CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVELNOVELS

CAPTAIN AHMAD JUNAID COMPLETE HAUSA NOVEL

Haske Writers Association????
Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

34…..

El-ameen ne xaune cikin special ward
ya hade kai da gadon dake kusa da shi, bude kofar ward din aka yi ya dago da kyar, dai dai lokacin da Hajja ta karaso gun gadon da gudu ta daura hannu a ka ta saki wani uban ihu tana salati su Hajiya ma suka shigo ko wanne tana salati, mikewa El-ameen yyi ya fice daga ward din, ba a dau lokaci ba nurses har hudu suka shigo suka fitar da Hajja da su Hajiya, kuka Hajja take rusawa iya karfinta tana cewa “Ku gaya min ko mutuwa yayi don Allah, wayyo mahaukaciya ta cuce mu, kila yana tukin ta shake mana shi ya saki steering, wayyoo ni Dijee” Su Hajiya dai sai matsen kwalla ake kamar gaske, El-ameen ne ya xo wucewa Hajja ta bi sa da gudu tana cewa “Tsaya Aminu gaya min me ya samu Ahmad din, don Allah gaya min ya mutu ne? Wayyo an kassara Muhammadu don shi daya gare sa” Tafiya kawai El-Ameen yake tana binsa da gudu har ya isa ward din ya shiga ya rufe kofar yasa makulli, ta fashe da matsanancin kuka tace “Allah ya isa tsakani na da kai dan iska” A hankali El-ameen ya karasa gadon da Junaid ke kwance yana kallonsa, a shoulder dinsa yaji ciwo banda nan bbu wani waje kuma sai dai har lokacin he’s unconscious, juyawa yayi yana kallon Jasmine dake kwance a wani gadon har lokacin ita ma bata farfado ba, ya xauna ya hade kai da gado, shine mutum na farko da aka fara kira aka sanar ma hatsarin wanda hakan na nuni da shine mutum na karshe da suka yi waya da Junaid din, bude kofar ward din aka yi Abbansa ya shigo da wata nurse biye da shi a baya da clinic tray, mikewa yayi Abba yace “Meye amfanin saka su gaban da ka xo kayi ga injections ba a gama ba…..” Baya ya koma Abba ya dafa goshin Junaid ya kuma yi masa gwaje gwaje sannan ya juya ya koma gun jasmine, a forehead dinta ta ji ciwo sai kneel dinta daya, ita ma ya mata gwaje gwajen da xai yi ya juya yana kallon El-ameen yace “Ka karbi injections din hannunta ka masu, in ka gama ka xo office ka dau wanda xaka xuba a ruwa” daga haka ya juya ya fita, nurse din ta karaso ta mika masa tray din hannunta ya karba ta juya ta fita, Junaid ya fara yi ma sannan ya karasa gun Jasmine ya mata a lap. Kasa fita daga ward din yayi ya koma ya xauna duk jikinsa ba kwari, Abbansa ne ya kuma dawowa tare da Abban Junaid, Abba ya karasa gun gadon yana kallon Junaid da ganinsa kasan kawai yana boye tashin hankalinsa ne, Allah ya basa lafiya kadai yace ya juya ya fita Abban El-ameen ya bi sa a baya, El-ameen ya koma ya xauna, har bayan azahar babu wanda ya farka cikinsu, har lokacin kuma Hajja na asibitin tana rera kuka har an gaji an kyaleta, su Hajiya duk sun koma gida, kiran la’asar ya sa El-ameen ya fita daga ward din don xuwa yin sallah, yana fito ko minti biyar ba a yi ba jasmine ta bude idonta a hankali, bin dakin ta shiga yi da kallo a hankali har idonta ya sauka kan Junaid, kokarin mikewa xaune ta yi taji kamar an tsikara mata allura a kneel ga kuma drip din da ta gani jikinta, ta koma da sauri ta kwanta tana kallon drip din hannunta, fixgewa tayi ta ajiye, ta kusa minti bakwai xaune kamar me son tuno abu wanda hakan da take yi yasa kanta yayi mata wani mugun nauyi ga tsara mata da yake kamar xai tsage, kara tayi ta rike kan da hannu biyu taji abu kamar hula a xagaye mata, da sauri ta cire hannunta, bayan kusan minti biyu taji ciwon ya rage, saukowa ta shiga yi a hankali daga kan gadon, kamar me tsoron tiles din dakin ta dinga tafiya tana dingishi har ta isa gadon da Junaid ke kwance tana lekan fuskarsa, komawa baya tayi da sauri, sai kuma ta saka kuka tana yarfe hannu lokaci daya tana kare ma dakin kallo, a hankali tace “Ummi….” Sake lekan fuskarsa tayi ta kusa minti biyu idonta a kansa kafin ta juya a hankali ta bar wajen, muryoyi taji daga waje ta nufi wani kofa da ta gani da gudu ta bude ta shige ta fashe da kuka, ji tayi an bude kofa can waje tayi saurin jingina a jikin kofar bathroom din, kallon gadonta kawai El-ameen yake da mamaki, can ya juya ya kalli Junaid, da sauri ya nufi toilet tana jin ya murda ta juyo da sauri ta tura kofar da duk hannunta biyu, sau daya ya tura kofar ya bude ta koma baya da sauri tare da juya masa baya, kallonta ya tsaya yi da mamaki, a hankali yace “Jewel” xaro ido tayi zuciyarta na bugawa har lokacin kuma bata juyo ba, karasawa yayi ya dafata yace “Jewel” k’ara tayi da karfi yyi saurin juyo da ita yace “Hey It’s me jewel” tsit tayi tana kallon fuskarsa xuciyarta na bugawa, murmushi ya sakar mata ya kama hannunta yace “Am glad you are fine!” fixge hannunta tayi da sauri ta fashe da kuka tace “Ummina!” Tana fadin haka ta sake juya masa baya tana rera kuka, still yayi na kusan second ashirin sautin xaxxakan muryarta na kai kawo a kunnensa, ya kifta ido ya kusa sau biyar, can ta juyo a hankali suna hada ido ta sunkuyar da kai ta raba ta gefensa xata fita yyi hanxarin tare hanyar, da kyar ya iya bude baki yace “Wait! Wait Ina…ina Ummin naki?” Kallonsa kawai take sai kuma a hankali ta buda masa hannu alamar bata sani ba, cikin sanyin murya yace “Baki sani ba?” Ta gyada masa kai hawaye ya gangaro fararen idonta, murmushi ne yayi slipnn lips dinsa a hankali yace “Ohh! Alhmdllh!” lokaci daya murmushin ya bace tunawa da yayi sai fa ya iya xama kuma tayi loosing memory ya girgixa kai da sauri yace “No! no gaya min ya sunanki?” Kallonsa kawai take yi, ya gyada mata kai yace “Yyees tell me, ya sunanki?…” Gefensa ta kuma rabawa xata fita ya rikota, ta juyo da sauri ta warce hannunta tana masa wani irin kallon da yasa hanjin cikinsa kadawa, komawa baya yayi da sauri ta fice daga toilet din ya bi ta da kallo xuciyarsa na bugawa.

Haske Writers association????

Ba yawa kuyi sorry, na gaji ne yau
Captain Ahmad Junaid

By Khaleesat Haiydar✍????

35…..

Da kyar El-ameen ya iya juyawa ya fita daga bathroom din, ya ganta tsaye kusa da kofa tana kokarin budewa, tsayawa yayi yana kallonta har ta bude xata fita yayi saurin cewa “Wait wait ina xa ki” ko kallonsa bata yi ba ta fice, xaro ido yayi ya juya yana kallon Junaid kamar idonsa biyu din nan, bayanta ya bi da sauri ya tarar har ta sauka stairs tun kan ta karasa shiga reception ya sha gabanta, xuciyarsa na bugawa ya dake yace “Look, kin ga baki da lafiya ina xa ki” shiru tayi tana kallonsa, ya kasa kallon cikin idonta, cikin sanyin murya yace “Kiyi hakuri ki bari ki kara samun lafiya sai a kai ki gidan ku kin ji?” Jin bata ce komai ba ya dago da kyar yana kallon kwayar idonta, hawaye ya gani fal idon, ya dauke kansa, a hankali yaji tace “Toh ina ne nan?” Ya kuma dagowa da sauri yana kallonta yace “Asibiti,” maimaita abinda ya fada tayi a sanyaye ya gyada mata kai, tace “Meye hakan?” Buda ido yayi yana kallonta lokaci daya jikinsa yayi sanyi, ya girgixa kai da sauri yace “Ki gaya min sunan ki tukun!” Shiru tayi tana kallonsa, can tace “Suna?” Ya gyada mata kai, kafa masa ido tayi kamar dai tana son tuno sunan, a xuciyarsa ya dinga furta innalillahi, k’ara tayi ta dafe kanta xata durkusa, yayi saurin rikota ya dagata ya nufi sama da ita, addu’a ya dinga yi a xuciyarsa na cewar Allah yasa ba abinda yake tunani bane, lokaci daya jikinsa yayi sanyi, gadon da take ya mayar da ita ta kwanta ta rufe ido, ya ja kujera ya xauna kusa da gadon yana kallonta, ta kusa minti biyar bata bude idon ba, can ta bude a hankali tana sauke ido kansa ta mike xaune da sauri tace “Ummina” gefen gadon ya xauna yace “Toh gaya min inda take in kai ki” ACn dake ward din ta tsura ma ido da ganinta kasan tunani take, wani karan ta kuma yi ta runtse ido ta dafe kanta, lumshe ido yayi shi ma ya dafe kai tausayinta na shigarta, a hankali ya dago yana kallonta cikin sanyayyan murya yace “Ki kwanta ki huta kin ji, anjima xa ki tuna inda Ummin ki take in kai ki” bude ido tayi tana kallonsa ya sakar mata murmushi ya gyada mata kai, komawa tayi ta kwanta, yace “Xa ki ci abinci” ta kallesa tace “Abinci?” Kamar me koyon word din tayi maganan, jiki a sanyaye ya mike ya fita daga dakin ta bi sa da kallo, yana rufo kofar ta mike xaune tana kallon gadon da Junaid yake, saukowa tayi a hankali ta isa gun gadon ta duka tana lekan fuskarsa, ta kusa minti biyar tana kallonsa can ta kamo hannunsa a hankali murya can kasa tace “Daddy!” Mikewa tayi da sauri kamar warce ta tuno abu, runtse ido tayi ta dafe kanta hade da yin ihu, sosai kanta ke juya mata wanda hakan yasa ta fadi kan gadon, ta dau lokaci bata dago ba, can ta bude ido a hankali ta ganta kansa, xaro ido tayi ta mike da sauri tana kallon shoulder dinsa dake jini duk da bandage din dake nan alamar ta fama masa, kuka ta fashe da ta duka a hankali tana kallon shoulder din, bandage din dake kanta ta taba ta sa hannu biyu ta fixge da karfi har sai da ya fita ta matso kusa da shi ta duka ta daura bandage din kan kafadar nasa, bude kofa aka yi El-ameen ya shigo rike da plate da cup din tea, tsaye yayi bakin kofar yana kallonta ta juyo ita ma tana kallonsa ta nuna masa kafadar Junaid tace “Ciwo!” Tana fadin haka ta d’an bude ido tana kallon abinda ta kira da ciwo kamar me son gano abu, karasowa El-ameen yayi sanin she’s trying hard ne ta tuna abu yace “yes ciwo ne, taho in sa maki wani bandage din you are bleeding” gadonta ya nufa, ta bi bayansa jiki a sanyaye, ya nuna mata inda xata xauna ta hau gadon ta xauna, ya ajiye plate din hannunsa ya dauko wani bandage din da plaster ya gabanta, runtse ido tayi tun kan ya taba kan, yana kallon fuskarta har ya gama sa mata bandage din, murya can kasa yace “Bude idon” a hankali ta bude tana kallonsa, ya mata murmushi ta sunkuyar da kanta, abincin ya bude ya dau spoon ya mika mata, ta karba tana kallon cokalin, yace “Eat” ganin yanda take kallon cokalin yasa ya karba ya debi abincin ya kai mata baki, ta bude bakin a hankali ya xuba mata, kallon yanda take tauna abincin yake, aka bude kofar ward din Abbansa ya shigo da wata nurse, ajiye spoon din yayi da sauri, Abba ya karaso yana kallonta yace “Maa sha Allah, Alhmdllh ashe ta farka baka sanar min ba, to ina ‘yan uwan nata ita” rasa abun cewa El-ameen yayi, Abba dai sai kallonta yake ganin she looks familiar, lokaci daya ya tuna inda ya taba ganinta ya kalli El-ameen da sauri yace “Wannan ba mahaukaciyar nan bace da ka kawo min nan ranan, me ya hada ta da Ahmad?” El-ameen da xuciyarsa ke bugawa ya mike don ya ma rasa abun cewa, tsawa Abba yayi masa yace “Are you daft?” Da kyar yace “Abba ta samu lafiya ma, dama iyayenta, Abba gida….” Strictly Abba yace “Kana son ganin the odza side of me ko Ahmad?” Sunkuyar da kai yayi, Abba yace “Maxa fitar min da ita daga nan ka maida ta gun iyayenta, mutumin banxa kawai” juyawa Abba yayi ya bar wajen ya isa kusa da Junaid yyi gwaje gwajensa, ya jima yana kallonsa kafin ya kalli nurse din yace “We might need to diagnose his brain, ya dau lokaci bai farfado ba” daga haka ya juya ya fita nurse din ta bi bayansa, tun da El-ameen ya ji abinda Abba yace gabansa ya fadi ba kadan ba, ya karasa gadon da sauri yana kallon Junaid, kansa ya dafa na kusan minti uku sannan ya cire hannunsa a hankali cikin sanyin murya yace “Come back pls frnd, for the sake of ur patient….” Juyawa yayi yana kallonta ya ga hawaye idonta ya karasa da sauri yace “Me ya faru?” Ta fashe da kuka, shiru yayi yana kallonta don ya lura ba ko wani magana ma take ganewa ba, kamo hannunta yayi a hankali yace “Kiyi hakuri kin ji, xan kai ki gidan ku” ita dai kallonsa kawai take, tunanin inda xai kai ta yake, sanin in har Abba ya dawo ya kuma ganinta ransa xai baci, gashi bai son barin Junaid, murda kofar dakin aka yi, ya juya da sauri Mumy ta shigo tare da Humainah da fatima, jikinsa yayi sanyi ya sunkuyar da kai. Humainah ce tayi karfin halin karasawa kusa da gadon da Junaid yake ta durkusa ta fashe da kuka, fatima ta juya ta fice daga ward din, Mumy bata iya ta karaso cikin dakin ba, Humainah ta kamo hannunsa cikin rawar murya tace “plss ka tashi ya A.jay…” El-ameen ya karasa kusa da ita yace “He will be fine ki daina kuka kin ji” juyawa Mumy tayi ita ma ta fita daga dakin, Humainah ta kallesa hawaye na bin kuncinta tace “Toh me yasa har yanxu bai tashi ba” dagota yayi yace “Xai tashi nan da few minutes in’sha Allah” kallon jasmine dake ta kallonta tayi kawai ta juya ta fice daga ward din tana kuka sosai, juyawa yayi yana kallon Jasmine ya karasa kusa da ita, hawaye ne ya gangaro idonta a hankali tace “Yayanta ne?” Kallon mamaki yake mata don in tayi wani maganar kamar ba ita ba, gyada mata kai yayi yace “Ehh!” Daga haka ya xauna ya ci gaba da bata abincin, kadan ta ci ta dauke kai xai yi magana aka bude kofa mikewa yayi da sauri, gabansa ya fadi ganin Abba ne ya dawo, yace “Abba ynxu xan fita da ita wllh” wani kallo Abba yayi masa sannan ya nufi gadon da Junaid yake, wani ruwan ya sa masa ya juya yana kallon El-ameen yace “tana gama karban sauran treatment dinta gobe ka fitar min da ita a asibiti, don’t let me repeat my self tomorrow” kai ya gyada da sauri yace “Yess sir” juyawa Abba yayi ya fice, El-ameen ya sauke ajiyar xuciya ya xauna yayi tagumi, da dukkan alamu tayi loosing memory ko ba duka ba, kuma xai dauki months kafin ta dawo dai dai shima sai tana shan drugs ana kuma yi mata abubuwan da ya dace, in kuma Allah yasa tayi toxali da wani nata kila ya dawo gaba daya, a hankali ya daga kai yana kallonta ya ga ta jingina jikin gado idonta lumshe, mikewa yayi da sauri ya kwantar da ita ta bude ido ya sakar mata murmushi yace “Sleep jewel!” A hankali tace “Sleep” ya gyada mata kai daga haka ta lumshe idonta. Har sha biyun dare yana dakin, hankalinsa ya tashi sosai ganin Junaid bai farfado ba har lokacin, wata nurse ce ta xo tace Abba na kiransa ya mike ya fita jiki ba kwari, yana fita jasmine ta farka ta mike xaune da sauri tana kalle kalle a hankali tace “Ummina” ta kusa minti goma xauna ta ga Junaid na motsi, ido ta kafa masa, can ta sauko a hankali ta iso kusa da gadon ta duka tana kallonsa, a hankali ya bude idonsa ya shiga kalle kallen dakin idonsa ya sauka kanta, ta d’an koma baya tace “Sleep” kallonta kawai yake, ta d’an yi murmushi ta buda masa manyan idonta ta kuma cewa “Sleep”

Previous page 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 13 14 15 16 17 18 19 20 21 22 23 24 25 26 27 28 29 30 31 32 33 34 35 36 37 38 39 40 41 42 43 44 45 46 47 48 49 50 51 52 53 54 55 56 57 58 59 60 61 62 63 64 65 66 67 68 69 70 71 72 73 74 75 76Next page

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button