ki d’an bata kunu ko kadan ne ta sha” Mama tace “Toh” sannan ya fita daga parlorn, xamowa tayi daga jikin mama ta kwanta kasan tiles, mama ta d’agota tace “Sannun Kinji Baiwar Allah, Allah ya sauwake maki” kara ta saki alamar bata son tashi a kasan, Mama ta kyaleta ta tafi kitchen, mikewa Junaid yayi ya isa gabanta ya durkusa, kallonsa kawae take kafin ta kauda kanta, ya d’agota a hankali yace “Sorry Jasmine, get well soon” mikewa tayi ta kwace hannunta a nasa ta fara tafiya, ya bi ta da kallo ganin yanda take tafiya, can jikin bango taje ta tsaya, ya mike ya koma kujera ya xauna, har mama ta fito kitchen rike da pap bata bar jikin bangon ba, Mama ta ajiye bowl din hannunta ta karasa ta kamo hannunta, da kyar ta biyota suka dawo parlor ta xaunar da ita ta shiga bata kunun amma taki sha, da ta takurata mikewa tayi ta dawo kusa da junaid ta xauna gefen shi ta jingina jikinsa ta rufe ido gam, duk tayi wani laushi da ganinta kasan bata da lafiya, shi kam kallonta kawae yake wani tausayinta ya dinga ji, ya ji dama ciwon ya dawo jikinsa, ya rungumota jikinsa a hankali yace “Sorry My Jasmine” mikewa mama tayi ta mika masa kunun tace “Toh ka bata Junaid kila ta karba ko kadan ne” yyi murmushi ya karba ya janyeta daga jikinsa ta bude ido tana kallonsa, ya debi kunun kadan ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri, rasa yanda xae yi ya bata yayi, kawae ya ajiye, ita ko ta sauka kasa ta kwanta, bayan minti goma El-Ameen ya shigo parlorn, ya ajiye ledan hannunsa ya d’agota yana kallon junaid yace “Ta sha kunun” girgixa masa kai kawai yayi, El-Ameen ya jawo bowl din kunun ya debo ya kai mata baki, ta kauda kae da sauri, ya hade rai yace “I will knock you, c’mon bude baki” kara ta saki ya xuba mata kunun a baki ta xubar da sauri, ya daka mata tsawa, nan da nan jikinta ya dau rawa ya debi wani ya bude bakin ya xuba mata, da kyar ta hadiye hawaye na sakkowa idonta, Junaid ya jinginar da kansa jikin kujera ya lumshe ido, haka El-Ameen ya dinga bata tana karba da kyar har tayi four spoon sannan ya ajiye, ya fara hada drip da xai sa mata da alluran da xai mata, ita ko kwanciya tayi kan tiles ta rufe ido, yana gama hada alluran ya D’ago ta ta bude ido, gown din jikinta ya d’aga don a lap xae mata alluran, kallon junaid yayi yaga idonsa na kansu, da sauri junaid ya kauda kai, El-Ameen ya kwantar da ita yayi mata alluran, tun bai gama ba ta fara kokarin mikewa, duk jikinta yayi xafi ba kadan ba, ya maidata ya kwantar har ya gama sannan ya dagota yace “Sorry” komawa baya kawae take hawaye na xuba idonta, El-Ameen ya d’an yi murmushi don hawayen shaidar wataran xata dawo me hankali ne sai dai fatansa daya kar tayi loosing memory dinta, kusa da junaid ta koma ta xauna gefensa ta daura kanta a kafarsa ta rufe ido, yana son ya lallasheta duk da yasan ba gane nufinsa xata yi ba amma bae son yin hakan gaban El-Ameen ya ya kafa masu ido, hakan yasa ko kallonta bai yi ba, El-Ameen yayi murmushi ya mike ya nufi kitchen don dauko cup yyi mata diluting drugs ya bata ta sha, Junaid ya kai fuskarsa dai dai nata a hankali yace “Sorry Jasmine….” Ta bude idonta da suka sauya launi tana kallonsa, da sauri ya D’ago jin fitowar El-Ameen, ko kallonsu bai yi ba yi diluting drugs din da ruwa ya dawo kusa da su ya xauna ya dagota yace “Tashi ki sha magani” kara ta saki ta boye fuskarta jikin junaid tana shishshige masa kamar xata shiga jikinsa, El-Ameen ya mata wani tsawa, jikinta na rawa ta rike Junaid tana ihu, janyeta El-Ameen yayi ya hade rai yace “Keehh” cup din ya kai bakinta ta ki budewa, ya mata wani rankwashi ta kwala ihu, da sauri ya jawota ya juye maganin bakinta ya rufe hancinta, sae da ya tabbatar ta shanye su gaba daya sannan ya cire hannunsa hancinta, lkci daya duk ta amayo maganin jikinsu gaba daya su ukun, daga nan ta dinga amai gashi bata ci komai ba, El-Ameen ya mata wani tsawan da ya rikitata ta fasa ihu xata mike ya fixgota da karfi ta fado kansa ya rungumeta tsam jikinsa, sunkuyar da kai junaid yayi jin wani abu da bae taba ji ba a xuciyarsa a lkcn, a hankali ya shiga cire shirt din jikinsa da ya baci da amai, Mama jummai dake tsaye daga bakin kofa cike da tausayinta taji kamar tayi mata hawaye duk ita ma jikinta yayi sanyi, mikewa junaid yayi har lkcn bae kallesu ba ya haura sama, El-Ameen ya bi sa da kallo, a hankali ya d’ago kanta jin ta sakar masa jiki gaba daya ya ga bacci tayi, kamar me rada yace “Jewel!” A hankali ta bude ido tana kallonsa.

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button